Skip to content
Part 29 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

“Saboda alamun rashin gaskiya sun bayyana a gareki, da farko tun rasuwar Ummi kin furta cewa *shikenan ta kashe ta huta* kuma da kunnena naji kin ambata amma kince ke baki faɗa ba, ga kuma shatin yatsun ki jikin cup din da aka sawa Ummi guba, yanzu kuma na miki tambaya kin kasa amsa min hakan yana nufin baki da gaskiya kenan.”

“Menene zaisa na kashe Ummi, meye ribata idan na yi hakan?”

“Nima abunda nake son na sani kenan meyasa kika kasheta?”

Yayi Maganar yana taka burki a gefen titi tare da zarowa Ablah ido ransa a haɗe tamau ya cigaba da cewa.

“Kece kika kashe Ummi, dan haka ki faɗamin gaskiya meyasa kika kasheta, tun muna mu biyu domin kuwa ni sai na iya rufa miki asiri ki tuba zuwa ga Ubangijin ki, amma hukuma bazasu taɓa ɗaga miki ƙafa ba ki sanar dani meyasa kika kasheta?”

Raurau idanun Ablah tayi hawaye ya cika mata idanu wato dai kowa ya yarda cewa itace tayi kisan, kanta ta girgiza tare da cewa.

“Ban taɓa kisan kai ba, kuma bana fatan nayi, bana tsoro dan za’a kaini hanun police domin kuwa nasan ina da gaskiya kuma duk mai gaskiya baya taɓewa, ya kamata mu tafi lokaci na ƙurewa.”

Numfashi Al’ameen ya saki tare da zuba mata idanu tsantsar gaskiya yake hangowa cikin idanunta domin kuwa ƙwayar idanunta su suka bayyana hakan, sosai ta basa tausayi dama ya mata hakane Saboda ya fahimci wani abu game da ita amma ba dan yana zarginta ba, motar yaja suka ƙarisa police station ɗin, fitowa ya zaga ya buɗe mata tare da cewa.

“Muje.”

Gaba yayi ta bisa a baya, har ciki cike da girmamawa police ɗin suke gaisawa da Al’ameen sanin Dpo bazai fito a wannan lokacin ba yasa Al’ameen kiran Sargent Joshua ya danƙa masa Ablah tare da ce masa.

“Muje waje ina da magana da kai.”

Da to Sargent Joshua ya amsa tare da fita Ablah ya kalla yace mata.

“Na kawoki kamar yadda na miki alƙawari, amma ki sani gaskiyar ki itace kawai zata fitar dake, ina zargin ki da kashe Ummi, idan har wannan zargin ya tabbata sai nafi kowa tsanarki, ki riƙe wannan.”

Yayi Maganar yana saka kai ya fice da kallo Ablah ta bisa tana share hawayen idanunta.

A tsaye ya taradda Sargent Joshua, dubansa yayi tare da cewa.

“Joshua gata na kawota kamar yadda na muku alƙawari, ina son kubi komai a hankali ku bayyano gaskiya sannan bana son duka kar wanda yayi kuskuren saka hanu a jikinta domin kuwa saka hanu jikinta shine babban kuskuren da zaku tafka na faɗa muku ku bi komai a sannu domin gano gaskiya.”

Yayi Maganar cikin karariya, murmushi Sargent Joshua yayi tare da cewa.

“Insha Allah zamubi komai a sannu.”

Kansa Al’ameen ya ɗaga tare da ciro kuɗi a mota ya basa, sosai Sargent Joshua yayi godiya tare da shigewa ciki, shiga motar Al’ameen yayi tare da dafe kansa yana jin babu daɗi, wayarsa ya ɗaga tare da kiran Nabil ringin ɗaya ya ɗaga.

“Kana jina ko Nabil ya binciken da na saka akan rayuwar Ablah dana iyayenta na jika ne shuru?”

“Eh to dama yau ɗin nan nake da niyyar zuwa Company na sameka na gama bincike akan su, mutanen kirki ne iyayenta basu da abokan faɗa tunda suka zo unguwar babu wanda ya faɗi wani abu mummuna akansu sai dai abu ɗaya ne daya kulle min kai, kowa sai yace bai san dangin su ba, kamar baƙin haurene ma’ana buzaye mahaifiyarta da mahaifinta su biyu ne kawai sukazo unguwar basu da kowa gaskiya, wannan shine abinda na gano.”

Numfashi Al’ameen ya saki tare da cewa.

