Skip to content
Part 23 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

“Ke fa a rayuwarki Amnat har abada bakya taɓa ƙarfafawa mutum gwiwa kinfi so ki dinga sanya masa sanyin jiki, kene kike kallon wannan ƙaramin abun, akan babba, ni kallon ƙaramin abu nake masa, kuma ki sani zamu dawo da tunaninsa gareta cikin ƙanƙanin lokaci, wannan ba wani abu mai wahala bane a wajena wai ko kin manta da wayece Jamila.”

Murmushi Amnat ta saki tare da cewa.

“Hmmm! Jamila kenan, har abada mai hali baya taɓa fasa halinsa, ta yaya zan manta da waye ke Jamila, ko kin manta kin ijiye min tabo na ƙwacen saurayi da kika min, na sani ke kinma fi Nafeesa hatsabibanci, sai dai ki sani a wannan karon kun taro babban yaƙi ne wanda cimma nasarar ku abune mai wahala domin kuwa idan juninku sammako ne to wani shi a tafe ya kwana, wato ke Nafeesa kin haɗe da Jamila saboda son duniyarki, har kin manta da abinda ta min, to kema kibi a hankali domin kuwa abunda tayi min kema bazai tsallake kanki ba.”

Tayi Maganar tana miƙewa tare da barin wajen gabaki ɗaya numfashi Nafeesa ta saki tana duban Jamila.

“Kinga abunda nake faɗa miki gabaki ɗaya ta sauya ni babu ruwana akan abinda ya shiga tsakanin ku, ban damu da maganarta ba ƙawata, ina sauraronki mafita kawai nake nema.”

Bakinta Jamila ta taɓe tare da amsar wayar Nafeesa tana matsowa kusa da ita, numbern Al’ameen ta lalubo tare da tura masa saƙo.

“Assalamu alaikum barka da hutawa malam Al’ameen, ya hutawa domin kuwa nasan kai ɗin saraki ne, shi kuma saraki dole yana cikin hutu, haƙiƙa kai mutum ne na musamman a rayuwa komai naka yana tafiya ne akan tsari kana da abubuwan burgewa a tare da kai, dalilin kenan da yasa ka shiga raina, ina maka fatan alkairi I love You.”

Ta tura saƙon da special numbern Nafeesa wanda babu wanda ya santa da wannan numbern number ce wacce take sayan data kawai da ita, murmushi ta saki Jamila tare da cewa.

“Da waɗannan zaki fara aika masa da saƙon naki, zuwa 2week muga mai zai sauya kafin ki bayyana masa kanki, nasan wannan saƙon da zai tsinta a wayarsa zaisa ya fara tunani a kanki wanda shi muke buƙata tunaninsa.”

“Yesss! Na fahimta zan ɗaura daga inda kika tsaya dole ma Wannan gayen yazo hanu, tashi muje na rakaki kafin Baba ya dawo sarkin mita, insha Allah next week zanzo gida na sameki idan ma kuma mun haɗu a school shikenan.”

Tayi Maganar tana miƙewa tare da ɗaukar bag ɗin Jamila suka fice ta rakata.

Can kuwa asibiti, likitocin basu fito ba har wajen 8:30 duk jikin doctor musa a sanyaye yake tunda suka hango fitowar sa suka nufosa cikin tashin hankali, Aunty Amarya ce ta riga kowa yin magana har bakinta yana ɓari.

“Doctor ya jikin nata ta farfaɗo kuwa?”

Shuru doctor yayi tare da nufar Daddy ya dafa kafaɗarsa cikin sanyin jiki yace.

“Ka sameni a Office.”

Yayi Maganar yana shigewa, Daddy da Al’ameen tare da Haidar ne sai Faruq da yazo daga baya suka bi bayan doctor da hanzari, Daddy zama yayi tare da duban likitan yace.

“Doctor a wani hali matata take ta farfaɗo kuwa.?”

Doctor kansa ya sunkuyar tare da cewa.

“Bansan taya zan fara maka bayani ba Alhaji Ahmed, nayi mamaki matuƙa da muka samu matarka tasha guba, kuma guba mai ƙarfin gaske wacce take tsinka hanji, sannan kuma kunyi let wajen kawota asibiti.”

Al’ameen ne cike da zaƙuwa yasan wani hali mahaifiyarsa take ciki yace.

“Guba kuma DOCTOR a ina Ummi zata samu guba har tasha sai dai idan itama rayuwarta ake nema kamar yadda aka nemi na ƴaƴanta, amma yanzu tana wani Hali ne shine muke bukatar sani?”

Daddy cike da mamaki shima yace.

“Guba dai, to doctor ka sanar damu mana a wani hali take ciki.

