Skip to content
Part 48 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Abuja

Kwance yake a ɗaki, baisan kalar tunanin da yake yi ba, ya ji wayar shi na ƙara, yaso ya share ta, sai dai layin shi ne wanda daga ‘yan gidansu, su Muneeb sai tsirarun mutane suke da shi, yasan kiran zai iya zama mai muhimmanci, hannu ya miƙa da niyyar ɗauka kiran ya taimaka mishi ta hanyar yankewa, fasa ɗaukar wayar yayi, ya mayar da idanuwan shi ya lumshe, buɗe su yayi a hankali yana jin wani tsaki da yake neman ƙwace mishi da ya ƙi bari ya fito saboda baisan waye ba. Wayar ya ɗauko ya duba, da sauri ya ɗaga kiran yana kara wayar a kunnen shi ganin Naadir ne. 

“Naadir wallahi bansan kai bane ba…”

Daga ɗayan ɓangaren Naadir ya amsa shi da faɗin, 

“Bakomai Yaya. Ka ga ban zo ba ko?”

Kai kawai Rafiq ya ɗan ɗaga kamar Naadir ɗin yana ganin shi. 

“Ban samu dama bane, game ɗin dana bari da bikinka da rashin lafiyar ka masu muhimmanci ne, idan na sake barin wani zan samu matsala, ba don game ɗin ya fi ka muhimmanci ko wani abu ba Yaya…za ka min faɗa na sani.” 

Naadir yai duka maganar cikin harshen turanci yana sa Rafiq ɗin yin murmushin da bai yi niyya ba tare da faɗin, 

“Hausa Naadir, Hausa…”

“Yayaa mana, mantawa nake.”

Cewar Naadir da ko gida ya zo turancin shi yakan fi Hausar shi yawa, don ma Rafiq ɗin na hana kowa yi mishi turanci don baya so yaren Hausa ya ƙwace mishi kamar yadda Kanuri ya ɓace mishi, gara ma su Aroob suna ji, mayarwar ne ba komai ba. Amma shi da ƙarancin shekaru ya tsame shi daga cikinsu ya kaishi ƙasar waje saboda baya son yanda Dady yake takura su gaba ɗaya ya faru akan Naadir ɗin. Zuciyar yaron ba kala ɗaya bace da tasu gaba ɗaya, yana da wani irin rauni na ban mamaki. 

“Yaya Fawzan ya faɗa min magana. Bansan ko gaskiya ba ne.” 

Numfashi Rafiq ya sauke yana lumshe idanuwan shi 

“Gaskiya ne…”

Kawai ya iya faɗi, wasu za su ce ya kamata a ɓoye ma Naadir ɗin saboda yayi yarinta, sai dai ba haka suke ba, basa ɓoye ma junan su wani abu da ya shafi junan su, komin munin shi kuwa. 

“Meye ya canza yanzun?”

Naadir ya tambaya, shiru Rafiq ɗin yayi na wasu ‘yan daƙiƙu, kafin ya amsa da dukkan gaskiyar shi. 

“Ban sani ba Naadir, wallahi ban sani ba, idan na ce maka ga asalin abinda nake ji ƙarya nake…” 

Wannan karon Naadir ne yayi shirun. 

“Ni bai canza komai a wajena ba, ba Nuri da Daddy suka haifeka ba, na gane wannan, amma ban gane me yasa wani abu zai canza ba.” 

Buɗe idanuwa Rafiq yayi. 

“Jinina ba iri ɗaya bane da naku…”

Wata irin dariya Naadir yayi yana saurin faɗin, 

“Kayi haƙuri, ba abin dariya ba ne, nima bansan meyasa dariyar ta zo ba. Yaya wanne irin jini ne a jikinka? Ƙarshen ciwon da ka ji wanne kala ne ya fito?” 

Dan ɗaga kafaɗa Rafiq yayi yana amsawa da, 

“Ja ne…”

“Nima ciwon da na ji na ƙarshe kalar daya fito kenan, me kake son ce min? In ka tambayi su Yaya Fawzan ma ina da tabbacin nasu Ja ne, haka su Nuri ɗin…” 

Numfashi Rafiq ya sauke. 

“Kasan ba abinda nake nufi kenan ba Naadir, na baka shekaru sun fi Ashirin…” 

“Na sani, shi yasa nake so ka fahimce ni, tunda ka girmeni da yawa har haka, ƙila yaren Hausa ya fara min wahalar fahimta ne ban sani ba, jini duka jini ne, kalar su iri ɗaya ne, akwai rabe rabe dai in ka zo bama wani marar lafiya haka, banda wannan bansan me yasa za’a dinga ɗaukar shi da muhimmanci mai yawa ba. 

