Su Azrah ba su dafa komai ba, don ta basu ƙarfin gwiwa alalen ta yi musu. Cikin hukuncin Allah kafin Maghrib Sabeena ta warware, fura ta fita da kanta ta siyo mata. Da yake su Azrah ƙin zuwa Islamiyya suka yi. Bata matsa musu ba, don kafin ma ta yi magana sun shirya da kansu. Gidan suka tura suka yi alwalar sallar isha’i suka shige ɗaki abinsu. Ko da Ummi ta dawo ma Tasneem kaɗai ta fita ta yi mata sannu da zuwa. Su dukkansu ƙin fitowa suka yi.
“Me kuka dafa ne Tasneem? Yunwa nake ji wallahi.”
Cike da mamaki Tasneem ɗin take kallonta don bata damu da abincin su ba, ko Abba na nan takan yi wata bata ko kalli me suka dafa ba. Tun Tasneem na jagwalgwala musu har ta fara iyawa.
“Alale muka yi, akwai saura.”
“Zubo min.”
Kitchen Tasneem ta shiga ta sako mata guda ukun da ya rage ta zuba mata mai da yaji ta kawo mata. Tsakar gidan ta zauna tana kallon Ummi cike da mamaki. Tas ta cinye alalen don ya mata daɗi ba kaɗan ba. Kafin ta yi magana Tasneem ta ɗibo mata ruwa ta kawo mata.
Tana ajiye kofin wani almajiri na shigowa. Sai da ta ji zuciyarta ta yi wata irin mummunar faɗuwa. Aikam kiranta ake waje.
“Ka je ka ce bata nan.”
Ta faɗi, Ummi har sauri take ta haɗiye ruwan da ta kurɓa. Amman har yaron ya fice
“Wane irin ace bakya nan? In Alh. Madu ne fa?”
Tasneem bata ce komai ba, ta wuce ta shige ɗaki abinta. Miƙewa Ummi ta yi ta bi bayanta.
“Tasneem ki fito ki wuce ki je na san bai kai da tafiya ba.”
“Ni fa babu inda zan je Ummi.”
Rai a ɓace Ummi take kallonta, don yau haka ta gama walagiginta bin bashin gwanjunan da mutane suka ɗauka, da ƙyar ta samo ɗari biyu, gidan ‘yan uwa kuwa haɗe rai sukai ta yi da suka ganta. Don ta ga kwanakin nan biyu haɗe mata fuska suke. Asabe ma shekaranjiya ta ga shigewarta ɗaki, ‘ya’yan suka ce mata bata nan.
Shi ne Tasneem zata yi mata baƙin ciki, bayan tana da tabbacin in Alh. Madu bai kawo kayan ciye-ciye ba zai ba Tasneem ɗin kuɗi.
“Wallahi baki isa ba….bazan haifi ‘ya mai baƙin ciki ba. Gaisawar da za ku yi?”
Muryar Tasneem na rawa ta ce,
“Ummi rannan fa hannu ya riƙe min. Kuma kinsan ba kyau.”
Tafa hannaye Ummi take yi.
“Oh Allah ni Bara’atu, Tasneem ki ji tsoron Allah, ke dai kawai ki ce ba za ki je ba, kin koyi ƙarya ko? Alh. Madun ne ya riƙe miki hannu?”
“Wallahi ba ƙarya nake ba…”
Ta ƙarasa muryarta na karyewa, idanuwanta cike taf da hawaye. Don ko Ummi zata daketa yau ba zata fita wajen Alh. Madu ba.
“Don Allah Ummi ki ƙyaleta. Beena ma bata da lafiya yau har asibiti aka kai ta.”
Azrah ta faɗi. Da sauri Ummi ta shiga ɗakin tana duba Sabeena da ke bacci.
“Asibiti kuma? Me ya sameta?”
Hawayen daya zubowa Tasneem ta goge.
“Ciwon ciki, amma da sauƙi.”
Sauke numfashi Ummi ta yi, tana sake dubata, ta ga bacci take a nutse.
“Me yasa baki gaya min ba?”
Ta buƙata tana kallon Tasneem ɗin.
“Gani na yi ta ji sauƙi, kuma har mun siya magungunan da komai shi yasa, kiyi haƙuri.”
“Allah ya ƙara sauƙi…”
Ummi ta faɗa tana dorawa da,
“Amma in ya dawo gobe zaki fita ku gaisa. Bana son munafunci kina jina ko?”
Kai kawai Tasneem ta ɗaga mata, ba tambayar inda suka samu kuɗin magunguna ko ma jikin Sabeena bane matsalar Ummi, ganin Alh. Madu ne. Ficewa ta yi daga ɗakin, ranar ko Radio basu ji ba. Haka suka kwanta. Tasneem ta yi musu addu’a.
Bacci mai ƙarfi take yi, kafin ta buɗe idanuwanta, zuciyarta na wani irin dokawa kamar zata faɗo daga ƙirjinta. Ba shiri ta lalubi fitila ta kunna tana sa hannu a ƙirjinta ko hakan zai sa zuciyarta ta daina bugawa.
“Ya Tasneem na kasa bacci.”
Ta ji muryar Azrah na faɗi, ba ƙaramin tsorata ta yi ba don kamar daga sama ta ji maganar.
“Oh Allah Azrah kin bani tsoro.”
“Nima tun ɗazun na tashi. Mafarki na yi mai ban tsoro amma na kasa tuna ko na menene.”
Cewar Hamna data tashi zaune itama. Shiru suka zauna na wani lokaci kafin Hamna ta ce,
“Ko dai muyi sallah sai muyi addu’a?”
Su dukansu yarda suka yi da maganar Hamna. Tare suka fita tsakar gida suka ɗaura alwala. Nafila suka yi raka’a huɗu tare da gabatar da Addu’o’i. Jikin Tasneem Azrah ta kwanta nan kan dardumar ko Hijab bata cire ba, itama Hamna Qur’ani ta ɗauka tana kwanciya jikin Tasneem tare da buɗewa. A hankali suke sauraren ƙira’arta cike da fidda haƙƙoƙin tajwid har nutsuwa ta soma saukar musu.
*****
Sanin ba wani baccin kirki suka samu ba su dukansu shi yasa bata tashi kowa ba. Tsaf ta share ko’ina ta yi wanke-wanke. Wanka ta yi, sa’adda ta fito a tsakar gida ta samu Sabeena, don haka ta juye ruwan zafin itama ta yi mata sannan ta ɗora wa su Hamna nasu.
Bata tashe su ba har saida ta tabbatar ruwan ya yi zafi tukunna. Shiryawa suka yi su duka fes da su. Tasneem na jin yadda jikinta yake a sanyaye har lokacin.
“Ko za ku siyo mana biredi ne da ƙosai, mu sha shayi?”
Ta tambaya tana kallon su Azrah.
“Rana bata yi ba? Za’a samu ƙosai kuwa?”
Cewar Azrah.
“In babu sai mu dawo ai, mu duba dai.”
Hamna ta faɗi tana miƙewa tsaye da nufar inda jakar kayansu take ta ɗauko Hijabinta. Itama Azrah tashi ta yi. Kuɗin Tasneem ta basu da faɗa musu ko na nawa za su siyo tana bin bayansu suka fito tsakar gidan tare, ita tana wuce kitchen. Ruwan shayi ta ɗora musu ta koma ɗaki abinta.
