"A fusace na tashi tsaye na sa ƙafa na harbar da Dije na ɗauki wayata na kira DPO cikin ƙanƙanin lokaci ya bayyana a cikin gidana tare da yaransa. Nan take na ba shi umarnin tafiya da matana har da Dije. Wasu daga cikinsu suka je asibitin da aka kai matata suka taho da likitan da ya karɓi cin hanci daga wurinsu.
"Cikin nutsuwa DPO ya rinƙa bincikarsu ɗaya bayan ɗaya suna faɗa masa duk yadda abin ya faru, matar da suka saka ta jefar da jaririyar ce kaɗai ba a samu ba. Wai ta. . .