Don Nuri bata haifeka ba baya nufin wani abu a wajen mu Yaya, ba zai canza shekarun da mukai da kai ba, bana so ya canza wanda za mu yi da kai, ba sai na rantse ba ko zuciyar Nuri aka ciro aka duba wajenka ya fi na kowa yawa. Bata haifeka ba, kusancin da wadda duk ta ce ta haifeka zata nuna ma Nuri fiye da kai shine ka kwanta a cikin ta, Wallahi Yaya bana tunanin akwai macen da zata soka kamar Nuri. 

Baka da ‘yan uwan da za su soka kamar mu, ban damu in Maman da ta haifeka ta sake haifa maka wasu ƙannen ba, ban sansu ba, bana so in sansu, su Yaya za su iya matsawa daga zuciyarka su basu ɗan waje, ni kam bazan yi ba, babu wanda zan matsa wa ya samu waje…” 

Wani irin nauyi Rafiq yake ji zuciyar shi na yi tunda Naadir ɗin ya fara magana, baisan hawaye sun cika mishi idanu ba sai da ya ji zubowarsu ta gefen fuskar shi, don kwance yake kan bayan shi 

“Naadir…”

Ya kira da wani yanayi a muryar shi

“Ka bari in gama Yaya, ina faɗa maka ne kafin in zo, karka raba space ɗina da kowa, ba roƙon ka nake ba, ina faɗa maka ne saboda ba zai yiwu ba.” 

“Naadir…”

Rafiq ya sake kiran shi yana so ya tabbatar mishi da ba zai taɓa raba ƙaunar da yake mishi da kowa ba, don ya ji yadda muryar Naadir ɗin ke rawa yana kuma jin yadda numfashin shi yake fita, yasan kuka yake. Amma ya ƙi sauraren shi. 

“Nuri ma ina roƙonka Yaya, na san ka ji haushin ta da ta ɓoye maka gaskiya, don Allah karkai mata fushi da yawa, tana son ka Yaya, karka bari ta rasa yaron ta saboda ta yi kuskure… Kar kuma kuskuren ta yasa mu rasa Yayan mu…” 

Kai kawai Rafiq yake ɗagawa. 

“Ka yi magana Yaya… Ka bani wani tabbaci mana, wallahi zan taho yau.” 

‘Yar dariya Rafiq yayi yana jin wasu hawayen cike da idanuwan shi. 

“Ina ta so in yi magana Naadir, baka ba ni damar ba. Kar inga ƙafafuwan ka a gida…” 

“Ya zan san ba za ka raba min space da kowa ba?” 

Naadir ya buƙata yana sa Rafiq ɗin faɗin, 

“Saboda ko Aroob bata san na fi sonka akan ta ba…” 

Wannan karon dariya Naadir ya yi. 

“Mubar shi tsakanin mu then, Aroob zata danne ni da pillow idan ta sani.” 

Dariya sukayi su biyun.

“Babu wanda zai taɓa zuwa kusa da wajenka Naadir Mustafa Shettima…” 

Rafiq zai rantse yana jin yadda Naadir ɗin yake jinjina mishi kai. 

“Na gode Yaya, ka kula da kanka, ka ƙyale kowa wannan karon ka kula da kanka. Har matar ka…” 

Numfashi Rafiq ya sauke. 

“Tana gidan su…”

“Me ta je yi? Ziyara? Ko rainon Baby.”

“Naadir…”

Rafiq ya kira.

“Yaya na sani mana. Aroob ta faɗa min, muna siyan kayan Baby ne ma, zata kashe ni saboda na faɗa maka, but duka kunsan bana iya riƙe abu ya daɗe…” 

Numfashi Rafiq ya sake saukewa, baisan ya za ayi wani ya kusanci ƙaunar da yake musu ba har ma ya taɓa ta, su ɗin daban ne a wajen shi. 

“Ba ko ɗaya. Tana gidan su kamar yadda na ce maka.” 

