Kano
A cikin falo ya ɗaura agogon shi.
“Jawwad baka makara ba?”
“Ina kwana…”
Ya gaishe da Anty maimakon amsar tambayar da ta yi mishi yana ɗorawa da,
“Sosai ma, kuma meeting za mu yi wallahi.”
“Yaya ina kwana.”
Jawda ta gaishe da shi.
“Lafiya ƙalau. Ba za ki School bane yau?”
“Hutun tsakiyar zango muke yi.”
Jinjina mata kai ya yi yana ƙarasawa ya karɓi kofin da Anty ta bashi, a tsayen ya kurɓa yana yatsina fuska saboda bai ɗauka da zafi sosai ba.
“Anty zan ci wani abu a office….”
Girgiza kai ta yi don ta san halinshi.
“Kodai ka zauna ka ci ko ka jira in haɗa maka ka tafi dashi.”
Daƙuna fuska yayi yana tsugunnawa.
“A tsugunnen za ka ci abinci?”
“Allah na makara sosai…”
Ya ƙarasa yana zama, dankalin da ke plate ɗin gaban Jawda ya fara tsinta yana ci a hankali yana kurɓar shayin da ke riƙe a hannunshi. Wainar ƙwai ya ɗauka ya tura a bakinshi yana ajiye kofin ya miƙe da sauri.
“Sai na dawo…”
Ya faɗi a bakin ƙofa yana zura takalmanshi da ke ajiye a wajen.
“Jawwad…”
Anty ke kira, ina da sauri ya fice yana dariya. Girgiza kai ta yi kawai. Yasan in ya tsaya Anty na iya haɗa shi da kula da dankali a ciki sai ka ce ƙaramin yaro, abokanshi har zolayarshi suke a wajen aiki, ɗan gatan Anty. Mashin ɗin shi ya hau tare da yin addu’a kafin ya tayar ya fice daga gidan.
Sai dai ko nisa baiyi ba ya kula mai na gab da ƙare mishi. Sauke numfashi ya yi, ya san aikin Marwan ne, ba takaicin shi ƙarar da man ba, makarar da zai ƙara yi tsayawa zuba mai. Amma ba shi da wani zaɓi. Ba zai iya tsayawa ya ƙarasa gidan mai ba, bai ma san layin da zai samu ba, don haka yana hango wasu ‘yan bunburutu ya yi parking a gabansu yana saukowa daga mashin ɗin.
Na ɗari biyar ya ce a zuba mishi, ya basu dubu ɗaya. Sai dai babu canji.
“Ka ga, siyo min MTN na ɗari biyar ɗin in da masu kati a kusa. Don Allah kai sauri.”
Jawwad ya faɗi a ƙagauce, da hanzari mai man ya bar wajen yana barin Jawwad tsaye sai abokanshi da ke zaune kan benci da ke bakin titin. Lokaci-lokaci Jawwad yake duba agogon shi yana jan ƙaramin tsaki. Kallo ɗaya za ka yi masa kasan a ƙagauce yake da yabar wajen.
Kamar daga sama ya ji an ce,
“Jawwad?”
Muryar ɗauke da mamaki da shakku, zuciyarshi ta fara dokawa kafin wani abu cikin kanshi ya faɗa mishi ba zai yiwu ba, sai dai zuciyarshi na faɗa mishi a cikin mutane dubbu masu shigen muryar zai iya ganeta.
“Jawwad.”
Aka sake kira, da duk wani ƙarfi da yake ji yake son ƙin juyawa, amma jikinshi bai san wannan ba, a hankali ya juya yana jin maƙoshin shi ya bushe kamar ya kwana biyu bai sha ruwa ba, kayan da ke jikinta ya fara bi da kallo da suke a wulaƙance, sai robar da ke hannunta, kafin idanuwanshi su sauka kan fuskarta da yanayinta yasa zuciyarshi matsewa har yana jin iskar daya shaƙa ta ƙi kai mishi inda ya kamata.
‘Mama.’
Ya faɗi cikin kanshi, bakinshi a buɗe amma kalma ko ɗaya ta ƙi fitowa, wahala da halin rayuwa da ke tare da ita baisa fuskarta ta canza mishi ba. Baya tunanin kuma ko me zai samu fuskarta zai kasa ganeta.
“Jawwad…”
Ta sake faɗi, wannan karon muryarta na karyewa, hawaye na zubo mata. Ƙare mata kallo Jawwad yake don duk yadda baya so ya furta wa kanshi kalmar yasan bara take. Runtsa idanuwanshi ya yi yana son ya buɗe su ya ga ta ɓace, ya buɗe su ya ga bai ma sauko daga gadon ɗakinshi ba balle ya fito waje wannan yanayin ya tabbata.
“Jawwad baka son ganina ko?”
Muryarta tasa shi dole ya buɗe idanuwanshi yana tabbatar da ba mafarki yake ba. Ita ɗin dai ce a gabanshi.
‘Wallahi sai ka sakeni, kamal bazan zauna dakai ba.’
Muryarta ta dawo wa Jawwad, hannunshi yasa yana murza k
Ƙirjinshi inda zuciyarshi take ko zai ji sauƙin ciwon da take mishi.
‘Kai da yaranka ba matsalata bane, don ba a kayan ɗaki aka zubo min su ba, bazan zauna wahala da naƙasasshe ba, bayan ga mai lafiya na sona.’
Numfashi Jawwad yake ja da sauri da sauri, ko’ina a jikinshi kyarma yake, juyawa ya yi yana ƙoƙarin hawa mashin ɗinshi, da ƙyar ya samu ya hau, amma kyarmar da hannuwanshi suke yasa ya kasa saka mukullin cikin ƙofarshi. Hannunta ya ji kan bayanshi, riƙe jikinshi ya yi yana ɗauke numfashi.
“Don Allah ka saurare ni, wallahi ina ta nemanku, shekara uku ina nemanku ban san inda kuka yi ba. Jawwad don Allah ka saurareni…”
Take faɗi tana wani irin kuka da Jawwad yake ji har tsakiyar kanshi.
