Shiru ta yi ganin Bitil tsaye a kansu. Kan Soupy ta farga ta warce jaririyar daga hannunta.
Ta ɗaga ta sama tana kallo, sai kuma ta kwashe da dariya tana sake ɗaga jaririyar sama.
"Ina kuke, ku fito, mun samu REZA a yau. ASABE REZA sunanta, idan na haɗa ta da FAKRIYYA ta, ba ƙananun kuɗi za su kawo mana ba!" "Kuna ina ne!"
"Ku fito muyi bikin murnan haihuwar REZA."
Ta furta, da maɗaukakin sauti, tana sauke idanuwanta kan Ashana dake ƙoƙarin miƙewa da dukkan ƙarfinta.
"Ƙaryar duniyanci kike yi Ashana! A gabanki zan. . .