"Okay to shikenan na fahimta bara na miki transfer ɗin kuɗin amma ya kamata ace zuwa wunin gobe ki gama komai cikin gaggawa muke buƙatar wannan aikin."
"Karki damu Amarya kinfi kowa sanin wacece Mansura komai zai tafi dai-dai ke dai ki kwantar da hankalin ki domin kuwa asirin mu bazai taɓa tonuwa ba har abada mune da nasara sai burinmu ya cika."
Numfashi Aunty Amarya ta saki tare da cewa.
"Na sani bazaki bani kunya ba sai dai fa ni tsorona meye wannan wanda sukayi waya da Al'ameen ya gano ina tsoron kar ayi. . .