“I am sorry to say, Alhaji Allah ya yiwa matarka rasuwa, munyi iya bakin ƙoƙarin mu domin muga mun ceci rayuwarta amma abun yafi ƙarfin mu, matarka tasha guba ne a cikin abin sha, ma’ana nau’in ruwa na drink, sannan gubar mai ƙarfi ne, ta juma dasha kafin ku kawota asibiti, domin kuwa gubar ta tsitstsinka hanjin cikinta, ta kuma buga mata zuciya,kune kuka makara wajen kawota asibiti, da ace lokacin da tasha gubar kukayi gaggawar kawota asibiti da zamu iya karya gubar sai dai inda aka samu matsalar kafin ku kawota tuni gubar ta gama da hanjinta, kayi hkr Alhaji kwananta ne ya ƙare.”

Wani irin jiri ne ya fara ɗiban Al’ameen kansa dake sara masa ya dafe take idanunsa sukayi jajur cike da tashin hankali marar misaltuwa yake duban doctor.

“Me kake nufi, me kake nufi! Kana nufin Ummina ta mutu, ina ƙaryane ƙaryane Ummi bazata mutu ta barmu ba, Ida wasa kame DOCTOR ka daina!”

Yayi Maganar cikin tsawa yana huci Daddy kusan suman tsaye yayi ya gagara Magana sai kalmar innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Da yake furtawa, Doctor duban Al’ameen yayi tare da cewa.

“Meyasa zan maka wasa da mutuwa, Tabbas ta rasu a yanzu addu’a take nema daga gareku.”

Wani irin ijiyar zuciya Al’ameen yayi tare da huci yana jin ƙirjinsa na masa nauyi wani irin duhu yake gani layi ya fara tamkar zai faɗi Faruq yayi saurin riƙesa shima yana hawaye domin kuwa mutuwa ce mai jijjiga zukata, duban Faruq yayi yana girgiza kansa.

“An kasheta itama an kasheta, an kashe Ummi Faruq! Wh!y Why! Why! Meye mukayiwa rayuwa take juya mu haka, meyasa mutuwa zata rasa waye zata ɗauka sai Ummi, meyasa ni batazo ta ɗaukeni tabar Ummi ba, waye! Waye ne ya saka mata guba meyasa aka mata haka?”

Yayi Maganar yana riƙe ƙirjinsa dake bugawa da ƙarfi sosai yake jin ciwo da zafi a cikin ransa Tabbas kuka rahama shikam kukan ya gagaresa yau da zai samu yayi ya tabbata da zai samu sauƙin zogin da zuciyarsa ke masa, Faruq cike da tausayin Al’ameen ya girgiza kansa yana hawaye yace.

“Ka daina wannan maganar Al’ameen karki saɓo, Tabbas Ummi ta tafi ta barmu munyi rashin Uwa Al’ameen, to ya muka iya bazamu iya dawo da ita ba, ubangijin daya halliceta ya fimu sonta kuma shine ya karɓi abinsa, muyi hkr Al’ameen Tabbas da ciwo.”

Yayi Maganar cikin kuka gami da tausayi.

“Haidar ka faɗa musu Ummi bata mutu ba, ni nasan bazata tafi ta barmu ba, bari ma kuga naje na tasheta ina kiranta zata tashi.”

Yayi Maganar yana miƙewa a zabure ya fita da gudu runtse idanunsa Haidar yayi cike da matsanacin tausayin Al’ameen domin kuwa yafi kowa sanin shaƙuwar dake tsakanin sa da Ummi, Daddy kansa ya girgiza Tabbas yana cikin tashin hankali da tausayin kansa domin kuwa shi yayi Babban rashi hasken gidansa ta tafi ta barsa sai dai yafi tausayin Al’ameen fiye da kansa Haidar da Faruq bayan Al’ameen sukabi da sauri, numfashi Daddy ya saki hawaye na gangaro masa shima ya fita.

Al’ameen yazo dai-dai emargency ya hango ƙafar Ummi an turota a keke za’a kaita mutuware, da sauri ya tare su tare da cewa. 

“Ina zaku kaita kuke turata?”

Wata nurse tace.

“Doctor ne yace mukai gawar mutuware.”

Wani wawan mari ya ɗauketa dashi tare da nunata da yatsa yace.

“Uban waye yace miki ta mutu, waya gaya miki! Ummi bata mutu da ranta kuma yanzu zata tashi ku tsaya ku gani.”

Yayi Maganar yana yaye mayafin da aka rufe Ummi dashi, tana kwance idanunta rufe tamkar mai bacci, su Aunty Amarya da Momma da sauri suka ƙaraso wajen harda Maimu da taci kuka ta ƙoshi duk da bataji labarin mutuwar ba, hanu Al’ameen yasa ya kamo hanun Ummi cikin sanyin jiki yake cewa.

“Ummina ni nasan baki mutu ba, bazaki tafi ki barmu ba, nasani bacci kike dan Allah Ummi ki farka ki faɗa musu da ranki baki mutu ba.”