Shiru Naadir ya ɗan yi na wani lokaci kafin ya ce, 

“Ok. Ka ɗauki duk lokacin da kake buƙata Yaya, in ka gama ka je ku dawo, ina da bikin su Yaya Fawzan, ba taro nake so ba ka sani, bazan kuma dinga barin makaranta ina zuwa biki ba, ina kuma da wahalar sabawa da mutane, na karɓeta a matsayin matarka, bana jin zan sake karɓar wata, ko meye fix it Yaya, fix it ka dawo da ita.” 

Cike da mamaki Rafiq ya sauke wayar daga kunnen shi ya kalleta tukunna ya mayar yana faɗin, 

“Naadir ni kake faɗa wa abinda zan yi haka?”

“Um um fa, ina faɗa maka abinda ka koya mana ne kawai. Faɗa ma juna gaskiya ba tare da duba banbancin shekaru ba…ko ka sake koya wani abin ne da bana nan?” 

“Ƙaniyarka Naadir.”

Rafiq ya faɗi yana sa Naadir ɗin yin dariya. 

“Sai anjima Yaya. Zan sake kira.”

Kai Rafiq ya jinjina yana kasa mayarwa da Naadir ɗin amsar ƙaunar da yake mishi da ya jaddada, baya jin ƙarfi a jikin shi, yana sauke wayar daga kunne shi ya gyara kwanciyar shi. Zuciyar shi yake jin ta matse cikin ƙirjin shi, maganganun Naadir sun taɓa shi sosai da sosai. 

*****

Ƙwanƙwasa ɗakin ya ji an yi, a hankali ya amsa da, 

“Yes…”

Aroob ce ta turo ɗakin da sallama, hannun ta riƙe da mug, sai kuma plate a ɗayan. 

“Yaya ka fito…”

Ta faɗi tana ajiye plate ɗin da mug ɗin kan table ɗin da ke tsakiyar falon nashi, tunda taku biyu ne sai labule da ya raba tsakanin wajen baccin shi da kuma falon, amma bata ganin shi tunda labulen na da kauri sosai, ta dai san yana kwance. 

“Meye ne?”

Rafiq ya buƙata, don baya jin ƙarfi a jikin shi, baya son yin komai, tunda ya tashi yau dama baya jin fitowa daga ɓangaren baccin shi, ko sallah don Fawzan ya zo ne yasa shi zuwa masallaci. Balle wayar shi da Naadir ta ƙara kashe mishi jiki sosai. 

“Ka fito tukunna…”

Aroob ta sake faɗi don tana da tabbacin idan ta ce mishi abinci ne ba zai fito ba. Tana jin motsin shi alamar yana saukowa daga kan gadon. 

“Nikam kin takura ni sosai…”

Yake faɗi lokacin da ya ɗaga labulen yana fitowa, jikin shi sanye da yadi ruwan toka, idanuwan shi sun mata wani irin zuru-zuru. 

“Baka fito ka karya ba ne, shi ne na kawo maka.” 

Ba zai iya doguwar magana ba, takowa yayi ya samu waje ya zauna, tea ne ta haɗa mishi sai dankali soyayye da wainar ƙwai, ta saka mishi cokali mai ‘yan yatsu a cikin plate ɗin. Zaune ta yi a ɗakin, ruwan tea ɗin ya fara sha, tana jira ya ce ta cika mishi Milo ɗin zaƙi yayi yawa duk da babu sugar, amma bai yi magana ba, wainar ƙwan kawai ya cinye, dankalin ko ɗaya bai saka a bakin shi ba, ya kuma shanye ruwan shayin, mug ɗin ya ajiye yana kallon Aroob da faɗin, 

“Sai kuma me?”

Daga ganin yanayin shi ta san baya son yin magana, tana fitowa taga matar nan da wani mutumi da alamu suka nuna mijinta ne a zaune ta ji gaba ɗaya ranta ya mata wani iri, har Nuri ta ja gefe ta ce ace su tafi su ƙyale Rafiq ɗin ba yau ba. Amma Nuri ta ce Daddy ne ya kira su yana so a yi komai a gama, ko za su ci gaba da rayuwar su babu zullumi. Shi yasa ta shiga kitchen ta haɗo ma Rafiq ɗin Tea, ko me zai ji gara ya ji shi da ɗan karfi a jikin shi ko ya ne. 

“Ka zo in ji Daddy…”

Ta faɗi, yanayin muryarta na sa shi kiran, 

“Aroob…”

Kamar zata yi kuka ta ce, 

“Ka yi haƙuri Yaya, wannan ce ta dawo…”

Zuciyar shi da tai tsalle bai hana shi tambayar, 

“Wannan?”

