Bayan Malam Hassan da Hauwa'u sun dawo daga asibiti sai suka tarar da Asabe a tsakar gidan ita kaɗai, suka yi mata sallama amma ko kallonsu ba ta yi ba balle ta amsa sallamar da suka yi mata. Su ma babu wanda ya kalli inda take Hauwa'u ta shige ɗakinta tare da jaririyarta, shi kuma Malam Hassan ya sake fita sana'arsa.
Fitar Malam Hassan ke da wuya Asabe ta ɗauki hijabi ta fita, a ƙofar gida ta tarar da ƙawarta Rabi tana jiranta, ba tare da wani jinkiri ba suka nufi bakin titi suka tare napep. . .