Skip to content
Part 5 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Ɗaki ta koma ta kwanta, jinta take kamar marar lafiya. Ta jima a haka kafin ta yanke hukuncin tashi. Sun tara wanki kwanakin nan biyu. Don haka ta duba ta ga suna da sabulu, tattara wankin ta yi ta fito dashi waje ta ajiye.

Ta ɗauki jarkoki, ruwa ta ɗibo ta ciccika ko’ina, ta fara wankin kenan Ummi ta fito daga ɗaki. Gaishe da ita Tasneem ɗin ta yi tana ɗorawa da,

“In kina da wanki ki fito da shi Ummi, amma sabulun ba zai isa ba, in kina da wani sai ki ƙaro.”

Ɗaki Ummi ta koma ta haɗo wa Tasneem kayan wankin nata har da zanin gado, sai sabulu guda ɗaya da omo biyu. Sannan ta wuce banɗaki. Tasneem bata yi mamaki ba, ganin Ummi na alwala dai-dai wannan lokacin. Sallah kan lokaci bai dami Ummi ba sam. Tana kuma gamawa ta sa Hijab ta fice daga gidan ba tare da ta ce wa Tasneem ɗin ga inda ta nufa ba.

Wanki ta sha har wajen 12 tana fama. Don wasu kayan ma basu samu wajen shanya ba sai gidan su Tariq ta shiga ta shanya sauran a can ta dawo. Tunanin abinda zata dafa musu ta soma yi. Don bata son su Azrah su dawo makaranta babu abinda za su ci. Kazar da Alhaji Madu yakawo ce suka ci da safe dama.

Kitchen ɗin ta shiga, gawayinsu ko ruwan zafi bazai dafa ba. Ga yanayin sanyi ya fara shigowa. Har tausayin Sabeena ta ji da zata yi mata wanka da safe, saboda ruwan ya yi sanyi da yawa. Ledar taliyarsu ta duba ita ma ta yi ƙasa sosai. Gaba ɗaya ranta ya jagule, bata san yadda zata yi ba.

Addu’a take Allah ya dawo musu da Abba lafiya. Don in bai dawo ba za su sha wahala. Dabara ta faɗo mata da ta shiga ɗakin Ummi ta duba ko zata samo wani abin. Sai dai tana zuwa ta ga Ummi ta kulle ɗakinta har da kwaɗo a jiki. Tsaye ta yi a bakin ƙofar jikinta a sanyaye.

Sabeena ta fito tana kallonta.

“Yunwa ko Beena?”

Kai ta ɗaga mata a hankali kamar bata son amsawa, hannu Tasneem ta miƙa mata, ta ƙaraso tana kamawa. Riƙe yarinyar ta yi a jikinta tana jin idanuwanta sun ciko da hawaye. Bata san iya lokacin da suka ɗauka a tsaye ba, sai da ta ji ƙafafuwanta sun gaji tukunna ta zame tana zama ta zaunar da Sabeena a jikinta.

Suna nan zaune ta ji sallamar Ummi, da sauri ta amsa tana bin ledar da Ummin ta shigo da ita da kallo.

“Sannu da zuwa.”

Kallon su Ummi ta yi.

“Lafiya kuka yi zaune a nan kamar marayu.”

Ta tambaya. Cikin sanyin murya Tasneem ta ce,

“Beena ce take jin yunwa. Babu komai da zamu dafa a gidan.”

“To me kuke so in muku? Ubanku nawa ya bar min da zai tafi? Kuna gani dai rana ɗaya komai ya ƙare. Munafuncin banza ai na san ya bar miki kuɗi kika ɓoye saboda baƙin hali irin na ubanki.”

“Wallahi kuɗin ne na siyo mana fulawa muka kai aka murza taliya da su Ummi, sun ƙare kuma.”

Taɓe baki Ummi ta yi.

“Ni dai banda wasu kuɗi a hannuna gaskiya.”

Wani abu ne mai ɗaci ya yi wa Tasneem tsaye a wuyanta. Tana rasa hali irin na Ummi, ita bata damu da yunwarsu ba, ko me za su ci, ko ma ina suke samun abincin da za su cigaba. Halin Ummi zuwa yanzun ta san shi tsaf, ta kuma san ba zata bata kuɗi ta siyi abinci ba.

“Ki ara mana don Allah Ummi mu siyi wani abin. In Abba ya dawo sai in karɓar miki.”

Harara Ummi ta sake watsa mata. A hasale ta ce,

“Da yake binshi kika yi ya ce miki ya samo kuɗi ko? Satin shi nawa yau? Inda adalci ko aike ai sai ya yi mana. Tunda ya san ba wata tsiya ya bari ba da yasa ƙafa ya fita. Banda su kina jina ko?”

Hawayen da Tasneem take tarbewa ne suka zubo. Ta sa hannu ta share su kafin Ummi ta gani kuma ya zama wani abin.

“Zan fita in Alhaji Madu ya zo…”

Juyowa Ummi ta yi.

“Da gaske?”

Kai Tasneem ta ɗaga mata. Washe baki Ummi ta yi, fuskarta shimfiɗe da fara’a kamar ba lokacin ta gama faɗa ba. Jikin haɓar zaninta ta laluba, ta zaro kuɗi da suke a cukurkuɗe, ta warware, za su kai dubu shida. Dubu ɗaya ta zaro ciki tana mayar da kuɗinta ta miƙa wa Tasneem ɗin.

“Bawai kyauta na baki ba. Za ki biyani abuna wallahi, don ubanku ba zai tsallake ya bar min wahalarku ba. Ba zan iya ba.”

Miƙewa Tasneem ta yi da sauri tana karɓar kuɗin kafin Ummi ta canza zuciyarta ta hana su. Hannun Sabeena ta kama suka fice, shago suka je ta auni shinkafar hausa ta siyi  mai da farin magi da yaji. Sauran canjin ta biya ta siyi gawayi. A hanyar dawowa ta tsinci ledojin da zata kunna gawayi da su.

Bata sami Ummi a gidan ba, ta sake ficewa, sai baƙar leda da ta ajiye musu kan ƙofar ɗakin su, hakan na nuna wa Tasneem cewar ko meye a ciki nasu ne. Ɗauka ta yi ta buɗe, miya ce da nama a ciki. Kitchen ta kai ta ajiye ta haɗa gawayin ta fito.

Alwala tayi ta ɗora ruwa don gawayin ya soma kamawa tukunna ta sa Sabeena ta yi alwala itama. Sallah suka yi ta Azahar tukunna ta zauna zaman tsince shinkafa don ta san akwai tsakuwoyi sosai a ciki. Anan su Hamna suka sameta da sallamar su.

“Yaya wanki kika yi? Ba za ki jira mu zo mu yi tare ba?”

Hamna ta faɗi. Murmushi Tasneem ta yi.

