Murmushi Haidar yayi yana duban Nafeesa yace.
“Duniyata ki rabu wannan domin kuwa shi haka yake da zolaya, in dai Al’ameen ne sai ya iya saki kuka ma.”
Ɗan murmushi Nafeesa tayi tare da kai dubanta cikin motar da Al’ameen ya shiga tace.
“Farin ciki na, nima banji haushi ba, domin kuwa muddun zaka ga kyawuna kuma ka yabani, to kowa ma ya kusheni ban damu ba”
Tayi Maganar tana riƙe glass ɗin motar tare da duban Al’ameen tace.
“Bashi kaci ka tabbatar da lallai sai na rama domin kuwa ka kushe kyakkyawar budurwa kuskure ne hakan.”
Murmushin gefen baki Al’ameen yayi ba tare daya ɗago ya kalleta ba, ya furta.
“Lallai kuwa mafarki kike domin kuwa Al’ameen baya taɓa cin bashi, bare kuma har a nemi ya biya duk abinda zai fito daga bakina to daga zuciyata yake ɓullowa ma’ana itace gaskiyar Al’ameen, banga kyawun ba bare na ambace sa kona ya ba.”
Idanu Nafeesa ta zuba masa tana jin soyayyarsa na ƙara shiga zuciyarta, yana da kyau kuɗi da kuma iko, ga gadara da jin kai, Tabbas shine mafarkinta na mijin daya dace ta aura numfashi ta saki tare da lumshe idanunta tace.
“To dai a wannan lokacin Al’ameen ya ci bashi kuma biya ya zamo wajibi a garesa.”
Haidar zaiyi Magana Nafeesa ta ɗaga masa hanu tare da cewa.
“Ba sai kace komai ba Duniyata na fahimcesa, da alamu tasa budurwar mummuna ce bata kaini kyau ba shiyasa zai kushe ni.”
Murmushi Al’ameen ya saki shi maganarta ta ma dariya taso basa, Haidar ya kalla tare da cewa.
“Ka faɗa mata cewa gwani baya nuna kansa sai dai a nunasa, rashin isa da kuma rashin kamun kai shike sa mutum ya yabi kyawunsa, bana buƙatar kyawu a soyayya nagarta kawai itace nake buƙata ki fahimci wannan daga Al’ameen kinji Mrs Atiku.”
Wani irin ɗaci Maganar Al’ameen ta yiwa Nafeesa tare da tsinkewar zuciya Mrs Atiku kuma, domin kuwa Tabbas Magana ya faɗa mata to shi kuma wannan mutumin wani irin mutumi ne shi, mai tsaurin rai da faɗawa mutum Magana babu shakka, Lallai Tabbas bashi da sauƙin kai amma duk da haka zata iya dashi, tayi Maganar zucin tana cije bakinta, shi kansa Haidar baiji daɗin maganar da Al’ameen ya faɗawa Nafeesa ba, da yasan haka zai masa da baizo dashi duk da yasan halinsa amma dai baiyi tunanin zai kintata mata wannan rashin mutuncin ba.”
“Mrs Atiku kuma.?”
Ta furta tana kallon sa, ɗan murmushi Al’ameen yayi tare da cewa.
“Au sorry Mrs Aliyu zance, ba Atiku ba kuskuren harshe ne.”
Ajiyar zuciya Nafeesa ta sauƙe tana duban Haidar tare da cewa.
“Duniyata ni zan koma gida Mama bata nan ni kaɗai ne kuma aiki ma nake na fito.”
Murmushi Haidar yayi yace.
“Okay shikenan ba damuwa kije sai munyi waya, yau banga meenat ki gaishe ta idan kun haɗu.”
“Yau tana da school shiyasa bata zoba insha Allah zan isar mata da saƙon ka, to abokinmu nina shige na gode da ziyara.”
Tayiwa Al’ameen Sallama tana juyawa zata shige gida.
“Dakata.”
Al’ameen Ya furta yana dubanta tsayawa tayi tare da juyowa tana dubansa Haidar shima da kallo ya bi Al’ameen cike da jin haushin rashin mutumcin daya yiwa Nafeesa.
“Ya zaki tafi da wuri haka bayan baki gana da Farin watan naki yadda ya kamata ba.”
Yayi Maganar yana miƙo mata check na kuɗi tare da cigaba da cewa.
