"Umma meyasa Aunty Amarya zata hasala saboda kawai Yaya Al'ameen yana sona.
Murmushi Umma tayi tare da cewa
"Ke yarinya ce Ablah shiyasa ba komai hankalinki zai kawo miki ba, tana da dalilinta na yin hakan, mubar wannan maganar yanzu koma menene mu dage da addu'a babu abinda yafi ƙarfin ubangiji.
"Hakane Allah yasa mu dace, Umma idan nayi sallar la'asar zan shiga na duba Hafsa, da fushi nake da ita, munyi waya da ita akan zatazo ta, shuru bata zo ba bata kirani ba.
"Ta faɗa min jiya dana shiga dubata, tace ranar da zatazo. . .