“Ku da kuka je makaranta, ga Islamiyya kuma. Bana so wankin ya taru sosai shi yasa. Wani Karan sai mu yi tare ai.”

“Sannunki da aiki.”

Azrah ta ce tana ajiye ledar da litattafanta suke ciki ta shiga ɗaki, tsaye Hamna ta yi saida Azrah ta sake kaya ta fito tukunna ta shiga itama ta sake kaya. Tana fitowa jikinta da hijab wajen robobin ruwan su ta yi.

“Hamna me za ki yi? Jarkar nan ta miki girma. Ki bari ki ci abinci kuma sai ki ɗibo ruwan.”

Cewar Tasneem.

“Zan iya ɗauka fa wallahi, rannan ma na ɗauko ko Azrah?”

Girgiza kai Tasneem ta yi.

“Ai ban sani ba. Karki sake ɗaukar jarkar nan ko bana nan. Ki ɗauki bokiti in ma ruwan za ki ɗibo. Kuma ki dawo ki zauna sai kin ci abinci tukunna. Akwai na amfani yanzun ai.”

Turo baki gaba Hamna ta yi tana dawowa ta sami waje ta zauna. Tayata tsintar shinkafar suke. Kafin Azrah ta ce z

“Ina kika samo shinkafa?”

“Ummi ta ban kuɗi.”

“Alƙawarin me kika yi mata?”

Hamna ta tambaya tana tsareta da ido. Tiren da shinkafar ke ciki Tasneem ta ɗauka ba tare da ta amsa ba. Don bata son yanayin da ke muryar Hamna sam, bata son yadda a hankali halayyar Ummi ke nisanta ƙaunarsu da ita. Ko da ta zuba shinkafa kitchen ɗin ta zauna don kar ta fita su sake tsareta da tambaya.

Bakin kitchen ɗin suka dawo suka sa tabarma suka zauna. Sabeena ta sa ta ɗauko mata rediyonta a ɗaki, don ta ma manta da ita duk ranar. Kunna musu ta yi ansa waƙoƙin Hausa a Fm. Suna ji har ta gama abinci suka ci, sai da Hamna ta cika ko’ina na gidan da ruwa tukunna suka yi sallar La’asar suka shirya suka tafi Islamiyya.

*****

Washegari haka su Hamna suka tafi makaranta ba tare da ko sisi ba, har a ranta Tasneem take jin tafiyar da za su ci yau. Fatanta kar a ƙwalla rana mai zafi wajen dawowarsu. Don sanyin ba wai ya zauna bane sosai. Radio suke ji ita da Sabeena har bacci ya ɗauke su.

Ji ta yi ana sallama sama-sama kamar cikin mafarki. Buɗe idanuwa ta yi jin an sake sallamar kuma kamar muryar Abba. Da sauri ta miƙe tana fitowa. Abba ne ya dawo, bata damu da girman da ta yi ba, bata ma san lokacin da ta ruga da gudu tana faɗawa jikin Abban ba. Wata irin kewarshi na danne ta duk da gashi tsaye a gabanta.

Dariya Abba ya yi yana ɗago ta. Idanuwanta cike taf da hawayen da suka samu zubowa ta ce,

“Abba… Sannu da zuwa.”

“Menene na kukan kuma Tasneem? Ba gani na dawo ba.”

Abba ya faɗi yana jin zuciyarshi ta yi nauyi, ya san ba zai wuce matsalar Ummi ba, yana can amma hankalinshi gaba ɗaya yana wajen tunanin halin da suke ciki. Bawai sun gama aikin bane ba. Ya dawo ne da Kjarfinshi don ya bar musu abinda za su ci sai ya koma.

“Zo ki taya ni ɗibo kaya a waje.”

Da gudu ta koma ɗaki ta ɗauko Hijab ta rufama Abba baya. Buhun shinkafa ne ƙarami, taliya da macaroni sai mai a galan har biyu ɗaya manja ɗaya na ƙuli sai ledoji da Tasneem ba zata ce ko meye a ciki ba. Amma bakinta ya ƙi rufuwa.

Suna gama shigo da kayan duka Abba yace ma Tasneem.

“Ina kuka siyo gawayi? Ko rabin buhun a siyo a ajiye an huta da siyan kaɗan-kaɗan.”

“Nan baya wajen Salihu ya fi kyau Abba.”

Juyawa ya yi da niyyar fita Tasneem ta ce,

“Daka huta Abba, yanzun ka dawo fa.”

“A’a Tasneem kin san halin Ummin ku, kafin ta dawo gara duk abinda ake buƙata in siyo.”

Addu’a ta yi mishi, ya amsa yana ficewa, zama Tasneem ta yi ta tisa kayan a gaba tana kallo ranta na mata daɗi, rabon da ta ga buhun shinkafa sai dai ko in ta je shago awo, amma yau gashi a gidansu. A matsayin nasu.

“Dukkan sharri Allah ya nisanta mana kai da shi Abba.”

Ta tsinci kanta da faɗi. Abba bai jima ba ya dawo, sai lokacin ta lura da har ƙiba ya yi, ya sake, wadata daban ce, ta kuma fi alaƙanta kibar da yayi da rashin ganin Ummi. Ruwa ta kai mishi din ya watsa ko zai ji daɗi, ta tattara kayayyakin da ya kawo ta kai wasu kitchen ta samar musu wajen zama. Wasu kuma ta kai ɗakin su.

Har da kalanzir Abba ya siyo musu ɗan ƙaramin galan, dn haka yau gawayin ya yi mata saurin kamawa. Ruwa ta ɗora da niyyar macaroni za su ci ranar ta manta rabon da su ci ma. Abba na fitowa ya nufi ɗakin su ya ganshi a kulle. Tabarma Tasneem ta shimfiɗa mishi suka zauna. A nutse ya kalle ta.

“Ya kuke? Me yasa baki je makaranta ba yau?”

“Babu wanda zai zauna da Beena. Muna lafiya Abba. Ya aiki? Ka daɗe sosai.”

Jinjina kai ya yi.

“Na sani, wallahi kuna raina, ba ma mu gama aikin ba na dawo don in ga halin da kuke ciki.”

“Allah ya taimaka ya ƙara wadata Abba.”

“Amin thumma amin. Allah ya yi miki albarka ke da sauran ‘yan uwanki.”

Murmushi ta yi.

“Amin Ya Rabb…”

“Ayo cefane ko?”

Girgiza kai ta yi, don mansu na shafawa ya ƙare, ga sanyi fata da mai ma ya ta ƙare.

“A’a Abba muna da sauran yaji, gara a yi wani abu da kuɗin dai. Muna buƙatar man shafawa ma…”

Jin tayi shiru yasa Abba faɗin

“Da me kuma kuke buƙata?”