‘Karka saurareta’ shi yake ta maimaitawa cikin kanshi, Allah ya bashi sa’a ya samu ya saka mukullin cikin mashin ɗin ya murza yana tayar da shi. Ɗayan hannunshi yakaiy ya tunkuɗe nata da ke kan bayanshi yana jan mashin ɗin ba tare da ya duba ba ya hau titi.
Yana kaiwa inda zai iya juyawa ya yi kwana yana kama hanyar da zata mayar dashi gida, ko ganin gabanshi baya yi sosai, sau biyu yana kusan jan hatsari, bai damu da zagin da masu motar suke mishi ba. Kawai so yake ya ganshi a cikin gida. Gudun da yake yasa cikin mintina goma ya ƙarasa gida, shigowar da ya yi yana gabje ƙofa ta fara tabbatar da Anty ba lafiya ba.
Da sauri ta fito daga ɗaki, ta ganshi yana zare mukullin mashin, kallo ɗaya ta yi wa fuskarshi da ta yi fari kamar wanda ya ga fatalwa ta ce,
“Lafiya? Me ya faru?”
Girgiza mata kai Jawwad yake yi yana kokawa da numfashin shi.
“Jawda! Kawo min ruwa.”
Anty ta faɗi, tana kama hannun Jawwad ɗin ta zaunar da shi. Bai yi musu ba ya zauna a ƙasa, har lokacin numfashin shi ya ƙi dai-daita. Jawda ce ta fito da ruwa a kofi tana ba wa Anty.
“Yaya… Me ya same shi?”
Jawda ta tambaya tana ware idanuwa cikin tashin hankali. Anty bata ko juya ba balle ta kulata, ruwan ta ba Jawwad daya karɓa yana sha kamar sauƙin shi na tare da ruwan.
“Innalillahi, jinin meye wannan a ƙafarshi?”
Jawda ta faɗi tana tsugunnawa tare da zare takalmin Jawwad ɗin, wani irin yankane a gefen ƙafar ke fitar da jini sosai, ɗankwalin da ke kanta Jawda ta cire ba tare da tunanin komai ba tana dafe wajen da shi.
“Jawwad kai min magana… Me yake faruwa wai? Menene? hatsari kuka yi?”
Anty take tambaya a rikice. Girgiza mata kai yayi yana dafe kanshi da duka hannayenshi.
*****
“Don Allah karki tafi…karki barmu… Wallahi ban san yadda zan yi da su Jawda ba, kinga Abbu ba shi da lafiya. Don Allah mama karki barmu…”
Jawwad ke faɗi cikin kuka yana riƙo hijabinta. Juyowa ta yi ta fisge hijabinta tare da ture shi ya kuwa faɗi kan ɗan yatsan shi na hannun hagu, yana jin ƙarar da ya yi da azabar data shige shi har tsakiyar kanshi.
“Jarabar naci kamar ubanka. Me zan zauna in muku? Ka ɗauka haka na tsara rayuwa da yara kaca-kaca? Allah yaban wata damar da zan yi rayuwa yadda nake so. Ka yi duk yadda za ka yi da su kana jina? Bazan zauna ba, kuma koka nemeni ba samuna za ka yi ba…”
Azabar da hannunshi yake yi bai hanashi binta da kallo ba, ƙarar akwatin da take ja har cikin zuciyarshi.
*****
“Yaya!”
Muryar Jawda ta katse mishi tunanin da yake yi. Buɗe fuskarshi ya yi, yana dafa bango ya miƙe tsaye. Hanyar falo ya nufa, daga Anty har Jawda babu wanda ya hana shi. Bai kuma damu da ciwon da ke ƙafarshi ba. Kai tsaye ɗakinshi ya wuce yana doko ƙofar da ƙarfi kamar zai karyata.
“Ciwon dake ƙafarshi na buƙatar ɗinki…”
Anty ta faɗi.
“Bazai fito yanzun ba kin sani, bazai tsaya ba. Sai dai ko idan Izzat ta dawo ita kaɗai zata iya…”
Jinjina wa Jawda kai Anty ta yi da faɗin,
“Allah ya rufa asiri.”
“Amin.”
Jawda ta amsa. Don sunsan abinda kawai zai iya saka Jawwad shiga yana yi, abu ne da ba’a tattauna shi a cikin gidan, abu ne da yake da haramci mai girma a cikin gidan gaba ɗaya, ko da a bayan idon Jawwad ne kuwa. Falon suka koma, Jawda na ƙarfin halin kunna TV ɗin suka zuba wa ido ba don suna fahimtar abinda ake yi a ciki ba.
*****
Kaduna
A jikin motar Majida ta bar mukullin tana fita tare da doko murfin da ƙarfin da yasa Altaaf runtse idanuwanshi. Fushi take tunda ya ƙi yarda a tsaya a asibiti a duba shi. Ba kuma zai iya faɗa mata rashin lafiyar da yake bata da alaƙa da asibiti ba.
Rumfuna ne sun fi shida cikin gidan an shimfiɗa tabarmi, da yake akwai hali ga abinci da lemuka an fiffito da shi yasa wajen shaƙare yake da mutane. Numfashi Altaaf ya sauke, baya son hayaniya a halin da yake ciki. Inda son samun shi ne ya koma gida ya kwanta a ɗaki shi kaɗai.
Ƙarar shigowar text ya ji a wayarshi. Da sauri ya ɗauko yana dubawa. Ƙaramin tsaki ya ja ganin MTN ne suka aiko mishi da saƙon, gogewa ya yi yana duba saƙon da ke sama. Ya shiga, duk kusan iri ɗaya ne, sun fi guda hamsin duk shige suke da juna, ban haƙuri da neman yafiya, ga alamar ya shiga har an karanta amma kuma babu amsa.
‘Me yasa ba za ka yafe min bane haka Ashfaq?’
Ya faɗa cikin ranshi yana jingina kanshi da gaban motar, runtsa idanuwa yayi hotunan yaran na dawo mishi, zuciyarshi na sake sabon salon dokawa, zazzaɓi sabo na sake lullubeshi. Yana so wani ya faɗa mishi ya kwantar da hankalinshi babu abinda zai faru, ya faɗa mishi zuciyarshi ce kawai take wasa da ƙwaƙwalwar shi.