Aikam har ƙosan sun samu, ci suka yi suka ƙoshi har suka yi hamdala. Yanayin jikin kowa baya mishi daɗi, don haka suka sake komawa suka kwanta. Gyara kwanciya Hamna ta yi.
“Ni ina son yin guga ne ma. Allah yasa su kawo wuta kafin lokacin Islamiyya.”
“Amin dai, nima ina son yi wallahi, amma kaina nake son kwancewa ƙiwa ta hanani tun jiya. Yaya Tasneem za ki mun kitso in kwance?”
“Ki kwance mana Azrah. Sai in miki kafin lokacin ɗora girki ya yi, banason yin ranar abincin saboda za ku Islamiyya. Hamna kefa?”
Girgiza kai ta yi.
“Ba yau ba, kaina na min nauyi tun jiya.”
“Da kin koma bacci, Sannu.”
Azrah ta faɗi cike da kulawa. Ɗan ɗaga mata kafaɗa Hamna ta yi.
“Um um nikam, bana jin wani bacci, ɗauko kibiyar dai in taya ki kwance kan.”
Ai bata ma ƙarasa ba Azrah ta mike tana ɗauko abin taje kai da kibiya. Tana zama suka ji sallama da ta gauraye ɗakin, wani irin dokawa zuciyar Tasneem ta yi kamar zata fito daga ƙirjinta, ƙarfin dokawar na sata runtse idanuwanta gam da faɗin,
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”
Azrah ce ta amsa sallamar muryarta na rawar da ta rasa dalilin shi, kafin ta miƙe ganin Tasneem bata da shirin yin hakan. Hijab ta ɗauka, suka ji kamar mutane a tsakar gidan su. Kafin Tasneem ta jiyo muryar Ummi a gigice tana tambayar,
“Me yake faruwa? Lafiya?”
Ai bata tsaya ɗaukar Hijab ba ta miƙe zuwa ƙofa suna rige-rigen fita ita da su Azrah. Mutane ne sun fi takwas, fuskokin su Tasneem take kallo, amma daga ciki mutane bai fi biyu zuwa uku take tunanin ta gane ba take tunanin dukkansu ‘yan nan unguwarsu ne. Zuciyarta na bala’in dokawa take binsu da kallo, kafin ta ji Hamna ta riƙo mata hannu tana jijjigata.
“Ya Tasneem jini…”
Ta faɗa muryarta can ƙasan maƙoshi, sai da Tasneem ta kalli fuskar Hamna da ta yi wani irin ja kamar ta sha rana, da idanuwanta da suka fiffito waje cike da tashin hankali, kafin ta mayar da kallonta zuwa inda idanuwan Hamna suke a kafe. Ƙwaƙwalwarta ta fara faɗa wa zuciyarta likkafani ne, ba don farin zawwatin ba, sai don yanayin yadda yake a ƙulle daga ƙarshe alamar wajen ƙafafuwa da kuma kai, sannan kuma mutum ne a ciki, ko kuma gawa, kamar yadda wata murya ta faɗa mata.
Duk ba wannan ba, jini ne a wajaje da yawa jikin likkafanin, musamman ta wajen kan da ya hudo har yana ɗiga ta gefe alamar ya taru a wajen.
“Me yake faruwa wai? Lafiya? Waye wannan?”
Ummi ta tambaya tana ƙarasawa inda suke.
“Waye a cikin abin nan? Ni ina tsoron abin nan Yaya Tasneem.”
Azrah ta faɗi idanuwanta cike da hawaye, tana ɓoyewa bayan Tasneem kamar zata shige cikin jikinta. Bata su Tasneem take ba, amsa take jira mutanen da suke tsaye su bama Ummi.
“Wani bazai fara magana ba? Ya za ku shigo min gida da sanyin safiyar nan, ku ajiye min gawa a tsakar gida kuma kuyi tsaye kuna kallona?”
Ummi ta ce ranta a ɓace, saboda bacci take mai nauyin gaske suka tashe ta, ta ma yi mamakin yadda akai ta ji sallamar su, don hayaniya komin ƙarfinta bata katse mata bacci, amma yau a gigice ta tashi zuciyarta kamar zata bar ƙirjinta saboda dokawar da take. Ɗaya daga cikin mutanen da Tasneem bata gane bane ya kalli Ummi da wani yanayi a idanuwanshi. Yanayin da yasa jikinta ɓari, wani abu na faɗa mata ko me zai faɗa ba alkhairi bane, kunnuwansu ba za su so jin abinda duk zai fito daga bakinshi ba. Tana kallo ya fara motsa laɓɓanshi da maganar da zata canza musu komai, maganar da zata hargitsa musu duniyarsu gaba ɗayanta.
“Hatsari aka samu wajen aikin su Alhaji Zanna, gini ne ya rugozo da ma’aikatan gaba ɗaya, da yawan sun jigata, mutum shida Allah ya yi wa rasuwa, Mal. Muftahu na cikin su shi da Alhaji Zanna, yanzun haka shi ma an wuce da gawar gidan iyalanshi…”
A wani waje tsakiyar maganar da mutumin yake yi Tasneem ta daina fahimta, saboda komai ya mata shiru, bugun zuciyarta take ji har cikin kunnuwanta, tana jin shi a cikin buɗewa da rufewar da idanuwanta suke yi, bata san ƙafafuwanta sun yi sanyi ba saida ta ji su a ƙasa, hannuwa take ji suna riƙeta, ture su take saboda bata son komai ya taɓata ta, bata son komai indai ba abinda zai canza maganganun da kunnuwanta suka jiye mata bane ba. Idanuwanta kafe suke kan gawar Abba, kan jinin da ya taru gefen kanshi da ya fara gangarowa tsakar gidan a hankali, ba zata ce jan jiki ko rarrafe ta yi ba, ta san dai ta ganta gefen gawar Abba ne, hannuwanta duka biyun ta sa a jikin likkafanin tana taɓawa.
“Abba…”
Ta kira muryarta na fitowa da ƙyar, in ta ce iya ƙirjinta ke wani irin ciwo ƙarya take, don ciwon da take ji yawo yake a jininta.
“In sha Allah wannan karon in na dawo kasuwa za mu je mu yo siyayya da yawa. Duk abinda kuke so zan siyo muku.”
Ta ji muryar Abba cikin kunnuwanta.
“Ki kula da kanku, don Allah ku yi ta haƙuri da Ummin ku har Allah ya ganar da ita. Ku dinga mata addu’a kin ji ko?”
Ta sake jin maganganun shi kamar yana gabanta, jin kamar ta taɓa lema a hannunta ne yasa ta ɗauke shi daga gawar Abba da sauri. Dubawa ta yi, jini ne a duka hannuwanta biyun. A jikin zaninta take gogewa da sauri da sauri kamar wadda ta samu taɓin hankali.
Ɗagowa ta yi ta kalli mutumin da ya yi wa Ummi magana lokutta kaɗan da suka wuce.
“Yaushe ya rasu?”
Ta tambaya. Tana kallon yadda yake kokawa da maganar da zai yi kafin ya ce,
“Cikin dare, ba zance ga lokacin ba, amma biyu ta wuce. Ku yi haƙuri dukkan mai rai mamaci ne in…”
Katse shi Tasneem ta yi.
“Inda yaje muma za mu je ko? Bai yi sauri ba, mu kuma ba mu yi jinkiri ba.”