Girgiza kai Tasneem ta yi, ba don babu abinda suke buƙatar ba. Sai don bata son ɗora wa Abba wani nauyin, ta san siyayyar da ya yi na da yawa kuma ba ƙaramin kuɗi bane ba. Hannu yasa a aljihunshi ya zaro duka kuɗin da suka rage mishi ya ƙirga. Dubu sha uku ne.

Dubu biyar ya ware daga ciki ya miƙa wa Tasneem da faɗin,

“Duk wani abu da ba ku da shi ki siya muku.”

Ware idanuwa Tasneem ta yi,

“Abba sun yi yawa…. Kaima ka siyi wani abin. Kuma ka ce za ku koma wajen aiki, kuɗin motar komawa fa?”

Murmushi Abba ya yi.

“Da Alhaji zamu koma jibi in sha Allah. Shi ma ya zo ya ga nashi iyalan. Ke dai ki ɗauka ki je ki sissiyo muku.”

Cike da nauyin zuciya ta sa hannu ta ɗauki kuɗin. Hira suke da Abba har ta ƙarasa girkin, ta zuba mishi.

“Abba in Allah ya hore, in za’a koma hutun gaba tunda na ƙarshen zango ne a saka Sabeena ma.”

“Kamar kin shiga zuciyata. In sha Allah in na dawo za mu je a siyo uniform har ku ma a sake muku naku.”

Jinjina kai ta yi tana miƙewa. Ita da Sabeena suka fita. Man shafawa ta siyo musu, sai takalma silifas don ba ƙaramin jin jiki nasu suka yi ba. Musamman na Hamna da ɗinki ya fi biyar a jikinshi. Hancin takalmin ma daban ne aka samu aka saka. Biscuit ta siya ma Sabeena duk da ta san ƙarshe ma ba ci zata yi ba. Don kayan zaƙi bai dami yarinyar ba sam.

Ko dubu ɗaya bata kashe ba. Suka dawo. Ɗaki ta shiga ta ɓoye sauran kuɗin. Ta nunama ma Abba abinda ta siyo musu. Albarka ya samata tukunna ya fice daga gidan. Tsakar gida suka yi kwanciyarsu ita da Sabeena, tana biyema shirmen hirarta har bacci ya sake ɗaukar su.

*****

Abincin su suka ƙara ci suka yi sallar isha’i, da yake akwai wuta, suna zaune tsakar gida suna hira abinsu.

“Wallahi Abba kamar karka koma, mun yi kewarka sosai.”

Cewar Azrah. Murmushi Abba ya yi.

“Nima na yi kewarku. Amma aiki ne dole in koma.”

“Yaushe zaka dawo in ka tafi?”

Hamna da sai lokacin ta tsoma baki cikin hirar sa suke ta tambaya.

“Bansani ba, amma in sha Allah da na samu lokaci kamar yanzun zan dawo in ganku.”

Jinjina kai Hamna ta yi tana mayar da hankalinta kan Tasneem.

“So nake fa ki tuna min wasu abubuwa a Umdatul Ahkam, za mu yi test gobe in Allah ya kai mu.”

“Wai Hamna, ɗauko mu ga, Allah yasa ban manta ba nima. Yaushe rabo, in na kasa Azrah sai ta tuna miki.”

Miƙewa Hamna ta yi ta shiga ɗaki, Abba kallon su yake cike da ƙaunarsu, da yadda rashin wadatarshi bai hanasu maida hankali a karatunsu ba. Hamna na fitowa Ummi na shigowa da Sallama. Abba ne ya amsa mata. Su dukkan su fuskokinsu babu alamar murna da ganinta.

“Ka tuna kana da iyali kenan ka waiwaye mu.”

Ummi ta faɗi tana kallon Abba cike da takaici. Kai kawai ya girgiza bai ce mata komai ba. Ƙarasawa ta yi cikin gidan ta ajiye jakarta da wani buhu da ya ji duniya. Ɗakinta ta buɗe ta ɗaga labulen tana jefa Hijabinta ciki. Kanta tsaye kitchen ta nufa ta leƙa.

Kayan abinci ta gani da gawayin da ya siyo duk a ajiye. In ranta ya yi dubu ya ɓaci, saboda bata ga dalilin da zai sa Abba ya kwaso kayan nan ba, kamata ya yi ya bata kuɗin abinda ta ga dama ta siyo.

“Kuɗin da ka samo ɗin ne ka kaso haka? Saboda baƙin cikin karka bani in ƙaru? Shi yasa ka je ka kashe su haka ko?”

Kallonta Abba ya yi, muryarshi ɗauke da wani yanayi ya ce,

“Kayan abincin da na siyo ne laifi Bara’atu?”

“Ni ban ce laifi bane ba, amma ai baka san me muke buƙata ba, ko da za ka siyo sai ka bari in dawo in lissafa tukunna, satinka nawa baka gidan, meka bar min? Kasan yadda muke muna ci a gidan nan?”

Hawaye ne cike da idanuwan Tasneem, ji take kamar ƙasa ta tsage ta shige ciki ko kuma wani abin ya toshe mata kunnuwanta daga jin abubuwan da Ummi take faɗa wa Abba. Azrah ma ji take dama Ummin bata dawo ba, suna cikin nishaɗin su ta zo ta dagula musu komai.

“Ni dai na riga na siyo. Yanzun magana ta ƙare ai.”

Tafa hannuwa Ummi ta yi da faɗin,

“Lallai, ai wallahi yanzun aka fara magana, don kuɗi za ka bani, akwai abubuwan da nake buƙata da yawa.”

Hannu Abba yasa a aljihunshi ya zaro sauran kuɗin da suka rage, duka ya yi niyyar bata, amman kafin  ya miƙa mata ta warce kuɗin tana dunƙule su a hannunta. Buɗe baki Abba ya yi da niyyar magana, ganin yadda su Azrah suke kallon Ummin yasa shi fasawa. Miƙewa ya yi da niyyar barin gidan, muryar Hamna na rawa ta ce,

“Abba ina za ka je? Ita da ta shigo yanzun ya kamata ta fita…”

Cikin tashin hankali Abba ya juyo, sai dai kafin ya yi wani abu, da zafin nama Ummi ta ƙarasa inda Hamna take tana ɗauketa da wani irin mari da yasa Tasneem tashi tana son shiga tsakanin Ummi da Hamna ɗin, sai dai ta makara don kuwa Ummi ta janyo Hamna ta fara kaimata duka duk inda ta samu.

“Don Ubanki ni za ki faɗa wa magana? Hamna har nawa kike? Baƙin hali irin na Ubanki, Wallahi gara in karyaki in huta.”

Abba ne ya tako har inda suke, ranshi ya gama ɓaci matuƙa, ƙarfi yasa ya ɓanɓare Hamna daga hannun Ummi, yana janye Ummin gefe da faɗin,

“Meye matsalarki? Don Allah meye matsalarki a rayuwa Bara’atu?”

