Cikin sauri sauri Ablah ke haurawa step ɗin, duba tayi ga ROOM ɗin Ummi har zata shiga sai kuma ta fasa ta nufi room ɗin Aunty Amarya tana tura door ɗin tare da shigewa dai-dai Aunty Amarya na sako kanta zata fito daga room ɗin Ummi idanunta suka sauƙa akan Ablah da ta shige room ɗinta baya ta juya da sauri tare da laɓewa jikin door sai da ta tabbatar Ablah ta shige bedroom ɗinta sannan ta sauƙo ƙasa da sauri tana sakin murmushin mugunta, gabaki ɗaya fita tayi daga falon gudun idanun Ablah domin kuwa. . .