Sai da Asabe ta gama shan kukanta sannan ta ci gaba, "Lokacin da mijina ya gan ni da ciki ba ƙaramin daɗi ya ji ba, har sujjadar nuna godiyarsa ga Allah Ya yi. Ya rinƙa hidimta mini, ya hana ni yin duk wani aikin wahala, wani lokacin idan na ga ɗawainiyar da yake ta yi da ni alhali ba cikinsa ba ne a jikina sai na ji wani iri a zuciyata. Bayan na haihu Dantani ya ci gaba da zuwa wajena muna yin abin da muka saba, har sai da na haifi ƴaƴa biyar amma babu ko. . .