Skip to content
Part 4 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

Hajiya Mansura murmushi mai sauti ta saki tare da ɗaga wayarta tana duban hoton Khairi still dai murmushin ta kuma tare da dannawa Isah Alolo kira bayan ya ɗaga ne ta fara magana.

“Na maka transfer na 200k ga pictures ɗin Yarinyar na turo maka idan ka gama aikin zan ciko maka sauran, ka tabbatar kayi komai cikin sirri, ka kuma kula saboda tsaro bana son a samu kuskure duk da na yadda da aikinka, gawarta muke son mu gani, ka tabbatar bata numfashi kafin ka wurgar da ita.”

Dariya Isah Alolo yasa cikin ƙatuwar muryar sa yace.

“Kema kin sani babu kuskure a cikin aikina, ki zuba ido ki kuma saurari mummunan labari akan wannan Yarinyar.”

Yana gama faɗin haka ya katse kiran ba tare daya tsaya ya saurari mai Hajiya Mansura zatace ba.

Hajiya Mansura miƙewa tayi tsaye tare da saka dariya tace.

“Yanzu wasan zai fara, hmmm!!! Amarya zan dage domin ganin burinki ya cika saboda cikar nawa burin, Mansura bata yiwa wani bauta sai ta tabbatar da cewa itace zata more dukkan abinda za’a samu, ni kura ce zanci rabona kuma naci na wani, a gama aikin ni kuma na ɗaura nawa akanki amarya muje zuwa kiga yanda reshe zai juya da mujiya dole kiyi danasanin sanina a rayuwa, domin kuwa dukiyar da kike ƙoƙarin mallakewa su zamo naki ke ɗaya, bazai yiwu ba, wannan dukiyar tawa ce ki gama min aiki da kuɗinki ni kuma zanyiwa kaina da jikina wallahi!! Wallahi!!! Wallahi!! Wannan dukiyar tawa ce sai na mallakesu ko ta halin yaya bazan yadda na mutu a matsiyaciya ba.”

Tayi Maganar tana kuma sheƙewa da dariya ta samu waje ta zauna still dai dariyar take.

“Haba Amarya taya zan tsaya na zuba idanu ki zamo hamshaƙiyar mai arziki, ina sam baki dace da wannan matsayin ba, kamar dai yadda na saki kika zamo saliha mai tausayi da jin ƙan Hajiya Gaji da ƴaƴanta kuma mace ta gari a wajen mijinta surka ta gari a wajen Uwar mijinta salihar fuska, alhalin a ƙasan zuciyarki ke munguwa ce, to haka zan kasance saliha mai ƙaunarki a fuska, yayin da ni kaɗai nasan meke ƙarƙashin zuciyata, kinyi kuskuren amincewa dani Amarya, wani ma yayi rawa bare ɗan makaɗi.”

Dariya ta kuma tana tashi ta shige tollet.

Ƙarar wayar sa daya jiyo ya sashi juyawa yana cewa Madina ƙanwarsa.

“Ɗauko min wayata a daining Madina.”

Da to Madina ta amsa tare da miƙewa, Haidar momma ya duba tare da cewa.

“To amma momma jiya fa munyi waya dashi Salim ɗin, bai sanar dani cewa yana buƙatar kuɗi, sannan kwatakwata kwana nawa ne dana tura masa 80k just one month fa, ace har kuɗin sun ƙare sai kace wanda yake ciyar da gida, gaskiya momma bazan tura masa kuɗi ba, na fara gajiya da almobazarancin Salim saboda shi baisan wahalar neman kuɗi ba shiyasa yake kashe su a banza.”

Numfashi momma ta saki cike da rarrashi ta cewa Haidar

“Na sani Salim yana wasa da kuɗi, ko jiya sai da na masa faɗa, ya kuma cemin bazai sake ba, Papan ku, yace bazai tura masa ba saboda yana wasa da kuɗi, to amma kai a matsayinka na ɗan uwansa idan baka basa ba waye zai basa kayi hkr ka tura masa dan Allah kuma danni badan salim ba.”

Shuru yayi cike da sanyin jiki domin kuwa bazai iya bijirewa Maganar mahaifiyarsa ba, dole tasa ya amsa, dai-dai Madina na kawo masa wayarsa, karɓa yayi kiran na ƙara shigowa, numbern American ne hakanne ya tabbatar masa da Faruq ne, yana murmushi ya ɗaga tare da cewa.

“Mutanen American.”

Daga can Faruq yayi dariya tare da cewa.

“Gamu cikin American amma harna fara jin kewarku, da alamu ƙasar nan bazata min daɗi ba, kana kusa da Al’ameen ne.?”