Kai ya ɗaga mata a hankali. Wani abu da yake tsaye a maƙoshinta ta haðiye.
“Ki kula da su…”
Ta ji muryar Abba. Bata san inda ƙarfi ya zo mata ba, miƙewa ta yi tana juyawa. Ummi ce jingine da bango tana wani irin kuka kamar zata shiɗe. Ɗauke idanuwanta ta yi daga kan Ummi tana mayarwa kan su Azrah da ke kallonta suna son ta tabbatar musu da gaskiyar abinda suka ji.
“Abba ne a cikin abin nan? Abba ya rasu?”
Hamna ta faɗa. Har cikin zuciyarta Tasneem ta ji zafin maganganun da Hamna take yi, kamar tana zuba mata gishiri a sababbin ciwukanta takeji.
“Shi ne Hamna. Ya rasu da gaske.”
Dariya Hamna ta yi tana girgiza wa Tasneem ɗin kai tare da ƙarasowa, riƙeta Tasneem ta yi, ture Tasneem ɗin ta yi tana tsugunnawa gaban Abba.
“Abba ka tashi, ka tashi Abba kar mu zama marayu. Wallahi marayu wahala suke sha sosai Abba. Ka ga yadda su Ya Tariq suka zama. Ai ba za ka yi mana haka ba ko? Ba za ka bar mu kamar su ba… Waye zai siyo mana abinci? Abba waye zai bamu kuɗin makaranta? Wa zai hana Ummi ɗora mana talla?”
“Hamna..”
Tasneem ta kira sunanta tana riƙo mata kafaɗa, ture hannunta Hamna ta yi, ta saka rigarta ta goge hawayen da suka zubo mata. Sai ta yarda Abba ya barsu ne zata yi kuka. Bai barsu ba, bata ga dalilin da zai sa ta kuka ba.
“Abba don Allah ka tashi…Abba…”
Ko alamar motsi bata ga ya yi ba. Miƙewa tsaye ta yi hawaye na zubo mata. Kai kawo take a tsakar gidan, wani mutum da yake jin ba zai iya jurewa ba ya fice daga gidan. Kafin suma sauran su bi bayanshi don su ba su lokacin yin bankwana da Abban, shi yasa suka shirya shi tun daga can. Ba za su so iyalanshi suga yanayin raunukan da ke jikinshi ba.
Azrah kuwa kamar an kafeta a inda take, kallon su take, numfashinta take kokawar nema ta rasa, kokawa take amma ta kasa numfashi tunda suka fara magana, wani irin dubu ta gani ya gilma mata kafin komai ya ɗauke. Tasneem ce ta fara yin kanta da gudu ganin ta suma. Ɗagota ta yi tana jijjigawa.
“Itama ta rasu ko?”
Hamna ta tambaya tana tsare Tasneem da idanuwanta da har sun rine. Girgiza mata kai Tasneem ta yi tana sakin Azrah ta ɗibo ruwa ta zo ta shafa mata. Ajiyar zuciya ta sauke tana buɗe idanuwa. A firgice ta miƙe tana sake kallon su tukunna ta kalli inda Abba yake. Wani irin kuka ta fashe da shi, tana faɗowa jikin Tasneem, riƙeta ta yi. Ta kamo Hamna da ɗayan hannunta.
Sun fi mintina sha biyar suna wani irin kuka su biyun tana jinsu, don zuciyarta a bushe take jinta. Hawayen sun ƙi zuba, daga ciki suke mata ƙuna mai ciwo. Da ƙyar ta iya miƙar da su tana nufar hanyar magujin su, ruwa ta zuzzuba a butoci tana fara alwala, suma hakan suka yi duk da kukan su ya ƙi tsayawa.
Saida Tasneem ta sako Hijab tukunna ta zo ta kama Ummi da ke wani irin kuka.
“Me yasa Abban ku zai min haka Tasneem? Dawa zan yi faɗa yanzun? Ya zan yi da ku? Ya zan yi da rayuwata? Wallahi shi kaɗai ya rage min, banda wasu ‘yan uwa na kusa, shi kaɗai ne, shi kaɗai…”
Riƙeta Tasneem ta yi ganin yadda jikinta yake wani irin tsuma. Saida ta ɗan samu nutsuwa tukunna ta kamata ta kaita ɗaki ta barota. Su kam gawar Abba suka zagaye suna mishi addu’a. Basu tashi ba har saida aka shigo ɗaukar gawarshi. Nan tashin hankalin yake don Hamna kama shi ta yi ta riƙe gam tana kuka.
“Ina za ku kaishi? Don Allah ku tsaya. Ba mu shirya ba… Wallahi bamu shirya ba, Yaya Tasneem ki faɗa musu ba mu shirya ba…”
Girgiza mata kai Tasneem ta yi, zuciyarta na wani irin kuna.
“Ba’a shirya wa mutuwa, Hamna bata sallama balle baka damar kimtsawa. Ki mishi addu’a Allah yasa mutuwa sauƙi ce a gareshi…ƙaunar da ta rage tsakanin mu kenan…”
Tasneem ɗin ta ƙarasa tana riƙo Hamna, su duka biyun jikinta suka faɗa. Tana kallo aka ɗauki Abba aka saka cikin makarar da aka shigo da ita. Kallon su take lokacin da za su fita da shi. Sai lokacin ta lumshe idanuwanta.
‘Allah ya sada fuskokinmu a Aljanna Abba, Allah ya haskaka kabarinki kafin akai ka cikin shi, dukkan wahalar kwanan yau Allah ya sauƙaƙa maka.’
Ta faɗi a zuciyarta kafin ta ci gaba da jero ‘Innalillahi wa inna ilaihir raji’un’ babu tsayawa. Suna nan zaune tsakar gidan Sabeena ta fito, yadda ta gansu kwance jikin Tasneem haka ta samu waje itama tana kwanciya, don bata san me yake faruwa ba. Anan maƙota da suka fara shigowa suka same su.
Babu irin maganar da ba’ayi musu ba kan ko basu koma ɗaki ba, su tashi daga ƙasa, don rana har ta fara samun su, amma ko motsi ba su yi ba. Wata mata da ta zo ta kama Tasneem tureta ta yi da faɗin
“Ku yi abinda ya kawoku ku kuyale mu muji da rayuwar mu.”
Aikam ƙyale sun suka yi. Duk wanda zai shigo sai ya yi magana. Tasneem bata damu ba. Ba lallai wasu su ƙara damuwa da halin da rayuwarsu take ciki bayan yau ba, kamar yadda babu wanda ya damu da halin da suke ciki kafin yau, bata ga dalilin da zaisa su fara damuwa da su yanzun ba.
Bayan Kwana Uku
Kasancewar waya bata yawaita ba, sai tangaraho (Telephone) da tsirarun mutane masu wadata suka mallaka, ga rashin nutsuwa, kuma ‘yan unguwa babu wanda yasan inda ‘yan uwan Abba suke, ranar da Abba ya rasu ba’a samu faɗa wa wasu cikin’ yan uwanshi ko ɗaya ba. Har sai washegarin mutuwar tukunna.
Kullum sai matansu sun zo, suma haka. Har akai sadakar uku. Da yake su biyun da suka rage suna da wadata haka sukaita kawo buhunnan shinkafa ana dafe ma ‘yan zaman makoki. Da ido Tasneem take binsu, don ya zamar mata dole ta ci ko zata samu su Hamna ma su ci, amma wannan shinkafar baƙiƙirin take a idanuwanta.