Kallon shi Ummi take yi hawayen takaici ta ji sun zubo mata. Har yana da bakin da zai tambayeta matsalarta bayan yasa yaranta sun tsaneta, ko hira basa zama su yi da ita, har Hamna na faɗa mata ita ya kamata ta fice ta bar musu gida ba shi ba.

“Kana da bakin da za ka yi min wannan tambayar? Muftahu kana da bakin da za ka tambayeni matsalata? Bayan ka sa yarana sun tsane ni.”

Zafin zuciya irin na Hamna, ko alamar hawaye babu a idanuwanta, duk jibgar da ta sha wajen Ummi, zuciyarta a dake, muryarta can ƙasa ta ce,

“Abba don Allah ba gidan da za mu koma? Inda babu Ummi?”

“Hamna…”

Abba ya faɗi zuciyarshi na rawa, don ba a muryar Hamna ba kawai, har a fuskarta yana ganin tsanar da ta yi wa Ummi ɗin da yasa jikinshi yin sanyi. Ita kanta Ummi kallon Hamna take, wasu sabbin hawayen na zubo mata.

Daman duk cikin yaran Hamna tun tana ƙarama babu wata wadatacciyar shaƙuwa a tsakanin su. Tana wata shida ta yaye kanta da kanta.

Ko da ta fara girma ba yawan magana gareta ba, a rana banda gaisuwar safe, shi ma in ta tashi kafin su tafi makaranta Hamna bata sake mata magana, sai dai ko in ita ta yi mata magana ko ta aiketa. Bata taɓa sanin akwai ranar da Hamna zata faɗi maganar da ta yi mata zafi ba sai yau.

Juyawa Ummi ta yi tana shigewa ɗaki, Abba kuwa Hamna yake kallo. Muryarta can ƙasa ta sake cewa,

“Don Allah Abba ka mayar damu wani wajen inda ba zamu dinga ganinta ba.”

Daga zuciyarta take jin kalaman data furta ɗin, da gaske take jin bata son ganin Ummi, ko kaɗan bata son ganinta. Bata son abinda take ma Abban su, tana lura, ta san ba don Tasneem ba da yunwa ta kashe su. Ummi bata damu da ko sun ci ko basu ci ba. Halayen Ummi ba su yi mata ba, don suna cikin halayen da malamin su ya faɗa musu ba masu kyau bane a Islamiyya.

Da kuka Azrah ta shige ɗaki, ita kanta Tasneem ɗin tana jin hawaye na shirin zubo mata. Ba don abinda Ummi ta yi ba, sai yadda take fita daga zuciyoyinsu. Sai yadda Ummi ta zubda hawaye akan Hamna, shi ya fi komai ɗaga wa Tasneem hankali, Sabeena kuwa baccinta take hankali kwance, bata ma san me ake ba.

Ɗakin Ummi Tasneem ta nufa, tana barin Abba da ya kama hannun Hamna ya zaunar da ita kan tabarma, ya ma rasa me zai yi, don haka ya ɗauki kofin da ke ajiye gefe ya je ya ɗibo ruwa ya bata, hannunta na kyarma ta karɓi ruwan ta sha, sai lokacin ta ji zuciyarta ta karye. Wani irin kuka ta fashe da shi mai cin rai tana faɗawa jikin Abba.

“Me yasa Ummi ba zata zama kamar kowacce uwa ba Abba? Me yasa take maka haka? Me yasa bata son mu?”

Hamna take tambayarshi tana ci gaba da wani irin kuka da ya ɗaga mishi hankali. Riƙeta ya yi sai da kukanta ya fara tsagaitawa tukunna a nutse ya ce,

“Wa ya ce Ummin ku bata son ku?”
Shiru Hamna ta yi tana sauke ajiyar zuciya a hankali. Jin bata ce komai ba yasa Abba ci gaba da faɗin,

“Akwai halayen Ummin ku da basu da kyau, na sani amma haka wasu mutanen suke, Ummin ku na ɗaya daga cikin su, tana son ku ko da bata nuna muku ba. Ba za ki tuna ba, da kina ƙarama, lokacin kina ƙyanda haka Ummin ku take kwana bata yi bacci ba tana kula da ke, banda kuɗi lokacin, ita ta yi ta yawo sai da ta samo kuɗin da ta kai ki asibiti, Ummin ku na da halayya kala-kala, amma tana son ku sosai.”

Hamna na kwance jikin Abba tana kuma jin duk abinda yake faɗa.

“Ummi ta kwana bata yi bacci ba da banda lafiya?”

Kai Abba ya ɗaga mata. Ɗan jim ta yi kafin ta ce,

“Allah na fushi da ni ko Abba? Malamin mu ya ce kar ka yi ma iyayenka rashin kunya, musamman mahaifiya.”

Kai Abba ya sake ɗaga mata don jikinshi ya gama mutuwa. Hawaye suka sake zubo ma Hamna.

“Ka bata haƙuri Abba.”

“Zan bata haƙuri, amma kema sai kin min alƙawari ba za ki sake faɗin in kaiku wani waje da Ummin ku bata nan ba, sai kin min alƙawarin ba za ki ƙara tsanarta haka ba.”

Muryarta na rawa ta ce,

“Abba bana so Allah ya ƙara yin fushi da ni, bana so in zama munafuka, Ummi zata sake wani abin da zan tsaneta irin na yau, banaso in maka alƙawari in karya.”

Numfashi mai nauyi Abba ya sauke, Allah ya basu yara masu hankali, amma Bara’atu ta ƙi nutsuwa ta fahimci hakan, tana gab da rasa yaran bai kuma san yadda zai yi ya gyara hakan ba.
“Ki min alƙawari za ki yi ƙoƙari to, in ta yi wani abin za ki yafe mata.”

Sai da ta ɗauki ‘yan mintina tukunna ta ɗaga mishi kai, ɗagota Abba ya yi amma ta riƙe shi gam, don haka ya gyara zaman shi. Wani irin kaɗaici take ji, ji take gidan ya ƙara mata girma, kamar in ta saki Abba zata ɓace ne cikin gidan. Runtse idanuwanta ta yi gam tana ruƙunƙume Abba.

Tasneem kuwa tana shiga ɗakin Ummi ta sameta zaune kan gado tana matse hawaye. Goge nata hawayen ta yi, Ummi ta ɗago cikin kuka ta ce,

“Kema zuwa kika yi ki faɗa min maganar ko?”

Da sauri Tasneem ta girgiza mata kai.

“Don Allah Ummi ki yafe mata, ki daina kukan nan, hawayen da kike zubdawa akanta zai iya zamar mata fitina…”

“Ita bata san hakan ba ai Tasneem, ku duka kun tsaneni ko? Saboda ina faɗa muku gaskiya, kun fi son Abban ku akaina, don kawai halin rashin da muke ciki na damuna.”

