Kayan jikinta ta cire tare da ɗiban ruwa ta shiga wanka, ƙaramar riga ta sanya da dogon wando sannan ta faɗa saman gadon tana cewa Hafsa.
"Wash gaskiya na gaji, kaina harya fara min ciwo kinsan na tsani hayaniya."
Dariya Hafsa tayi tare da cewa.
"Ai kuwa daga gobe ya ƙare, iwar haka dai an gama ɗaureki da igiyoyi uku, har mun wurgaki ɗakin Al'ameen."
Dariya Ablah ta saka dai-dai Aunty Saude na shigowa ta zauna tare da cewa.
"Yauwa na manta ban sanar dake cewa munje munga kayan da Papa ya sanya miki a part ɗinki. . .