Basu kawo lokacin da Abba yake da rai ba, lokacin da suka fi buƙatar taimako, sai yanzun da ƙasa ta rufe mishi ido. Su dukkansu kallo ɗaya za ka yi musu ka san babu nutsuwa tare da su. Musamman Tasneem da ta yi baƙi tai wata irin ramewa. Rabon jikinta da ganin ruwa kwana uku, ta ma manta da wani abu wai shi wanka.
Haka kawai take jin duniyar na wuce mata da yanayin da ta kasa fahimta. Sabeena ta zame daga jikinta tana miƙewa da ƙyar.
“Ina za ki je?”
Hamna ta buƙata idanuwanta na cikowa da hawaye. A kwanaki ukun nan ko bacci zai ɗauke su a jikinta suke yin shi. Ko banɗaki zata je suna biye da ita, haka za su yi tsaye bakin ƙofar banɗakin sai ta fito su sake binta.
“Banɗaki zan je Hamna. Ku zauna yanzun zan dawo. Don Allah ku zauna karku biyo ni.”
Ta ƙarasa a gajiye, sai da ta tabbatar ba zasu bita ba tukunna ta fice daga ɗakin. Ko takalmi bata damu da shi ba. Da sauri ta nufi hanyar da zata fitar da ita daga gidan. Babu banɗakin da zata je, iska take so ta shaƙa daban da ta cikin gidan, numfashi take so ta ɗan yi ita kaɗai ko kanta zai ɗan rage mugun nauyin da yake mata. Bama ta ganin hanya sosai, bata kuma san inda zata nufa ba.
“Tasneem…Tasneem…”
Ta ji muryar Tariq kamar daga sama. Idanuwanta ta sauke kan fuskarshi da ke ɗauke da wani irin yanayi da ta kasa fahimta.
“Sai yau na ji Tasneem, wallahi ban sani ba… Ban sani ba da nazo tuntuni…”
A yanayin muryarshi kawai ta gane ya fahimta, ta gane duka taron mutanen da ke cikin gidan bata tunanin akwai wanda ya fahimci halin da suke ciki fiye da shi.
“Ina za ki je?”
Ya tambaya. Muryarta kamar ba tata ba ta amsa shi da,
“Ban sani ba. Ina son inyi numfashi ne, ina numfashi amma ina son yin wani daban…”
Kai ya ɗaga mata alamar ya fahimta, hanyar gidansu ya kama, ta bi bayanshi, kamar jira take ƙafafuwanta su taka tsakar gidan, anan ta baje. Numfashinta take kokawa da shi, don sai yanzun komai yake danneta, sai yanzun kukan da ya ƙi zo mata ya zo. Nan ƙasa ta kwanta tana sakin wani irin gunjin kuka da yasa Tariq jingina jikinshi da bangon wajen yana zamewa ya zauna.
Ba kukanta bane yasa hawayenshi zuba, ba tausayin yanayinta bane yasa shi kukan dake fitowa daga zuciyarshi. Sai dai famin da yanayinta ya yi mishi, ba kuma ita kaɗai bace, ko wucewa ya zo yi ya ga ana zaman makoki sai ya yi kuka.
Ɗagowa Tasneem ta yi ta saka hannu ta goge hawayenta wasu na sake zubowa.
“Ya kuka yi? Ya Tariq ya kuka wuce wannan yanayin?”
Muryarshi a dakushe ya ce mata,
“Ba ke za ki wuce yanayin ba, shi ne zai miki sauƙi. Yanzun Wannan lokacin ba ku ji komai ba Tasneem, sai babu kowa a gidan tukunna. Za ki yi numfashi ƙirjinki kamar zai buɗe, ciwon ba yanzun za ku ji shi ba…”
“Inbalillahi wa inna ilaihir raji’un…”
Tasneem ta faɗi tana sake rushewa da wani sabon kukan. Jikin Tariq ɓari kawai yake. Yana jin yadda komai yake son dawo mishi sabo. Hannu yasa a aljihu ya zaro wata takarda a duƙunƙune.
Da ƙyar ya warwareta yana ɗaukar wasu fararen ƙwayoyi guda biyu yasa a bakinshi yana tsotsa kamar duka nutsuwarshi na tare da hakan. Runtsa idanuwa yayi yana haɗiyewa yana jiran su fara ratsa mishi jijiyoyin jikinshi, yana son muryoyin da suka soma ihu cikin kanshi su yi shiru. Duhun ya gama mamaye shi duka, yana son ɓoyewa daga duniyar nan zuwa wata da duhunta ba zai bari komai ya taɓa hi ba.
Lokacin da ya ji muryar Tasneem sama-sama ya daina gane abinda yake faruwa a wajen duniyarshi.
“Na tafi kafin su Azrah su biyo ni.”
Da ƙyar ya iya ɗaga mata kai. Hijabinta ta sa tana goge fuskarta, ta ja wani dogon numfashi kafin ta barshi anan tana nufar hanya ta koma cikin gida.
Bayan Wata Shida
A watannin nan Tasneem ta ƙara jinjina wa duk wani maraya, don tana tsakiyar ɗanɗana maraici, zuciyarta bata sake tsinkewa sai ta kalli su Azrah, musamman Hamna da duk ta fi su fari, yadda ta yi duhu, sun rame duk sun fita hayyacin su.
Sai yanzun take jinjina maganganun da Tariq ya faɗa mata. Sai yanzun ta gane ma’anarsu. Komai bai danneta ba sai da aka watse aka barsu su kaɗai, ranar ta yi kuka kamar ranta zai fita. Maraicin na danne su da duk rana.
Da suna zuwa makaranta a ƙafa su dawo a ƙafa, sai dai suna matuƙar wahala don wata rana haka za su dawo ga rana ga yunwa kuma su samu gidan babu komai. Yanzun haka suke yini, Ummi in ta fita sai dare take dawowa, ɗan abinda ta samo ta basu haka za su ci, su rage wani da za su ba Sabeena don ita ba sanin halin da ake ciki ta yi ba.
Zullumin faɗan Ummi da babu abinda ya yi banda ƙaruwa ma kawai ya ishe su. Musamman ranar da ta dawo bata samo abin kirki ba. Akansu zata huce da zagi da gorin yadda Abba ya mutu bai bar musu komai ba. Musamman Tasneem zata ce ita ta san yadda tai Alh. Madu ya daina zuwa.
Yauma kamar kullum, su dukkansu a kwance suke bayan sun idar da Sallah. Yunwa ta sa ko Islamiyya sun kasa zuwa. Kallonsu Tasneem ta yi, da ƙyar ta dafa ƙasa ta miƙe, wani haske ta ga ya gilma mata, kafin kanta ya ci gaba da sarawa da ta san yunwa ce kawai ke ɗawainiya da ita.
Ɗaki ta shiga ta ɗauko hijabinta. Ta saka silifas ɗin da har sun huje daga tsakiyarsu saboda jikin da suka ji.
“Ina zaki je?”
Hamna ta tambaya tana tsareta da idanuwa.
“Yanzun zan dawo. Karku fita ko’ina.”
