Skip to content
Part 22 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Cikin sauri sauri Ablah ke haurawa step ɗin, duba tayi ga ROOM ɗin Ummi har zata shiga sai kuma ta fasa ta nufi room ɗin Aunty Amarya tana tura door ɗin tare da shigewa dai-dai Aunty Amarya na sako kanta zata fito daga room ɗin Ummi idanunta suka sauƙa akan Ablah da ta shige room ɗinta baya ta juya da sauri tare da laɓewa jikin door sai da ta tabbatar Ablah ta shige bedroom ɗinta sannan ta sauƙo ƙasa da sauri tana sakin murmushin mugunta, gabaki ɗaya fita tayi daga falon gudun idanun Ablah domin kuwa duk da ta yi komai a ɓoye tana tsoron wayon yarinyar, ita kuwa Ablah dube dube ta fara a bedroom ɗin Aunty Amarya wayam babu ita, har toilet sai da ta leƙa, numfashi ta saki tare da fitowa cikin sauri ta shiga room ɗin Ummi dai-dai Ummi ta fito daga wanka kenan, sallamar Ablah Ummi ta amsa tare da cewa.

“Ablah kece.”

“Eh Ummi nine, Aunty Amarya nazo nema.”

“Ayya Amarya bata shigo nan ba, ki duba bedroom ɗinta.”

Ummi tayi maganar tana zama jikin mirror ɗinta, Ablah kanta ta ɗaga alamun to tare da juyawa zata fita Ummi tace.

“Ablah zoki miƙo min maltinan nan tun ɗazu na ijiye sa ya huce na samu nasha, nasan yanzu maybe ya huce.”

Da to Ablah ta amsa tare da juyowa ta nufi wadrop ɗin hanu tasa ta ɗauki cup ɗin da maltinan ke ciki tazo ta miƙawa Ummi, amsa Ummi tayi tare da cewa.

“Na gode Ablah, amm ki shiga kitchen dan Allah ki ɗan sama min koda Indomie ne yunwa nake ji.”

“To Ummi bara naje.”

Tayi Maganar tana ficewa, murmushi Ummi tayi tare da Binta da kallo cike ƙaunar Yarinyar haka kawai take jin Ablah a ranta, bayan ficewar Ablah Ummi ta kafa kanta ta shanye maltinan tas ta ijiye cup ɗin.

Koda Ablah ta sauƙo bata nufi kitchen still dai Aunty Amarya ta cigaba da dubawa.

“Baki samu Auntyn bane?”

Taji muryar Maimu na tambayarta, dubanta Ablah ta kai ga Maimu tare da ɗaga mata kai alamun eh.

“Ai kuwa yanzu naga ta fice harabar cikin part ɗin nan ki duba waje tana nan.”

Numfashi Ablah ta saki tare da ficewa da sauri ai kuwa tsaye ta hangota jikin flowers ɗin dake zagaye a part ɗin ƙarasawa Ablah tayi cikin sauri tare da cewa.

“Tun ɗazu nake dubaki a cikin gidan nan ban ganki ba.”

“To ai yanzu kin ganni ya akayi ne kinji mummunan labari ne?”

“Banji mummunan labari ba, haka kuma kunnena bazaiji mummunan labari ba, ina son ki sanar dani waye kike neman rayuwarsa a cikin gidan nan?”

“Koma waye ne ki saurara zaki gani, meyasa ma zaki tambayeni ke da ya kamata kije ki kare rayukansu, kefa kikace zaki dakatar dani, to kuma meye na tambayata kinga na tsaya a nan ne saboda na samu nutsuwa Please Leave me a lone.”

“Na gama duba i zuwa ga mutanen dake cikin gidan nan, Al’ameen Ummi Maimu duk suna lafiya, shiyasa na tambayeki waye ne zaki kashe ko dai kawai kina min barazana ne saboda naji tsoro na amshi tayin mungun nufinki.”

Murmushi Aunty Amarya tayi tana duban Ablah cike da hango tsantsar wautar ta.

“Koma menene ki kauce ki bani waje, ki saurara ki gani ko barazana nake, sai fa ki sani yanzu haka nasan akwai randa yake gargarar mutuwa a cikin gidan nan, domin kuwa na ɗauke hankalinki ga shagala da saka min idanu, yayin da tuni na gama aikina hmmm! Tafi ki dubo ki gani waye ke shirin tafiya lahira.”

