Da Malam Hassan ya ga kawai so take ta tayar musu da fitina da safiyar nan, sai ya cewa Hauwa'u, "Ni na yi gaba sai kin taho." Ya fita daga ɗakin da sauri, Asabe ta watsawa Hauwa'u wani irin kallo ta ja dogon tsaki ta ce, "Ai indai ina raye a gidan nan, ba ki isa ki samu wannan tagomashin daga wajen Malam ba." Ta fice daga ɗakin ta bar Hauwa'u a tsaye riƙe da hijabi.
Zama ta yi a gefen gado tana tunanin irin wannan rayuwar da take yi a gidan Malam Hassan, ba ta. . .