Tasneem ta ce bata jira komai ba ta nufi hanyar fita daga gidan. Hanya ta miƙa da zata kaita gidan Anty Asabe, ‘yar uwar Ummi. Ba roƙonta abinci zata yi ba, don tun kafin rasuwar Abba ta fahimci halin mutane, ‘yan uwanshi ma sun watsar da su ballantana kuma Anty Asabe da ba wani kusanci suke da shi da ita ba. Mutane basa taimako saboda Allah, zata roƙe ta ne ko wanki ta dinga bata tana biyanta lada suna rage wani abin.
Da ƙyar ta iya kai kanta gidan saboda galaɓaita. Don ko da suka gaisa, ruwan da aka kawo mata kurɓa ɗaya tai mishi amma tana jin yadda cikinta ya tattare waje ɗaya.
“Anty Asabe zuwa na yi dama don Allah ko wankinku ne ku dinga bani sai ki biyani lada, wallahi abubuwa sun mana yawa sosai. Don Allah…”
Tasneem ta Kjarasa muryarta na rawa. Kallonta Anty Asabe ta yi, don in ba aike ba, Tasneem bata taɓa wanko ƙafa ta zo gidanta ba, kuma sam yarinyar bata yi halin mahaifiyarta ba, ga hankali da Anty Asabe ta kula Tasneem ɗin na da shi. Ba taimaka mata bane bata son yi. Suna da mai yi musu wanki, mijinta yake haɗawa duka ya kai a wanko a goge.
“Tasneem muna da mai wanki wallahi, duk shekarun nan babansu Muhsina can yake kai mana.”
“Ya Allah…”
Tasneem ta faɗi idanuwanta na cika taf da hawaye, bata san ya zata yi ba, ta dai san ta gaji da ganin ƙannenta cikin halin da suke. Yanayin ta da Anty Asabe ta gani yasa ta faɗin,
“Sai dai akwai ƙawata da take neman mai aiki, tun rannan ta yi…”
Bata ma bari ta ƙarasa ba ta katseta da cewa,
“Zan yi wallahi, komin yawan aikin zan yi.”
Ɗan murmushi Anty Asabe ta yi.
“Bansan ko ta samu ba, saboda wajen sati kenan da ta yi min maganar. Sai dai ki ɗan jira na aiki Muhsina, in ta dawo yanzun sai in aikata gidan mu ji.”
Jinjina kai Tasneem ta yi ba tare da ta ce komai ba. Miƙewa Anty Asabe ta yi tana dawowa da plate ɗin abinci ta ajiye wa Tasneem, cikinta wani ƙara ya yi da idanuwanta suka sauka kan abincin.
“Na gode. In kina da leda ki bani don Allah, zan juye a ciki.”
Don ba zata iya ci ita kaɗai ba. Zai fi musu albarka ko yaya ne in suka haɗu ita da su Azrah. Anty Asabe bata ce komai ba ta ɗauki abinci, a ledar ta juye mata tana ƙara mata wani. Har a ranta ta ji tausayin Tasneem ɗin, girma ya kamata da ƙarancin shekaru.
Da yake gidan Haj. A’i ƙawar Anty Asabe nan baya ne, Muhsina na dawowa ta aikata. Aikam aka yi sa’a bata samu ‘yar aiki ba. Don haka ta sake haɗa su da Muhsina kan cewar ta ga Tasneem ɗin, in yaso sun yi magana daga baya. Sosai Tasneem ta yi mata godiya tukunna suka wuce.
Tun kafin su shiga gidan Tasneem take ganin girmanshi. Balle ma da suka shiga wani tankamemen falo. Muhsina na rakata ta tashi ta juya abinta. Kallonta Haj. A’i ta yi a wulaƙance.
“Anya za ki iya kuwa?”
“Zan iya wallahi.”
Tasneem ta faɗi a ƙagauce
“Share-share ne da wanke-wanke, sai kuma za ki dinga kama min girki, bana son lalaci ko kaɗan, ba kuma na son ƙazanta da ha’inci, zan dinga baki dubu biyar duk wata. Na kori ‘yar aikina ne saboda tana min sata, ba za mu shirya ba in har naga abubuwa sun fara ɓacewa.”
“In shaa Allah duk zan kiyaye. Yaushe zan fara zuwa? Ina layin Mai Agwagi ne.”
Tasneem ta faɗi, don da’ yar tafiya ba laifi. Wani kallo Haj. A’i ta sake yi mata.
“Gobe ma zaki iya fara zuwa. Ki zo da wuri saboda wanke-wanken safe. Ki jirani ina zuwa…”
Ta ƙarasa maganar tana miƙewa. Ta ɗan jima kafin ta dawo, kuɗi ne ta miƙa wa Tasneem ɗin ‘yan naira dari-ɗari guda biyar.
“Ki hawo mota goben don karki zo min latti.”
Godiya Tasneem ta yi mata. Sa’adda ta fita daga gidan wani sabon ƙarfi take jin ya zo mata. Murmushin da ke fuskarta ya ƙi dishewa. Ko ba komai dubu biyar ba ƙaramin kuɗi bane a wajenta. Su Azrah za su koma makaranta, rashin makarantarsu na tsaya mata, Abba na son su da karatu ba kaɗan ba.
Anan shago ta tsaya ta siya musu garin kwaki da sukari ga kuma ledar abincin da Anty Asabe ta bata. Da sallamarta ta shiga gida, suka amsa mata. Ta ƙarasa kan tabarmar tana ajiye ledojin ta zauna ta ce Azrah ta ɗauko musu faranti a kitchen. Ba musu ta tashi ta ɗauko, abincin ta juye.
“Ku zo mu ci…”
Sabeena ta fara sa hannu, sai Azrah, Hamna kallon abincin ta yi, tana komawa kan ɗaya ledar gari da sugan da Tasneem ta ajiye sai ɗari biyun da ya rage, kafin ta kalli Tasneem, cike da rashin yarda ta ce,
“Ina kika samo abinci? Ina kika samo ɗayar ledar nan da kuɗin?”
Sai lokacin hankalin Azrah ya dawo mata na basu san inda Tasneem ta samo kayayyakin nan ba. Ita ma hannunta ta tsame daga abincin tana kallon Tasneem ɗin,
“Gidan Anty Asabe na je, na roƙe ta ta dinga bani wankin su ina yi don mu dinga samun na abinci, ita ta bani abincin nan, gari ne a ledar nan da sukari dana siyo. Na samu aiki a gidan ƙawarta da ke bayan gidan Anty Asabe, gobe zan fara zuwa in shaa Allah, matar ta ban ɗari biyar.”
Murmushi Hamna ta yi mata.
“Don Allah? Zan biki sai in dinga taya ki ayyukan.”
Murmushi ita ma Tasneem ta yi ganin Hamna ta sa hannu cikin abincin.
“A’a ba sai kin bini ba. Za ku yi zamanku a gida. In shaa Allah da an ban kuɗin farko zan saka Sabeena makaranta. Kuma sai ku koma.”
“Ke ba za ki koma ba?”
Azrah ta faɗi. Numfashi Tasneem ta sauke, don ta riga ta san ita da makaranta sun yi bankwana. Wanda ta samu Allah ya amfana, in dai su za su je ya isheta, zata yi duk wani ƙoƙari don ganin karatunsu bai tsaya ba, zata kula da su. Ba sai sun san ita tata rayuwar zata yita ne kawai don kula da su ba.
“Zan koma nima a hankali.”
