Hajiya Laila ta kalli Alhaji Kabir, zuciyarta cike da zafi da baƙin ciki. Ta fashe da kuka ta ce masa, "Alhaji, ‘Yan Biyu na haifa! Na gansu da idona! Amma yanzu sun ce min ɗaya kawai na haifa."
Alhaji Kabir ya riƙe hannunta, ya jawo ta a hankali suka zauna gefen gado. Sai da ya ga ta ɗan nutsu, sannan ya dubeta, "Ki kwantar da hankalinki, Matata, ki daina ruɗewa haka. Kin sani, lokacin da ki ka haihu ba kya cikin cikakken hayyacinki. Wataƙila hakan ne ya sa ba za ki iya tabbatar da adadin 'ya'yan da kika haifa. . .
