Skip to content
Part 28 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

“Inna Jumma meye kike haka ki kwantar da hankalin ki mana hukuma ne fa kike ƙoƙarin taka musu doka, ki nutsu ki barsu suje da ita nai miki alƙawari da safe zata dawo gida.”

“Kai min alƙawari, to bana buƙatar alƙawarin naka, au wayo wai kai zaka min Saboda ka mai dani jaririya ko, to ni na haifi ubanka ma ai bare kuma kai, hukumar banza hukumar wofi ni zaka faɗawa doka to na taka dokar dan ubanta, wallahi babu shegen daya isa ya fitar da wannan baiwar Allah daga gidan nan, zargin banza zargin wofi meye haɗin Ablah da Gaji da har zaku zargeta?”

Tayi Maganar tana ƙwace hanun Ablah daga wajen Al’ameen ta jata Sukayi bedroom ɗin Inna Jumma, Al’ameen Numfashi ya saki tare da duban Sargent Joshua yace.

“Officer kuyi haƙuri dan tsufa ke damunta, kuje insha Allah nai muku alƙawarin da safe zan kawo muku ita da hanuna.”

“Bazai yiwu ba mu koma babu ita, Saboda umarni aka bamu mu tafi da ita, doka ce dole ne sai mun kaita, dan haka zamu saka Sargent Merry taje ta fito mana da ita kayi hkr akan aikin mu muke.”

Murmushi Haidar ya yi tare da cewa.

“Ƙwarai kuwa akan aikin su suke abinda Daddy ya tashi yaje ya fito da Ablah ko kuma ku ƙyalesu su shiga su ɗaukota ta ƙarfi, ai dai suna da bindiga su nunawa Inna Jumma dole zata basu ita.”

Harara Al’ameen ya sakarwa Haidar tare da cewa.

“Kai dai wallahi baka da kirki ko kaɗan idan Daddyn ya shiga kokuwa zaiyi da Inna Jumma ya fito da ita ko an faɗa maka tana tsoron takwana ne, har yanzu baka gama sanin waye Inna Jumma ba, ba bindiga za’a nuna mata ba ko harbeta za’ayi bazata bayar da Ablah ba.”

Yayi Maganar yana jawo wayarsa daga cikin aljihun sa IG ya dannawa kira ringin ɗaya ya ɗauka tare da cewa.

“Zakin Ahmad Giwa yau kai da kanka kake kira.?”

Murmushi Al’ameen yayi tare da cewa.

“Nine ranka shi daɗe ya aiki.?”

“Aiki alhamdulillah! Meke faruwa jiya an kawo min takardar Case ɗin Mahaifiyar ka, mun bada umarnin azo ayi arresting ɗin yarinyar, zamuyi bincike insha Allah idan muka tabbatar da Yarinyar ita ke da laifi bazamu bari ba har sai mun tabbatar ta fuskanci mummunan hukunci dai-dai da laifin da ta aikata.”

Numfashi Al’ameen ya saki tare da cewa.

“Dalilin da yasa na kiraka ma yanzu kenan akan case ɗin, amm sunzo Arresting ɗin Yarinyar sai kuma mahaifiyar Daddy ta hana a tafi da ita ta dage lallai akan Yarinyar bazatayi kisan kai ba a ƙarshe ma dai tace baza’a tafi da ita ba, to ranka ya daɗe kasan halin tsufa da rikici, yanzu dai alfarma nake nema a bari insha Allah ni da kaina gobe zan kawo ta har station ɗin da kaina.”

“Wannan ai ba wani abu mai damuwa bane babu wata alfarma da zaku nema mu kasa muku ita kune fa hukumar, ba damuwa bara na kira commissioner insha Allah yanzu zasu sami umarnin dawowa karka damu.”

“To IG na gode sosai Allah yabar zumunci.”

“Bakomai ka gaishe da Daddyn naka ko, a masa godiya munga saƙo ranar Wednesday.”

Murmushi Al’ameen yayi tare da katse kiran yana kallon Haidar tsuka Haidar yaja tare da furta.

“Haka dai.”

Ya shige tare da zama murmushi Faruq ya saki yana kallon su domin kuwa ya lura kwana biyun nan rigima suke ji dashi, hanunsa Al’ameen ya zuba a aljihun sa, basu wani jima suka samu umarnin su ƙyale Yarinyar su dawo haka suka tafi ba tare da sun tafi da Ablah ba, muryar Aunty Amarya sukaji.