“No yana can part ɗin su, nima ina namu, kaga dan Allah karka nunawa Daddy baka jin daɗin ƙasar, zaiga kamar ya takuraka, ka daure karka basa kunya, karka manta rayuwarka Daddy yake so ya taimaka ƙarfin gwiwwa ya kamata ka basa.”

Kansa Faruq ya jinjina tare da cewa.

“Insha Allah, komai zai tafi dai-dai wai ina labarin Helina kuwa.”

Tsuka Haidar yaja tare da cewa.

“Kai nifa na gaji da wannan Yarinyar nayi blocking numbern ta, na kuma hana mu haɗu ka manta da ita kawai, kaga katse kiran nan ka kira Al’ameen tun ɗazu yake maganarka.”

Dariya Faruq ya saka yana katse kiran.

Dai-dai Rufaida na shigowa hanunta riƙe da akwati, da Sallama, momma ce ta amsa tana murmushi.

“Rufaida ya na ganki da akwati?”

Madina ce tace.

“Ai kuwa momma dole ki tambaya tafiya zakiyi ne da wannan tsohon daren malama.”

Hararar Madina Rufaida tayi tana karasowa ta zauna gefen Ya Haidar tana murmushi tace.

“Momma ni fa gajiya nayi da zama ni kaɗai babu abokin hira, shine nace kawai gara na dawo nan mu zauna da Madina zanfi jin daɗi.”

Murmushi Haidar yayi yana zungure mata kai yace.

“Cewa zakiyi kin gaji da zama babu surutu, aku sarkin Magana, to gaki ga Madinan, sai dai fa momma ki ja musu kunne idan suka kuskura suka takura min a gidan nan, zan karya miki yara.”

Yayi Maganar yana dariya, Rufaida ma dariya tayi tana tuno shawarar Maimu.

(Part ɗinsu zaki koma da zama domin ƙara samun kusanci dashi, ki san duk yanda zakiyi ki zauna sosai a zuciyar momma ki kuma yi ƙoƙarin ta gane cewa lallai kina son Ya Haidar na Tabbata zata zamo miki jigo kuma makami, sannan shi kuma Ya Haidar kiyi ƙoƙari shaƙuwa mai ƙarfi ta shiga tsakanin ku, idan kinyi hakan, daga nan zamu ɗaura a inda muka tsaya.)

Murmushi Rufaida tayi muryar momma taji tana cewa.

“Ai kuwa baka isa ba, yarana dole su wala a gidan nan, kinga Rufaida ku rabu dashi ki tashi kije ku ajiye kayan ki bedroom ɗin Madina dare yayi sai da safe.”

Da to Madina ta amsa suka miƙe suka shige itama momma nata bedroom ɗin ta shige, Haidar system ɗinsa ya jawo shine bai shiga ya kwanta ba sai 11:00pm.

******

Washegari da safe, Nafeesa bayan sunyi breakfast ne ta koma bedroom ɗinsu shuru tayi tare da tagumi, Haidar ne kawai a zuciyarta.

“Ya cika miskilancin tsiya, duk yanda zanyi domin ya nemeni, yaƙi fahimta, mtss!!!”

Taja tsuka tare da jawo wayarta, katinsa daya bata ta ɗauka, tana tunanin ta kira ne ko kuma ta haƙura ta gani ko zai nemeta, zuciyarta ne tace mata (Gara ki kirasa kawai karki tsaya garin jan aji ajin ya tsinke) idanunta ta lumshe zuciyarta na bugawa da ƙarfi ta saka numbern cikin wayarta tana tunanin bazai ma ɗaga kiranta ba, danna masa kira tayi kusan sau Uku tana kira yana tsinkewa bai ɗaga ba, cike da damuwa ta dafe ƙirjinta Tabbas tasa burin mallakar kadarori daga garesa, ba kuma zata yadda mafarkinta ya tafi a banza ba, lallai ne dole yau sai tai waya dashi ko ta haɗu dashi dole a cikin biyu sai ɗaya ta faru, ajiye wayar tayi tare da miƙewa ta fito falo, Nazifa da Baba ne kawai zaune Mama bata wajen, ranta ta haɗa ta juya zata koma bedroom ɗinsu taji muryar Baba.

“Nafi!”

Tsayawa tayi tare da juyowa ta amsa, da hanu ya mata alamar tazo babu musu kuwa ta ƙaraso tare da zama gefen Nazifa.

“Nafi! Yanzu ƴar Uwar ki Nazifa take tambayata na baku kuɗi zaku sayi kayan kwalliya da kuma dogayen riguna, kece kika kisata ko tazo ta tambayeni.”