Cike da son tabbaci ba. 

“Bansan me ya kamata in kirata ba…bana so in kirata komai ne ma. Suna babban falon ƙasa da su Nuri…” 

Ta ƙarasa maganar tana ɗauke mug da plate ɗin da ta shigo dashi tare da ficewa daga ɗakin da sauri, bayanta Rafiq ya bi, duk da bibbiyu take haɗa ƙafafuwan benen wajen sauka bai hana shi kamota ba, hannunta ya riƙo yana juyo da ita. 

“Ki nutsu Aroob, kina jina?”

Hawayen da ke idanuwanta ne ta ji sun zubo, kafin ta ɗaga mishi kai a hankali. Saida ya tabbatar ta nutsu ɗin tukunna ya saki hannunta, tare suka sauka falon, hannuwan shi da ya ji suna zufar da baisan dalili ba yasa cikin aljihun rigar shi, ɗaya bayan ɗaya yake kallon su daga inda yake tsaye, yana tsayar da idanuwan shi cikin na Yafindo, yana jin wani irin kusanci na ban mamaki tare da hakan. Tunda ya sakko take kallon shi, yanayin shi da takun tafiyar shi na sa zuciyarta wata irin dokawa. 

Zata rantse tana kallon Nawfal a cikin duk wani taku da Rafiq ɗin zai yi, hasken fata kawai Nawfal zai nuna ma Rafiq ɗin, sai sumar shi da take cikakkiya, Rafiq ɗin kuma ya aske tashi ƙasa sosai sosai. Kallon shi take tana gode ma ƙaddarar da ta haɗa fuskarta da tashi, tana jin burinta na Rahmar Ubangiji na ƙara ɗaguwa, don damar neman yafiyar laifin da ta yi ma Rafiq da ta samu ba abu ba ne ƙarami. Bakomai take nema da shi ba sai ya yafe mata. Ta tabbatar ma da Alhaji Mustafa damar hakan daya kirata a waya yana jaddada mata yadda za su yi yawo a manyan kotunan duniya don na ƙasar Najeriya ya musu kaɗan ita da shi idan tana tunanin zata karɓi Rafiq ne. Yanzun take jin murmushi ya ƙwace mata, tana ƙara ganin girman Rafiq ɗin, da ta san yana cikin shekarun shi na talatin da kusan uku, amma shi ne Alhaji Mustafa yake magana akai kamar yaro ƙarami ɗan shekara biyu. 

Rafiq bai motsa daga inda yake ba, duk da yasan ya kamata ya gaishe su, ko ya yi musu sallama, amma bakin shi yake ji kamar an ɗaure, don bai yi magana ba sai da ya ga Aroob ta fito daga kitchen ɗin ta zo ta gabanshi tana shirin wucewa. 

“Ina zaki je?’

Ya buƙata yana mayar da hankalin shi kanta, ɗan ɗaga mishi kafaɗa kawai ta yi, intai magana kukan da bata san dalilin shi ba zata yi. 

“Ina su Zafira?”

Ya sake tambayarta, Daddy ne ya saka musu baki da faɗin, 

“Magana za mu yi ne Rafiq, ni na ce su bar mana falon.” 

Daddy Rafiq yake kallo, bai ce komai ba ya kama hannun Aroob suna juyawa, da sauri Daddy ya ce, 

“Ina za ka je Rafiq?”

Tsaye yayi har lokacin hannun Aroob na cikin nashi. 

“Ba abinda zan saurara in basa wajen. Bana jin daɗin jikina Daddy ko me za ku faɗa min ban da ƙarfin maimaita musu, in ba zamu ji tare ba a barshi…” 

Rafiq ya ƙarasa maganar a gajiye, da gaske yake babu abinda zai saurara idan basa nan, koma menene dole za su ji, to meye amfanin hana su zama yanzun. Yanayin da ke fuskar Rafiq ɗin yasa Daddy jinjina mishi kai kawai, hannun Aroob ya saki don ta je ta kira su Fawzan ɗin. Babu musu kuwa ta wuce, sai lokacin Rafiq ya kalli Nuri, yanayin da ke shimfiɗe kan fuskarta na ƙarya wani ɓangare na zuciyar shi. Baisan ya fara tafiya ba sai da ya ganshi tsaye a gabanta. 

