Skip to content
Part 3 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jin Kai.

Amnat duban Nafeesa tayi tare da cewa.

“Gayen ya haɗu iya haɗuwa ga kuɗi ga wanka ga kuma class, yanzu ke Nafeesa wannan gayen bazaki sosa so na gaskiya ba, idan har kika samu kika auri wannan to wallahi kin dace, amma abun mamaki sai naga kuɗinsa kawai kike so ba shiba, baki taɓa saurayi mai kyau da ajin wannan ba, ƙawata idan zan baki shawara ki ɗauka, wannan gayen gara ki auresa ki huta, Mama ma ta huta, rayuwar barikin nan ba daɗi ne da ita ba, Nafeesa da ace nine na samu wannan damar taki bazanyi wasa da ita ba wajen rufawa kaina asiri, wallahi Auren sa zanyi muyi zaman mu na har abada domin kuwa nasan komai na rayuwa zan samesa.”

Nafeesa taɓe bakinta tayi tare da cewa.

“Ke kike hango wannan kyau da wankan ni ko kaɗan basa gabana, ke nifa babu son Wannan gayen ko kaɗan a zuciyata asali ma bana hango kyawunsa, kuɗin kawai nake son na kwasa, idan na gama samun abinda nake so, yasar da banza zanyi nayi gaba, ke koma ban gama samun abinda nake so a garesa ba, naga wanda ya fisa zan yasar dashi na ɗauki wannan dan haka daina min zancen Aure babu wannan batun baya gabana.”

“Yo amma Nafeesa kina gan…”

“Bar zancen dan Allah ja mota mu tafi kaina ya fara ciwo ga wannan nacaccen Alh Atiku Naira yana jirana.”

Tayi Maganar tana ɗagawa Amnat hanu, Amnat taɓe bakinta tayi tare da jan motar suka bar wajen ba tare da ta kuma cewa komai ba.

Yana parking Rufaida ta fita cikin sauri ta nufi part ɗinsu ranta a cunkushe, Maimu kanta ta girgiza tare da cewa Ya Haidar.

“Ya Haidar bara na shiga part ɗin Aunty.”

Kansa ya ɗaga mata alamun to yana tafiya, Maimu part ɗin Aunty ta shiga da sallama tana zaune ita da Atine Aunty Kanta ta ɗago tare da cewa.

“Maimu lafiya kuwa naga Rufaida ta shigo cikin damuwa?”

Ɗan murmushi Maimu tayi tace.

“Lafiya Aunty wai kanta ke ciwo yanzu ma wayarta na shigo bata, bara na haura na sameta.”

Ta yiwa Aunty ƙarya tana haura bedroom ɗin Rufaida akwance ruf da ciki ta sameta sai kuka take numfashi Maimu ta saki tare da zama gefenta tace.

“Kina bani mamaki Rufaida yanzu meye abin kuka anan bayan kece kike wasa da dukkanin damarki ki tashi muyi magana.”

Miƙewa Rufaida tayi ta zauna tana goge hawayenta tace.

“Wace dama na samu a garesa da har nayi wasa da ita, gani nayi baima san inayi ba, bare kuma har yabani damar da zanyi wasa da ita, ni kaɗai nake dakon sonsa shi baisan inayi ba Maimu anya rayuwa zata yiwu min babu yaya Haidar mtsss!!! Bansan yadda zanyi ya fahimci girman son da nake masa ba zuciyata har nauyi take min wani lokacin.”

“Hmmm!!! Shiyasa nace laifinki ne, kefa macece kuma kina da kyau da diri gami da ajin da namiji zai soki baki da makusa ko kaɗan, to meyasa zaki gagara shawo kan namiji ƙwaya ɗaya ki amshe Soyayyar sa, damar da kikayi wasa da ita, itace Yaya Haidar dai ɗan uwanki ne, kinfi ko wacce mace kusa dashi, wannan babbar dama ce da zakiyi Amfani dashi wajen juyo da hankalinsa gareki, ina fatan kin fahimci abinda nake nufi.”?