Amma hotunan yaran da ya ɗauka a zuciyarshi kawai sun ishe shi. Yanajin agogon bomb ɗin da ƙirgawa a cikin kanshi, kamar yana jiran wani abu ne ya fashe da shi gaba ɗaya.
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un.”
Altaaf ya furta cikin neman sauƙi daga yanayin da yake ciki. Ƙwanƙwasa glass ɗin murfin motar ya ji anyi, hakan yasa shi ɗagowa ya buɗe murfin motar.
“Ba dai jikin bane kuma?”
Aslam ya tambaya cikin kulawa. Kai kawai Altaaf ya iya girgiza mishi yana fitowa daga motar.
“Kabar mukullin a jiki.”
Juyawa ya yi yana zira rabin jikinshi ya miƙa hannu ya zaro mukullin yana rufewa. Cikin aljihu ya saka mukullin suna jerawa shi da Aslam suka nufi inda mutane suke ana karɓar gaisuwa. Sama-sama suka gaggaisa da mutane ya ɗauki buta ya yi alwala don ko Magriba bai yi ba yana kuma da tabbacin isha’i ta wuce.
*****
Aslam ne yasa aka kai su masaukinsu, ganin yanayin Altaaf ɗin, raka shi ya yi har ɗakin tukunna ya juya yana komawa. Kwanciya yayi ba don yana jin ko alamar bacci ba. Idanuwanshi ya lumshe yana sauke numfashi, dai-dai lokacin wayarshi ta ɗauki ruri. Bai ko motsa ba ballantana ya yi niyyar ɗauka har ta yanke.
Sake ɗaukar sabon ruri ta yi, hannu yasa ya zarota daga aljihunshi yana dubawa. Babu shiri ya ɗauka ganin Majida ce.
“Majee…”
Ya faɗi muryarshi can ƙasa.
“Baka ci komi ba, ka hito gani nan zan taho bakin kohwa sai ka ansa…”
Ɗan dafe kanshi ya yi.
“Banajin zan iya saka ma cikina komai.”
“Haka nan zaka kwanta da yunwa?”
Ta buƙata, yana jin damuwar da ke cike da muryarta.
“Har na kwanta ne.”
Ya ce a gajiye.
“Mi ke damunka?”
Runtsa idanuwanshi ya yi, jikinshi na wani iri da yadda yake so ya faɗa wa wani damuwarshi.
“Zazzaɓi ne kuma ya sauka, bacci kawai nake son yi…”
“Akwai abinda ke damunka, baka so ka hwaɗi manne kurun, kasan hushi nike dakai baka neman ba, ko baka lahiya kana cin abinci, ba abinda ke shiga tsakaninka da abinci…”
Ya manta Majida ta san shi, ko ya ce tasan Altaaf, ta san mutumin da ya koma kamar yadda ta san kanta, baya kuma fatan hakan ya canza. Zuciyarshi ta fara mishi ciwo da abinda zai furta mata
“Ina son ganin yaran mu ne Majee, ina son riƙe nawa ɗan a hannuna kamar kowa, sai yaushe zai faru damu?”
Shirun da ya biyo bayan maganar da ya yi yasa shi cire wayar daga kunnenshi ya duba don ya ga ko ta yanke ne, ya ga tana yi shirun dai Majida ta yi ya kuma san maganganun shi sun taɓa ta. Muryarta can ƙasa ta ce,
“Mi kake so in yi?”
Girgiza kai ya yi kamar tana ganin shi.
“Kin saurareni, shi ne kawai buƙatata a yanzun. Sai ki kwanta kuma karki bari maganganuna su dameki…”
“Hmm…”
Ta faɗi daga ɗayan ɓangaren
“Majee…”
Ya kira sunanta cike da yanayoyi da dama. Yasan tana saurarenshi duk da bata amsa ba. Hakan yasa shi ci gaba da faɗin,
“Ina sonki…ko me zai faru ina sonki wallahi.”
Da sauri ta ce,
“Kana bani tsoro, don Allah ka hito in ganka, wai minene?”
Ta ƙarasa maganar muryarta na karyewa, tana saka zuciyarshi matsewa a ƙirjinshi.
‘Ka sata kuka, hankalin ka ya kwanta.’
Wata murya ta faɗa mishi cikin kanshi. Tashi ya yi zaune.
“Kawo min wani abu, bari in fito.”
Da sauri ta ce,
“Mi kake so?”
“Komai ma…”
Ya ƙarasa yana mikewa tsaye, yana ji ta kashe wayar daga ɗayan ɓangaren. Ba don zai ci ba yace ta kawo, sai don in bai karɓa ba yasan ba zata daina tunanin wani abu daban na damunshi ba. Fita yayi ƙofar boys quarters ɗin da aka sauke su ya sake kiran Majida ya faɗa mata ta zagayo ta bayan gidan saboda mutane.
“Ka yi sallah kau?”
Ta bukata da ta ƙaraso, kai ya ɗaga mata yana karɓar ledojin da ke hannunta.
“Yawwa to, sannu.”
Duk da kallon fuskarta yake yi ya ƙi yarda su haɗa idanuwa. Hannu ya kai yana ja mata hanci, ta ture hannunshi tana dariya tare da matsawa.
“Sai wani ya ganka?”
Matsawa yayi yana haɗe space ɗin da ke tsakanin su. Ya kamo hannunta.
“Ba ruwana da wani, ni da matata.”
Kanta ta sunkuyar ƙasa, ɗan murmushi ya ƙwace mishi, kunyar Majida kan bashi mamaki, shekarun nan basu sa ta daina jin kunyarshi ba. Ranƙwafawa ya yi ya sumbaci gefen kuncinta.
“Ki je ki kwanta. Ki kula min da kanki.”
“Sai da sahe… Allah ya ƙara lahiya.”