“Nuri…”

Ya kira kamar babu kowa a ɗakin daga ita sai shi, kallon shi kawai ta yi idanuwanta na cikowa da hawaye, hakan na sa shi zama a ƙasa kusa da ƙafafuwanta, maganganun Naadir na dawo mishi, da gaske ne yana jin kusancin da bai taɓa ji tsakanin shi da wani ɗan Adam ba akan Yafindo, amma wajen Nuri daban yake a rayuwar shi, ita ɗin haske ce a komai nashi, yanzun ne ya ƙara sanin hakan. Kanshi ya ɗora jikin ƙafafuwan Nuri yana faɗin, 

“Bansan wane kalar wasa rayuwa take yi da mu ba…zai zo ƙarshe in dai kina tare da ni, kiyi haƙuri in a kwana biyun nan na sa kin ji kamar wani abu ya taɓa kusancin mu, banda mahaifiyar da ta wuce ki Nuri, banda hasken da Musulunci ya bani a rayuwata banda wani hasken bayan ki…” 

Wani irin numfashi da Nuri bata san tana riƙe da shi ba ta sauke, kalaman Rafiq ɗin na ɗaga wani dutse da ya danne mata ƙirji da tunanin rasa shi tun shekaranjiya, hannunta ta ɗora saman kanshi tana kallon Yafindo, kamar tana son faɗa mata Rafiq ɗin ɗanta ne, ko ita bata isa ta canza hakan ba. Hannu Yafindo ta sa tana goge hawayen da suka zubo mata, ita ma ɗin bata ce ɗanta ba ne ba, haihuwar shi kawai ta yi, in zatai ma kanta adalci ta san ɗansu ne, kowa ya ji labarin rayuwar su hukuncin da zai yanke kenan. Bata kuma zo da niyyar raba su da yaron su ba, ko da ta zo da hakan Rafiq ya nuna mata ba abu ba ne da zai yiwu yanzun nan. 

Sai dai zata yi ƙarya idan ta ce babu wani abu can ƙasan zuciyarta da yake kishi da kusancin da take gani tsakanin shi da Nuri, zata yi ƙarya idan ta ce bata so ace hannunta ne saman kan ɗan nata, a jikinta yake yanzun, ƙaunar da yake nuna ma Nuri ita yake nuna wa, sai dai ta rasa wannan damar daga ranar da ta miƙa ma su Nuri shi a Airport, yanzun can ƙasan zuciyarta take fatan bayan ya yafe mata ya bata dama ko ya take a rayuwar shi, ko yaya ne in yai hakan zata gode. Su Fawzan ma da suka fito gefen Nuri suka zauna, kusa da Rafiq ɗin suna zagaye shi kamar suna son hana koma meye zai taɓa shi ƙarasa wa inda yake. 

Yafindo suka zuba ma idanuwa, ita suke jira ta yi musu bayani. Wata irin dokawa zuciyarta take cikin ƙirjinta, shekaru masu yawa tana tunanin ranar nan, hannun Alhaji Osama ta ji cikin nata yana haɗa ‘yan yatsun su guri ɗaya ya dumtse, alamar yana tare da ita, tunda take a rayuwarta, ta karanta litattafai da yawa, ta kalli fina-finai da yawan gaske, sai dai akan Alhaji Osama da matar shi Hajiya Maimunatu tasan cewa mutanen da takan gani a fina finan ƙasar waje za su iya fitowa a duniyar mu ta Hausawa har su yi rayuwa, ta yi shekaru tare da su tana jinta kamar tana yawo a wata duniya da ko yaushe zata iya watso ta asalin duniyar ta da take cike da hargitsi. 

A gurin da ta yi bautar ƙasa ta haɗu da Alhaji Osama ya zo ziyara wajen abokin shi, inda ya manne mata tun tana nesa da shi har ta fara kula shi, nan ta ji bai jima da dawowa ƙasar Najeriya ba, rayuwar shi da ta iyalan shi gaba ɗaya ya yi ta ne a ƙasar Jamus, yanayin ƙaunar da ya nuna mata ne yasa ta faɗa mishi dukkan sirrinta da ko iyayenta a wannan lokacin basu sani ba, sati biyu ya ɗauka ba tare da ya waiwaye ta ba, ta shiga firgici mai yawa don har sai da ta yi tunanin ba zai iya aurenta da tabon da son zuciya yasa taima rayuwarta ba, sai dai ƙaunar da ya nuna mata ba zata iya mishi ƙarya ba, gara gaskiyarta ta kore shi da su gina rayuwarsu kan ƙaryar da tasan komin daɗewa zata iya fitowa ta ruguza musu ginin da suka yi. 

