Skip to content
Part 42 of 67 in the Series Aminaina Ko Ita? by Rasheedat Usman

“Umma meyasa Aunty Amarya zata hasala saboda kawai Yaya Al’ameen yana sona.

Murmushi Umma tayi tare da cewa

“Ke yarinya ce Ablah shiyasa ba komai hankalinki zai kawo miki ba, tana da dalilinta na yin hakan, mubar wannan maganar yanzu koma menene mu dage da addu’a babu abinda yafi ƙarfin ubangiji.

“Hakane Allah yasa mu dace, Umma idan nayi sallar la’asar zan shiga na duba Hafsa, da fushi nake da ita, munyi waya da ita akan zatazo ta, shuru bata zo ba bata kirani ba.

“Ta faɗa min jiya dana shiga dubata, tace ranar da zatazo ɗin ta tashi da zazzaɓi mai zafi, ga babu waya a hanunta bare ta sanar dake wayar mamanta ne suke amfani dashi, to shima sun sai dashi sun je asibiti, babu kuɗi a hanunsu ga kuma rashin lafiya dan ko jiya ma sai da na aika musu dubu Uku ki mata uzuri.

Jinjina kanta Ablah tayi cike da gamsuwa da maganar Umma kafin ta tashi ta hau gyarawa Umma ɗaki.

Nafeesa da Jamila sun juma sosai a gidan Jamila sai 2:30 suka nufi Companyn su Al’ameen basu wani sha wahala ba wajen shiga Companyn ko da suka nemi Office ɗinsa wata ma’aikaciya ce ta kaisu har bakin Office ɗin nasa, sakatariyar sa suka samu zaune Office ɗin Nafeesa ta nufa yayin da Jamila ta zauna a wajen jiranta, sakatariya ganin Nafeesa zata shige ba tare da neman izni ba ya sata saurin tashi ta tari gabanta tare da cewa,

“Baiwar ya haka zaki saka kai ba tare da izni ba, wannan Companyn ba haka yake ba dole sai da izni ake shiga, sannan bai sanar dani zaiyi baƙuwa mace ba yau.

Ɗago idanunta Nafeesa tayi ta dubi Sakatariyar tare da sakin murmushi tace,

“Okay saboda zan shiga Office ɗin Mijina sai na nemi iznin ki, baki san ni wacece a wajen sa ba shiyasa kike ƙoƙarin tare ni matsa ki bani waje na shige koshi bazai min iyaka da wannan Office ɗin ba bare kuma ke baiwar sa.

Murmushi sakatariya tayi tare da cewa,

“Koma wacece ke bazai yiwu na barki ki shiga ba dole sai da umarnin sa, kiyi haƙuri ina kan aiki nane ki jira na shiga na miki Magana dashi saboda kince ke budurwarsa ne, da wani ne ma dole sai ya karɓi takadda mun basa time ɗin da zai gansa.

Murmushi Nafeesa ganin ta mata magana cikin lumana yasa ta ɗaga kanta alamun

“Wa zance masa.”

“Nafeesa.”

Tayi Maganar a taƙaice, sakatariya na shiga Office ɗin Jamila tace mata

“Kibi bayanta ki shiga ba lallai ya bari ki gansa ba, idan ba shiga kikayi kai tsaye ba.

Ba tare da ta bawa Jamila amsa ba, ta saka kai ta shiga, sakatariya dake jiran Al’ameen ya shiga tollet ne taga Nafeesa ta shigo cike da mamaki tace

“Wai ya haka ne ba ce miki nayi ki dakata nayi magana dashi ba shine zaki saka kai ki shigo Please get out ki jirani a waje tukunna.

Tayi Maganar dai-dai Al’ameen na fitowa, tsayawa yayi cike da mamakin meya kawota Office ɗinsa kuma, jin muryar ta yayi tana cewa sakatariya.

“Babu inda zani idan kin isa ki fidda Ni, na faɗa miki koshi mai Office bai isa korata ba bare kuma ke! Gashi nan tsaye ya koreni idan ya isa.

Murmushi Al’ameen yayi tare da takowa har gabansu duban sakatariya yayi tare da cewa,

“Hajara mena ce miki, karki kuma barin wanda bani appointment dashi ya shigo min Office, amma bakiji ba, shine zaki turo min wannan tacacciya ƙasƙantacciyar macen marar daraja da kamun kai ta shigo min Office, hmmm! Kin kyauta wannan ya zama na ƙarshe da zaki sake min haka.