Shiru Tasneem ta yi don ta san in ta ce ta fahimtar da Ummi za su ɗauki duka daren ne suna abu ɗaya ba tare da Ummi ta fahimceta ba. Ba ta zo bane don ta fahimtar da Ummi kan yadda halayenta ke nisanta ƙaunarta da zuciyoyinsu. Ta zo ne ta tabbatar da ta yafe wa Hamna.

“Ki yi haƙuri, don Allah ki yafe mata, da mu ma in mun ɓata miki rai.”

“Hmmm”

Ummi ta faɗa cike da takaici da ƙunar zuciya, tana jin ta ƙara tsanar Abba, duk shi ya ja mata wannan matsalar.

“Ummi mana, don Allah.”

Tasneem ta faɗi tana jin wasu hawayen za su zubo mata.

“Shikenan ya wuce.”
Ɗan murmushi ta yi tana ma Ummin sai da safe da bata amsa mata ba. Fitowa ta yi ta samu su Abba a zaune, hannu ta kai ta kama na Hamna da hakan yasa ta buɗe idanuwanta, miƙewa ta yi daga jikin Abba, Tasneem na taimaka mata ta tashi. Kwanciya ta yi a jikin Tasneem ɗin yadda suke a tsaye.

Kallon Abba Tasneem ta yi, da idanuwanta take nuna mishi kar ya damu zata gyara komai. Kai ya jinjina mata da murmushin ƙarfin hali.
“Sai da safe Abba.”

Bai iya magana ba sai kai da ya jinjina mata, da Hamna riƙe a jikinta suka shiga ɗaki, Abba ya jima zaune a wajen yana gode wa Allah da ya bashi Tasneem, ko ba komai ta zame musu kamar Hasken Lantarki a rayuwarsu. Tare da ita komai yana zuwa musu da sauƙi.

*****

A kwance ya samu Ummi sa’adda ya shiga ɗakin, ko da ta ji shigowarshi bata nuna alamu ba, don ko motsi bata yi ba.

“In har baki gyara halayenki ba, kina gab da rasa yaranki Bara’atu, don Allah ki gyara, ba don ni ba, don kanki, don kar yaranki su tsaneki.”

Abba ya faɗi muryarshi can ƙasa. Tunda ya shigo tana jinshi, bata ƙaunar ganin shi ne , ko me yake faruwa shi ya janyo musu, rashin wadatar shi ce ta a ja musu komai. Tunda ya buɗe bakinshi ya fara magana take jin kamar yana zuba mata wuta. Miƙewa ta yi zaune ta juyo tana kallon shi.

So take ta tuna dalilin da yasa ta aure shi tun daga farko ta rasa, don ba zaɓinta bane ba, zaɓin mahaifinta ne ya kuma rasu ya barta da wahala da zaɓinshi, ba tun yanzun ta san ita ba sa’ar auren shi bace ba, tana da kyau, kamata ya yi a ce tana gidan hutu, inda zata ci me kyau ta sha me kyau, ba zama da Muftahu da bai ƙareta da komai ba banda rabon yaran da yasa suka tsaneta yanzun.

“Aurenka bai ƙare ni da komai ba, babu ranar da zan tashi ban yi da na sanin aurenka ba Muftahu.”

Runtse idanuwanshi Abba ya yi, wani abu na tokare mishi zuciya. Lokutta da dama in ta guma mishi wani baƙin cikin yakan zauna ya yi tunani, yana neman dalilin da zai sa ya ci gaba da zama da ita, tun farko-farkon auren su ya fara gane halayyarta, tun lokacin son da yake mata ya soma dishewa har ya neme shi ya rasa.

Sai dai ba zai iya rabuwa da ita ba saboda amanarta da mahaifinta ya danƙa mishi, sai kuma don yaranta, amma in dai don jin daɗi ne na zaman aure, ba zai tuna ranar da ya samu na rana ɗaya da Bara’atu ba. Yana so ya faɗa mata shi ma ya yi da na sanin aurenta, kyawunta daga wajene kawai. Amman a gajiye yake jinshi, ba zai iya wani sabon tashin hankalin ba.

Don haka ya zagaya ya hau kan gadon can ƙarshe ya kwanta. Cikin takaici Ummi take kallon shi, idanuwanta na cika da hawayen baƙin ciki.

“Don Allah ka sauwaƙe min aurenka in huta, Muftahu ka sake ni ko zan samu farin ciki.”

Ta ƙarasa siraran hawaye na zubo mata, har cikin ƙashinta take jin yadda ta gaji da zama da shi. Maganganun da take ba ƙaramin ɗaga mishi hankali suka yi ba, ko motsi ya kasa don kar hakan ya sake tunzurata su duka shaiɗan ya yi musu busa ya yi abinda zai yi dana sani, zuciyarshi zafi take kamar zata tsaga ƙirjinshi ta fito.

Innalillahi ya shiga jerowa, yana ji ta sauka ƙasa ta kwanta, tun yana jin sautin kukanta har ya daina. Ya daɗe idonshi biyu kafin wani wahaltaccen bacci ya ɗauke shi.

*****

Ranar da Abba ya tafi su dukan su ji suke kamar marayu. Ummi ta fita harkar su, gaisuwar su ma da ƙyar take amsawa, dama ba wuni take gidan ba. In ta fice abinta sai dare za su ganta. Ranar nema ta dawo ana idar da sallar Maghrib. Jinsu suke a takure, Sabeena na rungume jikin Tasneem, Hamna na ɗayan gefen ta kwanta jikin ƙafadarta, haka Azrah ma, da Ummi ta shigo haka suka sake naniƙe mata, kamar za su koma cikin jikinta.

Sun ci abinci, don haka suna yin alwalar sallar isha’i suka shige ɗaki, suna idarwa, Hamna na zaune tana karatun Ƙur’ani aka rafka sallama wai ana son ganin Tasneem. Da hijab a jikinta don haka miƙewa ta yi.

“Fita za ki yi yanzun?”

Azrah ta buƙata da alamar tuhuma a muryarta. Ɗan murmushin ƙarfin hali ta ɗora a fuskarta da faɗin,

“Bana son tashin hankalin Ummi, in na je muka gaisa shikenan.”

Kan katifa Azrah ta hau tana juya bayanta. Da sauri Tasneem ɗin ta fice daga ɗakin kafin Hamna ta idar da karatun ta yi mata wata maganar, Ummi ta gani tsaye bakin ƙofa, haɗa idanuwa suka yi, murmushi Ummi ta yi mata tare da ɗan ɗaga mata kai. Ta manta rabon da ta ga murmushi a fuskar Ummi sai yau.

Sa’adda ta fita Alhaji Madu na cikin mota, glass ya sauke yana washe mata haƙora. Cike da takaici take kallon shi, tare da tausayawa yaranshi da suke tashi da sanin yadda da duk fitarshi yake zubda musu mutuncin su. Ta ɓangaren da yake ta ƙarasa ta yi tsaye a wajen tare da gaishe da shi.