“Amma dai naga alama kamar Al’ameen kana ɗaurewa wannan Yarinyar gindi, ai wannan tamkar kareta kakeyi karka manta fa da mahaifiyarka ta kashe amma har kake ƙoƙarin mata katanga, wannan tamkar rashin kishin Uwarka kake.”

Tayi Maganar cike da zafin zuciya da mungun jin haushin Al’ameen daya kare Ablah daga tozartar hukuma, Al’ameen idanunsa ya runtse har cikin zuciyarsa maganar Aunty Amarya ta sokesa, (Wannan ai rashin kishin Uwarka ne) ya maimaita Maganar a cikin zuciyarsa haɗa ransa Al’ameen yayi cike da izza yace.

“Ake zarginta dai tunda ba’a tabbatar ba.”

“Au shiyasa kake kareta saboda zarginta ake.”

Ta kuma ƙara jefa masa tambayar, cike da hasala yace.

“Saboda ba itace tayi kisan ba?”

Gabaki ɗayan su ɗago idanu sukayi suna kallon Al’ameen yayin da ya haɗe ransa tamau ya zauna shi a rayuwarsa ya tsani yawan tambaya Aunty Amarya cike da tsinkewar zuciya tace.

“Ban gane ba ita tayi kisan ba idan ba ita bace to waye ne tunda harka tabbatar da wanda yayi kisan?”

Cije bakinsa Al’ameen yayi zuwa yanzu ya fara hasala da tambayar Aunty Amarya cike da ɓacin rai yace.

“Oh haba Aunty wannan wani irin tambaya kike min haka ne, ta yaya zansan wanda yayi kisan tunda ba duba nakeyi ba.”

“Ka fara duba mana Al’ameen tunda har ka dubo ba Ablah bace tayi kisan.”

Miƙewa Al’ameen yayi ba tare daya kuma yiwa Aunty Amarya magana ba ya kwashi wayoyinsa ya haura sama cikin jin haushin Aunty Amarya, Haidar girgiza kansa yayi yace.

“Hmmm! Ko kema kya tambaya Aunty ni na rasa gane kan Al’ameen akan wannan Yarinyar, mtsss amma dai wallahi dole ne sai ta fuskanci hunkuci.”

“Kai da kake da tunani kenan amma shi da basirarsa ta ɓace masa ai kaga kare wacce ta kashe uwarsa yakeyi.”

Daddy ne yayi gyaran murya tare da cewa.

“Ya isa haka maganar koma menene hukuma zata tabbatar Faruq ɗauki system ɗinsa ka haura masa dashi kai kuma Haidar kaje ka kwanta dare yayi.”

Da to duk suka amsa kowa yayi nasa wajen Aunty Amarya duban Daddy tayi da bata gane alƙibilarsa ba tace.

“Daddyn Al’ameen banfa gane alƙibilar ka ba akan wannan maganar ya zaka koresu bayan kana gani magana muke yaushe daren yayi tara ne fa, ko saboda ɗanka yayi fushi yabar wajen shiyasa suma zaka koresu?”

Murmushi Daddy yayi yana duban Aunty Amarya tare da cewa.

“Hmmm! Amina kenan su Haidar ɗin ba ƴaƴana bane kike nufi, kina bani mamaki abun magana baya miki kaɗan okay ke kika sani.”

Yayi Maganar tare da miƙewa zai bar wajen Aunty Amarya haɗa fuska tayi tare da cewa.

“Ni na sani zakace ko Saboda na damu da lamuranku ko yayi kyau komai ma ku faɗa min dai-dai ne amma dai bazan fasa faɗan gaskiya ba.”

“Shiyasa ai nace miki ke kika sani Saboda na riga da nasan halinki Amina, amma sai kiyi hankali da Al’ameen karki cikasa kisa ya tunzura domin kuwa zuciyarsa tana da zafi, ba lallai ya jurewa matsawarki ba, yafi tsanar yawan tambaya da naci a rayuwarsa, ke kuma na hango su acikin idanunki.”

Daddy yayi Maganar tare haurawa sama Aunty Amarya cike da jin haushi tana cije yatsa ta tare da duban su Samira dake zaune tsawa ta daka musu.

“Zaman Uban me kuka zauna kunayi, da kuka zuba mana ido, ku tashi ku tafi bedroom ɗinku.”

Samira taɓe bakinta tayi kasancewar bata da kunya itama harma tafi Afnan rashin kunya tace.

“Ni babu inda zani kallo nakeyi idan na gama zan shiga tunda a falo nake ba’a tsakar gida ba.”