Sai bayan da aka ɗaura auren ta da shi ne ya sakata a gaba har gida ta faɗa ma iyayenta abinda ta faɗa mishi, ta kuma roƙi yafiyar su akan rusa yardarsu da ta yi, haka ranar da ya aure ta ya haɗa su da matar shi Hajiya Maimunatu ya kuma faɗa mata abinda ya kamata ta sani akan Fadila ɗin, ya tabbatar mata da ya faɗa mata ne don yasan ba ko yaushe sirri yake binnuwa ba, gara ta ji daga bakin su da ta tsinta a waje. Zaɓi ya rage nata na yin duk abinda ta ga ya kamata da sirrin Fadila ɗin, bayan ya mata nasiha mai shiga jiki akan matsayin rufa ma ɗan uwanka Musulmi asiri, illolin gori da nuna yatsa akan ƙaddarar waninka. 

Sosai Fadila ta tsammaci gori daga wajen Maimunatu, ko da wasa maganar bata taɓa haɗa su ba, asalima ba shiga harkarta take ba, sukan gaisa, in wani abu ya faru na farin ciki ko jaje a dangin ɗayan su sukan je ma juna, yaran su kuma babu wani abu wai shi ‘yan Ubanci a zamantakewar su, Hajiya Maimunatu ta tabbatar da hakan bata faru ba. Mace ce mai karamci a nata yanayin. Har abada kuma Fadila ba zata manta abinda sukai mata ba, tana da tabbacin cikin mata dubu kamarta ba za su wuce su biyar da suka taki irin sa’ar rayuwar data taka ba. 

Sosai ta dumtse hannun mijinta da yake cikin nata, tana wani irin sauke numfashi da wasu hawaye masu zafi da suka zubo mata. Rayuwar na ɗaukarta ta watsata shekarun da zata yi komai don komawa ta sake zaɓukanta da ta yi, da zata iya komawa baya don ta gyara komai da ta yi, amma babu wannan damar, zata iya komawa baya ne ta ga duk wani kuskure da ta yi a rayuwarta ba tare da zata iya yin komai don ta gyara shi ba. 

***** 

Ba zata ce ga yadda akai suka fara gaisawa da Nawfal ba, amma da alaƙar su ta yi nisa ya faɗa mata larabci yai mata ta amsa mishi shi ne abinda ya fara burgeta da shi. A sirrance suka ƙulla alaƙa a shekararta ta biyu da zuwa ƙasar. Don ko Zainab bata bari ta sani ba, tunda Nawfal ɗin ya gargaɗeta da cewar zai iya rasa aikin shi idan aka sani, tun ranar farko da ya fara riƙe hannunta ta ji kuskuren hakan har cikin ƙasusuwan ta, sai dai takan ga yadda Turawa, Larabawa da kuma Indiyawa sukan yi soyayyarsu a fina-finai, ana riƙe juna, kamar hakan ba komai bane ba a al’adar su. 

Ta manta da cewa akwai hijabin addini da ya raba abinda ya halasta a al’ada da kuma abinda ya halasta a addini da fina-finai ba za su taɓa nuna mata ba. Bayan wannan akwai wata irin makauniyar soyayyar Nawfal da ta rufe mata idanuwa, namiji ne shi da mafarkinta yake hura ma burinta wutar samu, zata yi koma meye don ganin ta mallake shi, don tare da shi dukka sauran mafarkanta za su zama gaskiya. Tun suna haɗuwa da Nawfal a wajen cin abinci da yake da sirri, har suka fara haɗuwa a wajen da suka fi zuwa domin cin abinci, yana kuma ɗaukarta a mota su tafi yawo, watan su shida da fara soyayya yana faɗa mata duk abinda kunnuwanta suke son ji ta biye ma zuciyarta da shaiɗan tana miƙa mishi mutuncin ta. 

Zata yi ƙarya idan ta ce ta yi wani kuka ko da na sani a ranar da hakan ta faru, don a lokacin babu wata murya da ta yi saura mai gaya mata gaskiya a cikin ƙwaƙwalwar ta, babu komai banda soyayyar Nawfal da yake nuna mata mai wuyar mantawa, sosai suka ci gaba da haɗuwa suna kuma more soyayyar su yadda ya kamata, bata taɓa tunanin wani abu ba, don ta gama bashi kanta, da dukkan zuciyarta, bata bashi dalilin da zai barta ba a nata haukan, duk abinda yake so tana ƙoƙarin ganin ta yi mishi. 