“Tasneem, ki zagaya ki shigo ciki mana.”

Fuskarta a haɗe ta girgiza mishi kai.

“Nan ma ya isa. Ina jinka.”

“Haba Tasneem, ni bari in fito to sai mu gaisa sosai.”

Kafin ta buɗe baki ya fara turo murfin motar har yana shirin buge ta saboda kyarmar jikin da yake. Matsawa ta yi gefe, ya fito yana mayar da murfin ya rufe. Tsayawa ya yi gefenta kamar kafaɗar shi zata gogi tata.

“Tunda mun gaisa ni zan koma ciki, dare ya soma yi.”

Ɓata fuska Alhaji Madu ya yi yana faɗin,

“Me yasa kike haka ne Tasneem? Kamar da ba ‘yar makaranta ba.”

Harara ta watsa mishi, tana jin kamar ta kwaɗa mishi mari, don ba shi da sauran mutunci a idanuwanta. Ganin yana ƙara matsawa yasa Tasneem juyawa, hannunta da ya riƙo yasa tsikar jikinta gaba ɗaya tashi.

“A’uzubillahi…”

Ta faɗi tana ƙwace hannunta tana murzawa da ɗayan kamar hakan zai sa ta daina jin riƙon da ya yi mata ko ta goge shi gaba ɗaya daga jikinta. Idanuwanta cike taf da hawaye take kallonshi, ko’ina na jikinta kyarma yake don kuwa ko a ‘yan uwanta maza babu wanda ya taɓa riƙe mata hannu, ko bisa larura da duk fitar da suke da Tariq bai taɓa riƙe mata hannu ba.

Ko titi za su tsallaka sai dai ta riƙe rigarshi dam, amma yau namijin da bai da kusanci da zama muharraminta ya riƙe mata hannu a banza, yasa an rubuta mata zunubi. Ganin tsanarshi dake cikin idanuwanta yasa shi saka hannu a aljihu yana ɗibo kuɗi ‘yan ɗari bibbiyu da bata san yawansu ba yana miƙo mata tare da faɗin,

“Ga wannan, sai gobe ko? Zan zo da wuri don mu samu mu gaisa sosai. Kar ki ji komai, duk abinda kike buƙata ki faɗa min, ko me kike so zan siyo miki shi, in ma kuɗi ne zan baki.”

Runtsa idanuwanta Tasneem take tana buɗe su da sauri-sauri, zata yi kuka amma ba a gabanshi ba, cike da tsanar kanta tasa hannu tana karɓar kuɗin da ya riƙe dam, sai da ya haɗa da hannunta yana murzawa tukunna ya saki kuɗin yana wani ƙanƙance mata idanuwanshi.

Jikinta na ɓari ta shiga gida, har da gudu-gudu ta haɗa, Ummi na tsakar gida a zaune bakin ƙofa, bata ma kula da cewar Tasneem ɗin a hargitse take ba.

“Har ya tafi? Me ya kawo miki?”

Ta tambaya, kuɗin da ke hannunta ta miƙa wa Ummi gaba ɗaya tana juyawa zata nufi ɗaki.

“Yaushe ya ce zai dawo?”

Juyowa Tasneem ta yi, da idanuwanta da suke cike da hawaye take kallonta, tana son ganin menene babu a tattare da Ummi, me yasa ba zata zama kamar sauran iyaye mata na ƙawayenta ba. Amma ta rasa ganin komai, muryarta can ƙasan maƙoshi ta ce,

“Kin samu abinda kike so Ummi, ko yaushe ya ga dama zai dawo.”

Bata jira amsarta ba ta shige ɗaki, taɓe baki Ummi ta yi, ƙasa-ƙasa take faɗin,

“Shegen baƙin hali, arziƙi na binki kina gudu.”

Ɗaki ta shige itama don ta ƙirga kuɗin da Alhaji Madu ya ba Tasneem. Ita kuwa tana shiga ɗakin ta samu su Azrah suna kwance har sun saki net, hijabinta ta cire ta soma ajiyewa. Kafin ta sake fita da sauri. Ruwa tasa tana wanke tafin hannunta da damtsen ta inda Alhaji Madu ya taɓa, sai dai har a zuciyarta take jin yabar mata shatin hannunshi da bata san ranar gogewarshi ba.

Hawaye ne masu ɗumi suke zubo mata, gajiya ta yi da dirzar hannunta da har ya fara zafi, don haka ta koma ɗaki, cikin net ɗin ta ɗaga ta shiga, tukunna ta ziro hannu ta kashe fitilar da ke kunne, kuka take data ɗauka a hankali ne, don sam bata san shesshekarta na fitowa fili ba, sai da ta ji Hamna ta ce,

“Me yai miki? Ya miki wani abu ko?”

Duk da cikin duhu ne bai hanata girgiza kai ba, sai dai ta kasa magana, sai ma wani kukan da ya sake ƙwace mata, cike da tsoro matsananci, in ta mutu bata san bayanin da zata yi wa Allah ba, Ummi ta ja mata, ba kuma zata tayata ɗaukar zunubin ba, don kowa da nashi kason, tana jin Hamna na matsowa ta riƙeta, juyawa ta yi tana sake fashewa da kuka.

Azrah ma hannun Tasneem ɗin ta lalubo ta dumtse gam cikin nata, su dukkansu ukun kuka suke yi, duk da basu san dalilin nata kukan ba, ita ta kasa yin shiru balle ta lallashe su. A haka har bacci ya ɗauke su.

*****

Duka jarabawar da akai guda biyu Tasneem ta yi, don Ummi ba zama take ba ballantana ta je makaranta. Ko kwana biyun da Abba ya yi da ya tambaya ƙarya ta yi mishi cewar sun fara hutu don bata son Ummi ta ɓata mishi rai. Da yake kwanakin gudu suke, sai taga kamar jiya aka fara, musamman su Azrah, ta ga saurin gamawarsu.

Sai dai hutunsu ya mata daɗi ba kaɗan ba, ko ba komai kafin lokacin Islamiyya ya yi suna ɗebe mata kewa. Akwai kuɗi a hannunta tun wanda Abba ya bari, su na da komai na abinci wannan karan. Har da su Maggi a kayan da Abba ya kawo da yawa. Alhaji Madu bai sake dawowa ba tun ranar da yazo ya bata kuɗi.

Zata yi ƙarya in ta ce da Isha’i ta yi gabanta baya faɗuwa, har sai ta ga dare ya yi sosai bai zo ba, Ummi ta kulle musu gida take iya samu ta yi bacci. Addu’a take Allah kar ya dawo dashi.

“Ya Tasneem dama ki yi mana alale.”

Cewar Azrah.