Ta faɗi har lokacin kanta na ƙasa, hannunta ya saki yana amsawa da
“Amin…”
Tsaye ya yi sai da ya ga ta sha kwana tukunna ya koma cikin gidan zuwa ɗakin da za su kwana. Ledojin ya ajiye a ƙasa yana zama kan gado, wayar da ke hannunshi ya duba yana danne-danne. Kafin ya tsinci kanshi da kiran lambar Ashfaq. Ƙirjinshi ke dokawa tare da bugun wayar.
“Meye?”
Ya ji an faɗi, sai da ya ɗan zabura saboda bai taɓa zaton za’a ɗaga wayar ba. Hannu yasa yana share zufar da ta fara fito mishi.
“Ashfaq?”
Ya kira yana son tabbatar da ko ya yarda wayar ne wani ya ɗauka, ko kuma Tariq ne ya ɗaga. Jin an yi shiru yasa shi sake faɗin,
“Faq?”
“Meye wai?”
Wani numfashi mai nauyi Altaaf ya saki, muryar Ashfaq ɗin ta canja mishi, sai dai ba zai iya tuna asalin yadda take a da ba balle ya haɗa ta da ta yanzun. Da ya san Ashfaq zai ɗaga da ya tsaya ya tsara abinda zai faɗa mishi, ya kuma san in har damar nan ta wuce shi da wahala ya ƙara samun irinta.
“Babu wanda zan kira, babu wanda na yarda da shi a halin yanzun…”
“Duk shekarun nan wa kake kira? Ina matarka?”
Ashfaq ya tambaya ta ɗayan ɓangaren da alamun da ke nuna gab yake da katse kiran.
“Karka kashe Ashfaq…don Allah karka kashe. Bazan iya faɗa mata ba, bazan iya faɗa wa kowa ba ko da na tabbatar da abinda nake shirin faɗa maka…. Saboda bansan ta ina zan fara ba… Ɓangare ne dana ke tunanin na rigaday na wuce…”
“Ka bar shan sigari ka koma zuƙar hayaƙin maganin sauro ko Altaaf?”
Ashfaq ya yi maganar cikin yanayin da ke fassara ‘anya kana da hankali’. Ɗaga mishi kai Altaaf ya yi cike da yarda don shi kanshi ji yake in dai da hankalinshi to yana gab da barin shi. Sigarin da Ashfaq ya kira na saka shi wasa da yatsun hannun shi, yana buƙatar ta fiye da komai a yanzun.
“Ina tunanin ina da yara…’yan biyu Faq.”
Yana jin dariyar da Ashfaq yake yi ta cikin wayar, dariya yake yi sosai, da ya yi kamar zai bari sai ya sake dasa sabuwa, cikin dariyar ya ce,
“Tariq na tunanin ya ga Yasir, kai kana tunanin kana da yara guda biyu… Ni ina kwance da harbi a jiki….”
Dariya ta hana Ashfaq ƙarasa maganar, da ƙyar ya samu ya ci gaba da faɗin,
“Kuma ka rasa wa zaka kira ka faɗa wa sai ni? Wayama muke ko? Yaushe muka zo nan?”
Altaaf ma bai san lokacin da dariya ta kubce masa ba. Sosai suke dariya shi da Ashfaq ɗin kamar sababbin mahaukata, kafin Altaaf ya goge ƙwallar da ya ji tana bi mishi fuska da bai san ko ta mecece ba.
“Ban san yadda zan yi ba…in yarana ne…”
“Ka daina magana kamar baka san hakan zai iya faruwa ba. Ka je ka tabbatar idan yaranka ne tukunna…”
Kai Altaaf ya ɗaga yana jin yadda komai ya sake danne shi, wani irin sabon tashin hankalin da ya saukar mishi tare da tunanin komawa Kinkiba.
“Nag…”
Ya fara, Ashfaq ya yi saurin katse shi.
“Karka sake kirana, karka sake damuna da saƙonni… Yafiya abu ne me kyau na sani, hali ne na mutane masu kirki. Na jima da manta yadda duka biyun suke. Ba zai faru a tsakanin mu ba.”
Kafin ya ce wani abu, Ashfaq ya kashe wayar daga ɓangarenshi. Kan gadon Altaaf ya ajiyeta yana kwanciya ya haɗe jikinshi waje ɗaya, kamar yadda yake jin komai ya haɗe mishi, sabon amai na taso mishi, ga zufa da yake ji har cikin tafukan hannunshi saboda tashin hankali. Inda zai samu sigari daya rage zafi.
Saidai a yanayin da yake ji ko daga kan gadon ba zai iya sakkowa ba ballantana ya fita wajen neman sigari. Rufe idanuwanshi ya yi, maimakon ya samu sauƙi sai ma hotunan yaran nan da ya cika mishi zuciya. Bai yi kokarine kauda su ba, ƙarfin shi na yau gaba ɗaya ya gama ƙarewa.
**
Abuja
Amai ta ji yana neman taso mata, da ƙyar ta dafa kujera tana miƙewa, da bin bango ta gano ɗakinta, kai tsaye banɗaki ta wuce, ba wani abu bane a cikinta, don haka ba ƙaramar wahala ta sha ba wajen kakarin aman, har haƙarƙarinta amsawa yake yi. So ta yi ta ɗan watsa ruwa ko zata samu sauƙi-sauƙi amma bata da ƙarfin da zata cire kayan jikinta ma.
Fitowa ta yi tana janyo ƙofar banɗakin, nan kan kafet ta kwanta, hawaye masu zafi na bin gefen fuskarta. Bata zaci Rafiq zai tsallaketa ba tare da ya ce komai ba, ya kamata ya ce wani abu, duka labarinta ta juye mishi, sirrin da daga shi sai Samha ne suka sani. Ba zata manta lokacin da suka haɗu da Samha ba, wajen siyan ankon bikinsu da Rafiq ne.
*****
“Ki ɗauki purple ɗin nan, kin ga muma ita muka fitar ankon sister ɗina…”
Samha ta faɗi, ɗan murmushin ƙarfin hali Tasneem ta yi, don shigowarta shagon kallo ɗaya tai wa Samha ta ɗauka zata yi girman kai, ba don kyan da take da shi ba kawai, sai don yanayinta gaba ɗaya da yake nuna ta fito gidan da kuɗi suke zaune. Amma sai ta bata mamaki da ta yi mata magana.