Ta faɗi m, maganar ta zauna musu, abincin suka gama ci, ta ce in basu ƙoshi ba su ƙara da garin, har Sabeena kai ta girgiza mata. Hira suka ci gaba da yi cikin jin daɗin canjin da ya zo musu na farko tun rasuwar Abba.
Sai da suka yi sallar isha’i tukunna Ummi ta dawo.
“Sannu da zuwa.”
Hamna ta faɗi. Kallon ta Ummi ta yi, don ba wai ko yaushe Hamna ke mata sannu da zuwa ba. Gaisuwar safe kawai take haɗa su in sun ga juna kenan.
“Ba wata tsiya na samo ba da kike saurin min sannu. Nima banci ba, babu wanda ya ban kuɗina, Jummai sai gyaɗa na sungomo da na samu an siyo mata.”
Miƙewa Hamna ta yi ta shige ɗaki, bata yi magana bane don wani abu, ta yi ma Ummi sannu da zuwane kawai saboda tana cikin jin daɗi, amma sai da Ummi ta rusa mata ɗan farin cikin da take ciki. Azrah ma bayan Hamna ta bi da hannun Sabeena cikin nata. Suna barin Ummi da Tasneem.
“Wannan gyaɗar zan soya su Hamna su zagaya min da ita, don bazan yi asara ba wallahi.”
“Talla Ummi?”
Tasneem ta tambaya muryarta can ƙasa. A tsawace Ummi ta amsa da,
“Eh tallar, don banda abinda zan ci da ku da shi. Wallahi in kika zuga su suka ƙi zuwa ku zaku zauna da yunwa. Don in ba’a je min tallar nan ba, babu wanda zan ba abinci a cikin ku, kuna ganin wahalarku da ubanku ya barni da ita, danginshi ba shegen da ya tuna damu balle yace zai kawo mana wani abu…”
Runtsa idanuwa Tasneem ta yi tana jin wani abu ya yi mata tsaye a wuya.
“Na samu aiki. Ba sai sun fita talla ba, Abba baya son tallar nan.”
“Kin samu aiki? Yaushe?”
Kallonta Tasneem ta yi.
“Ɗazun Ummi, Anty Asabe ta samarmun a gidan ƙawarta.”
Jinjina kai Ummi tayi.
“Asabe munafuka ce wallahi, don baƙin munafunci nan na je ta ce bata da inda zata samo min aiki, shi ne ke har ta samo miki ko? Ya mata kyau!”
Shiru Tasneem ta yi, ledojinta Ummi ta kwasa tana shigewa ɗaki. Itama Tasneem ɗakin ta wuce ita ma, kafin Ummi ta dawo ta sake sauke mata wani faɗan. In dai kan abincin da take basu ne da ko isarsu baya yi sau ɗaya a rana zata ɗora wa su Azrah talla ta riƙe kayanta. Tasneem ma ta yi mamaki da sai yau Ummi ta yi maganar, don kullum ta basu jininta kan farce take karɓa, ta san Ummi ba zata dinga basu abu haka kawai ba, sai sun mata wani abin.
*****
Bata koma bacci ba bayan ta yi sallar subhi, sai da ta share ko’ina da ina, ta yi wanka, ta kunna radio tana jiran ta ji bakwai ta yi sai ta fita. Aikam ƙarfe bakwai na yi ta sa hijabinta ta tafi. Hankalinta a kwance yake saboda akwai sauran garin kwakin da zai ishi su Azrah har rana.
Mota ta hau kuwa. Kafin wani lokaci har ta isa maigadin gidan tsoho ne, cike da ladabi Tasneem ta gaishe da shi, ya amsa fuskarshi babu yabo ba fallasa. Data shiga cikin falon da suka zauna jiya tai ta sallama babu wanda ya amsa, waje ta samu ta zauna a ƙasa ta rakuɓe, tana jinta wani iri. Babu motsin komai sai Tv da ke yi da sauti ɗan kaɗan a falon.
Agogon ɗakin ta zuba wa idanuwa, lokaci zuwa lokaci takan ƙara yin sallama amma shiru, sai ta saka wa ranta bacci suke, bata son yin ba dai-dai ba, tunda bata san ko’ina na gidan ba, da ko share-share ta fara yi don ta rage aiki, ganin babu mai fitowa yasa ta mayar da hankalinta kan Tv tana ƙoƙarin fahimtar fim ɗin da ake yi amma ta kasa.
Haj. A’i bata fito ba sai wajen takwas da rabi, jikinta sanye da rigar bacci doguwa sai wasu takalma da kallo ɗaya za ka yi musu ka san suna da laushi a ƙafarta.
“Ina kwana.”
Tasneem ta faɗi a sanyaye. Kallonta Haj. A’i take yi kamar tana son gane inda ta taɓa ganinta maimakon amsa gaisuwar da ta yi mata. Ganin hakan yasa Tasneem faɗin,
“Kince inzo da wuri. Ina ta sallama ban ji kowa ba.”
Ɗan ware idanuwa Haj. A’i ta yi.
“Oh, ai da kin fara aikinki baki jira ni ba. Bacci nake yi.”
“Ban san inda komai yake ba.”
Kai Haj. A’i ta ɗaga da cewa,
“Biyoni in nuna miki.”
Miƙewa Tasneem ta yi tana bin bayanta, har suka ƙarasa wani kitchen mai girma da ya ƙawatu, tunda Tasneem take bata taɓa ganin irinshi ba.
“Ya sunanki?”
“Tanseem.”
Ta amsa a sanyaye .
“Tasneem kin ga kitchen ɗinmu da muka fi aiki a ciki, akwai wani a ɗayan bangaren. Yarona ɗaya ne a gida yanzun, sauran duk suna makaranta sai ƙarshen sati wasu suke zuwa, wasu kuma ƙarshen wata ko in sun samu hutu. Amma za ki share kowanne ɗakunansu kullum ki goge saboda ƙura…”
Kai Tasneem take ɗaga mata, haka suka zagaye gidan da duk da babu bene, babba ne sosai, Haj. A’i na nuna mata ko’ina, tana mata bayani, wani ɗaki suka shiga, da ya sha banban da sauran ɗakunan baccin, don shi da aka tura gado ta gani a falo suka fara cin karo da shi.
Numfashi ta ji Haj. A’i ta sauke da fadin
“Haidar anan aka yi bacci kenan…”
Inda idanuwan Haj. A’i suke Tasneem ta kai nata, kwance akan kujera wani matashin saurayi ne da Tasneem bata iya ganin fuskarshi ba, saboda kanshi a juye yake, ƙafarshi ɗaya a ƙasa, kusan rabin jikinshi ma ba a kan kujerar yake ba. Juyi ɗaya zai yi ya faɗo ƙasa.
“Sai nan ma, kullum zaki share ki goge, akwai ƙaramin kitchen ba wani girki ake a ciki ba. Can ƙofar ɗakin baccin shi yake da banɗaki a ciki. Akwai kwandon da na nuna miki ciki zaki zubo kayan wankin sai ki kaisu ɗakin wankin da na kai ki…”
“Mummy…go away.”
Haidar ya faɗi muryarshi can ƙasan maƙoshi, yana jan jikinshi yahau kan kujerar sosai, tare da juyowa ya buɗe idanuwanshi a hankali.
“Ba inda zani, ka tashi ka yi sallah.”