Tayi Maganar tana sakin murmushi, zaro idanunta Ablah tayi a mungun firgice ta juya cikin falon da gudu, shi kuwa Al’ameen fitowar sa kenan daga room ɗinsa ya shiga na Ummi, da Sallama shuru yaji babu amsa hakanne ya sashi tunanin ko tana toilet ne, zama yayi bakin bed ɗinta sai yaji tamkar hucin nishin mutum dubansa ya kai jikin dressing mirror Ummi ya gani kwance sai wani irin nishi da gurnani take ga kumfa dake fita daga bakinta, a mungun firgice Al’ameen ya miƙe da gudu ya sunkuya gaban Ummi tare da saka hanu ya ɗago ta yana.

“Ummi! Ummi! Ummi meya sameki, ki faɗa min Ummi meya sameki.!”

Duk Maganar da Al’ameen yake sam Ummi bata san yanayi ba domin kuwa ta gama fita daga cikin hayyacinta jin cikinta take tamkar hanjin cikinta na tsinkewa.

“Ummi kimin Magana! Meya sameki.”?

Sakinta yayi tare da tashi a gigice ya fito yana kwaɗawa Aunty Amarya da Daddy kira.

“Daddy Daddy! Aunty Amarya Aunty Amarya! Kuzo ku taimaki Ummi! Ummina zata mutu.”

Turus Ablah ta tsaya jin maganar da Al’ameen keyi, wani irin tsinkewa zuciyar ta yayi wato Aunty Amarya Ummi ta kaiwa hari, ya akayi ban fuskanta ba harna shiga bedroom ɗinta, bakinta ta cije idanunta na cikowa da hawaye ta haura da gudu ta nufi bedroom Ummi, a kwance take tuni numfashinta ya fara sarƙewa, ga kumfa da bai daina zuba daga bakinta ba, dubanta ta kai ga cikin Ummi ya kumbura sosai, wani irin kuka ta saki mai cin rai ta gagara ceton ran wannan baiwar Allah mai ƙaunarta, rasa me zata mata tayi sai kuka kawai da take, Ummi hanun Ablah ta kama ta ɗaura akan cikinta sai hawaye suka zubo mata daga idanunta, cikin sarƙewar murya da baya fita sosai Ummi ta fara magana.

“A…..a…… Ablah bansan me nasha a cikin….wan…..wannan lemon ba, mutuwa zanyi…. Ablah ki taimakeni ki zauna da Al’ameen kiyi rayuwa dashi ta har abada….ki auresa…nasan za…za…zaki kula da rayuwarsa dan All…”

Wani irin tari ne yazo mata ya dakatar da maganar da take ƙoƙarin yiwa Ablah, sai kuma jini ya fara biyo bayan wannan kumfar daga bakinta, idanunta ne suka fara kafewa yayin da suka koma kalar ruwan ɗorawa, Daddy da Aunty Amarya Al’ameen harsu Maimu da gudu suka shigo bedroom ɗin, Aunty Amarya riƙo Ummi daga hannun Ablah tayi a gigice tana jijjiga ta.

“Innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Yau kuma wacce irin masifa zamu gani, innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Mun shiga Uku, Ki tashi Ummin Al’ameen, Daddyn Al’ameen meya sameta.?”

Tayi Maganar hawaye na tsere saman fuskarta, cike da alamun gigita na munafurci, Daddy shima cikin tashin hankali ya dubi Al’ameen daya gigice ya rasa ina zaisa ransa yace.

“Aminu maza tashi ka ɗauketa muje asibiti hanzarta bara naje na gyara motar.”

Daddy yayi Maganar yana miƙewa ya fita da sauri, yayin da cikin Hanzari Al’ameen ya ɗago Ummi da gaggawa ya fito da ita yayin da Aunty Amarya da Maimu suka rufa musu baya, Ablah saurin riƙo hanun Aunty Amarya tayi, juyowa tayi tare da dubanta ganin babu kowa duk sunbi Al’ameen da Daddy yasa Aunty Amarya sakin dariya tare da ƙwace hanunta tana duban Ablah tace.

“Ya kikaga wasan, na buga kuma wasan yayi kyau, domin kuwa babu tabbacin asibitin ma zata ƙarasa da rai, guba tasha a maltina wanda ƙa’idar gubar 30 minute ta gama tsinka jijiyoyi da hanjin mutum sannan ta kai wannan lokacin babu wani makari da za’a bawa Mutum domin ya samu tsira, ita kuwa ta kai 50 minute dasha kinga kuwa sunanta marigayiya.”