Sakatariya cike da tsoro tace

“Sorry Sir ba laifi na bane cemin tayi ita budurwar kace shiyasa nace bara nazo na sanar da kai Saboda karna hanata shigowa nayi laifi.

Cikin tsawa Al’ameen yace ke mahaukaciya ce idan budurwa tace ita meyasa bazata kirani a waya ba na fito da kaina na shigo da ita ko kinga na miki kama da wanda zaiyi alaƙa da wannan abun, meyasa bazaki kira wayar Office ɗin nan ba ki tambayeni ko baki da numbern ne?”

Cikin rawar jiki sakatariya tace

“Kayi hkr sir nayi laifi bazan sake ba, zan kiyaye gaba insha Allah sorry sir.

“Fita ki bani waje wannan ya zamo na ƙarshe idan kika kuma makamancin wannan zan ɗauki hukunci a kanki get out.

Da sauri ta juya ta fice, shi kuwa table ɗinsa ya zauna tare da jawo system ɗinsa ba tare daya kalli Nafeesa ba, bakinta Nafeesa ta taɓe tare da tahowa ta zauna a kujerar dake zagaye da table ɗin tace,

“Dama ka daina aibatani domin kuwa duk ba mafitarka bace bazan taɓa barin rayuwarka ba, saboda ni ƙaddarar ka ce, babu yadda ka iya dani dole ka rungumeni.

Murmushin gefen baki Al’ameen yayi kansa naga system ɗinsa ya furta.

“Mace marar daraja irinki bazata taɓa zama ƙaddarata ba, ko da kuwa ta zamo dole ne ƙaddarar zata sauya ban taɓa ganin Mace marar aji da kamun kai ba irinki, meya kawoki office ɗina.?

Murmushi Nafeesa tayi tace,

“Kasan abinda ya kawoni Office ɗinka Soyayyar ka ce, zuwa yanzu ya kamata ka amshi tayin soyayyata, saboda na damu da kai ya kamata ka damu dani.

“Bazan taɓa amsar soyayyarki ba, bazan soki ba, kuma na tsaneki ya kamata ki gane nafi ƙarfinki.

Murmushi still Nafeesa tayi tare da cewa

“Ni kuma gashi ina sonka, zan ƙaryata maganar ka na ƙiyayya a gareni, Al’ameen dole fa ka soni idan ba haka ba abu biyu zasu faru.

“Koma me zai faru bazan taɓa sonki ba, duk abinda zai faru ya juma bai faru ba.

Dariya Nafeesa tasa tana kallon sa tace

“Okay idan har bazaka soni ba, to Tabbas zaka rabu da AMININKA kuma ɗan uwanka rabuwa ta har abada domin kuwa na shiryawa shiga tsakanin ku, kasan me, zan sanar dashi cewa kaine ka aibatasa a gareni ka sanar dani mutumin banza ne shi yana kuma neman matan banza na rabu dashi na dawo gareka kaine ke sona da gaskiya dalilin kenan dana ƙisa, kayi tunanin ya zai ɗauki Maganar a dai yanzu yana sona fiye da kai zan iya basa ko wani umarni kuma yabi muddun zan sosa.

A matukar razane Al’ameen ya miƙe tsaye cike da mamakin Nafeesa wacce irin Mutum ce marar imani ya furta

“What! Me kike tunani zai faru Nafeesa idan har aminina Haidar yaji wannan baƙin saƙon naki, so kike ki shiga tsakanina da aminina, to baki isa ba, baki da wannan zarrar ni AL’AMEEN nafi ƙarfin kaidinki wallahi, duk tsiyarki da makircin ki,  haka zakiyi ki barnk nonsense, marar lissafi da kamun kai, idan banda jakar ƙwaƙwalwa irin taki a ina kika taɓa ganin an haɗa shayi da kunu, kin san ko da gani nafi ƙarfin ajinki, to bari kiji idan ke ƙwaƙwalwar ki ta kifi ce toshashshiya, to ni tawa a buɗe take, ki fita a hanyata kafin na tozarta rayuwarki bana son kisan ainihin color na shiyasa nake binki a ruwan sanyi idan kika sake fushi na ya fara aiki a kanki wallahi sai na saka miki tsoron fitowa waje, sai zuciyarki ta tsinke a duk sanda kikaji an ambaci sunana bake kaɗai kika iya makirci ba ni ubanki ne a wannan fage , ki kiyayeni kafin na koyawa rayuwarki darasi, ko da yake na miki uzuri da alamu baki samu tarbiyya daga wajen iyayenki ba, wawiya jaka daƙiƙiya marar zuciya.