“Okay ba damuwa na gode, bara na jira Isma’il shi kuma naji mai zaice sai munyi waya.”

Yayi Maganar yana katse kiran.

“Buzaye hmmm! Biri yayi kama da mutum, domin kuwa yanayin kyawunta yafi kama dana buzayen to amma meya fito da iyayenta daga Niger ya kawosu Nigeria.?”

Bakinsa ya cije domin kuwa bashi da amsar tambayar sa, motar yaja tare da harbawa titi.

“Ablah! Ablah! Ablah! Oh ikon Allah ni jummai ina kallon ikon Allah yarinya ata ƙwala miki kira shuru haka sai kace kin zauna akan kunnenki.”

Inna Jumma tayi Maganar tana tura toilet ɗin Ablah ko tana ciki, wayam babu kowa.

“Ablah agogo sarkin aiki yanzu haka tana nan kitchen Harta sammaka ƴar butan uwa, yau Monday ne zata fara zuwa makaranta yanzu haka ta manta ne, bara naje na sameta maza tazo ta shirya kar tayi let.”

Tayi Maganar tana saka kai ta fita, kitchen ta nufa Ladiyo ce kawai take aikin, har ƙasa Ladiyo ta durƙusa ta gaishe da Inna Jumma amsawa tayi tana ce mata.

“Ke ladiyo ina Ablah ta shiga ne.?”

“Ai Ablah ta kwana biyu bata shigowa kitchen Al’ameen ya hanata yace tasa karatun a gaba ta mai da hankali akansa, yau tun safe ma ban ganta ba.”

“Ha’a ikon Allah to ina Yarinyar ta shiga karfa wannan ɗannan ƴan sandan sunmin zagon ƙasa sun tafi da ƴar mutane.”

Tayi Maganar tana fitowa da sauri da ihsan taci karo zata tafi school.

“Ke Ihsan ina kika gano min Ablah ne.?”

“Ɗazu na ganta sun tafi da yaya Al’ameen amma bansan inda sukaje ba.”

“Ina Al’ameen ɗin yake.?”

Tayi tambayar dai-dai Al’ameen yana shigowa.

“Gani a bayanki.”

Ya furta yana shigowa, cike da masifa Inna Jumma tace.

“Ina ka ɗauki ƴar mutane ka kai ina Ablah.”

Ɗan murmushi Al’ameen ya saki tare da cewa.

“Oh Inna Jumma matsala school na Kaita kin san dama yau ne ya kamata ta fara zuwa ko nayi laifi?”

Yayi matar Saboda bai son hayaniya ajiyar zuciya Inna Jumma ta sauƙe tare da cewa.

“Alhamdulillah! Ai nayi zaton wajen waɗannan makiran ƴan sandan ka kaita, ja’ira shine ko ta shigo tamin sallama tana rawar kai zata school, shikenan bara naje yaushe zata dawo?”

Ɗan shuru Al’ameen ya mata Saboda bai san yanzu kuma wacce ƙarya zai mata ba, iska ya fesar tare da cewa.

“Zasu iya kai la’asar maybe, so amma tace min zata biya gidan su na sanar dake maybe ma zata kwana acan.”

“Gidan su kuma Al’ameen to amma meyasa bata sanar dani ba?”

“Kai Inna Jumma kin fiye tambaya da yawa, baki tashi daga bacci ba yarinyar nan ta tafi nine nace karta tasheki zan sanar dake idan kin tashi idan kuma baki yarda ba sai ki bari idan ta dawo ki tambayeta.”

Ɗan dariya Inna Jumma tayi tare da dukan kan Al’ameen tace.

“Shegen saurin fushi, ai baka min ƙarya na yadda Allah ya dawo da ita lafiya.”

Da ameen ya amsa tare da haurawa sama cikin sauri gudun karta kuma masa wata tambayar.

Yana shiga bedroom ɗinsa ya dannawa Khalil kira ringin ɗaya shima ya ɗaga tare da Sallama amsawa Al’ameen yayi tare da cewa.

“Ya ake ciki meka gano min game da aikin dana baka.?”

Yayi Maganar dai-dai Aunty Amarya ta saka hanu zata buɗe door ɗin room ɗin Al’ameen jin yana waya ya sata tsayawa ba tare da ta shiga ba ta kasa kunne tana jin abinda yake faɗa.

“Good Job, yauwa ka tabbatar da komai yayi ready insha Allah ina zuwa yanzu na sameka kafin na shige Company ina dai ka tabbatar da cewa ka gano komai akan Case ɗin kasan na kai Yarinyar Police station ɗin yanzu.”