“Bari in ɗauke ta kawai…”
Tasneem ta faɗi tana zarar guda huɗu, ita bikin gaba ɗaya ba shi bane matsalarta, fitar da anko bashi bane damuwarta, sai dai su Azrah ba za su barta ta huta ba in bata fito da shi ba. Auren da take da tabbacin ba wani daɗewa zai yi ba. Kuɗin ta biya tana fitowa daga shagon, sai dai me, kamar jira hawayen da ke shirin kubce mata suke yi. Hannu tasa tana gogesu, amma kamar tunzurasu take.
Tun da aka kawo kuɗin aurenta, kamar an buɗe mata ɓangaren da take tunanin ya daɗe da bushewa ne, sai yanzun zaɓukan da ta yi suke danneta, sai da ta ɗanɗana soyayyar Rafiq tasan ta yi babban kuskuren da zai zame mata tabo na har abada. Kausar ce ƙawar da take da ita nagartacciya a rayuwarta. Mamansu Kausar da kanta ta ja ta gefe wajen walimar bikin Kausar ɗin ta roƙeta da ta ƙyale mata yarinya ta zauna gidan mijinta lafiya.
Ta ƙaunaci Kausar da zuciyarta ɗaya, ta kuma girmama roƙon mahaifiyarta, bata sake nemanta ba, ko kalar gidanta bata sani ba. Sauran tarkacen ƙawayen da ta yi ma, soyayyar Rafiq ta sa duk ta watsar, sai dai ba zai gyara komai ba. Bazai dawo mata da darajarta ba, Haidar ya soma ƙwace babban ɓangare daga ciki, sauran kuwa da kanta ta rarraba a titi.
Kuka take sosai har sai da ta daina tafiya, mutane sai kallonta suke, in ma magana suke bata ji su ba, ga ƙirjinta kamar zai rabe gida biyu. Ji ta yi an riƙo hannunta ana janta, runtse idanuwa ta yi tana buɗe su da sauri, kayan jikin Samha ta fara ganewa, bata yi gardama ba, hawayenta kuma ba su daina zuba ba. Haka ta bita har bakin wata mota, buɗe mata Samha ta yi da alamar ta shiga. Bata yi musu ba ta shiga, ba tare da tunanin komai ba.
Ɗayan ɓangaren Samha ta zagaya ta shiga ta kunna motar ta ja suka fita daga cikin kasuwar. Waje ta samu gefe ta yi parking tukunna ta kalli Tasneem da ke kuka har lokacin.
“Me yai zafi ke kuwa? Kuka a cikin kasuwa? Kina ganin yadda mutane suke kallonki har an fara taruwa?”
Samha take faɗi da damuwa a muryarta. Kallonta Tasneem ta yi da fuskarta da har ta kumbura ta ce,
“Kallon da mutane suke min ne ƙarshen damuwata…”
“Ki gwada ni, me yake damunki?”
Girgiza kai Tasneem ta yi, bata san Samha ba, ta yi zaɓuka marasa kyau da ba zata iya komawa baya ta gyara ba, akwai wani abu tare da ita da yake faɗa mata bata da asara don ta juye wa Samha duka damuwarta, tana son faɗa wa wani, ko zata daina jin nauyin da ƙirjinta yake mata.
*****
Samha bata taɓa sa ta ji daban ba, bata taɓa ce mata kin yi kuskure ba, don ta gane ita da kanta ta san ta yi kuskuren ba sai ta sake maimaita mata ba. Samha ƙawace da Allah ya jeho mata lokacin da take cikin halin buƙata. Hannu tasa kan cikinta tana runtsa idanuwanta.
“Ina kaunarka tun kafin fitowar ka, ƙila kai ba zaka guje ni ba, ba za ka riƙe ni da kuskuren da na yi ba…”
Ta faɗi hawaye na sake zubo mata. In Rafiq na son magana da ita yasan inda zai sameta, ta wa kanta alƙawari in ba tsautsayi ba, ba zata sake nuna mishi fuskarta ba tunda baya son ganinta, ta kuma cancanci dukkan hukuncin da yai niyyar ɗauka. Shi ne abinda take nanata wa zuciyarta da ta ƙi yarda, banda bori babu abinda take mata. Tana gaya mata Rafiq yai musu komai su biyun, amma karya rabu dasu.
*****
Kanshi dafe yake cikin hannuwanshi, numfashin shi yake son saitawa amma abin na neman gagara. Hakan yasa shi sake jinjina wa su Fawzan, kanshi ya ɗauki ɗumi, ga ƙirjinshi da ya yi nauyi yana zafi kamar ana hura mishi wuta saboda rashin wadatacciyar iska. Miƙewa tsaye ya yi yana zuwa ya buɗe windows ɗin ɗakin gaba ɗaya, ya je ya kunna fanka yana sake kai gudun AC ɗin ƙarshe, amma bai samu numfashin shi ya koma dai-dai ba.
Zama ya yi ƙasa yana kwantar da kanshi da ke ciwo kamar zai tarwatse kan kafet. Runtsa idanuwanshi ya yi gam, ko zai daina ganin Tasneem da jerin mazajen da ba zai iya ɗora musu fuskoki ba. Zuciyarshi na ci gaba da tafasa. Ɗagowa ya yi zumbur kamar wanda aka tsikara.
“Ya akai na sani? Ya akai na gane?”
Ya tambayi kanshi, amma ya rasa amsa, wani haske ya ji ya gilma mishi ta cikin idanuwanshi, hakan yasa shi rufe su, sai dai hasken har cikin kanshi ya jishi da wani irin ciwo da yasa ya dafe kan yana kiran sunan Allah. Numfashi yake sama-sama yana samu kan na ɗan mishi sauƙi. Da rarrafe ya ƙarasa wajen gadonshi ya kama gadon ya hau.