Dariya tasa domin kuwa duk maganar da yake gasa mata ko kaɗan babu wanda ya mata zafi aranta ita dai burinta shine ta mallakesa mai makon ranta ya ɓaci sai ma dariya da tayi tare da cewa

“Da zaka daina aibatani da zai fi maka sauƙi, wallahi Al’ameen tunda nasa raina a kanka sai na sameka, ina tunanin har yanzu baka gama sanin wacece Nafeesa ba, abu mafi sauƙi a gareka shine ka ijiye wannan shegen girman kan naka da izza ka dawo gareni zai fi mana sauƙi daga ni har kai, ka daina haɗa hatsabibanci na da naka domin kuwa nawa ya girmi naka, Ni daka gani wallahi zan iya rabaka da iyayenka, rabuwa kuma ta har abada bare kuma wani abokinka ko ɗan uwane oho muku dai, shi Haidar ɗin ƙanin ubanka ne da zaka dinga shayinsa kana tsoronsa idan yasan kana sona sai meye, tsoron me zakaji Aminine fa kawai a gareka, akan meye ni zaka cuceni saboda ka faranta masa, wallahi muddun baka soni ba sai na saku a cikin masifa daga kai har Haidar ɗin, dan na soshi shine bazaka soni ba, ko sanda na soshi a lokacin ban sanka ba, ban haɗu da kai ba, shiyasa nayi kuskuren fara Soyayya dashi, amma yanzu da na ganka sai na naji sam shi ba soyayya nake masa ba kaine wanda ka dace da rayuwata ba shiba, dan haka dole ka soni, ka ƙaun….

Sauƙan marin da taji saman fuskarta shine ya hanata kai Maganar dake bakinta ƙarshe, yatsun hannunsa ne suka bayyana saman fuskarta hakan bai ishesa ba sai da ya kai mata mari Uku ya sauƙe mata hanu tasa ta dafe saman fuskarta, tare da furta

“Al’ameen ni ka mara saboda ina faɗa maka gaskiyar zuciyata, ina faɗa maka ne abinda zan aikata akan soyayyarka Saboda ka kiyaye, amma shine zaka mareni ba marina zakayi ba ko kashe ni zakayi bazan taɓa rabuwa da kai ba Saboda kaine duniyata kuma muradin rayuwata, karka saka a zuciyarka cewa zan rabu dakai cikin sauƙi.

Idanunsa ne sukayi jajur cike da tsananin ɓacin rai tunda yake a rayuwarsa bai taɓa tsanar Mutum ba Kamar yadda ya tsani Nafeesa cike da ɓacin rai ya nunata da yatsa tare da cewa,

“Na mareki kuma yanzu na fara saka hanu a jikinki muddun baki rabu da rayuwata ba, yau naga jarabar tsiya, duk abinda zaki furta daga bakin ki karki kuskura ki kuma ambaton iyayena domin kuwa su mutanene masu daraja da kowa ke girmama su, sunfi naki iyayen amfani wa al’umma saboda kowa ƙaunarsu yake, ko ina kika tsaya kika ambato ambassador Ahmad Giwa sai kinga girmamawa daga idanun jama’a, sannan me kikace zaki rabani da Haidar to Bismillah dan Allah karki fasa idan kika fasa to baki haifu da jini ba, bari kiji duk duk abinda kika faɗa a cikin Office ɗin nan tamkar kinyi recording ne, domin kuwa Haidar zai kalla da idanunsa kuma zai tsaneki tsana ta haƙiƙa a yau dai ƙarshen makircin yazo kuma Haidar zai tsaneki zakiyi biyu babu babu ni babu Haidar.

Dariya Nafeesa tasa fararen haƙwaranta na bayyana ta ɗaga idanunta tare da duban CCTV Camera dake Office ɗin wacce take wayam babu ita tare da cewa

“Kalli cctv camera ɗin taka ko tana aiki.