“Na fahimta amma meyasa kike basa ƙwarin gwiwwa akan wata mace, kina nuna masa yaso waccar Yarinyar idan tana da nasaba da addini, hakan yamin ciwo a zuciyata mussaman da naji daga bakinki Maganar ta fito.”

Murmushi mai sauti Maimu ta saki har haƙwaranta ya bayyana duban Rufaida tayi tace.
“Ina sane nayi hakan saboda na zaburar dake ki gane cewa muddun baki tashi kin tsaya akan yaya Haidar ba, zaki iya rasashi ya kufce miki, kinga karki tsaya kallon ruwa kwaɗo ya miki ƙafa gara ki fara lalubo Soyayyarki a zuciyarsa tun kafin lokaci ya ƙure miki domin kuwa da alamu hankalinsa ya fara tafiya ga wannan Yarinyar.”

“Maimu da alamu kin fini gogewa a wannan fagen, ki sani a hanya domin ƙwato Soyayyata.”

Murmushi Maimu ta saki tare da cewa.

“Angama ƴar Uwata, insha Allah sai Yaya Haidar ya dawo hanunki zai soki Soyayya mai tsanani zai kalli dukkan wasu mata tamkar maza kece kawai zaki kasance mace a idanunsa.”

“Na yarda dake Maimu nasan zaki iya.”

Murmushi Maimu tayi tare da miƙewa tana cewa.

“Bara na ƙarisa part ɗin mu, nasan yanzu Ummi na jirana akwai aiki sai kin shigo.”

Har falo Rufaida ta rako Maimu ta wuce sannan ta koma.

Hajiya Mansura na faɗa miki hankalina bazai taɓa kwanciya ba muddun ina kallon Ummin Al’ameen da waɗannan yaran nata shida reras, wallahi zuciyata tamkar zata buga haka nake ji, mtsss ya kamata musan abun yi na gaji da zura idanu ina kallo wata rana tazo ta ƙwace dukiyar Daddyn Al’ameen ni a barni da ɗan kaɗan, domin kuwa ko yau Daddyn Al’ameen ya faɗi ya mutu Ni ce na shiga Uku bazan mori komai ba, yara mata biyu fa kawai nake da, ita kuwa maza biyu mata huɗu, shikenan ta ƙwace dukiyar ni ta barni a wulaƙance, Hajiya Mansura ya zanyi da wannan Ƙaddararriyar matar.”

Aunty Amarya ce mai wannan maganar cikin matsanancin tashin hankali, Hajiya Mansura Numfashi ta sauƙe tare da nisawa tace.

“Ki kwantar da hankalinki Amarya kin san dai bana taɓa rasa mafita, kefa Amarya ki godewa Allah domin kuwa kece mai nasara akan Hajiya Gaji, domin kuwa zaki zame mata macijin sari ka noƙe ne, karki manta da cewa zuwa yanzu Hajiya Gaji ta gama yarda dake, bazata taɓa tunanin cewa zaki cuceta ba, kinga ko dama abinda muke buƙata kenan ta yarda dake, aikin mu zai fara ne daga yanzu, ni na gama yanke hukunci, yawan yaran nata zamu rage mata, gara ku dawo dai-dai.”

Cike da rashin fahimta Aunty Amarya tace.

“Mu rage yawan ƴaƴanta kuma, ban gane abinda kike nufi ba?”

Murmushi Hajiya Mansura ta saki tare da miƙewa tsaye ta goya hanunta a bayanta tare da cewa.

“Bamu da wata mafitar da ta wuce muyi kisan kai, zamu saka a kashe ƴaƴanta huɗu abar mata biyu, kinga kunya Drow.”

“To amma Hajiya Mansura anya wannan shawarace wacce zata yiwu kuwa, akwai hatsari fa sosai cikin wannan aikin, sannan idan asirin mu ya tonu mun shiga Uku.”

“hmmm to ƙarya kike hankalinki baya tashi idan kingan su domin kuwa da hankalinki yana tashi bazaki kawo tsoro cikin ranki ba, kinga Amarya muddun kina neman biyan buƙatar ki, dole ne sai munyi kisan kai, idan kuma kika saka tsoro cikin zuciyarki kina kallo ALH AHMAD zai faɗi ya mutu, ki tashi da tumulin takaba kawai kinyi zaman iska, sai dai kiga Hajiya Gaji ta kwashe dukiyar.”

