"Shekarata ashirin da yin aure, amma ban taɓa samun haihuwa ba. Wannan matsalar tana yawan damuna, na sha zuwa wajen likita ya gwada ni, amma abu ɗaya yake faɗa min shi ne; lafiyata ƙalau kawai lokacin haihuwar ne bai yi ba, amma matana sun ƙi yarda sam a yi musu gwajin a ga lafiyarsu kuma sun hana ni ƙarin aure wai lafiyarsu ƙalau amma a cewarsu. Watarana ina zaune a office abin duniya ya ishe ni, sai na shirya na tafi wajen aminina tun na yarinta, domin na faɗa masa matsalata ko yana da shawarar zai. . .