“Ba sai in akwai wake da yawa ba tukunna.”

Hamna ta faɗi tana daƙuna wa Azrah fuskarta.  Murmushi Tasneem ta yi.

“Akwai wake da yawa ma Abba ya kawo, ina gudun kar ya fara ƙwari ma. Sai dai kamar rana ta yi yanzun.”

Da sauri Azrah ta ce,

“A’a wallahi rana bata yi ba, zan taya ki gyarawa ma, ko Hamna zamu taya ta.”

Ɗaga kai Hamna ta yi, alamar yarda da maganar da Azrah ɗin ta yi.

“Ki ɗauko waken yana kitchen, Hamna ɗauko turmi.”

A tare suka miƙe, Hamna ta ɗauko turmin ta kawo mata ta ajiye, janshi gabanta Tasneem tayi tare da faɗin

“Dubo min Beena bacci take ko me, tun ɗazun ko motsinta ban ji ba.”

Ɗakinsu Hamna ta nufa, ganin Sabeena ta yi har ta sakko daga kan katifa tana ta juye juye kan ledar tsakar ɗakin.

“Beena?”

Ta kira a ɗan tsorace kafin ta shiga cikin ɗakin gaba ɗaya, kamata ta yi tana tsugunnawa ta ɗorata a jikinta, har idanuwanta sun juye sun wani yi fari.

“Beena…”

Hamna ta sake kira tana jijjigata.

“Cikin ki ke ciwo?”

Ta buƙata don ta san ciwon Sabeena baya wuce ciwon ciki, tana yawan yinshi akai-akai. Ganin Sabeena na wani irin nishi-nishi kamar ma bata san me ake a duniyar ba yasa Hamna ƙwala wa Tasneem kira. Jin kiran bana lafiya bane yasa Tasneem barin waken data fara zubawa cikin turmi ta miƙe babu shiri tana nufar ɗaki, Azrah na rufa mata baya.

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”

Tasneem ta faɗi cikin ruɗani tana sa hannu ta ɗauki Sabeena tana duddubata.

“Me ya sameta?”

Ta tambayi Hamna hankalinta a matuƙar tashe. Idanuwan Hamna cike da hawaye ta ce,

“Nima bansani ba… Kawai na ganta ne a kwance.”

Hijab ɗin da ke ƙasa Tasneem ta sa hannu ta ɗauka ba tare data kula da cewar na Hamna bace ba, a birkice ta saka Hijab ɗin tana fitowa tare da saka takalma. Ko ta kan su Azrah da ke mata magana bata bi ba, don hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba, lafiya ƙalau suka karya.

Kanta tsaye kemis ɗin Emma ta nufa, su Azrah suka tsaya suka ɗauki waken suna mayarwa kitchen. Tukunna suka saka hijabai da niyyar binta.

“Mu duba ko da kuɗi, na ga bata ɗauka ba.”

Hamna ta faɗi, inda suka san Tasneem na ajiye kuɗi suka duba, duka kuɗin da suka gani suka kwasa suna bin bayanta don sun san ba zata wuce shagon Emma ba. Can ɗin kuwa suka sameta a tsaye tana maida numfashi.

“Gaskiya ki kaita asibiti zata fi samun kulawar da ta dace.”

Emma ya faɗi cikin hausar shi da ke fita rangaɗam. Tasneem ko amsa bata bashi ba ta karɓi Sabeena da ke hannunshi ta saɓata a kafaɗa. Sai da ta juyo ta kula da su Hamna. Muryar Hamna a sanyaye ta ce

“Mun ɗauko kuɗin da muka gani a jakarki.”

Hannu ta miƙa ta amshi kuɗin a wajen Azrah, da ƙyar ta iya dai-daita muryarta da faɗin,

“Ku koma gida, kun ga asibiti zan kaita. Azrah ko taliya ki dafa muku. Don Allah ku bi a hankali wajen kunna gawayin.”

Idanuwan Hamna cike da hawaye take girgiza wa Tasneem kai.

“Ni dai mu tafi tare.”

Cike da damuwa Tasneem ɗin ta amsata da cewa

“Kin ga asibitin Zana zan kaita, akwai nisa sosai Hamna, ga siyan kati da magani, kar kuɗin ko ba za su isa ba.”

Hannunta Azrah ta kama tana girgiza mata kai. Hawayen da suka zubo ea Hamna ta goge

“Sai kun dawo.”

Ta faɗi, kasa magana Tasneem ta yi kawai ta juya tana nufar titi, ta ɗauka akan halin Ummi ta san menene tashin hankali, sai yau, sai yanzun da take jinta kamar duniyar ta tattaru waje ɗaya. Bata taɓa zuwa asibitin Zana ba, ta dai san can ne take ji ana cewa ana kai yara in basu da lafiya.

Bata san motar da ya kamata ta shiga ba, ga Sabeena da take jin tana wani irin nishi a jikinta, bata san kuka take ba, don ko saukar hawayen bata ji a kuncinta ba, sai da taga hanyar na mata biji-biji, ta runtsa idanuwanta ta buɗe su tukunna ta san hawaye ne cike da idanuwan.

“Tasneem!”

Taji an ƙwalla mata kira, bata damu da ko waye ba, don bata shi take ba, sai da ta ji an sake kiranta a karo na biyu tukunna ta juya, ba tare data yarda da kunnuwanta ba. Don babu yadda za’ai ta dinga jiyo muryar Tariq bayan bai daɗe da tafiya ba. Gyarama Sabeena zama ta yi a kafa&arta, ta sa ɗayan hannunta ta matso hawayen dake cike da idanuwanta.

Tariq ne, murmushi ya yi mata daya sa hawayen ta sake zubowa yana takowa ya ƙaraso inda take.

“Duk sa’adda komai ya yi min duhu sai Allah ya kawoka Ya Tariq.”

Ta ƙarasa muryarta na karyewa da ya ɗauke murmushin da ke fuskar Tariq ɗin, balle da ya ga hawayen da sun ƙi tsayawa daga idanuwanta.

“SubhanAllah. Tasneem me yake faruwa ne.”

Muryarta can ƙasa saboda kukan da take yi ta ce,

“Beena ce, ban san me ya sameta ba, wallahi lafiya ƙalau muka karya da safe.”

Karɓarta Tariq ya yi yana tallabeta a hannunshi.  Damuwa bayyane a fuskarshi yake kallon Sabeena dake hannunshi

“Yanzun ina za ki kaita?”

Fuskarta Tasneem ke gogewa duk da har lokacin hawaye bai bar zubo mata ba

“Asibitin Zana.”

Ware idanuwa Tariq ya yi.

“Ai ya yi nisa Tasneem, kuma rana ta yi, ga su da wulaƙanci, akwai ƙaramin asibiti nan ƙasan mu, muje sai mu fara kaita nan. Kin ga kafin mu gano asibitin Zana daga nan Bachirawa ita kanta ta sha wahala.”

