Malam Hassan ya yi tsaye yana kallonta fuskarsa shimfiɗe da mamaki. "Asabe ya na ga kina ja da baya kamar kin ga dodo?"Cike da masifa ta ce, "Ya ba zan ja da baya ba? Ka fita kai kaɗai kuma na ga ka dawo tare da jaririya ai dole ka ba ni tsoro."Malam Hassan ya yi murmushi ya kalli jaririyar sannan ya kalli Asabe ya ce, "Wannan jaririyar da ki ke gani wata kyauta ce ta musamman da Allah Maɗaukakin Sarki Ya ba ni..."Ba ta bari ya gama maganarsa ba ta tari numfashinsa, "Malam ban. . .