HIKAYAR ABDULLAHI MASUNCI DA ABDULLAHI ƊANRUWA
Abdullahi ya kasance masunci, wanda yake da mata tasa ɗaya da 'ya'ya tara. Ya kasance talaka, bai mallaki komai ba a duniya, face komarsa ta kamun kifi.
Kullum yakan tafi bakin teku ya jefa koma, idan ya kama kifi kaɗan sai ya sayar ya yi wa iyalinsa hidima da 'yan kuɗin da Allah ya hore masa a wannan rana. Haka kuma idan ya kama kifi mai yawa sai ya sayar ya kashe kuɗin duka wajen sayen abinci da nama da kayan marmari iri-iri, ya kai gida su yi ta. . .
Ma Sha Allah. Allah ya ƙara basira.
#haimanraees
Masha Allah