Wayarshi yake nema, bai ganta cikin ɗakin ba, tunawa ya yi tana falo ya barta inda suka zauna da Tasneem. Yana buƙatar wayar, amma baya son ganin Tasneem, ko kaɗan baya son ganinta. Tashi ya yi yana tsayuwa na ‘yan mintina don ya tabbatar zai iya tafiya ba tare da ya faɗi ba. A hankali ya buɗe ƙofar ɗakin yana takowa cikin sanɗa.
Fara dubawa ya yi ya ga bata falon, ga wayarshi nan ajiye kan kujera, da sauri ya ɗauki wayar yana zira takalmanshi suma da suke cikin falon ya fice daga gidan gabaki daya. Ƙofar gida ya yi tsaye ba tare da ya san inda zai je ba. Tambayoyi yake da su da yawa, ya rasa me yasa yake da tabbacin Nuri ba zata amsa mishi ba.
Wayar ya danna yana cire mukullin jiki, lambar Muneeb ya lalubo ya kira yana karawa a kunnen shi. Bugu biyu Muneeb ɗin ya ɗaga.
“Rafiq.”
Ya faɗi ta ɗayan ɓangaren da sigar gaisuwa.
“Ka zo gidana yanzun…”
Rafiq ya faɗi a ƙagauce.
“Lafiya dai ko? Rafiq me yake faruwa?”
Hannu Rafiq yasa ya murza goshin shi inda yake jin wani ciwo na daban na tattaruwa.
“Ka zo kawai… Zan faɗa maka in ka zo… Don Allah ka yi sauri…”
“Gani nan, ina wajen aiki ne, zan kai mintina talatin ko da zan ƙaraso. Zaka iya jira har lokacin? In ba zaka iya jira ba in kira Faruk ya fi kusa…”
Girgiza kai Rafiq yayi kamar Muneeb ɗin na ganinshi kafin ya ce,
“Zan jira…”
Yana sauke wayar daga kunnenshi ya sakata cikin aljihunshi. Ya kasa tsayuwa waje ɗaya, da ka ga yadda yake kai kawo ba sai an faɗa maka ba ka san yana cikin yanayi na damuwa.
“Abu ɗaya na buƙata Neem, gaskiya kawai na ce ki faɗa min kafin in buƙaci soyayyarki. Me yasa? Me yasa za ki min haka?”
Rafiq ya faɗi yana girgiza kanshi. Kafin zuciyarshi ta yi wata irin dokawa da ya ji har cikin bakinshi.
“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”
Ya dinga maimaitawa yana runtsa idanuwanshi ko zai samu ta ɗan nutsu, amma kamar ma yana tunzurata. Ba tare da ya buɗe idanuwanshi ba ya ciro wayarshi daga aljihu yana ɗan dumtse ta tukunna ya buɗe idanuwa. Lambar Nuri ya kira.
“Assal…”
Bai bari ta ƙarasa ba ya katse ta da faɗin,
“Nuri ina Fawzan?”
Shirun da ya ji ta yi na ƙara gudun zuciyarshi, wani irin tsoro marar misaltuwa na ziyartarshi.
“Yaya…”
Numfashin da Rafiq ya sauke sai da ya ji ƙafafuwanshi na son kasa ɗaukarshi.
“Karka sake tsorata ni haka Fawzan… Na yi yarinta da bugun zuciya.”
Dariyar Fawzan ɗin ta daki kunnenshi tana sauƙaƙa mishi wasu ɓangarori da bai san suna mishi ciwo ba sai yanzun.
“Hanyar kace ta faɗa min yadda kake sona ko?”
Hararar shi Rafiq ya yi kamar yana ganinshi.
“Zaka fara surutun ka… Ya jikin ka?”
“Ni na warke…Alhamdulillah”
“Allah ya ƙara sauƙi. Ka dai zauna sai an sallame ka. Kana jina?”
“Yes Sir.”
Fawzan ya faɗi cike da tsokana, amma Rafiq ɗin yasan ya ji shi. Kashe wayar Rafiq zai yi Fawzan ya ce,
“Ball ɗin yau ta yi kyau ko kuwa?”
Nuri da Rafiq yasan tana nan zaune tare da Fawzan ɗin zata ɗauka yana tambayarshi labarin wasan ƙwallon ƙafa ne. Amma ya gane abinda Fawzan yake tambayarshi. Yana tambayane idan komai lafiya, yana kuma tabbatar mishi da zai saurara ba tare da ya bari Nuri ta gane komai in baya so ba.
“Karka damu…ba wani abu bane da bazan iya ɗauka ba In sha Allah, kai dai ka huta kawai.”
Rafiq ya faɗi, rashin Fawzan ɗin ne yasa shi ya kira Muneeb, ko cikin abokanshi Muneeb ne kawai yake sanin kaɗan daga cikin sirrikanshi. Gara ya raba damuwarshi da Fawzan ko ba komai ɗan uwanshi ne, ko da ba zai bashi shawara ba.
“Ko dai ya aka tashi ka faɗa min, ina nan.”
Jinjina kai Rafiq ya yi, Fawzan na nufin in har komai ya cakuɗe kiranshi kawai Rafiq ɗin zai yi. Sauke wayar ya yi daga kunnenshi yana mayarwa cikin aljihu. Duk da jin muryar Fawzan ya nutsar da shi ta wani ɓangaren, sai da ya sauke wayar ne ya ji har lokacin zuciyarshi bata daina dokawa ba.
‘Zafira’ wata murya ta faɗa mishi can ƙasan zuciyarshi, baya taɓa jin faɗuwar gaba irin haka idan ba wani abu bane ya sami wani makusancin shi. Sai da ya ɗauko wayarshi yake tunanin rabon da ya ji muryarta ma. Damuwarshi ta danne son jin lafiyarta a satikan nan.
Kiranta yayi har ta yanke bata ɗauka ba. Sai da ya kira sau huɗu tana yankewa bata ɗauka ba, wani abu na faɗa mishi ba lafiya ba. Babu yadda za’ai lafiya ƙalau ta ƙi ɗaga wayarta. Ko bacci take zata ji ringing ɗin wayar ai. Bai haƙura ba ya ci gaba da kira, da duk yankewar da zata yi bata ɗauka ba da yadda zuciyarshi ke ƙara jagule mishi.