Yayi Maganar yana jijjigata shuru kakeji koda motsi Ummi batayi ba hakanne ya tabbatarwa Aunty Amarya ta mutu wani irin nishaɗi da farin ciki taji a zuciyarta Al’ameen jin shuru Ummi taƙi motsawa ya sashi kifa kansa jikin ta sai yanzu kuka mai sauti da tsuma zuciya yazo masa.

“An bata guba tasha ta mutu domin kuwa Ummi bata da baƙin cikin da zata sha guba Tabbas bata sani ba aka bata, waye yake kashe mu an ɗauki Rayuwar Ikram anzo ɗaukar na Ashfat Allah ya tseratar da ita, sai gashi anyi Nasara akan Ummi!”

Miƙewa yayi tare da riƙe Haidar ya cigaba da cewa.

“An sawa Ummi guba a cikin gidan mu, Tabbas ko waye yayi wannan kisan ko waye ya tozarta mu ya yanke mana farin cikin mu, nayi alƙawarin ganin bayansa bazan taɓa yafewa wanda ya kashe Ummi ba, wallahi sai nasa yayi mutuwar wulaƙanci wanda koda gawarsa sai tayi wahalar ganewa, na rantse da Allah muddun na gane ko wanene sai na ɗauki fansar jinin Ummi dana ƴar uwata.”

Yayi Maganar yana kifa kansa jikin Haidar tsabar kuka da yake yama gagara Magana, shi a yanzu ya fara zargin akwai mungu a cikin gidan su domin kuwa babu baƙon da zai shigo ya sawa Ummi guba.

AUNTY Amarya yankan jiki tayi ta faɗi tare da suman ƙarya, cikin gaggawa likita yasa aka kwantar da ita, daƙyar aka samu ta farfaɗo da kuka tana ambaton Ummin Al’ameen, sosai take kuka cikin tashin hankali yayin da aka kai gawar Ummi mutuware, Al’ameen tsabar kiɗima da tashin hankali gagara tsayuwa yayi ya juya da gudu ya shiga mota su Faruq basu ankara ba sai tashin motar sukaji da sauri Haidar ya bisa da gudu yana cewa ya tsaya domin kuwa tuƙi a halin da yake ciki akwai matsala sai dai ina kunnen Al’ameen ya toshe baya jinsu gudu kawai yake cikin motar yayinda hawaye ke gudu saman fuskarsa ikon Allah ne kawai ya isa dashi cikin gidan, ko parking bai daidaita ba ya buɗe motar ya fito da gudu ya shigo falon nasu, Inna Jumma da Ablah suna zaune yayin da Ablah ta kwanta cinyar Inna Jumma hawaye na gangarowa daga idanunta sukaga Al’ameen ya shigo da gudu idanunsa duk sun sauya kala ya haura sama bedroom ɗin Ummi ya faɗa tare da nufar inda ya ganta shigowarsa ɗazu hanu yasa ya ɗaga cup ɗin da Ummi tasha maltina yabi sa da kallo hawaye na gudu saman fuskarsa, Tabbas a cikin wannan maltinan aka sawa Ummi guba to waye ne waye ne ya kashe Ummi a cikin gidan nan.

Tambayar da yake jefawa kansa kenan yayin da bashi da amsar tambayar sa, sai dai yafi zargin sai dai ko wani ne daga cikin ƴan aikin gidan aka haɗa baki dasu domin a cutar da ita idanunsa ya runtse hawaye na zuba shikenan yanzu sun cucesa sun rabasa da farin cikin sa.

Ablah da kallo tabi Inna Jumma a tsorace, tare da tashi tace.

“Inna Jumma, akwai abinda yake faruwa a asibitin nan, da alamu Ummi tana cikin gagarumar matsala kiyi duba ga yanayin Yaya Al’ameen ya shigo cikin tashin hankali.”

Tayi Maganar tana miƙewa tare da haurawa sama da gudu, bedroom ɗinsa ta duba baya nan, dawowa tayi ta shiga ROOM ɗin Ummi yana zaune ya takure a gefe sai kuka yake tamkar mace, itama Ablah hawaye ne taji yazo mata da sauri ta ƙarisa ta sunkuya a gabansa tare da cewa,

“Yaya Al’ameen ina Ummi, kukan me kake haka?”

Gagara bata amsa yayi sai kukansa daya tsananta, kanta ta girgiza tare da miƙewa tayi baya tana cewa.

“Ummi ta mutu ko, ta kasheta wannan kukan da kake itace amsar tambayata Ummi ta mutu shikenan hankalinta ya kwanta.”

A firgice ya ɗago yana kallon ta jin kalamanta yana nuni da kamar tasan wacce ta kashe Ummi miƙewa yayi tare da riƙo kafafarta cikin tsawa yace.

“Waye ne! Waye ya kasheta?”

<< Aminaina Ko Ita 22Aminaina Ko Ita 24 >>

1 thought on “Aminaina Ko Ita 23”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.