Wani haushi da munguwar tsanar Aunty Amarya ne ya dura a zuciyar Ablah, tamkar baƙar macijiya kububuwa haka take kallonta, hawayenta ta goge cikin nauyin ƙirji tace.

“Tabbas kin buga wasan, amma hakan bashi yake nuna kinyi Nasara ba, domin kuwa mutuwa da rayuwa suna hanun Ubangiji ne, ba keba, tunda nake a rayuwata ban taɓa ganin azzaluma irinki ba, Ummi bazata mutu zata rayu, ki duba yadda kika dage kina kuka tamkar bake bace kika sakata cikin wannan halin da take ciki ba, meyasa zaki bita asibiti Saboda kiga numfashin ta na ƙarshe ne ko?”

“Hmmm! Bani da lokacin amsa miki wannan tambayar yanzu domin kuwa asibiti zani ki bari idan mun dawo da gawarta sai na amsa miki tambayarki.”

Tayi Maganar tare da dariya ta fice, Ablah runtse idanunta tayi tare da fashewa da kuka tana durƙushewa da gwiwowinta, dubanta ta kai ga cup ɗin da Ummi tasha maltinan, itace ta miƙa mata da hanunta tasha ajalinta, ƙara sakin kuka tayi cike da munguwar danasanin shigowa bedroom ɗin Ummi da harta miƙa mata guba tasha cikin rashin sani, Tabbas Aunty Amarya ta cuceta ta sata cikin zullumi da danasani, ta bawa baiwar Allah guba da hanunta tasha, meye hukuncinta a wajen Ubangiji.”

Zama tayi daɓas ta cigaba da rera kukanta cike da tashin hankali, ganin kukan bazai amfaneta ba, ya sata tashi ta tafi bedroom ɗinta alwala ta ɗauro ta hau Sallah tana yiwa Ummi addu’a Allah ya tashi kafaɗunta Tana addu’ar tana kuka mai cin zuciya.

Can kuwa asibitin tuni aka shige da Ummi cikin emargency Al’ameen yana zaune sai hawaye kawai suke tsere saman fuskarsa, a mungun firgice yake da halin da umminsa ke ciki, idanunsa ya runtse yana jin zuciyarsa na ƙuna, Aunty Amarya kusa dashi tazo ta zauna tare da jawo Al’ameen kafaɗarta itama hawaye na zubo mata cikin rarrashi take cewa Al’ameen.

“Al’ameen ka daina kukan nan haka, kukanka yana ƙara ɗaga min hankali sai naji tamkar kuna tunanin idan babu rayuwar mahaifiyarku bazan iya riƙe kuba, ni kaina ina cikin munguwar tashin hankali, domin kuwa Ummi ni kaina itace gatana a cikin gidan nan, tamkar ƙanwa ta jini haka take ɗaukata, na fiku shiga cikin tashin hankali Al’ameen, ka daina kukan haka insha Allah Umminku zata tashi bazata mutu ta barmu ba.”

Tayi Maganar cikin shashsheƙar kuka mai cin zuciya, Al’ameen wani irin tausayi da ƙaunar Aunty Amarya yaji, ɗago kansa yayi tare da saka hanu ya share mata hawayen ta, cikin sanyin murya yace.

“Ki daina kuka Aunty domin kuwa zan iya jure nawa ciwon zuciyar amma bazan iya jure naku keda Ummi ba, baki da wani banbanci da Ummi a wajen mu Aunty kema uwace mai ƙaunar mu, dan Allah hawaye ya daina zuba a idanunki, Ummi tana cikin mawuyacin hali, ina jin ciwo da zafi a cikin zuciyata, na tsorata da lamarin Ummi.”

“A’a Al’ameen karka ce haka karka tsorata babu abinda zai sami Umminka, insha Allah zata tashi muyi Rayuwarmu kamar yadda muka saba, ji nake kamar na ɗauke mata ciwon na dawo dashi kaina, insha Allah zata samu lafiya.”