Ɗago kanta Nafisa tayi ta kalli Nazifa cike da mamaki domin kuwa ita bata ma san maganar ba, shuru tayi tare da sunkuyar da kanta.

“Magana fa nake miki Nafi! Kin min shuru kece kika sakata ta tambayeni kuɗi, baku da suturar sawa ne, ko dole ne sai kunyi kwalliya kyan fuskar da Allah ya baku bai isheku ba, har sai kun ƙara da wani fenti saboda rashin godiyar Allah, ko ban muku ɗinki a Sallah bane, to bani dashi bazan bayar ba, domin naga alama so kuke na dinga almobazaranci da kuɗi, ina zubar dashi a banza, to baza’ayi wannan shirmen dani ba, ku tashi ku tafi ku bani waje ko sisi bazan baku ba.”

Ai kuwa Nafeesa kamar jira take ya gama Maganar ta miƙe ba tare da tace komai ba sai dai har cikin zuciyarta tana cike da baƙin cikin mahaifin nasu, Nazifa ma bayan Nafeesa tabi cikin sanyin jiki, suna shiga bedroom ɗin Nafeesa ta ɗauke Nazifa da wawan mari tana nunata da yatsa cikin huci tace.

“Dan ubanki nine nace miki kije ki tambayesa kuɗi, ko kinga ina saka raina da abun hanunsa, shima yaushe ya saka suturar arziki bare ya sawa ƴaƴansa, ina ruwana da kuɗinsa ina da zuciya na kaina nake nema ban dogara dashi ba, sai dai ke da baki da zuciyar da kare ya cinye zuciyarki ki ta bibiyar sa yana wulaƙantaki amma banda dai nikam, daga yau Nazifa idan kika kuma zuwa neman abu wajen Baba kika saka sunana aciki na rantse da Allah sai nai miki walaƙanci marar zuciya.”

Ta ƙarisa Maganar tana jawo jakarta kuɗi ta ɗauko dubu hamsin ta miƙa wa Nazifa.

“Gashi kije ki sai kayan kwalliyar tunda malalacin uban naki ya kasa baki, ke kuma baki da zuciyar nema.”

Nazifa idanunta ne sukayi jajur tabi hanun Nafeesa da kallo wanda take miƙo mata kuɗin, kanta Nazifa ta kaɗa tare da cewa.

“Bana buƙatar kuɗin hanunki Aunty, domin kuwa ba daga halak suka fito ba, ta hanyar Haram ne, ni kuwa bazan taɓa cin Haram ba a rayuwata, kema da kike ci ina miki fatan Allah ya shiryeki, Aunty na roƙeki ki daina aibata Baba domin kuwa komai tsiya ya haifeki, kuma ba uban banza bane, raina yana ƙuna a duk sanda kika kira Baba da munguwar kalma, na sani Baba baya bamu kuɗi, amma ya mana gata tunda harya samu a makaranta Arabic da boko kuma ya biya mana, ya bamu ci dasha mai kyau, sannan duk shekara yana mana ɗinki, ki faɗa min me uba zaiyiwa yaransa bayan wannan, Aunty…”

Cikin tsawa mai ƙarfi Nafeesa ta ɗagawa Nazifa hanu.

“Ya isa haka!!!! Ya isa!!! Ba iya karatu da ciyarwa bane kawai haƙƙin mu akan Baba, idanunki sun rufe ba kuma kya da wayo shiyasa bakya fahimtar abubuwa da dama, to amma ki sani, ni dai Baba baya bani haƙƙina na ƴarsa, kuma bazan fasa kalamaina a kansa ba, zaifi miki alkairi ki gimtse bakinki ki daina min wannan wa’axin domin kuwa bazanji ba, kuɗi kuma karki karɓa kanki kika yiwa asara bani ba.”

Nazifa kanta ta kaɗa tare da zama tayi shuru duk abinda Baba ya musu bataji zafinsa ba, sai dai tafi jin zafin maganganun Nafeesa akan Baba, gabaki ɗayan su babu wanda ya kuma yiwa wani Magana a cikin su, Nafeesa wayarta ta kuma ɗauka tare da ƙara kiran numbern Haidar.

Haidar dake zaune a Office yana fama da aiki a system ɗinsa yana lissafin kuɗaɗen da kayan zasu kawo musu yaji ringin ɗin wayarsa dubansa ya kai kan wayar, baƙuwar number, hanu yasa ya ɗaga tare da yin shuru, jin an ɗaga anyi shuru yasa Nafeesa itama tayi shuru kuzan 15 minute babu wanda ya yiwa ɗan uwansa Magana cike da hasala Haidar yace.