 Idanunsa ya ɗaga tare da kallon wajen wayam babu cctv camera ɗin an finciketa, kallonsa ya mayar ga Nafeesa cike da munguwar mamaki ba tare da yayi magana ba tsabar takaici da baƙin ciki, murmushi Nafeesa tayi tare da cigaba da cewa

“Karka kana yawan kirana da ƴar bariki idan har nayi wauta har cameran tsoro ta ɗauki zance na to Tabbas ban amsa sunan Bariki da kake kirana dashi, duk inda kake tunanina na wuce nan Al’ameen akan muradin raina babu abinda bazan iya aikatawa ba, nasan kana mamakin ya akayi aka cire cctv cameran, hmmm! Kuskuren da kikayi shine na mannata jikin bango kuma dai-dai tsayi na , shiyasa bansha wahala wajen cireta ba, na cireta ne na yasar da shegiya gata a ƙasa sanda kake yiwa wannan shashashar sakatariyar taka hargowa saboda ka maida hankalin ka gareta ban isheka kallo ba, shine ya bani nasarar cireta, Al’ameen Nafeesa ba kanwar lasa bane, ya kamata kayi nazari akan maganata, kayi duba izuwa ga tsakaninka da ɗan uwanka, domin kuwa ta dalilin juyawa soyayyata baya zaka iya rasa abubuwa da dama, zan barka zuwa kwana biyu kayi nazari game da ni.

Tayi Maganar tana ɗaukar bag ɗinta ta fita daga Office ɗin Al’ameen kansa ya riƙe cike da tashin hankali tare da fara tsorata da Nafeesa anya kuwa mutum ce, numfashi ya saki tare da zama yana zubawa cctv camera idanu da take wurge a ƙasa lallai yana buƙatar taimakon SAFWAN shida NABIL su kaɗai ne zasu iya kawo musu mafita, dole ne ya nemi Safwan domin kuwa ya shiga matsalar da tafi tasa ta sanadin Hindi da Safna dole shine zai nuna masa hanya.

Yayi Maganar zucin yana ture system ɗinsa gefe domin kuwa bazai iya aikin ba

Ko da ta fito mungun kallo ta jefawa sakatariya tare da ficewa ita da Jamila, Haidar dake tsaye ne shida ma’aikatan su, ya hango Nafeesa ta fito daga site ɗin Al’ameen tana dariya cike da mamakin meya kawota Companyn su yake binta, cikin sauri ya biyo bayan su, Nafeesa murmushi tayi domin kuwa ta hango sa ta kasan idanunta, kuma tasan dole zai biyota, sunzo daf fita yasha gabansu tare da ce,

“Nafeesa ya na ganki a nan, me kikaje yi Office ɗin Al’ameen?”

Tsayawa tayi tare da sakin murmushi ta ɗago idanunta ta kallesa, murmushi ta kuma sakar masa tare da cewa,

“Haidar masoyina, gaskiya ina jinjinawa soyayyar da kake gwada min kuma hakan yana sawa naji cewa bazan samu wanda zai soni tamkar kai ba, sai dai ni babu ruwana da wannan burina kawai na kasance da wanda ni nake so ba wanda shine yake sona ba, ni bana sonsa, wannan tambayar bani zakayiwa ba, Al’ameen zaka yiwa domin shine ya gayyaceni Office ɗinsa da magiyar dan Allah nazo, so tunda AMININKA ne, shine ya kamata ya baka amsar tambayar ka bani ba, ban sani ba ko abinda muka tattauna yana buƙatar sirri domin Al’ameen mutum ne na musamman.

Tayi maganar tana sakin dariya tare da raɓawa ta gefensa ta wuce bayanta Jamila tabi itama tana sakin murmushi, Haidar maganganun Nafeesa sosai suka ɗaure masa kai ya kasa fahimtar me suke nufi, Al’ameen shine ya gayyaceta tare da magiyar dan Allah tazo, to me hakan yake nufi Al’ameen Mutum ne na musamman ban sani ba ko maganar da mukayi tana buƙatar sirri

Yayi maganar zucin cikin kiɗima da rashin fahimtar zancen

“To meye tsakanin Al’ameen da Nafeesa da har zata kirasa mutum na musamman,  lallai akwai wani abu dole Al’ameen ya warware min wannan zaren domin shine kawai yasan inda bakin zaren yake.

Yayi Maganar yana juyawa tare da nufar Office ɗin Al’ameen tura Office ɗin yayi kamar a fusace babu ko Sallama ya tsaya a gaban Al’ameen tare da furta.

“Al’ameen meya kawo Nafeesa Office ɗin ka.

Ɗago idanunsa Al’ameen yayi tare da zubawa Haidar su ba tare da yayi magana ba, domin kuwa baisan wacce amsa zai basa ba.

<< Aminaina Ko Ita 41Aminaina Ko Ita 44 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×