Tana shekararta ta uku, lokacin kuma Zainab ta riga da ta gama, dama ita takan yi mata faɗa da ta kula kamar wani abu na faruwa tsakaninta da Nawfal ɗin, don haka ta ci gaba da cin karenta babu babbaka, har sati takan yi a wajen Nawfal, idan ka gansu za ka rantse mata da miji ne. Hankali bai fara shiga jikinta ba sai lokacin da ta fara rashin lafiyar da ta saka ta zuwa asibiti babu shiri, likitan daya dubata kuma ya tabbatar mata da tana da shigar ciki wata ɗaya. Ranar ji take kamar a mafarki take rayuwa, bata san lokacin da ta ƙarasa gidan Nawfal ba. 

Tana zuwa ta ƙwanƙwasa ya fito, murmushin shin nan yai mata mai kashe mata jiki yana kama hannunta ya jata cikin gidan tare da mayar da ƙofar ya rufe, sai dai yanayin yadda ya ga jikinta a sanyaye ne yasa shi kallonta da tambayar, 

“Lafiyar ki? Ko jikin ne?”

Da wani irin nisantaccen yanayi ta ce, 

“Ina da ciki Nawfal.”

Kallon ta yake kamar wani kai ya ƙara tsirowa ta gefen kan da yake manne a jikin ta. Kafin dariya ta ƙwace mishi. 

“Ba abin dariya ba ne Nawfal, magana za mu yi, aure ya kamata muyi, bansan ya zan yi da cikin da ke jikina ba, don Allah ka ce wani abu…” 

Take faɗa duk wani tashin hankali na duniya yana haɗe mata waje ɗaya. Dariyar ya ci gaba dayi da ya ji ta kira aure, ita da shi ta kira ma aure, yana da tabbacin bata taɓa sanin ƙabilanci da ƙabilar shi ta larabawa take da ita ba, ko bai san sama da ƙasa zata haɗe kafin ahalin shi su yarda su karɓi Fadila a matsayin surikarsu ba, shi ma ba zai iya aurenta ba, da gaske tun ranar da ya fara ɗora idanuwan shi akanta, yanayinta da komai nata yasa shi sha’awarta, sai dai bata taɓa wuce hakan a wajen shi bs, akanta ya fara karya dokar shi ta bin ɗaliban makarantar, duk da suna kawo kansu wajen shi sosai, yana kiyayewa ne saboda za’a iya korar shi daga aiki, yana kuma son aikin don yana bashi dalilin ƙin komawa ƙasar shi ta Kuwait, duk kuwa yadda dangin shi suke son ya koma gida. 

Fadila ma ya kasa haƙura da kwaɗayin shi ne akanta, shi ne dalilin da yasa ya biye mata. Kallon ta yake yanzun ɗin ma ganin da gaske take yi akan maganar auren ta da shi. 

“Bazan iya auren ki ba Fadila, tunanin me kike yi?” 

Ko ina na jikin ta kyarma yake, musamman zuciyarta da take dokawa har cikin kunnuwanta, kallon shi take da bayyanannen tsoro a kan fuskarta. Gam ya ja ƙofayyana kulle zuciyarshi da duk wani emotions da zai iya samun fitowa, fuskarshi babu komai akai ya sauke idanuwan shi cikin nata. 

“Ni da ke bamu taɓa wuce wani abu da ya girmi nishaɗi ba, bansan me na yi da ya saki tunanin ko zuciyata kin isa ki hango ba balle ki samu waje a ciki, ba kuma zan baki haƙuri ba don babu kuskuren da na yi, ban yi komai da babu amincewar ki ba…”

Hannu Fadila ta sa tana dafe cikin ta da yake yamutsawa da sabon tashin hankali. Innalillahi wa inna ilaihir raji’un take son furtawa amma kamar an kulle mata baki, sai lokacin nauyin komai yake danne ta, abin da yake tsaye a wuyanta take son haɗiyewa amma ta kasa, sau uku tana buɗe bakinta da niyyar magana amma babu abinda yake fitowa. Numfashi take ja ta bakinta tana fitar da shi a wahalce. 

“Nawfal???”

Ta kira sunan shi cike da shakku da alamun tambayoyi da dama, muryarta can ƙasa, idanuwanta na kasa yarda shi ne tsaye a gabanta. Zuciyarta na ƙin aminta da abinda kunnuwanta suka ji. Nawfal bazai mata haka ba, ba zuciyarshi kawai ta iya hangowa ba, tana da yaƙinin har cikinta ta shiga ta samu wajen zama. 