“Duk wanda ya kira idan bashi da abin cewa zan katse wayar ni ina da aikin yi.”

Murmushi Nafeesa ta saki cikin kashe murya tace.

“Sorry Ya Haidar nayi zaton bakai ka ɗaga wayar bane shiyasa nayi shuru, ko ka gane mai Magana.?”

Shuru Haidar yayi yana tunanin ina ya taɓa jin muryar nan, Tabbas yasan muryar sai dai ya manta inda ya santa.

“No ban gane mai Magana ba.”

Nafeesa taɓe bakinta tayi tare da cewa.

“Nafeesa ce wacce ka taimaka ka taɓa kawota unguwar mai tama sakamakon ciwon ciki daya turketa a hanya.”

Lumshe idanunsa Haidar yayi tare da sakin ajiyar zuciya, a hankali cikin nutsuwa yace.

“Oh sorry nafeesat, Ni kaina na kwana biyu ina buƙatar numbern ki, ya jikin naki.”

Murmushi Nafeesa ta saki tace.

“A’a Ya Haidar baka neman Number na domin kuwa daka damu da Number na, na Tabbata zaka samu, ko ka manta jiya ka ganni a airport kaƙi kulani sannan kuma kace ka kwana biyu kana buƙatar number na.”

Sosa kansa Haidar yayi cike da kunya kafin yace.

“Eh Tabbas na ganki, akwai uzuri ne da yawa a gabana shiyasa ban samu na miki Magana ba, sorry, Jikin naki da sauƙi dai ko.?”

“Ehh da sauƙi sosai, fatan kana lafiya ya kuma aiki.?”

“Aiki dai ba daɗi domin kuwa baya barin mu mu sami lokaci, ya akayi Nafeesa dama kina ajiye da Number nane.?”

“Ba dole na ijiye numbern ka ba, Ya Haidar kana da mahimmanci a rayuwata, shi kuma abu mai mahimmanci ko yaushe killace sa ake, tun ranar daka taimakeni nake jinka a raina, harta mamana tana son ganinka domin ta maka godiya.”

Murmushi Haidar yayi tare da ajiye biron hanunsa yana ture system ɗinsa gefe, jingina yayi jikin kujerar yana jin muryarta har cikin zuciyarsa

“Babu buƙatar Uwa ta yiwa ɗanta godiya, meyasa kika sanar da Mama nine na taimakeki, banso idan nayi abin alkairi a sanar da wani.”

Murmushi Nafeesa tayi tare da kwanciya ta jawo filo, domin kuwa da alama tarkon ta ya fara harbawa inda ake bukata, Nazifa bakinta ta taɓe cike da takaicin rayuwar da ƴar uwarta keyi, Nafeesa ce masa tayi.

“Kaima kasan abinda bazai yiwu bane ƙin yabon gwani a lokacin da ya dace, ko ka manta da zancen bahaushe ne da yake cewa, yabon gwani ya zama dole, ita dai Mama tana son ganinka Allah yasa zakazo.”

“Amsa kiran Uwa ai dole ne akan ɗanta, ki cewa Mama insha Allah gobe ina zuwa, amm ina cikin uzurin aiki yanzu insha Allah zamuyi waya zuwa dare.”

Yayi Maganar dai-dai Al’ameen yana shigowa office ɗin domin kuwa meeting zasu shiga, zama yayi tare da harɗe ƙafarsa yana kallon Haidar.

Lumshe idanunta Nafeesa tayi tare da cewa.

“Okay ka kula da kanka.”

Murmushi yayi yace.

“Okay thank.”

Wayar ya katse, yana duban Al’ameen daya tsaresa da idanu.

“Da wacce zan Aura nake waya naga ka tsare ni da idanu.”

Cike da izza yana taɓe baki ya ɗaga kafaɗarsa cikin ƙasa da muryar sa wanda ya zamo masa ɗabia tamkar baya son Magana yace.

“Waya tambayeka da wa kake waya.?”

“Idanunka sune suka tambayeni, wai dan Allah Al’ameen na tambayeka, me Mace ta maka ne haka ka tsanesu.?”

Ɗago idanunsa yayi ya kalli Haidar yana sakin murmushin gefen baki, tare da cewa.

“Wayace maka na tsani mata, karka manta da macece ta haifeni, ni fa tsanar mata nayi ba, kawai dai ita mace damuwa ce shiyasa bana buƙatar haɗa inuwa da su.”

“Damuwa kuma wani irin damuwa.”