Na lokacin ya manta da tashi damuwar da duk wata tambaya da yake da ita, kawai so yake Zafira ta ɗaga wayar ya ji tana lafiya. Komai zai zo da sauƙi in babu abinda ya sameta. Zai kamo bakin zaren tashi matsalar, amma yana buƙatar sanin ‘yan uwanshi dukansu lafiyarsu ƙalau. Yana buƙatar wannan nutsuwar.
A haka Muneeb ya ƙaraso ya same shi, lokacin ya kira Zafira babu adadi bata ɗaga ba. Muneeb na fitowa daga mota ya ce,
“Lafiya wai? Ka bani tsoro wallahi.”
Girgiza mishi kai ya yi,
“Ban san me ya samu Zafira ba, na kirata ya fi sau goma bata ɗagawa…”
Runtsa idanuwanshi Muneeb ya yi kamar Rafiq ya watsa mishi wuta, kafin ya matsa baya taku biyu yana buɗe idanuwanshi da wani irin yanayi akan fuskarshi. Jin ya yi shiru yasa Rafiq ɗauke idanuwa daga kan wayar dake hannunshi yana mayarwa kan Muneeb. Kafin ya ware idanuwanshi cikin gane abinda ya yi.
“Karka damu…”
Muneeb ya faɗi, duk da haka akwai wani yanayi a muryarshi da yasa Rafiq saurin tura wa Zafira gajeran saƙo da faɗin,
‘In kin zo ki kira ni.’
Kafin ya mayar da wayar gaba ɗaya cikin aljihunshi duk da har lokacin ba wai zuciyarshi ta nutsu bane, sai don shi mutum ne da yake duba halin da mutanen da ke kusa da shi zasu shiga akan abinda yake aikatawa kafin nashi yanayin, duk da a wata biyun nan ya rasa kanshi. Muneeb ɗin ya ƙi haɗa ido da shi.
“Ka nisanta ni da unguwar nan sai mu yi magana.”
“Ina za mu je?”
Muneeb ya buƙata yana juyawa wajen motar shi tare da buɗe murfin ya shiga mazaunin direba, sai da Rafiq ya shiga ya rufo shima, tukunna ya ce,
“Ko ina banda nan.”
Kai kawai Muneeb ɗin ya ɗaga mishi yana jan motar baya ya samu ya juya yana hawa titi. Rafiq kam jingina jikinshi yayi sosai da jikin motar. Ya rasa tambayar daya kamata ya fara yi wa Muneeb. Yana son sanin yadda akai ya gane Tasneem ba budurwa bace ba. Sai dai babu yanda za ai kalaman su fara fitowa kan su gauraya da iskar da zata gifta ta kusa da Muneeb ma ballantana ya sani.
Sirrin shi na da muhimmanci a wajenshi. Ballantana sirrin daya shafi gidan aurenshi, sirrin daya shafi Tasneem. Bai san lokacin da suka ɗauka ba. Kawai ji ya yi Muneeb ya tsayar da motar. Ɗagowa Rafiq ya yi ya gansu a tsaye bakin Blue Cabana. Kallon Muneeb ya yi.
“Haka nace wani waje, sai ka kawoni restaurant?”
Ɗan ɗaga kafaɗunshi Muneeb ya yi yana zare mukullin motarshi.
“Nan ya fara zuwa raina.”
Bai jira amsar Rafiq ɗin ba ya buɗe ya fito, hakan yasa shima ya fito yana rufe murfin. Mukullin Muneeb yasa ya kulle motar tukunna suka jera suna shiga wajen tare da Rafiq. Ɓangaren manyan mutane da akafi kira da VIP Muneeb ya nufa don ko basu da maganar da za su yi nan suke zama.
Kuma bayason wani a wajen ya gane Rafiq. Komai zai warware in wani ya gane Rafiq ɗin, duk da ba ƙaramin kallo za kai mishi ba kafin ka gane shi. Daga shiga har yanayin askin shi, amma mutane basa gajiya da ba Muneeb mamaki. Lemuka yasa a kawo musu duk da yasan da wahala Rafiq ɗin ya sha.
Daukar kofi ɗaya Muneeb ya yi yana kurɓa don ya jiƙ maƙoshin shi. Rafiq na zaune da wani nisantaccen yanayi a tare da shi. Sake kurɓar lemon Muneeb ya yi yana shirin haɗiyewa Rafiq ya ce,
“Na taɓa aure a baya?”
Lemon Muneeb ya ji ya bi wata hanya ta daban yana sarƙeshi, lokaci ɗaya ya fara tari, babu shiri ya kwankwaɗe duka abinda ke cikin kofin yana ƙara zuba wani, ko motsi Rafiq bai yi ba, kallon Muneeb ɗin yake har tarin ya tsagaita mishi yana gyaran murya. Hannu ya kai yana goge idanuwanshi da suka kawo hawayen wahala.
“Me ya sa kake min tambayar nan? In ka taɓa aure kai baka sani ba, ni ne zan sani?”
Gyara zama Rafiq ya yi, ba sai ya karanci ilimin gane yanayin ɗan Adam bane zai fahimci yanayin Muneeb ya nuna alamun rashin gaskiya. Sai dai ya rasa dalilin da yasa zai mishi ƙarya.
“Saboda babu abinda yake dai-dai a rayuwata Muneeb, zan iya tuna har yarinta ta, abotarmu, in ba na fara samun taɓin hankali bane, na san lokutan da muke fita kuma nine nake tuƙin, lokaci ɗaya na tashi na fito na shiga mota na kasa tuƙawa? Me yasa? Ban yi magana ba saboda Nuri da kanta ta ce min sai dai in na manta dama can driver gareni…sai nake ɗauka a tunanina ne kawai… Abubuwa da yawa suna faruwa da nake jin akwai tushen su, amma na rasa… In su Nuri sun ƙi faɗa min, me yasa kai ba zaka faɗa min ba?”
