Alƙali ya cewa Malam Hassan ya zauna. Daɓas haka ya zauna, duk tufafin jikinsa sun jiƙe da zufa..
Likita ya ce, "Ya maigirma mai shari'a na gama bayanina zan iya tafiya?" Alkali ya ce, "Za ka iya tafiya."
Malam Hassan ya sake tashi tsaye ya ce, "Ya mai shari'a ina roƙon alfarmar wannan kotu mai adalci ta tuhumi matata Asabe inda ta samo waɗannan yaran tun da an ce ni har abada ba zan iya haihuwa ba."
Da sauri Asabe ta tashi tsaye ta ce, "Wallahi duk wanda ya faɗi wannan maganar. . .