Shuru Aunty Amarya tayi cike da nazarin maganganun Hajiya Mansura Tabbas idan ta tsaya kallon ruwa tofa kwaɗo zai jefa mata ƙafa to ma tsoron me zataji ita da kowa ya gama amincewa da ita a cikin gidan, murmushi ta saki mai sauti tare da cewa Hajiya Mansura.

“Kina da gaskiya muddun nayi wasa to fa zanga wasa, shata min layi kawai na hau hanya, idan ta kama ko Ummin Al’ameen ɗinne itama sai mu aikata”

Dariya Hajiya Mansura ta saki mai sauti tare da cewa.

“Good Ƙawata, yanzu abinda zai faru bari muga tana da yara shida Al’ameen Maimu Khalifa ashfat Samira And Khairi, shi Khalifa da ashfat suna London karatu ba, ita kuma Samira tana boarding school, zamu fara da Khairi ita zamu fara kashewa, da ita zamu fara musu Sallama na Tabbata kuma babu mai zarginki, domin akwai Amana da yarda tsakanin ku, Isah Alolo zamu saka yayi kisan, ki turo min pictures ɗin ta da zan basa sannan ki saka mana ido akan fitarta da kuma wajen da zataje ta, shi kuma zaiyi amfani da wannan Detail ɗin wajen iske ta, naji alart na dubu ɗari huɗu, mu basa na aiki, sannan..”

“Aunty Amarya!!! Aunty Amarya!!! Aunty

Amarya!!!”

Muryar Maimu ya dakatar da Hajiya Mansura da Maganar da take jiyo sautin kiran da take yiwa Amarya, Aunty Amarya amsawa tayi, Maimu ta shigo cikin nutsuwa, Murmushi tayi ganin Hajiya Mansura, tace.

“Momy Mansura, sannu da zuwa ashe kina ciki.”
Hajiya Mansura murmushi ta saki cikin sakewar fuska tace.

“Ina ciki yanzu ai nake tambayar Amarya ku, ya karatu.”

“Karatu Alhamdulillah!! Amm Aunty Amarya key ɗin motar ki zaki ara min zanje gidan su Safara’u zan amso assignment ɗina, tawa motar tayar ta samu matsala sai an sauya wata, kuma babu wata tayar, Ummi kuma ta hanani nata, nasan kekam bazaki hanani ba Aunty Amarya.”

Murmushi Aunty Amarya ta saki tare da cewa.

“Oh Ummin Al’ameen sai kace wanda zaki cinye motar, ai kuwa bazan hanaki ba, kije falo na, tana kan desk ki ɗauka.”

Da to Maimu ta amsa tare da ficewa tana dariya, Hajiya Mansura bakinta ta taɓe suka cigaba da ƙulla ƙullar su, ta juma sosai cikin room ɗin Aunty Amarya kafin ta tafi.

“Oh ni jikar mutum Huɗu, Amarya kizo ki rabani da wannan ja’irar Yarinyar taki, tabi ta isheni, sai famar ɓuruntu take min.”

Ummi dake zaune gefe tare da Aunty Amarya ne tayi dariya tare da cewa.

“To fa yau kuma Minal da Inna ne ake faɗa, Amarya sai ki tashi kije rabiya kafin a kaure da kokawa.”

Dariya Aunty Amarya tayi tace.
“A’a Ummin Al’ameen ni babu ruwana kece zakije wannan rabiyar faɗan.”
Ummi murmushi tayi tare da ƙwalawa Minal kira, tana cewa.

“Meena ta, mazo zoki amsa rabu da Inna kizo wajen Ummin ki.”

Minal baki ta tura tare da miƙewa tana tura bakin ta taho, Khairi ce ta shigo hanunta riƙe da school bag tayi matuƙar gajiya jikin Aunty Amarya ta faɗa kasancewar tayi sabo sosai da ita tamkar Ummi haka takejin Aunty Amarya.