Wasa Muneeb yake da cup ɗin hannunshi ya ƙi ɗago da kai, zufa yake ji tana taruwa a bayan wuyanshi, bai san yadda zai kalli Rafiq ya yi mishi ƙarya ba, bai kuma san yadda zai faɗa mishi gaskiya ba, sai dai baya tunanin zai yafe mishi lokacin nan idan ya gane ƙaryar da ya yi mishi. Bayan haka akwai alƙawarin da su duka suka ɗaukar wa Nuri na ganin sun kare Rafiq ɗin daga gaskiyar.
Kallon shi Rafiq yake yi, shirun shi na ƙara tabbatar mishi da cewar akwai abu mai girma da su duka suke ɓoye mishi. Yawo yake da tunanin shi, amma ya kasa tuna komai, baya ganin komai a wannan ɓangaren sai ƙaton filin da babu komai a ciki. A ɓangare ɗaya kuma ya fara tunanin wani abu na damun ƙwaƙwalwar shi, ko cutar mantuwar da yake ganin tana kama tsofaffi a fina-finai na ƙasar waje ce ta tsallako Nigeria ta fara sauka akanshi.
“Ni Engineer ne ko?”
Ya tambaya yana son tabbatarwa, a hankali Muneeb ya ɗaga mishi kai ba tare da ya kalli fuskarshi ba.
“Ka yi soyayya da Zafira?”
Da sauri Muneeb ya ɗago kanshi yana kallon Rafiq ɗin.
“Kun yi soyayya ko bakuyi ba? Ina son sanin taɓin hankali bai same ni ba.”
Rafiq ya ƙarasa, don ba don Tasneem ta bashi labarin da ta bashi ba, a yanzun da suke zaune daya fara tunanin ko darensu na farko ba gaskiya bane, a tunanin shi ne kawai.
“Mun yi.”
Muneeb ya faɗi yana kurɓa lemonshi, kamar yana son wanke kalmar daga harshen shi.
“Ta yi aure, shekaru biyu kenan, me yasa ba za ka manta taba? Me yasa ba zaka haƙura da ita ba?”
Girgiza mishi kai Muneeb yake yi.
“Karkai haka Rafiq, ba saika raba raɗaɗin da kake ji tare da ni bane zan san kana jinshi. Ba saika fama min tabon da nake fama da shi ba…”
Dafe kanshi Rafiq ya yi cikin hannuwanshi, yana jin da gaske wani abu na damun shi ko da ba taɓin hankali bane ba. Ɗagowa ya yi yana kallon Muneeb da idanuwanshi da suka sauya launi ya ce,
“Don Allah ka faɗa min gaskiya, kasan wani abu da ni ban sani ba.”
Jinjina mishi kai Muneeb ya yi.
“Na sani, amma bazan iya faɗa maka ba.”
Muneeb ya ce yana gyara zamanshi kan kujerar da yake. Amsar da yaba Rafiq ɗin ita ce dai-dai a yanzu. Bai mishi ƙarya ba, bai kuma karya alƙawarin da ya yi wa Nuri ba. Kallon shi yake cike da tausayi da wani abu da ya fi ƙarfin fassara.
“Ka bar gaskiyar nan inda take Rafiq, shine kwanciyar hankalin kowa…”
Numfashi Rafiq ya sauke yana miƙewa. Don ji yake kanshi zai iya tarwatsewa saboda tunanin da ya yi mishi yawa. Muneeb ɗin ma tashi yayi ya sa hannu ya zaro wallet ɗinshi a aljihun bayan wandonshi. Kuɗi ya ƙirga ya ajiye kan table ɗin wajen yana bin bayan Rafiq ɗin da har ya fita daga ɓangaren da suke.
Tafiya kawai Rafiq yake baya kallon gaban shi, kawai so yake ya ji shi a waje, don iskar da ke wajen ta mishi kaɗan. Bai kula da ‘yan mata huɗun da suka shigo wajen ba suka yi karo da ɗaya, har jakar da ke riƙe a hannunta ta faɗi ƙasa.
“Ya Salam…”
Ta faɗi tana tsugunnawa.
“Yi haƙuri don Allah…”
Rafiq ya faɗi, ɗago kai ta yi tana buɗe baki, da alama magana zata yi amma ta kasa cewa komai, yanayin da sau ɗaya ya taɓa jin shi ya kuma manta dashi yana barin wajen ya dawo sabo, ya gane budurwar, ya taɓa ganinta a KFC kwanakin baya. Akwai wani abu tattare da ita da yake ganin ya sani, yana jin ya santa da daɗewa, amma ya kasa tuna a ina ne.
“Don Allah na sanki?”
Ya tambaya. A hankali ta girgiza mishi kai, jakarta ta ɗauka tana miƙewa. Daƙuna fuska Rafiq ya yi, koma a ina ne ya santa.
“Ke kin sanni?”
Ya sake tambaya dai-dai lokacin da Muneeb ya ƙaraso yana faɗin,
“Rafiq? Lafiya?”
Girgiza mishi kai Rafiq ya yi har lokacin fuskarshi a daƙune. Ganin kallon da yarinyar take wa Rafiq ɗin ne kamar ta gane shi yasa Muneeb tura shi.
“Muje…”
Tafiyar kuwa suka yi, amma sai da Rafiq ya juyo ya sake kallonta, yana da tabbacin ya santa koma a ina ne, har cikin ƙasusuwanshi wani irin kusanci a tsakaninsu da bai taɓa ji a tare da wani ba.
“Na san ta Muneeb, ko a ina ne ma na santa.”
“Baka santa a ko’ina ba.”
Muneeb ya faɗi da tabbaci a muryarshi. Rai a ɓace Rafiq ya ce,
“Ban santa a ko’ina ba, ko kuma tana cikin gaskiyar da ba zaka iya faɗa min ba?”
Mota Muneeb ya buɗe ya shiga, faɗa Rafiq yake nema ya ga alama, yana kuma da duk wani dalili da zai yi hakan, amma ba zai bashi abinda yake so ba, ba zai biye mishi ba. Da yasan abinda yake son tsokanowa da ya haƙura da sanin gaskiya, komin hargitsin da rashinta yake haifar mishi a yanzun. Ya kai mintina biyar da zama kafin Rafiq ya shigo yana jan murfin motar kamar shi ya yi mishi laifi.