Ganin yanayin da ke fuskarta yasa Nawfal kama hannunta yana janta, mamaki ya hanata yin komai banda binshi, har ya kai ta bakin ƙofa ya hankaɗa ta, ba don bangon da ta dafa ba, babu abinda zai hanata mummunar faɗuwa. 

“Ko meye kike tunanin yake tsakanin mu ya zama tarihi a yau!!!” 

Bakin shi kawai take ganin yana motsi, kunnuwanta sun daina jin sauran kalaman, tashin hankalin da take ciki da maganganun shi na farko sun sa komai tsaya mata cik. Girman kuskuren yarda da shi na danne ta. Tana ji ya kama hannun ta yana fita da ita daga cikin gidan, don kamar bom ɗin da zai tarwatse da shi haka yake kallonta a yanzun. 

“Ki zubar da cikin da yake jikin ki…ki yi ko me za ki yi Fadila. Amman karki sake nuna min fuskar ki.” 

Ya ƙarasa maganar yana komawa haɗe da rufe ƙofar shi. Ba zata ce ga yadda ta koma gida ba, ba zata ce kwana nawa tayi a cikin ɗakinta a kwance ba, babu wanka, babu abinci, sallah ma ba zata ce ga abinda take karantawa a cikin ta ba. Har sai da wata baturiya Alicia da suke mutunci da ita ta zo don ta duba ko tana lafiya ta ga halin da take ciki, ita ta haɗa mata ruwan wanka ta kai ta banɗaki, ta kuma gyara mata ɗakin, ta bata abinci ta ci, bata san lokacin data gaya ma Alicia abinda ya faru ba, komai da komai kuwa. Tare sukai kuka ranar, da taimakon Alicia ta koma asibiti, da taimakon Alicia da ta saka ta shiga wasu ajujuwa don taimaka ma yanayin da take ciki, da mata masu ciki da yawa irinta da suke tunanin zubar wa, program ne da zai nuna maka illar abinda kake son yi da yadda za ka iya zama cikin da na sani har abada. 

Nan suka ƙara taimaka mata wajen ganin girman kuskuren da ta yi, da kuma wanda zata yi idan ta zubar da cikin, haka ta ci gaba da rayuwa kamar ba ita ba, kullum zata tashi taje ajujuwan da take da shi ta dawo ta kwanta gari ya waye, har watanni suka ci gaba da ja, watan haihuwarta shi ne yai dai-dai da watan da zata gama karatunta, daga ranar da Nawfal ya kama hannunta ya fitar da ita daga gidan shi bata sake jin ɗuriyar shi ba, a bakin wasu ɗalibai take jin ya ajiye aikin da yake a makarantar, zuwa lokacin bata damu ba, saboda bata jin zuciyarta zata sake tarwatsewa fiye da yadda take a tarwatse. 

Lafiya ƙalau tayi jarabawar ta ta ƙarshe, ta kammala komai, ta kuma haifi santalelen yaron ta da kammanin da yake mata da Nawfal na sa ta jin kamar ta jefar da shi a asibitin ta gudu, idan komai na mata kamar mafarki, kamar ba rayuwarta ba, hakan ya ƙare lokacin da ta haɗa akwatinta da nufin komawa gida. Lokacin tasan ba zata taɓa shiga gida da yaron da ta saka ma suna da Rafiq ba, zuciyarta zata daina aiki kafin ta shigar musu gida da ɗan gaba da Fatiha, abu ne da ba zai taɓa yiwuwa ba. A airport ta rubuta wasiƙa ta riƙe, duk da har suka sauka ƙasar Najeriya bata san me zata yi ba, lokacin kwanakin Rafiq Arba’in da biyu a duniya. 

Bayan sun sauka ne ta hango su Nuri da Daddy a tsaye, bata san me yasa ta je ta basu Rafiq da sunan ajiya ba. Yanzun ta san ƙaddarar su ce gaba ɗayan su ta zo musu a haka, tare da Alhaji Osama kuma tasan banbancin makahon so da sahihin so, makahon so taima Nawfal ya barta da tabon da zai ci gaba da binta har ƙarshen rayuwarta.

<< Alkalamin Kaddara 47Alkalamin Kaddara 49 >>

1 thought on “Alkalamin Kaddara 48”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.