“Ga wannan kyauta ne daga gareni zuwa ga farin cikin ɗan uwana ina tayaki murna Nafeesa kinyi dacen samun Mutum na gari, da zaki kula ki maida hankalin ki da tunaninki garesa shi ɗaya Tabbas da bazaki taɓa kokawa a Rayuwarki ba, samunsa a matsayin mijin Aure Tabbas babban Nasara ce a rayuwa, ni nasan Abokina mutumin kirki ne mai riƙo da alƙawari, ina fatan kema zaki riƙe masa alƙawarin sa.”
Wani irin nishaɗi da farin ciki ne suka dura a zuciyar Haidar take ɓacin ran da yake ji ya goge jin kyawawan yabon da Al’ameen ya masa, murmushi ya saki yayin da yake duban Nafeesa tare da mata alamun ta amsa, hanu tasa ta amshi check ɗin tare da furta.
“Na gode.”
Dubanta ta kai ga check ɗin 500k kyautar kuɗin da Haidar bai taɓa mata ba kenan, ɗan murmushi ta saki tana ƙara cewa.
“Farin ciki na, ka tayani godiya amma fa duk da wannan toshiyar bakin daya bani bazai hanani ramako ba.”
Murmushi Haidar yayi tare da cewa.
“Waya faɗa miki zamu yafe masa ai kafin ki rama ma sai na fara rama miki.”
Kansa kawai Al’ameen ya girgiza yana murmushi tare da zuge glass ɗin motar ba tare daya ce komai ba, Nafeesa da Haidar sun juma suna hira a yayin da rabin hankalin Nafeesa ke kan Al’ameen sam bata gajiya da kallonsa ji take tamkar ta haɗiye sa, murmushi ta saki tana ƙara dubansa yayin da shi ko kaɗan baima san tanayi ba, kallon ta mayar ga Haidar tace.
“Na shige sai munyi waya.”
Murmushi ya mata kafin sukayi sallama ta shige gida, Haidar motar ya buɗe tare da duban Al’ameen yace.
“Muje uban ƴan walaƙanci.”
Murmushi Al’ameen ya saki tare da ijiye wayar yaja motar sanda suka fita a layin suka hau titi kafin Al’ameen yace.
“Wulaƙancin me kuma na maka Abokina, budurwar taka fa ba laifi ta ɗanyi kaɗan ba sosai ba.”
“Tambayata ma kake kenan wulaƙancin me ka min, bayan ka gama faɗa mata maganganun da basu dace ba, shi ne kake tambayata me kayi, to wai ma ina ruwanka idan kai bata maka ba, ni ai tamin kuma dai a hakan nake son kayana ɗan rainin hankali kawai.”
Dariya Al’ameen yayi yace.
“Allah ya huci zuciyar abokina.”
Harara Haidar ya jefa masa tare da kawar da kansa gefe.
Ita kuwa Nafeesa tunda ta shiga bedroom ɗinsu ta faɗa saman bed tare ƙanƙame check ɗin tana lumshe idanunta, fuskar Al’ameen kawai da bakinsa take hangowa sosai gayen ya tafi da ita, da alamu zai iya Soyayya.
“kyakkyawa ne yana da kyawawan idanu bakinsa ɗan ƙarami yana da kwarjini ga Kuma kuɗi Tabbas idan na auresa zan huta ni da mama bazan taɓa kukan talauci ba, ta ina zan fara dawo da tunaninsa gareni, yauwa *LAMI* itace kawai zata tayani neman wannan hanyar.”
Ta furta Maganar tana dariya tare da miƙewa zaune ta jawo wayarta hoton sa ta buɗe tare da zuba masa idanu kiss ta yiwa picture ɗin tare da miƙewa ta faɗa tollet tana dariya cike da farin ciki, duk da ya faɗa mata maganganun da ba dai-dai ba sai dai ko kaɗan hakan baisa taji bata sonsa ba.
Ablah tana zaune a harabar gidan tayi shuru zuciyarta cike da tunani, taji tsayuwar mutum a kanta idanunta ta ɗaga tare da duban wanda ke tsaye a kanta, Aunty Amarya ce, kanta ta ɗauke daga dubanta ta mayar ƙasa, zama gefenta Aunty Amarya tayi tare da cewa.
“Kin zauna anan kina tunanin wani zaɓi zaki ɗauka acikin wanda na baki ko, to ki daiyi tunanin daya kamata wanda zai kawowa rayuwarki sauƙi, duk da ba wannan bane ya kawo ni, nazo ne na sanar dake cewa, zanyi kisan kai a cikin gidan nan, kuma bazan sanar dake wanda zan kashe ba, sannan zanyi kisan ne ta inda bakiyi tsammani ba, idan kin isa ki dakatar dani.”