Numfashi Al’ameen ya saki tare da kwantar da kansa jikin Aunty Amarya, Daddy kam tsabar tashin hankali shi maganar ma ta gagaresa, domin kuwa ji yake tamkar zai yanki jiki ya faɗi, idan har ya rasa Gaji bai san ina zai saka kansa ba, tamkar rabin rayuwarsa yake jinta, ta rayu dashi tun kafin ya zamo wani abu a rayuwa, tun bashi da komai harta kuɗin makarantar sa Gaji ta biya masa da kuɗinta, ta ƙaunace sa da rabu da mutanen da sukafi kowa mahimmanci a gareta, Saboda shi, ta zaɓesa fiye da iyayenta, tayaya zai iya mantawa da halaccin Uwar gidan sa tayaya zan iya rayuwa babu ita.

Runtse idanunsa yayi wani irin hawaye ne mai ɗumi ya zubo masa.

Likitocin sun kai kusan awa Uku a cikin emargency, har yanzu basu fito ba abinda yake daɗa tsinkawa Daddy da Al’ameen zuciya kenan.

Al’ameen wayarsa ya ɗaga tare da turawa Haidar text ya sanar dashi Ummi ba lafiya suna asibiti.

Cikin tashin hankali Haidar dake zaune cikin bedroom ɗinsa ya fito, tare da sanar da Momma, babu shiri itama momma ta ɗauki hijabin ta suka nufo asibitin da Haidar.

“Fushi Amnat take dani Jamila, Saboda wannan dalilin dana sanar dake yanzu, na rasa meye tsakaninta da Haidar da ta damu a kansa matuƙa, ni kuwa wallahi bazanyi rayuwa dashi ba, domin kuwa Al’ameen shine wanda yafi dacewa dani ba Haidar ba, yafi sa kuɗi kyau da kuma iko, to akan me bazan rabu dashi ba, wallahi koda ace da Auren Haidar a kaina zan iya mutstsike Auren na kashe sa naje na auri wanda zan huta talauci ya yanke min.”

Dariya Jamila tasa tare da cewa.

“Shegiya ƙawata hmmm! Mai idon cin Naira ni na rasa wani irin shegen son kuɗin tsiya ne dake, kema fa kin san halin Amnat ta tsani yaudara, sai dai fa ni kin burgeni, don koni ce na samu damar da kika samu abinda kike ƙoƙarin yi shi zanyi, ina bayanki kuma zan taimaka miki a duk lokacin da kike buƙata, yanzu abinda zakiyi shine, ki rage shiga harkar Haidar ki fara ja baya dashi, wayarsa ma ki rage ɗagawa idan fara ganin sauyawa daga gareki dole zaiyi ƙoƙarin ja baya daga gareki.”

“Allah ƙawata! Ta inda kikafi min Amnat kenan, domin kuwa ke bakya taɓa kwaye min, yanda kikace haka za’ayi, to amma shi kuma Al’ameen ɗin fa ta wace hanya kike ganin zan fara jawosa gareni.”

“Hanyace mai sauƙi ƙawata domin kuwa jawo hankalin namiji ga macen bariki irin mu abune mai sauƙin gaske ƙawata.”

Murmushi Nafeesa tayi tare da cewa.

“Ƙawata shifa wannan Al’ameen da kike gani ba irin waɗannan mazan bane da ake jawosu take, shi wannan yana da izza da kuma taurin kai da alamu Irin mazan nan ne masu tsaurin ra’ayi da kuma ji da kai, jawo hankalin sa zuwa garemu dole sai mun shirya wataƙil ma sai mun haɗa da barazana.”

Dariya Jamila tasa tace.

“Duk izzarsa da taurin kansa zamu iya dashi dole ne sai ya soki ya dawo gareki, ina ƙara sanar dake cewa wannan ƙaramin aikine.”

“Ba ƙaramin aiki bane”

Sukaji muryar Amnat daga bayansu tana tsaye ta harɗe hanunta tafi minti sha biyar tsaye tana sauraronsu, da kallo suka bita suna mamakin yaushe ta zo basu lura ba, ƙarasowa tayi ta zauna tare da cigaba da cewa.

“Ƙwarai kuwa ba abu bane mai sauƙi kamar yadda Jamila take iƙrari, karku manta da cewa shi wannan da zaku kaiwa tsafka ɗan uwane na jini kuma AMINI ga Haidar dan haka dole kusan cewa akwai tarin ƙalubale a gareku, sannan ba ma lallai bane kuyi Nasara saboda shi wanda kike buƙata yanzu Al’ameen ba ɗaya yake da irin mazan da muke yaudara lokaci guda ba, saboda shi ZAKI ne karo dashi ba abu bane mai sauƙi…”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Aminaina Ko Ita 21Aminaina Ko Ita 23 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×