Skip to content
Part 30 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

“Okay to shikenan na fahimta bara na miki transfer ɗin kuɗin amma ya kamata ace zuwa wunin gobe ki gama komai cikin gaggawa muke buƙatar wannan aikin.”

“Karki damu Amarya kinfi kowa sanin wacece Mansura komai zai tafi dai-dai ke dai ki kwantar da hankalin ki domin kuwa asirin mu bazai taɓa tonuwa ba har abada mune da nasara sai burinmu ya cika.”

Numfashi Aunty Amarya ta saki tare da cewa.

“Na sani bazaki bani kunya ba sai dai fa ni tsorona meye wannan wanda sukayi waya da Al’ameen ya gano ina tsoron kar ayi wata magana game dani kin ga har yanzu burina bai cika ba bana son na faɗi ba tare da nasara ba.”

“Hmmm! Amarya Ni ce fa Mansura meyasa kike mantawa da sheɗanci nane karki manta fa, bamu bar ƙofa koda kanƙani bane wanda wani zai fuskanci halin da muke ciki bare yayi tunanin tona mana asiri, Ablah itace kawai tasan sirrin mu, ita kuma bata da hujjar tona mana asiri dan haka ki kwantar da hankalin ki, itama Ablar zamu kawo ƙarshenta.”

“Hmmm! Shikenan Hajiya Mansura na gode.”

“Okay yayi sai najiki.”

Tayi Maganar tana kashe wayar numfashi Aunty Amarya ta saki tare da goge gumin fuskarta ta sauƙo falon a daining table ta hango Al’ameen da Daddyn sa a zaune sai su Maimu sauƙowa tayi ta ƙariso daining ɗin tare da zama.

“Good morning Aunty.”

Al’ameen ya gaisheta cikin sakewar fuska shi tuni ma ya manta abinda ya faru jiya murmushi ta saki ta amsa.

“Morning Al’ameen harka fito kenan, yau akwai Office ko.?”

“Eh yau Monday akwai Office, amm Daddy ɗazu fa nayi sammakon kai Ablah police station saboda na musu alƙawari, kuma dole mu maida hankali akan wannan Case ɗin domin kuwa bazan iya yafe jinin Ummi ba, dole ne a gano koma wanene yake wannan kisan domin ɗaukar mataki, bazamu yadda da kowa ba wanda har zamu ji zuciyarmu ta bamu bashi bane yayi kisan, duk wanda bincike ya faɗa kansa koda kuwa nine ko kai a shirye nake sai dai ban sanar da Inna Jumma cewa na kai Ablah police station ba, na sanar da ita taje school ne kuma zata shige gidan su ta kwana gudun faɗan Inna Jumma yasa nayi wannan ƙaryar.”

Ɗan murmushi Daddy ya saki tare da furta.

“Good Zakina Gara da kayiwa Inna haka, idan ba haka ba yau wuni za’ayi ana rikici da ita, ni kaina wannan kisan da barazanar da ake yiwa rayuwar iyalina yana ɗaga min hankali, dole ne gano ko wanene maƙiyin mu dake kawo mana farmaki, zamuyi waya da commissioner a tabbatar da an gano gaskiya akan wannan Yarinyar domin ina nazarin wasu abubuwa game da ita.”

AUNTY Amarya numfashi ta saki tana duban Daddy da Al’ameen, wai bazasu ƙyale maƙiyinsu ba, (hmmm! Ai kowa dole ƙyale wannan maƙiyin domin kuwa sai yaga ƙarshen ku) tayi Maganar zucin tana yamutsa fuska cikin nuna alamun tashin hankali tace.

“Ya kamata kam gaskiya domin kuwa mu kammu da muke cikin gidan nan rayuwa muke cikin tsoro Saboda bamu san ran waye kuma za’a hara ba a nan gaba, kaga muna cikin tashin hankali ni wallahi cikin tsoro nake a gida kana tsoro haka ma idan ka fita waje, sam bamu da nutsuwa wannan wacce irin rayuwa ce.”

Maimu ce tace.