Sosai Tasneem take ƙoƙarin ɓoye mamakin da ke fuskarta, na tiƙeƙen ƙato kamar wanda Haj. A’i ta kira da Haidar ace bai yi Sallah ba har lokacin, abin ya mata wani iri. Har suka juya suka fice daga ɗakin bai ƙara motsawa ba. Bata kuma sake tashin shi ba.
Wanke-wanke Tasneem ta yi, tana jinjina yawan kwanonin da tukwanen da aka ɓata, don a bayanin Haj. A’i basu da yawa a gidan. Sai ta sa wa ranta ko na kwanaki ne aka tara, kafin wani lokaci ta gyara kitchen ɗin ta goge ko’ina, don Allah bai ɗora mata ƙiwa ko ha’inci ba. Haka ma ko’ina ta share tas ta gogge.
Haj. A’i ta ce banda nata ɓangaren. Don haka ɗakin Haidar kawai ya rage mata. Ta kai minti biyu a bakin ƙofar tana tunanin shiga, ƙwanƙwasawa ta yi har sau biyu amma shiru, sake ƙwanƙwasawa ta yi a karo na uku, da ba’a amsa ba ta yanke shawarar shiga, duk da haka da sallamarta.
Ta yi mamakin ganinshi zaune ya kafeta da idanuwa, sai da zuciyarta ta doka. Ganin ta da tsintsiya da mopper a hannu yasa shi gane sabuwar ‘yar aikin da Haj. Ta kawo ce.
“Baƙuwace ke, zan faɗa miki sau ɗaya ne kawai. Ba’a ƙwanƙwasa min ɗaki, in wani abu za ki yi ki turo ki yi ki fita, saboda in bacci nake zai iya sa min ciwon kai…”
Tunda ya soma magana kai kawai Tasneem take ɗaga mishi, akwai wani abu tattare da idanuwanshi da yadda yake kallonta da bata so, zuciyarta bata sake dokawa ba sai da ya ce,
“Ki kulle min ƙofa.”
Hannunta da ke kyarma tasa ta tura ƙofar, zagayawa ta yi daga bayanshi tana soma sharar duk da ɗakin babu wani datti, banda gwangwaneyen lemuka da ke tsakiyar ɗakin a ajiye da ta gani tun shigowarsu da Haj. Ko da ta zo share wajen jikinta na mata wani iri, sau biyu suna haɗa idanuwa da Haidar amma bai daina kallonta ba.
Ya sake kayan ɗazun da ke jikinshi, wani wando ne duk ƙafafuwanshi a waje, sai riga mai yankakken hannu, ita kam jikinta na mata wani iri, don bata saba zama ita kaɗai da wani namiji a ɗaki ba. Tana son ta ce ya janye ƙafafuwanshi ta sharo wajen don akwai gwangwaneyen lemo amma bakinta ya mata nauyi.
Saima ƙara matso da ƙafafuwanshi da ta ga ya yi wajen.
“Zan share.”
Ta tsinci kanta da faɗi.
“Na hanaki ne?”
Ya tambaya a hasale, hannunta na rawa tana ƙara takure jikinta don karta taɓa shi, inda Allah ya so ta da hijabinta duk aikin da take bata cire ba, ta yi dabara ta sharo wajen da sauri tana tattarawa. Sai nishi take kamar wadda ta yi gudu, ga zuciyarta da ke dokawa, ga Haidar daya kafeta da idanuwa.
Ɗakin baccin shi a hargitse yake, ko ina kaya ne kaca-kaca, kan gado da ƙasa, banda zube suke ba zata ce kayan wanki bane don har da ƙamshin turare a jikin su, haka ta tattara su waje ɗaya. Ta share, ta gyara gadon, ɗakin ya yi fes da shi, ta saka kayan cikin riga ɗaya don ta ƙulle ba sai ta dawo ɗakin ba ta ji shigowar Haidar ɗakin.
Juyawa ta yi, sai lokacin ta ƙare mishi kallo sosai, dogo ne, baƙi ne sai dai fuskarshi na da cika, ko kuma girmanshi ne yasa ya yi mata haka bata sani ba, da sauri ta ke tattara kayan, ta bayanta ya wuce ƙafafuwanshi na gogar jikinta.
“Auzubillah!”
Ta faɗi da karfi tana runtsa idanuwanta kamar ya goga mata wuta, da sauri ta tattara kayan ta miƙe tana ɗaukar abin sharar ta fita daga ɗakin zuwa falo, da gudu ta ɗauki mopper ta fice, ƙirjinta na dukan uku-uku, ɗakin wanki ta je ta kai kayan. Kitchen ta koma ta samu Haj. A’i ta fito da dankalin turawa mai yawa.
Ƙasa Tasneem ta sakko da shi ta zauna kan tiles tana ferewa. Ta jima da yake da yawa, kuma tana bi a hankali karta kwashe shi, ita ma Haj. A’i hidimarta ta shiga yi, duk da ta yaba da aikin Tasneem ɗin, komai ya fita tsaf-tsaf bata faɗa ba. Da yawansu haka suke farawa daga farko.
Ita ta nuna ma Tasneem yadda take so a yayyanka tukunna, ayyukan da yawa, Tasneem ita ta soya dankalin, har da su farfesun nama Haj. A’i ta yi . Sai yanzun ta ga yadda ake kwanoni na ɓaci. Ko da suka gama ayyukan tsaf, suka zuba a kuloli sai da ta sake yin wanke-wanke. Ta goge kitchen ɗin.
Wani babban kwano Haj. A’i ta zuba wa Tasneem farfesun nama a ciki, ta cika mata plate da dankali da soyayyen ƙwai, ta kuma ce mata ta haɗa shayi ga ruwan zafi nan da kayan shayi. Kallonta Tasneem take cike da mamaki, murmushi kawai Haj. A’i ta yi, ta bar wa Tasneem kayan shayin ne ta haɗa da kanta saboda tana son ta ga hankalinta.
Ita ba irin mutanen nan bace masu rowa, ko masu kuɗin da za su ɗauki ‘yan aiki su su ci mai daɗi su hana wanda suka taya su aiki. Ba haka halinta yake ba. Abinda duk suka ci shi duka ‘yan aikin da ke gidan suke ci har da maigadi, bata iya halin tsiya da rashin wadata ba. Lipton kawai Tasneem ta saka a ruwan zafin da siga, don yunwa take ji jikinta har ya soma ɓari. Dankalin da ƙwai ta ci, ko rabi bata iya ci ba. Naman ma yanka biyu ta ci, sosai ya yi mata daɗi.
Leda ta gani ta ɗauka ta juye dankali ta tsame naman daga cikin romonshi ta juye ciki shima ta ƙulle tana ajiyewa gefe. Anan kitchen ɗin ta yi zamanta. Ta daɗe sosai har Haj. A’i ta dawo ta sameta.
“Tasneem anan kika zauna. Taso akwai ɗakin masu aiki, tunda ke ba kwana za ki dinga yi ba. Sai ki zauna ki huta kafin ki gama aikin ki.”
Miƙewa Tasneem ta yi da ledar ta a hannu. Ganin Haj. A’i ta bi ledar da kallo yasa Tasneem saurin faɗin,
“Dankalin dana rage ne da nama. Bazan iya cinyewa ba, zan kaima ƙannaina.”
