"Kunne za ki fasa min?"
Muryarshi ta gane, gashi ɗayan hannunshi da take ji kamar wuta na mata yawo a jiki, hannunshi dake bakinta ta gartsa wa cizo tana hankaɗe shi, numfashi take zuciyarta kamar zata fito saboda dukan da take.
"Innalillahi wa inna ilaihir raji'un..."Ta faɗi tana kallon Haidar da ya zuba mata idanuwanshi cike da ɓacin rai. Nata idanuwan cike da hawaye, muryarta na rawa take faɗin,
"Na shiga uku, don Allah ka rufa min asiri, karkai mun sanadin aikina. Wallahi shi kaɗai ne hanyar abincin mu. Don Allah ka. . .
Hmmmmm.
Oka