“Aunty Amarya yunwa nakeji, yau Ummi ƙwai kawai ta soya min Allah duk ban ƙoshi ba yunwa nakeji.”

Girgiza kanta Ummi tare da cewa.

“Ina kuwa zaki ƙoshi aike bakya ƙoshi Khairi cikin ki zurfi garesa komai kikaci anjuma babu, ke gaki uwar ci.”

Aunty Amarya ce tace.

“Ummin Al’ameen babu ruwanki cikin wannan lamarin, bafa dake take Magana ba, Auntyn ta take faɗawa, dan haka karki shiga tsakanin ƴa da Uwa, tashi muje Khairi na, na haɗa miki abinci ko.”

Khairi gwalo ta yiwa Ummi tare da miƙewa tabi bayan Aunty Amarya, Ummi murmushi tayi sosai take jin daɗin yadda Aunty Amarya ta ɗauki yaranta tamkar nata ƴaƴan babu wani banbanci.

Hancin motarsa ya danno cikin Companyn, a parking space yayi parking tare da fitowa fuskarsa sam babu alamun dariya, tunda ya fito ma’aikatan suke risinawa suna gaishesa, amma tsabar MISKILANCI irin na Al’ameen hanu kawai yake ɗaga musu babu wanda ya amsawa gaisuwar, harya shige Office ɗinsa, Ibrahim ne ya taɓa Salihu tare da cewa.

“Wallahi na tsani gaishe da mutumin, ya cika girman kan tsiya, mutum shi kullum babu rahama a fuskarsa, gaisuwa ma ya amsa yana ganin asara ne mtsss Allah ji nake kamar nabar aiki a Companyn nan saboda mutumin nan.”

Salihu dariya yasa tare da cewa.

“Ko kaima ka faɗa, amma ni sai nake ganin kamar ba baƙin hali bane, haka yanayin sa, yake, idan ka lura shifa koda ma’aikata masu office bai cika magana ba, saɓanin Oga Haidar dashi babu ruwansa kowa nasa ne.”

“Hmmm koma yaya ne shi dai ya sani bara naje na sanar da Oga Haidar ya shigo yace idan ya shigo nazo na sanar dashi.”

Da to Salihu ya amsa kowa yayi wucewar sa harkar sa.”

Office ɗinsa ya shiga ya zauna yana jawo takaddun dake ajiye saman table ɗin, ya fara dubawa, ya ɗan juma cikin Office ɗin Haidar ya shigo zama yayi tare da fuskantar sa, yace.
“Wai kunyi waya da Faruq kuwa zuwa yanzu yaci ace sun isa just 9 hours fa, na kira layin nasa baya tafiya.”

Ɗagowa Al’ameen yayi tare da ajiye biro dake hanunsa yace.

“Numbern sa bazai shiga ba ai dole sai ya sauya layi, maybe zuwa dare zai kira.”

Yau naga mood ɗinka ya sauya meke faruwa da alamu kana cikin farin ciki.

Murmushi Haidar ya saki yana lumshe idanunsa tare da dafe ƙirjinsa yace.

“Nayi kyakkyawan kamu ne Al’ameen?”

“Kyakkyawan kamu kuma to faɗi muji na tayaka farin cikin.”

Ɗan dariya Haidar ya saki tare da cewa.

“Budurwa nayi kuma dai da alamu matar Aure na samu, gay zan rigaka Aure fa, kyakkyawa ce ta ajin farko, har yanzu sunanta yana ajiye a zuciyata Nafeesa, sai dai fa na kasa tunkararta da alamu bata ma san ina sonta ba.”

Tsuka mai ƙarfi Al’ameen yaja tare da haɗa fuskarsa tamau yace.

“Mtsss!!!! Aikin banza ni nayi zaton wata magana mai mahimmanci zaka faɗa min ashe wannan shirmen banzan ne, yanzu kai Haidar akan mace kake wannan dariyar haka, to kabi a sannu domin kuwa mata sheɗanune mafi yawansu ba ko wacce mace bace zata soka saboda Allah, mafi akasarin su, sunfi son mutum dan kuɗin sa ko saboda kyawunsa, dan haka ka kiyaye kasan irin macen da zaka kula.”

