Yayin da ƴan'sanda suka isa police station da Malam Hassan, kai tsaye ofishin DPO suka wuce da shi. Yana rungume da jaririyar a ƙirjinsa, jikinsa sai faman rawa yake kamar mazari.
A kan kujerar da take gaban tebur ɗin DPO aka ba shi umarnin zama, bayan ya zauna sai ya kwantar da jaririyar a kan cinƴarsa ya ƙura mata idanu sai sharar barcinta take hankalinta kwance, tausayinta ya mamaye zuciyarsa ba zato ya ji ƙwallar tausayinta ta taru a cikin idanuwansa..
Kyakkyawa ce sosai, kallo ɗaya za ka yi mata ka tabbatar da haka, yanayin tufafin da suke. . .