Sake baki Aunty Amarya tayi tana kallon Samira tace.

“Rashin kunya zaki min Samira dake baki da mutunci, to zageni.”

Maimu ce tace.

“Kiyi hakuri dan Allah Aunty Samira meye hakan Auntyn kike faɗawa wannan maganar, meyasa baki da kunya ne ke, kinsan idan baki shiga hankalinki ba, zan haɗaki da yaya Al’ameen kin dai san halinsa ba ƙyale wannan rashin kunyar taki zaiyi ba.”

Hararar Maimu Samira tayi tare da miƙewa tsaye tana jan tsuka tace.

“Mtsss! Idan kin faɗawa yaya Al’ameen ɗin dan Allah ya kasheni tunda mala’ika ne, ku kuke tsoronsa.”

Tayi Maganar tana barin wajen Afnan a hasale ta miƙe tare da jawo rigar Samira ta bawa tana cewa.

“Tsaya ƙaramar fitsararriya, tacacciya, baki isa yiwa uwata rashin kunya ba a cikin gidan nan, ni nafiki rashin kunya walla…”

Wani wawan mari Samira ta ɗauke Afnan dashi tana fisge hanunta daga jikin rigar ta nunata tayi da yatsa tare da cewa.

“Ƙarya kike ki haɗa kanki dani idan ana lissafa marassa kunya dole ma a duniya zanzo ta ɗaya kika ƙara kuskuren riƙoni wallahi sai na miki illa.”

Dafe fuskarta Afnan tayi sosai marin ya shige ta, Aunty Amarya ne tayi saurin shiga tsakanin su tana kama hanun Afnan tace.

“Ki rabu da ita Allah ya shiryeta.”

Tayi Maganar tana jan hanun Afnan suka bar wajen, kanta Maimu ta girgiza tare da dakawa Samira harara ta shige.

“Wannan wani irin rainin hankali ne, a shigo har cikin gidan nan saboda cin mutunci, wai anzo kamaki, to wai wani shegen ne yace ke ake zargi cap amma yau anci mutunci na acikin gidan nan na ɗauko amanar Yarinyar sannan azo a nemi tozarta ni, duk ma laifin Amadu ne kuma wallahi sai na ɓata masa rai Allah ya kaimu gobe ni da shine.”

Kanta Ablah ta sunkuyar hawaye na gudu saman fuskarta kuka take sosai harda shashsheƙa Inna Jumma jawota tayi jikinta tare da cewa.

“Kukan me zakiyi, share hawayen ki naga ubanda ya isa ya kaiki hanun ƴan doka, harma zakiyi asarar hawayenki akan wannan maganar banzan tashi muje na kaiki bedroom ɗinki kiyi baccinki ki kwantar da hankalin ki.”

Miƙewa Ablah tayi Inna Jumma ta rakata har bedroom ɗinta ta rarrasheta Sosai kafin ta fita, tana fita Ablah ta ɗauki wayarta da sauri ta turawa Hafsa text.

_Ina cikin matsala Hafsa wai ni ake zargi da kashe Ummi har police sunzo kamani, an gano shatin hanuna jikin cup din kinsan na ɗauki cup na shiga ban ɗauka ba bata fidda ɓarawo ina tsoron matar nan Hafsa Saboda cikakkiyar marar imani ce idan kin jini shuru to ki tabbatar ina hanun hukuma ne.”_

Ta tura text message ɗin tana goge hawayenta.

*****

Nafeesa bata ga saƙon Amnat ba sai yanzu da ta kunna wayarta duban saƙon tayi tare da sakin murmushi wai kiji tsoron dai kace ita tsoron Allah take, numfashi ta saki tare da ɗago wayarta ta dannawa Al’ameen kira kusan kira huɗu baiyi picking call ɗin ba, bata daddara ba ta kuma danna masa kira.

Yana kwance cikin tunani da damuwar maganar Ablah yaji wayarsa tana ringin yana ji yaƙi ɗagawa a zatonsa Haidar ne, jin kiran yaƙi ƙarewa ya sashi jawo wayar yana dubawa baƙuwar Number (waye kuma wannan) furta cikin zuciyarsa tare da ɗaga kiran ya kara wayar a kunnen sa yayi shuru.

Jin an ɗaga yasa Nafeesa lumshe idanunta tana murmushi, saurin sauya muryar tayi tare da sallama.

“Assalamu alaikum barka da dare.”