“Hakane Daddy ni kaina Wallahi cikin tsoro nake, ko abincin gidan nan har ta ga ruwa cikin tsoro nake sha a cikin gidan nan muna cikin tsoro a waje ma bamu tsira ba, abun yayi yawa Daddy ka duba kaga Ashfat a sanadin wannan barazanar ta rasa ƙafarta ga kuma Aknam ta rasa rayuwarta ga Ummi, rai biyu akayi asara a cikin gidan nan da ƙafa ɗaya, kaga dole hankalin mu zai kasance kullum a tashe ya kamata a kawo karshen wannan tashin hankalin Daddy domin kare rayukan mu da alamu wannan tsinannen mai kisan so yake ya ƙarar da dangin mu, kuma Daddy ita wannan Ablah fa zai iya kasancewa itace tayi kisan saboda bamu santa ba rana tsaka aka kawota cikin gidan nan, wataƙil Saboda haka ta dinga bibiyar yaya Al’ameen domin ta samu ta shigo gidan nan ta cutar damu, ni dai ina ji a jikina itace tayi kisan.”

Afnan ce tace.

“Zato zunubine Maimu koda ya kasance gaskiya, ni fa wallahi ban yadda wannan Ablar zata iya kisan kai ba, kina kallon yarinya salaha babu ruwanta da wani bata damu da duniya ba, ta yaya zata iya kisan kai, ni Wallahi ban yadda itace tayi kisan nan ba kuma ni abinda na lura dashi a wannan barazanar da ake mana, ƴaƴan Ummi kawai kaiwa hari saboda dani da ihsan da Aunty kama Inna Jumma da part ɗin su yaya Haidar da yaya Faruq duk ba’a barazana ga rayuwar su sai na ƴaƴan ɗakin Ummi, yaya Al’ameen akwai lauje cikin naɗi acikin wannan lamarin.”

Aunty Amarya zaro idanunta tayi tana kallon Afnan, (kuji shegiyar yarinya mai shegen baki to me take nufi, lallai kuwa zanci ubanki da alamu zan kawo miki harin ba dan kin mutu ba, sai dan na kore wannan zargin a zuciyarki.)

Muryar Al’ameen ne ya katse mata zancen zucin da take.

“Na juma da fahimtar wannan Afnan dalilin kenan da yasa na tsananta bincike kuma insha Allah koma wanene na kusa ganowa kuyi haƙuri ku kwantar da hankalinku babu abinda zai sameku, saboda gomnati ta bawa Daddy jami’an tsaro domin kare lafiyar mu, daga yau babu mai fita shi kaɗai sai da hukuma.”

Daddy ne ya nisa tare da cewa.

“Eh daga yau babu mai fita shi kaɗai a cikin gidan nan sai da hukuma saboda kare rayukanku ku kiyaye.”

Sun ɗan juma suna tattaunawa kafin sukayi breakfast ɗin kowa ya watse Inna Jumma ita yau dama kai mata nata akayi bedroom ɗin ta.

Al’ameen a harabar gidan ya ga Haidar tsaye yana jiransa musabaha sukayi tare da buɗe motar suka shiga…

Tuƙi yake cike da nutsuwa ya kunna ƙira’ar Sheikh munshawi suna sauraro a nutse sun ɗanyi nisa da tafiya Al’ameen yaji saƙo ya shigo cikin wayarsa, hanu yasa ya ɗago wayar yana kallon Haidar da duk ransa ke ɓace da alamu baya cikin Happiness, wayar ya duba.

_Soyayya tsiro ce dake tofowa mutum ba tare daya shirya ba ko yayi shawara dashi, zuciyar so sam bata da haƙuri idan ba ta samu abinda take so ba, takan birkice harma ta haukace idan ta rasa muradin ta, ni kaine muradin zuciyata kuma mahaɗin bugunta ina sonka._

Ya karanta saƙon cike da mamaki, ƙara maimaita karantawa yayi yana kallon numbern da aka kirasa dashi, wannan numbern ne dai wanda aka kirasa dashi daren jiya, bakinsa ya cije tare jan doguwar tsuka yana goge saƙon daga cikin wayarsa, dubansa ya kai ga Haidar tare da cewa

“Aliyu!”