Tayi Maganar tana duban fuskar Ablah tana sakin dariya, wani irin tsinkewa zuciyar Ablah tayi, Tabbas tunda ta faɗa zatayi ne amma ya zamo waji gareta ta dakatar da ita saurin kallon Aunty Amarya cike da firgici, dariya Aunty Amarya ta kuma sawa tana cewa.
“Ya naga kamar kin tsorata, irinku ai basa nuna tsoro, kefa mai wayo ce kuma zaƙwaƙura firgicin me kuma zakiyi.”
“Burinki bazai cika ba, zan dakatar dake babu randa zai salwanta a cikin gidan nan, wai meyasa ne kike wannan rashin imanin, ran Mutum fa ba ran ɓera bane ko kiyashi da zaki kashe ba tare da jin tsoro ba, meye dalilinki na wannan kisan me kike buƙata daga garesu nasan dole akwai dalilin da yasa kike wannan rashin imanin dan Allah ki dakata haka kefa musulma ce, shin baki tsoron haɗuwarki da Ubangiji, a yayin da zai tuhumeki akan waɗannan rayukan da…”
“Dakata haka, bana buƙatar wa’azinki ki riƙe kayanki, na dai sanar dake zanyi kisa kuma zanyi.”
Tayi Maganar tana miƙewa tabar wajen.
Cike da munguwar tsoro Ablah ta bita da kallo take jikinta ya fara ɓari bata san waye harin Aunty Amarya ba, bare tayi ƙoƙarin dakatar da ita, bata kuma san yaushe zatayi kisan kuma bata san ta wacce hanya zatayi ba, Lallai akwai Babbar matsala idanunta ta runtse hawaye na gudu a saman fuskarta, miƙewa tayi cikin sanyin jiki ta jinginu jikin bango sai kuma ta fashe da kuka sosai take kukan tamkar ranta zai fita domin kuwa ita bata taso cikin irin wannan Rayuwar ba, rayuwa cikin tsoro da fargaba.
Al’ameen bayan Sunyi parking ne ya shigo cikin part ɗin kansa tsaye turus ya tsaya yana ƙare mata kallo kuka take tsakaninta da Allah tamkar ranta zai fita, take yaji shima ransa ya baci tausayinta ne ya dirar masa a zuciyarsa, ita sam bata lura dashi ba domin kuwa hankalinta yayi matuƙar tashi sam bata cikin nutsuwarta, nufar inda take yayi tare da tsayuwa ya zuba hanunsa a cikin aljihu karo na farko daya fara kiran sunanta.
“Ablah”
Ya ambaci sunan cikin slow voice ɗinsa, wani irin razana tayi jin muryar sa domin kuwa rabon da ta gansa tun ɗazu da ta masa ɓarna a bedroom ɗin Ummi, saurin goge hawayenta tayi tare da juyowa ta dubesa da idanunta da sukayi ja ba tare da ta amsa ba.
“Biyoni muje ciki.”
Kanta ta ɗaga alamun to cike da tsoro domin kuwa ita duk a nata tunanin hukuntata zaiyi akan laifin da ta masa,shigewa yayi tabi bayan sa, bisa mamakinta Al’ameen bai tsaya a falo ba ya shige bedroom ɗinsa, tsayawa tayi tana duban su Maimu da Afnan dake zaune a falon kamar bazata haura ta bisa ba sai kuma wata zuciyar tace kije karkiyi laifi , haurawa tayi tare da tura door ɗin nasa a hankali tayi sallama, wani irin ƙamshin turaren room ne ya doki hancinta, a rayuwarta tana bala’in son ƙamshi, idanunta ta lumshe tare da saka ƙafa ta shiga cike da mamaki take duban ROOM ɗin nasa yanda yayi matuƙar tsaruwa, tamkar na mace komai a tsare yake a ROOM ɗin, tsayawa tayi a tsakiyar falon shiko gogan yana zaune cikin ƙaramar kujera mai biyu kallonta yayi tare da mata nuni da gefen sa yace.
“Ki zauna a nan”
Zaro idanunta Ablah tayi tare da girgiza kanta ta nemi gefe guda ta zauna a ƙasa, bai damu ba sai ma tambaya da ya jefa mata.
“Meya saki kuka.?”
Tamkar aradu haka taji tambayar tasa, numfashi ta sauƙe sai kuma hawaye ya gangaro mata na tausayin su, cikin sanyin murya tace.
“Babu komai ba abinda yake damuna.”
“Ba abinda na tambayeki ba kenan cewa nayi meya saki kuka.?”
“Ba komai.”
“Haka kawai kike kuka, kukan daɗi yake miki ne.?”