“Kaga Haidar a yanzu kana kan giyar Soyayya bazaka fahimci duk abinda zan faɗa maka ba, sai dai ka sani aduk sanda ka faɗawa tarkon mace a lokacin zata fara tunanin juyaka ta mai daka ƙarƙashin ikonta, zata fi son Kanta fiye dakai, Sannan komai kake dashi zata fara tunanin nata ne, mita da ƙananan Magana shine ɗabiar sa, daga nan kai kuma zaka fara shiga cikin damuwa da yawan tunani.”

Dariya sosai Haidar yasa, har haƙwaransa suka bayyana, Al’ameen da kallo ya bisa kafin Haidar yace.

“Sam wannan ba hujja bace domin kuwa ba ɗabi’un mace ta ƙwarai ka ambata ba, kana ambaton ɗabiun matan banza ne, a yayin da mu kuma muke addu’ar samun mace ta gari, dan haka baka da hujja anan.”

Taɓe bakinsa Al’ameen yayi tare da miƙewa yana cewa

“Idan kaga dama ka tashi mu tafi meeting”

Yayi Maganar yana ficewa murmushi Haidar yayi cike da ƙaunar abokin nasa, da kuma addu’ar Allah ya yaye masa wannan halin nasa ya miƙe yana ɗaukar wayarsa ya fita.

*****

Kusan misalin ƙarfe Uku da rabi babu alamar Khairi bata dawo daga makaranta ba, Ummi ganin har zuwa wannan lokacin babu Khairi Ummi cikin tashin hankali ta fito falo tana kwalawa Aunty Amarya kira Aunty Amarya dake kitchen ne ts fito da sauri tana cewa.

“Gani anan”

“Amarya Khairi fa har yanzu bata dawo daga school tun ɗazu nake duba agogo shuru, hankalina ya tashi, 1:30 fa take dawowa gidan nan, shima Idi drevern shuru.”

Aunty Amarya cike da nuna tashin hankali na munafurci tace.

“Bata dawo ba har yanzu nafa yi zaton ta dawo tana room ɗinki me, to amma bata wajen Inna Jumma kuwa.?”

Ummi cike da tashin hankali tace.

“Bana tunanin tana wajen Inna, tanaa dawowa daga school fa, room ɗinki take shigewa ko nawa, amma bara na duba room ɗin Inna.”

Tayi Maganar tana nufar room ɗin Inna Jumma, Amarya murmushi ta saki a hankali ta furta.

“Zata dawo amma sai dai gawace.”

Tayi Maganar tana bin bayan Ummi, itama Inna Jumma cike da tashin hankali har jikinta na ɓari suka fito compaunt ɗin gidan, babu drever babu alamar da, AUNTY Amarya part ɗin su Faruq da Haidar duk sanda ta shiga amma babu Khairi, Inna Jumma waya ta ɗaga ta kira Al’ameen, yana zaune a Office ɗinsa kiran ya shigo, murmushi ya saki ganin numbern Inna Jumma.

“Ya akayi tsohuwa, me kuma zan taho miki dashi sarkin kwaɗayi.”

Inna Jumma cike da tashin hankali gami da sanyin jiki tace.

“Aminu har yanzu fa Khairi bata dawo gidan nan ba, shima drever bai dawo ba, hankalin mu yana tashe ka tashi maza kaje school ɗin ka dubo.”

Al’ameen agogon hanunsa ya duba huɗu saura, to kuma ina Khairi ta tsaya domin kuwa makaranta sun juma da tashi, numfashi ya sauƙe tare da cewa.

“Ku kwantar hankalinku, bara naje school ɗin na gani.”

Da to Inna Jumma ta amsa tare da katse kiran, Al’ameen key ɗin motar sa ya ɗauka tare da wayoyinsa ya fita, school ya nufa, babu kowa sai mai gadi, kasancewar mai gadin ya sansa yasa Al’ameen tambayarsa.

Cike da mamaki mai gadin yace.

“Ai kuwa tun ɗazu naga motar dake ɗaukarta yazo sun tafi amma da mamaki ace har yanzu basuje gida ba.”

Dafe kansa Al’ameen yayi tare da miƙewa tsaye yana yiwa mai gadin godiya ya tafi.

Koda ya shiga motar driving kawai yake amma sam hankalinsa baya jikinsa, tunani yake ina Khairi ta tsaya haka zuwa yanzu hankalinsa ya fara tashi domin kuwa muddun Khairi tana halin lafiya bazata kai warhaka a waje ba, yayi nisa da tafiya yazo dai-dai zoo road kamar wanda akace ya ɗaga idanunsa ya hango motar da ake ɗauko khairi daga school a gefen hanya, burki ya taka tare da fitowa da sauri ya nufi motar…”

<< Aminaina Ko Ita? 3Aminaina Ko Ita? 5 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.