Kai ta ɗaga mishi suna jerawa tare, a zuciyarta tana ma Allah godiya da duk sa’adda komai zai cakuɗe mata sai Tariq ya zo.

“Bansa ran dawowarka yanzun ba.”

Ta faɗi a sanyaye. Sauke numfashi mai nauyi Tariq ya yi don shi ma bai tsammaci zuwan nashi nan kusa ba. Sai dai damuwarta ta danne tashi wannan karan.

“Na tafi ban tsaya mun yi sallama ba ko?”

Ya tambaya maimakon amsa maganar da ta yi mishi, ɗan kallonshi ta yi, tana murmushi a wahalce kafin ta jinjina kai da faɗin,

“Ka dawo yanzun…ya wuce”

Shima murmushin ya yi.

“Na gode…”

Ya ce, basu ƙara magana ba har suka karasa asbitin. Komai yazo ma Tasneem da sauƙi kasancewar Tariq ɗin, waje ta samu ta zauna tana riƙe da Sabeena. Shi ya je ya yanki kati da duk abinda ya kamata kafin su zauna bin layin ganin likita. Da yake wajen mata daban, na maza daban, sai dai murmushi kawai da suke mayar wa juna duk in sun haɗa ido.

Nauyin da ta ji ya danne mata ƙirji ɗazun ya yi sauƙi kamar ganin Tariq ɗin ya ɗauke mata shi. Ko da layi yazo kansu ita ta shiga da Sabeena, ba kamar sauran asibitocin gwamnati ba musamman ƙanana, sosai suka dudduba Sabeena, yana ƙarawa da yima Tasneem ɗin tambayoyi.

Magungunan da ya rubuta ya ce ta je ai ƙoƙari a siyo don akwai allurai da ake buƙatar ayi ma Sabeena ɗin kafin su tafi. Tana fitowa Tariq ya taso

“Ya dai?”

“Magunguna da allurai za’a siyo.”

Takardar ya karɓa da faɗin,

“Ki zauna da ita in fita in siyo. Ya ɗan fi sauƙi a waje.”

Kuɗin dake hannunta ta miƙa mishi, sai dai dubu biyu ya zara a ciki da faɗin

“Barsu haka, akwai kuɗi a hannuna ko ba zai isa ba.”

Kai kawai ta iya ɗaga mishi tana samun waje ta zauna. Ya kai mintina ashirin kafin ya dawo, da kanta ta sake komawa wajen likitan ya dudduba duka magungunan ya nuna mata ƙa’idojin shan kowanne tukunna ya yi ma Sabeena alluran. Suna hanya harta daina nishin da take, ta yi luf a jikin Tariq da alamun bacci take.

“Da ba ka zo ba bansan yadda zan yi ba.”

Tasneem ta faɗi, har a zuciyarta tana jin daɗin zuwan nashi. Murmushi kawai Tariq ya yi mata, har suka kai gida, da gudu su Hamna suka taso.

“Ya jikin nata?”

“Me ya sameta?”

“Ta ji sauƙi?”

“An dubata?”

Su duka suke jero mata tambayoyin a tare, hannuwanta ta ɗaga musu tana murmushi.

“To ‘yan jarida. An dubata, kuma ta ji sauƙi, bacci ma take yi.”

Kai suka jinjina. Sannan suka gaishe da Tariq, Azrah na ɗorawa da

“Yaushe ka zo?”

“Ba daɗewa Azrah. Hamna ya makaranta?”

“Alhamdulillah…”

Ta amsa tana murmushi. Sabeena ya miƙa wa Tasneem da ta kwantar da ita kan tabarmar a hankali tana gyara mata kwanciya tare da ajiye ledar magungunan a gefe. Hannu Tariq yasa a aljihu ya ɗauko kuɗi yana miƙa wa Tasneem.

“Ga kuɗin ki, na hannuna ma sun yi yawa.”

Girgiza kai ta yi.

“Ka riƙe Ya Tariq, hidimar tai yawa ai.”

“Ki karɓa Tasneem.”

Ya faɗi da wani yanayi a muryarshi da yasa ta kasa yi mishi gardama. Karɓar kuɗin ta yi.

“Ni zan koma.”

“Zaka koma? Ba kwana za ka yi ba?”

Hamna ta jefe shi da tambayar da Tasneem ɗin ta bude baki don tai mishi. Su duka suka tsare shi da idanuwa.

“A’a amma zan dawo dana samu lokaci in shaa Allah.”

“Allah ya kaimu. Ka gaishe da Yaya Ashfaq.”

Azrah tai maganar. Hamna kuwa shiru ta yi bata ce komai ba. Tasneem yake kallo, yana jiran tace wani abu, amma ta yi shiru itama.

“Allah ya ƙara sauƙi. Ki kiyaye da bata magungunan yafda likita ya faɗi.”

Shirun dai ta sake yi. Ganin ba zata ce komai ba yasa shi juyawa. Bin bayanshi ta yi har cikin soron gidan kafin ta ce,

“Me yasa?”

Juyowa yayi yana kallonta

“Me yasa zaka tafi? Me yasa komai ba zai koma kamar da ba?”

Ta buƙata tana jin wani sabon kuka na shirin ƙwace mata. Kewarshi na mata nauyi a zuciya. Idanuwanshi taga sun ƙara ƙanƙancewa.

“Zan dawo…”

Girgiza kai take, hawaye na zubo mata.

“Tasneem… Ki kalleni.”

Ɗago kai ta yi tana sauke idanuwanta cikin nashi.

“Zan dawo. Kina jina? Zan dawo, ki kula da kanki, ki kula da su.”

A hankali ta ɗaga mishi kai tana ƙoƙarin mayar da hawayenta, a cikin idanuwanshi akwai gaskiyar da take karanta, akwai tabbacin cika alƙawarin da ya ɗaukar mata, akwai gaya matan da yake ta zama mai ƙarfin gwiwa.

“Ina buƙatar ki da ƙarfin zuciyarki Tasneem, ba ni kaɗai ba, har su Azrah, kina ɗaga mana buri kan cewar komai zai yi sauƙi.”

Maganganun shi sun ƙara dakar mata da zuciya. Hannu tasa ta goge hawayenta.

“Ka kula da kanka, addu’a ta na tare dakai Ya Tariq.”

Murmushi ya yi mata yana juyawa ba tare da ya ce komai ba, ta fahimta, bata buƙatar ya ce komai. Sai da ta daina ganinshi tukunna ta sauke numfashi mai nauyi, juyawa ta yi tana komawa cikin gida da ƙwarin gwiwar ba wa su Sabeena kulawar da suka kasa samu wajen Ummi.

<< Alkalamin Kaddara 4Alkalamin Kaddara 6 >>

1 thought on “Alkalamin Kaddara 5”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×