Karaf! Asabe ta haɗa ido da Malam Hassan, ta sunkuyar da kanta ƙasa da sauri saboda wani irin kwarjini da ta ga ya yi mata. Cikin nutsuwa ya je ya samu wuri mai kyau ya zauna yana kallon shari'ar da Alƙali yake gudanarwa cikin nutsuwa. Ko kaɗan bai kalli inda su Asabe suke zaune ba, duk da ya lura hankalinsu gaba ɗaya yana kansa.
Suna nan zaune har aka yi shari'ar mutum biyar aka zo kansu, bayan magatakarda ya kira Asabe da Malam Hassan sun fito gaban kotu.
Sai Alƙali ya kalli Malam Hassan. . .