Murmushi Haidar ya saki tare da cewa.

“Hmmm!!!! Ba dukkan mata bane suke da fuskar daka ambata zato zunubine koda ya kasance gaskiya, idan zakayi mu’amala da mutum ka kyautata masa zato, ni dai ina sonta kuma ina ji a jikina ta gari ce, ina sonta sosai Al’ameen ya kamata ka tayani son abinda nake so.”

“Haidar kenan, duk da bansan wacce kake Magana a kanta ba, sai dai zuciyata bata kwanta da ita ba, sai nakeji a jikina kamar bata dace da rayuwarka ba, kana da right ɗin da zakayi rayuwa da abinda kaso, amma ina ƙara tuna maka, kafin ka amince da Mutum ka fara zurfafa tunani da bincike akansa domin gano ainihin wayeshi.”

“Hmmm!!! Al’ameen…”

Hanu Al’ameen ya ɗaga masa tare da cewa.

“Basai kace komai ina maka fatan alheri Allah yasa ta gari ce.”

Da ameen Haidar ya amsa kafin suka koma magana akan Companyn su, sune basu tashi ba sai 5:30pm kowa motarsa ya hau suka taho tare.

Da misalin goma na dare Al’ameen ya sauƙo falo hanunsa riƙe da wayarsa, kusa da Aunty Amarya ya zauna yana cewa Maimu.

“Ke Maimu jeki kawo min abinci na nan”

Da to Maimu ta amsa ta je ɗauko masa, Aunty Amarya ce tace.

“Al’ameen ɗazu Khairi take cemin wai kace gobe bazaka kaita school, kuma dai ka sani bata yadda kowa ya kaita school idan ba kai ba.”

Al’ameen duban Aunty Amarya yayi tare da cewa.
“Aunty drever ya kaita ni ina da meeting da ma’aikata 7:30am bazai yiwu na Kaita school ba, gaskiya sai dai tayi hkr kawai drever ya Kaita.”

Aunty Amarya cike da nuna ta isa da Al’ameen tace.

“Dole fa kai zaka kaita, idan yaso idan ka sauƙeta sai ka shige Companyn, tunda akwai Haidar sai ya wakilce ka kafin ka iso.”

“Amma Aunty Amarya wannan meeting ƊIN fa yana da…”

“Kaga ban tambayeka hujja ko dalili ba, umarni kawai nake baka ka kaita school idan kuma bazaka bi umarnin nawa ba, sai naji.”

Numfashi Al’ameen ya saki dai-dai Maimu ta kawo masa, dakakkiyar doya wacce tasha jar miya, gabaki ɗaya rabin miyar nama ne, table ɗin tsakiyar falon ta jawo ta ajiye masa a gabansa tare da ɗaura abincin a kan table ɗin ta juya kawo masa ruwa, duban Aunty yayi tare da cewa.
“Ni na isa naja da umarninki Aunty Amarya, amma dai ki sani Allah muddun bata shirya da wuri ba, tafiya ta zanyi sai dai ta hkr da zuwa school ɗin.”

Ya yi Maganar cike da biyayya tamkar da ummi yake Magana domin kuwa duka ɗaya ya ɗauke su babu bambanci yanda yake yiwa Momy biyayya itama haka yake mata, murmushi Aunty Amarya tayi tare da cewa.

“Yauwa ko kaifa, bara ma tayi latti ba, ni da kaina zan tashi na shiryata da wuri saboda karma ka mana mita.”

Murmushi Al’ameen yayi tare da saka spon da Bismillah ya fara cin abincin, Afnan ce ta sauƙo daga sama jikinta sanye da three cutter ɗin wanda da kuma best fara sol mai shara shara duk ana hango rigar mamanta, ko a jikinta ta nufosu kasancewar Afnan bata da kunya ko kaɗan idanun Al’ameen ne ya sauƙa a kanta da take nufo su, ajiye spon ɗin yayi cikin ɓacin rai, cike da tsanar Afnan domin kuwa ba Yarinyar ya tsana ba, munguwar ɗabiarta da rashin kunyarta ya tsana, a kaf ƙannansa yafi jin haushinta, cikin tsawa mai rikitarwa yace.