Ɗago idanunsa Haidar yayi tare da kallon Al’ameen daya kirasa da normal sunansa.

“Kayi mamaki na kira ka da Aliyu ko, Me yake damunka ne da alamu kana cikin damuwa.?”

Numfashi Haidar ya saki damuwar Nafeesa ke damunsa tun jiya baisan wani hali take ciki ba, ya kirata ba amsa mtsss yaja tsuka tare da cewa.

“Hmmm! Maganar ba ta mota bane Al’ameen amma dan Allah muɗan biya gidan su Nafeesa mana idan babu damuwa.”

“Na fahimci matsalar kun samu saɓani da gimbiyar taka kenan ko, no problem da ina son zan biya Companyn su khalil ne akwai binciken da na saka yamin akan Ablah so amma ba damuwa muje gidan su Nafeesan idan yaso shi khalil na masa waya yazo Company mu tattauna, amma ni fa Haidar zuciyata bata yadda da wannan Yarinyar Nafeesa ba, ka sata a zuciyarka Sosai sai nake ganin Kamar ba yarinya mai gaskiya bace amma babu yadda na iya da zuciyarka Saboda ta mace akanta sai dai kayi taka tsantsan gaskiya ni ban yarda da Yarinyar nan ba.”

Duban Al’ameen Haidar yayi ba tare daya tanka masa ba domin kuwa yadda yake jin zuciyarsa ko magana baya son yi, shima dai Al’ameen bai kuma Magana ba har suka isa ƙofar gidan su Nafeesa, parking yayi tare da duban Haidar yace.

“Sai ka kirata.”

Hanunsa Haidar yasa cikin aljihun sa zai ciro wayarsa wayam babu wayar shuru yayi yana tunani, tsuka yaja tare da cewa.

“Kaga na manta wayar ma bedroom ɗina, bani taka na kira ta.”

Miƙa masa wayar Al’ameen yayi numbern Nafeesa ya saka tare da danna mata kira.

Spoon ta ɗago zata kai abinci bakinta taji wayarta tayi ƙara, ijiye spoon ɗin tayi tare da ɗago wayar numbern Al’ameen, ɗan zaro idanunta tayi tare da furta.

“Al’ameen kuma ya kirani da ainihin numbern wayata, ko dai ya fahimci nice nake kiransa da special number na, shine zai kirani.”

Ɗan murmushi ta saki zuciyarta na cewa.

“To meye a ciki idan ya gane kece kike kiransa dama ai dole yasan kece, damuwar me zakiyi keda kika shiryawa yaƙi domin sa.”

Murmushi Ablah ta saki kiran har ya tsinke wani ya kuma shigowa hanu ta saka ta ɗaga kiran tare da cewa.

“Assalamu alaikum da wa nake Magana.?”

Numfashi Haidar ya saki yana lumshe idanunsa jin muryar Nafeesa da alamun tana halin lafiya numfashi ya sauƙe tare da cewa.

“Ameen wa’alaiku mussalam Duniyata.”

Dam ƙirjin Nafeesa ya buga jin muryar Haidar ranta ne ya ɓaci muryar Al’ameen taso ji ba muryar sa ba, ranta ta haɗe muryarta a daƙile ta amsa.

“Farin ciki na dama kaine ka kirani da baƙuwar Number, numbern waye wannan ɗin.”

Murmushi Haidar ya saki tare da cewa.

“Numbern Al’ameen ne, muna ƙofar gidan ku kiyi sauri dan Allah zamu shige Company time na ƙurewa.

“Okay gani nan fitowa.” tayi Maganar ta miƙewa da kallo Nazifa ta bita tare da taɓe bakinta.

A tsaye ta samu Haidar jikin mota.

Dube dube ta fara ta ina zata hango Al’ameen sai dai ko ƙeyarsa bata hango ba, yana cikin mota wacce take da baƙin glass wato tintak, tsayawa tayi tana ɗan yamutsa fuska.

Haidar numfashi ya saki yana duban Nafeesa har cikin zuciyarsa yake jin Soyayyar ta yana ratsasa.