Ɗan shuru yayi yana sauraron khalil kafin ya kuma cewa.

“Okay na fahimta sai nazo.”

Yayi Maganar yana katse kiran tare da shigewa tollet cikin sauri domin baya son yayi let ɗin fita Office yau.

Aunty Amarya tunda taji maganganun Al’ameen hankalinta yayi mungun tashi wani irin gumi ne ya keto mata zuciyarta ta tsinke, (in dai ka tabbatar da ka gano komai akan case ɗin na kai Yarinyar station ɗin yanzu ina zuwa ka tabbatar da komai yayi ready.)

Idanunta ta rufe tare da buɗewa fasa shiga room ɗin nasa tayi ta koma nata da sauri wayarta ta ɗauka hanunta na ɓari ta kira Hajiya Mansura tana ɗagawa ta fara magana cikin tashin hankali.

“Mansura akwai gagarumar matsala domin kuwa tusar mu tana neman hura wuta, da alamu Al’ameen ya fara bincike akan mu, domin kuwa yanzu naji yana waya da wani kan Case ɗin har naji yana cewa idan harya tabbatar daya gano komai yana zuwa wajensa yanzu, ina tsoron sunana ya fito yanzu cikin zargi.”

Runtse idanunta Hajiya Mansura tayi ita kanta ta razana da wannan labarin da amarya ta kawo mata.

“Kina jina dole mu ɗauki matakin kare kai yanzu domin kuwa na fahimci akan wannan Yarinyar da ake zargi ya fara bincike a hasashena akwai wata alaƙar zuciya tsakanin ta dashi shiyasa ya damu akanta ai bai fara binciken ba sai da akace ita ake zargi ya zamo wajibi mu kore wannan zargin da ake mata hakan shine zai kawar da hankalinsa ga binciken da yakeyi.”

“Naji Hajiya Mansura matakin gaggawa muke buƙata meye mafita kenan.”?

“Mafita ɗaya ce amarya kuɗi zaki turo wanda zai kai 700k mu samu mayen kuɗi muyi amfani dashi amma kar mu bari yasan mune abinda zai faru akwai wanda na sani mai bala’in son kuɗin tsiya dashi zamuyi amfani zamuyi komai ne ta cikin waya zamu samu sabon layin waya wanda bashi da rigista muyi amfani dashi, wajen kiransa mu basa aikin zamu ijiye masa wannan kuɗin muce yaje waje kaza ya ɗauka ba tare da ya ganmu ba, idan ya ɗauki kuɗin zamu sanar dashi cewa lallai zamu ƙara masa biyun wannan idan yayi aikin yadda muke so hakan zai basa damar samun ƙwarin gwiwwar aikin zamu masa tura wawa rami ne domin a kamasa a madadin wanda yayi kisan kin fahimta.”

“Taya hakan zata faru sannan ki ƙara buɗe maganar yadda zan fahimta sosai.”?

“Maganar a buɗe take idan muka basa kuɗaɗen ya yarda zaiyi aikin to zamu sakasa ne yaje ya kaiwa Al’ameen farmakin kissan kai tunda na sanshi tsohon ɗan ta’adda ne, mu kuma zamu nemi gmail na daban wanda zamu buɗesa da layin da babu rigista, mu turawa Al’ameen saƙon za’a kashe sa har time ɗin zamu gwada masa kin ga zai tanadi jami’an tsaro domin kare lafiyarsa daga nan kuma za’ayi ram da shi, ana kamasa dole ne za’a saki Ablah Saboda tana hanun hukuma akayi kisan dole zargi zai bar kanta kin fahimta idan har ta fito maganar bincike akan ta ya ƙare sai dai fa ki sani bazamu bar Ablah ba dole zamu san yadda zamuyi da ita domin kawar da ita Saboda na fahimci ita matsalar muce a yanzu tana da alaƙa da Al’ameen kuma tasan sirrin mu barinta babbar barazana ce a garemu, ina fatan yanzu kin fahimce ni.”

Numfashi Aunty Amarya ta saki tana dafe goshin ta tace.

“Na fahimta Kuma shawarar tamin amma ta yaya zamu iya kawo ƙarshen Ablah?”

“Ba shi bane yanzu a gaban mu, sai mun gama da wannan matsalar tukunna kafin mu dawo kanta.”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Aminaina Ko Ita 28Aminaina Ko Ita 30 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×