“Keee!!!!!! Mahaukaciya, baki da hankali ne, ko jaka ce ke, juya ki koma ki cire waɗannan matsiyatan kayan, karki kuskura ki iso nan, domin kuwa kina isowa zan karyaki, wawiya wanda bata san darajar kanta ba.”

Ai kuwa kaf wajen sanda kowa ya tsorata da jin tsawar Al’ameen gabaki ɗayansu da kallo suka bita, girgiza kanta Ummi tayi cikin takaicin halin Afnan ta hauta da faɗa.

“Haba Afnan, bakya gani ne zaki fito da wannan best ɗin cikin mutane ko kin manta idan mu iyayenki ne, Haidar da ma’aikata suna shigowa cikin falon nan, mutunci ne su ganki a haka, meyasa ke kike da taurin kai ne baki jin Magana, ki koma kije ki sako rigar mutunci ki dawo.”

Wani irin haushi Aunty Amarya taji jin zagin da Al’ameen da Ummi suka yiwa ƴarta Afnan, amma tsabar iya makirci na Aunty Amarya sai itama ta hau Afnan da nata faɗan amma cikin zuciyarta tana cike da haushin Ummi da Al’ameen.
“Ba magana ake miki bane Afnan kike tsaye, ki juya kije ki sauyo wasu kayan, shasha marar jin magana.”

Afnan bakinta ta tura cikin ɓacin rai da rashin kunya tana ƙunƙuni ta haura tana cewa.

“Ni a gidan nan duk abinda nayi ba dai-dai bane saboda kawai an tsaneni.”

Tayi Maganar tana haurawa, Aunty Amarya miƙewa tayi tare da cewa Ummi.

“Bara dai nabi Yarinyar nan naci ubanta.”

Tayi Maganar tana haurawa da sauri Ummi bata ce komai ba ta cigaba da kallon tv, shi kuwa Al’ameen ji yake a ransa wata rana sai ya karya Afnan Tabbas.

Koda Aunty Amarya ta haura bata kalli room ɗin su Afnan ba, ta shige nata bedroom ɗin zama tayi tare da cewa.

“Aikin banza aikin wofi, matsiyata, sun saka min yarinya a gaba duk neman su cinye min ita, kuma wallahi aniyarku sai ya biku dole ne ma na nemawa Afnan maganin baki, ɗan iska mai jajayen kunnuwa sai famar zazzaga mata zagi kake, to uwarka ce ka faɗawa jakar, kafin kuwa kuga bayan Afnan duk sai naga ƙarshen ku.”

Tayi Maganar a fusace tana ɗago wayarta ta dannawa Hajiya Mansura kira ringin ɗaya ta ɗaga Aunty Amarya ce tace.

“Ɗazu na miki transfer ɗin kuɗin da kikace zasuyi aikin, gobe nake son a kashe Khairi, zataje school da misalin 7:39am su tashi 2:15pm ki sanar da Isah Alolo cewa zan ɓatawa drevern da zai ɗaukota lokaci, har sai wajen 4 idan ta gaji da jira zatace zata fito ta tari adaidaita ta dawo gida, shi kuma sai yayi amfani da wannan damar yaje ya ɗauketa gawarta kawai nake buƙatar ya dawo gidan ba tare da ruhi ba ba kuma na son kuskure cikin aikin yayi komai cikin kula.”

Dariya Hajiya Mansura ta saka tare da cewa.

“Baki da matsala ki saka a ranki Khairi ta zamo gawa, kinsanni bana kuskure cikin aiki na komai zai tafi dai-dai.”

Aunty Amarya Numfashi ta saki tare da katse kiran ta buɗe data hoton Khairi ta tura mata, sannan ta ajiye wayar tana sakin murmushi mai sauti tare da cewa.

“Duk ɗan da ya hana uwarsa bacci, shima kuwa bazai runtsa ba, nine nan zanga bayanki Hajiya gaji.”

<< Aminaina Ko Ita? 2Aminaina Ko Ita? 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×