Kanta ta girgiza masa alamun a’a, murmushi Al’ameen yayi tare da cewa.
“Ƙarya kike ba haka kawai kike kuka ba, akwai Abinda yake damunki, zaman gidan nan ne baya miki daɗi ko kuma akwai wanda yake hantarar ki ne, idan akwai ki sanar dani na ɗauki mataki?”
Ablah cikin zuciyarta tace (ji wani rainin hankali cikin gidan nan akwai mai hantarata ne sama da kai ni baka san damuwata tafi ƙarfin wannan tambayar da kake min ba, kukan tausayin rayuwarku nakeyi) numfashi ta saki tare da dubansa tace.
“Babu ko ɗaya, Abbana ne ya faɗo min a raina shine abinda ya sani kuka musamman idan na tuno da irin wahalar da Ummana tasha Saboda inganta rayuwar mu.”
Tayi masa karya dan Saboda karya kuma mata wata tambayar, shi kuwa tausayinta yaji sosai domin kuwa rashin mahaifi abune da yake da ciwo a zuciya musamman ma irinsu da suke talakawa marassa ƙarfi, harga Allah yana jin soyayyar Yarinyar a zuciyarsa shiyasa baya ƙaunar abinda zai taɓa rayuwarta ko mutuncinta, numfashi ya saki tare da cewa.
“Kiyi hakuri, wannan itace ƙaddarar ku, kowa da yadda Allah yake ƙaddara masa tasa Rayuwar.”
Kanta Ablah ta ɗaga ta amsa da.
“Hakane na gode sosai.”
“Okay Sannan na gama da registration ɗinki, insha Allah on Monday zaki fara tafiya school sannan daga yau na dakatar dake daga masu aikin cikin gidan nan, ki tsaya kawai ki maida hankali ga karatunki sannan ina gargaɗinki da cewa, karki kuskura ki saurari wani namiji a school ko ma a waje ko ƙawa ɗaya kawai na yadda kiyi, zansa a saka min idanu a kanki idan kika kuskura naji kin tsaya da wani ko kin tara ƙawaye to fa wallahi ranki zai ɓaci ki kiyaye.”Ablah da kallo ta bisa yadda yake kafa mata doka tamkar ubanta, bakinta ta taɓe tare da amsawa da to ta miƙe zata tafi har tazo bakin ƙofa taji muryar sa.
“Na faɗa miki na dakatar dake daga cikin masu aikin gidan nan, ki kula karna kuma ganinki cikin su.”
Kanta kawai Ablah tasa ta fice daga bedroom ɗin nasa ba tare da ta amsa masa ba, murmushi ya saki tare da lumshe idanunsa Tabbas itace zaɓinsa kuma muradinsa sai dai bazai iya furta mata kalmar so ba, gudun kadda ta rainasa domin da zarar namiji ya furtawa mace kalmar so, to a wannan lokacin take ganin dai-dai dashi take.
Ita kuwa Ablah tunda ta fito daga bedroom ɗin nasa take leƙen ta ina zataga Aunty Amarya domin kuwa bata san ta ina zata fara shirinta ba, har kitchen ta leƙa babu Aunty Amarya, zama tayi gefen Maimu tare da zuba tagumi tana tunanin ina Aunty Amarya ta shiga, Maimu ne ta dubeta tare da cewa.
“Ablah lafiya kuwa kikayi tagumi?”
Ɗan murmushin yaƙe Ablah tayi tare da cewa.
“Lafiya lau, amm Aunty Amarya tana ina?”
Ta jefawa Maimu tambaya, kafaɗarta Maimu ta ɗaga tare da cewa.
“Ban sani ba gaskiya don tunda na zauna a nan banganta ba.”
Numfashi ta saki tare da jinginuwa jikin kujerar tayi shuru.
A yayin da Aunty Amarya ke bedroom ɗin Ummi cikin sauri jin Ummi na wanka cikin tollet ya sa Aunty Amarya saurin ɗaukar maltina dake kan wadrop ɗin Ummi da alamu ijiyewa tayi ya huce tasha, murmushi Aunty Amarya ta saki tare da saurin sunce bakin zaninta wannan dai gubar da ta zubawa Al’ameen cikin abincin shi ta ɗauka ta zuba cikin wannan maltina da Ummi ta juye a cikin cup, ta girgiza sa, murmushi ta saki tana kallon ƙofar tollet ɗin tare da nufo hanyar ficewa cikin sauri gudun kar wani ya shigo ya ganta.
Ablah kuwa hankalinta gagara kwanciya yayi taji gara kawai ta haura sama ta duba taga ina Aunty Amarya take…