Kai kawai Haj. A’i ta ɗaga mata. Tasneem ta bi bayanta tana sauke numfashi. Don bata son ta ɗauka ta ɗibar mata wani abu ne. Ɗakin babbane har da Tv a ciki da fanka.
“In za ki yi kallo ga remote ɗin can. In ma bacci za ki yi to, in za ki min wani abu zan zo in kira ki.”
“Na gode.”
Tasneem ta faɗi, don bata zata akwai kalar su Haj. A’i ba. Karamcin matar ya tsaya mata. Duk da haka bata son ta zaƙe a ƙasa ta yi zamanta.
*****
Aikin ranar ma ba mai yawa bane, abincin dare ne ma kala-kala, shi ma ƙarfe biyar sun yi komai sun gama. Wata kula Haj. A’i ta samu ta cika wa Tasneem abincin daren a ciki. Ta saka mata a leda, ɗari biyar ta sake bata ta yi mata sallama. Har hawaye ta yi a hanya, don bata taɓa zaton hanyar samun abinci zata zo musu cikin sauƙi haka ba.
Ranar har Ummi suka rage wa abincin, don ya musu yawa. Ita ma ta ji daɗi, har fara’ar da suka jima basu gani a fuskarta ba ta yi musu. Baccin farin ciki suka yi a nutse ranar.
*****
Da duk kwanakin da za su wuce na zamanta da Haj. A’i da yadda take karantar irin karamcin matar, kullum sai ta bata ɗari biyar in zata koma gida, ga abinci kala-kala, haka kuma in zata dafa wani abin sai ta saka Tasneem a gaba ta ga yadda ta yi.
Ɗakin Haidar Tasneem take fara gyarawa don duk yawancin lokutan yana bacci, wani lokacin kuma baya ma ɗakin. Da sauri-sauri haka zata gyara ta fito. Bata ƙara haɗuwa da shi ba, hakan kuma ya mata daɗi. Kuɗin da Haj. A’i take bata adanawa take, kuɗin motar zuwa kawai take ɗauka Naira talatin, sai ko in za su siyi sabulun wanki.
Ranar da ta cika kwana talatin ba ƙaramin aiki suka yi da safen ba. Don Haj. A’i ta ce mata yaranta har su uku za su dawo daga makaranta. Aikuwa wajen ƙarfe sha ɗaya Tasneem na jera kuloli a dining suka shigo da sallamarsu. Maza biyu sai mace guda ɗaya. Duk da ba farare bane suna da kyau sosai. Ga su tsaf-tsaf.
“Cikina har ƙullewa yake saboda yunwa.”
Macen ta faɗa tana nufo dining ɗin da Tasneem take tsaye. Kallon Tasneem ta yi da a daburce ta ce mata,
“Ina kwana. Sannu da zuwa.”
Dariya yarinyar da ko zata girmi Tasneem ɗin ba zai wuce shekara uku ba ta yi.
“Sannunki da aiki, sunana Hamida.”
“Tasneem.”
Jinjina kai Hamida ta yi tana jan kujera ta zauna.
“Tasneem…”
Ta maimaita sunan na mata daɗi, plate ta janyo ta soma buɗe kulolin, wucewa Tasneem ta yi tana gaishe da samarin su biyu.
“Ke ni bana so ana gaishe da ni, duk aita baka girma ana sa kana jin kunya.”
Ɗaya daga ciki ya faɗa, ɗayan kuma kai kawai ya ɗaga wa Tasneem.
“Karki damu da Ahmad.”
Haj. A’i ta faɗa da alama da wanda ya yi magana take. Tasneem bata ce komai ba ta wuce ɗakin da takan zauna. Tunda ta gano tashar da ake Hausa bata sake taɓa remote ɗin ba. Suna shirye-shirye masu daɗi.
Sai wajen sha biyu da wani abu, Haj. A’i ta zo ta yi mata magana don a ɗora abincin rana. Wannan karon har da Hamida a kitchen ɗin, sosai suke hira da Haj. A’i da ‘yartata gwanin sha’awa. Sai suke sa Tasneem na jin dama haka suke hira cikin nishaɗi da Ummi, kewar Abba na danne mata ƙirji da wani irin ciwo.
Tasneem ta fito ta ajiye jug ɗin zoɓo da Hamida ta yi a dining ta ga Haidar zaune a wajen, sai da gabanta ya faɗi, hannunta na rawa ta ajiye. Tana jin kallon da yake mata, da sauri ta zo zata bar wajen ya ce,
“Ke ba ki iya gaishe da mutane ba ne?”
A hankali ta ce,
“Ina wuni?”
“Mtswww bar wajen nan.”
Haidar ya faɗi. Da sauri kuwa ta bar wajen bata jira ya sake faɗa mata ba. Ta ji daɗi da Hamida ta ɗauki sauran kayan ta kai ita ta tsaya wanke kwanonin da suka ɓata. Nata abincin ta ci a kitchen ɗin ita kaɗai. Don karta fito zuwa ɗaki ta sake haɗuwa da shi.
Sai da ta tabbatar sun gama tukunna ta fito ta wuce su a falo tana kwashe kwanonin. Tana cikin aiki a kitchen Haj. A’i ta shigo.
“Sauran abincin ki kwashe ki tafi da shi Tasneem. Ga kuɗin aikin ki nan, dubu goma ne saboda na ji daɗin yadda kike aiki babu ha’inci, ko da zaki siya wa ƙannenki wani abu. Ban ce duk wata haka zan dinga baki ba.”
Muryar Tasneem ɗauke da wani yanayi ta ce,
“Wallahi sun yi yawa ma. Kullum sai kin bani kuɗi, kuma kina bani abinci.”
Ɗan murmushi Haj. A’i ta yi, ta yaba da hankalin Tasneem, ta kuma sha gwadata ta fannin kuɗi ko abinci, har a kitchen takan ajiye kuɗi, amma Tasneem bata taɓa ɗaukar mata ba, haka zata ɗaga kuɗin ta goge wajen ta mayar da su ta ajiye, wani lokacin har abu take sawa ta danne kar su faɗi.
Haka abinci, in ba wanda ta rage ba, ko su suka rage sai dai ta haɗa waje daya, in Haj. A’i bata ce ta ɗauka ba, bata taɓawa, gashi bata da karambani. Ta bata ne don ta ga tana bukatare kuɗin sosai. Kuma ita macece da abinta bai rufe mata ido ba.
“Ki ɗauka bakomai. Kin yi wani abin da shi.”
“Na gode. Allah ya ƙara arziƙi ya baki ninkin su.”
“Amin Tasneem. Zamu fita duka gidan, inkin ƙarasa aikinki za ki iya tafiya sai gobe in Allah ya kaimu.”
Jinjina kai Tasneem ta yi.
“Allah ya tsare hanya. Na gode.”
Amsawa Haj. A’i ta yi tana ficewa daga ɗakin. Tasneem na jin fitar su. Aikinta ta ci gaba da yi, gidan ya yi shiru, hankalinta a kwance yake don ta san ita kaɗai ce a gidan. Karatun Qur’ani take a hankali wani sashi cikin Suratul-Ra’d zuciyarta na mata wani sanyi.
Sanin ita kaɗai ce a gidan yasa ta sakin wata gigitaciyyar ƙara jin mutum a bayanta, hannu yasa yana rufe mata baki, ɗayan hannun kuma maƙale a ƙugunta. Da take kiciniyar ƙwacewa.
Mu je zuwa.