“Har naji sanyi dana ganki nayi missing ɗin ki farin cikina hankalina ya tashi jiya banyi baccin kirki ba, nata kiran wayarki bakya picking ƙarshe ma aka kashe wayar, nayi zaton ba lafiya ba shiyasa duk hankalina ya tashi, na kuma tura miki text shima ba reply amma alhamdulillah! Tunda kina lafiya.”

“Ayya naga kiranka da daddare wayar bata hanuna ne tana hanun Maryam, nima sai dare ta kawo min wayar ƙauye naje sai na bar mata wayar shiyasa aka samu wannan matsalar.”

“To amma Nafeesa meyasa da kikaga kirana baki biyo baya ba, kin san tashin hankali dana shiga kuwa.”?

“Dare ne yayi shiyasa ban biyo kiran ba, nayi tunanin kayi bacci, amma ai tunda kaga ina lafiya ai magana ta ƙare ko, ni zan koma aiki nake yiwa Baba na fito sai anjuma.”

Tayi Maganar tana juyawa ba tare da ta saurari mai Haidar zaice ba, da kallo ya bita yana mamakin sauyawar da ta masa daga jiya zuwa yau, sai dai dole zai mata uzuri da alamu akwai abinda ke damunta ne, motar ya buɗe tare da duban Al’ameen yace.

“Muje.”

“To Mister romio”

Ya masa maganar cikin zolaya murmushi Haidar ya saki Al’ameen yaja motar suka bar wajen.

 Zaune take ta takure waje guda cike da tashin hankali duhu ne baƙiƙƙirin a cell ɗin da aka ijiye ta, hawaye ne suke gudu saman fuskarta bata taɓa zaton zata zo koda duba wani bane cikin police station bare tayi tunanin ita za’a kawo, sosai take kuka harda majina, kalaman Al’ameen su suke mata yawo a cikin kunnuwanta wato shima kansa zarginta yake Lallai wannan Duniyar tana da ban al’ajabi, wani da aikata laifi wani dabam kuma da karɓar hukunci wannan wacce irin rayuwa ce, haskota da aka yi da totila mai bala’in haske ne har sai da ta rufe idanunta shine ya katse mata zancen zucin nata.

“Taso muje munafuka yarinya ƙarama dake har kinsan kiyi kisa ki ɓata Rayuwarki Case ɗinki yana hanun *Dsp Habu Sarki* kin shiga hanu yarinya babu sassauci.”

Hawayen fuskarta Ablah ta goge tare da miƙewa tsaye ta biyo bayan sa wani ɗaki daban aka kuma kai ta mai ɗauke da kujera biyu da tebur a tsakiyar kujerun.

Nuni ya mata da kujera ɗaya ya bata umarnin ta zauna, zama tayi a takure ya fice ya barta bata juma da zama ba Dsp Habu Sarki ya shiga fuskarsa a ɗaure babu alamun wasa fari ne sol dogo kyakkyawa, babu uniform ɗin police a jikinsa normal kaya ne a jikinsa zama yayi tare da furta.

“Ablah Yahya Sani, muna zarginki da kashe Hajiya gaji Uwar gidan AMBASSADOR AHMAD GIWA, meyasa kika kasheta.?”

Kanta Ablah ta girgiza hawaye na tsere saman fuskarta tace.

“Bani na kasheta ba.”

“Okay bake bace to waye ya kasheta.?”

“Ban sani ba ranka ya daɗe bani da masaniya akan wannan kisan.”

 Teburin gabansa Dsp Habu Sarki ya daka da ƙarfi cikin tsawar da ta firgita Ablah yace.

“Ƙarya kikeyi kece kika kasheta, ki daina min wannan kukan munafurcin ki sanar dani meyasa kika kasheta, idan ba haka zaki faɗa cikin azaba tunda bazaki faɗa ta ruwan sanyi ba?”

Hawaye ne ya zubowa Ablah a firgice take domin kuwa tsawa yana gigitata kanta ta hau girgizawa cike da tsoro ta gagara magana.

“Karna kuma ganin wannan Hawayen naki idan ba haka ba na tsiyayar miki da idanu, munafuka, zakiyi Magana ne ko sai na saka an illata min ke?”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Aminaina Ko Ita 29Aminaina Ko Ita 31 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×