Shuru Al’ameen yayi yana ji a zuciyarsa kamar ya taɓa jin muryar sai dai ya rasa inda yasan muryar.”

“Wasallam barka wake magana?”

Ya jefa mata tambayar shuru Nafeesa tayi ta rasa wa zata ce masa sai can tace.

“Feenat sunana.”

“Okay kiran me kike min da wannan tsohon daren wai ma tukunna uban waye ya baki Number ta?”

Numfashi Nafeesa ta saki tana kashe murya tace.

“Samun numbern ka ba abu bane mai wahala a wajen mutumin da yaƙe ƙaunar ka, kai mutum ne na musamman kaga kuwa dole ne mu soka Allah yasa zan samu wajen shiga a zuciyarka.”

Wani wawan tsuka Al’ameen yaja tare da katse kiran ya ijiye wayar yana furta .

“Crazy girl mtsss!”

Nafeesa da kallo tabi wayar jin anja tsuka kuma an katse kiran, wani irin haushi ne ya kamata tare da wurgar da wayar karon farko da namiji ya taɓa mata wulaƙanci, ringin wayar tayi saurin duban wayar tayi ko shine ya kirata *HAIDAR* tsuka taja tare da kashe wayar.

“Banza maye.”

Ta furta tare da saka kanta ta kwanta.

Haidar da kallo yabi wayar tasa cike da damuwa, kai.

“innalillahi wa’inna ilaihirraji’un! Wai to meke faruwa ne da Nafeesa bata taɓa min haka ba sai yau anya kuwa lafiya ko dai na yiwa Nafeesa laifi ne ban sani ba”

Wayar ya ɗauka ya tura mata text.

_Jikina yana bani cewa ba lafiya ba, ban taɓa kiranki baki ɗaga min waya ba sai yau, ban sani ba ko laifi na miki, idan har laifin nayi ina mai bawa farin ciki na haƙuri bana kaunar ɓacin ranki farin ciki na domin kuwa kece hasken dake haska rayuwata i miss You_

Ya tura mata saƙon tare da yin shuru cike da damuwa.

Ita kuwa Rufaida alwala ta dauro ta hau sallar nafila ta juma tana sallar kafin ta idar hanunta ta ɗaga sama ta hau addu’a.

“Ya ubangiji kaine gatan kowa ka fimu sanin halin da muke ciki ya Allah kai kace mu roƙeka zaka amsa mana, ya ubangijina zuciyata tana cikin wani hali na son wanda baya sonta ya Allah ka kawo min mafita a cikin wannan lamarin idan akwai alƙairi tsakanina da Yaya Haidar ya Allah ka saka masa soyayyata a cikin zuciyarsa idan kuma babu alkairi a tsakanin mu Allah ka cire min sonsa cikin zuciyata Allah ka tausaya min.”

Ta ƙarisa addu’ar tana shafawa a jikinta, sallayar ta naɗe tare da kwanciya bayan Madina tayi shuru hawaye na zubowa saman fuskarta.

*****

Washe gari da sassafe kafin Inna Jumma ta fito Al’ameen ya ɗauki wayarsa da key ɗin motar sa ya fito bedroom ɗin Ablah ya kwankwasa, jin ana kwankwasa door ɗinta yasa Ablah dake zaune tana karatun Alkur’ani rufewa tare da tashi ta buɗe ƙofar yana tsaye jikin door ɗin idanu ya zuba mata cike da tsantsar ƙaunar ta, gani yake tamkar kullum ƙara kyau take.

“Ina kwana yaya Al’ameen.”

“Lafiya”

Ya amsa ransa a haɗe babu alamar wasa.

“Ɗauko hijabinki muje.”

Sanin inda zasuje yasa Ablah babu musu ta ɗauki hijabin ta, gaba yayi ta bisa a baya, mota suka shiga yaja motar da karfi suka bar gidan.

Sunyi nisa da tafiya taji muryar sa a daƙile.

“Meya kaiki ɗakin Ummi har kika ɗauki cup ɗin nan?”

Ya jefa mata tambayar wani irin tsinkewa zuciyar Ablah yayi ta rasa amsar da zata basa kanta ta sunkuyar tare da yin shuru.

“Babu amsa kenan.?”

Ya kuma tambayarta nan ma dai Ablah shuru tayi.

“Meyasa kika kashe Ummi?”

A matuƙar razane ta ɗago idanunta ta tana kallon sa, kanta ya ɗaga mata alamun ehh…

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Aminaina Ko Ita 27Aminaina Ko Ita 29 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×