Skip to content
Part 11 of 33 in the Series Asabe Reza by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

Miƙewa ta yi a hankali saman gadon, kanta ta dafe da ya mata wani gim-gim-gin, agogonta ta kalla, ƙarfe 9:30 na safe, sai kuma ta sauko da sauri, kunya ce ta kamata, tuna yaushe rabonta da yin Sallah, tun ranar da ta ji labarin auren Hamoud, dama shi ne silar sa ta yin, da kuma ya ƙi ta, ita ma sai ta saki addininta, ba irin tuban mahaifiyarta ta yi ba ke nan, dominsa take kula da addinta, tuna kalmomin da Soupy ta gayamata mahaifinta na yawan gayawa mahaifiyarta ta yi, sun zauna sosai a zuciyarta, su kaɗai ke sata nishaɗi cikin labarin, ‘Oh! Domina za ki tuba ba domin Allah ba.’ murmushi ta yi a ƙasan ranta, tana ƙara jinjina girman lamarinsu.

Da wannan tunane-tunanen ta ɗauro alwalar ta tada sallah, ta daɗe tana addu’a da ɗan abin da Hamoud ya koya mata, a karo na farko a rayuwarta da tawa kanta addu’a, da mahaifinta, da mahaifiyarta.

Shiryawa ta yi ta fito falon tana kallon Soupy da kewa Mamanta tausa, murmushi ta musu kamar babu abin da ke damunta, a daidai nan kuma wayarta ta ɗauki ƙara, sunan Hamoudi da ta gani saman wayarta ya sata komawa cikin ɗakin da sauri tana mai ɗora wayar a kunnenta.

“Ki yi haƙuri!”

Ya furta da sautinsa da ya sata zama bakin gadon tana runtse ido.

“Kinji”

“Hmm! Ta furta a hankali.

“Ban san me zance miki ba, amma ina roƙanƙi da ki dubi girman Allah ki zo yanzu mu haɗu, akwai tarin zantukan da ban san ya zan jera miki su ba. Kin san wurin ai, TEEMA ICE CREAM & SNACKS”

“Mari…”

Ta furta da ɓacin ran da ke taso mata tundaga jijiyar kanta.

“Mari kuma? Wane irin mari?”

“Na sani ai, Hamoud  ka daina so na ko? In rabu da kai? Ni kake tunanin zan iya barinka?”

“A’a, haba, duk me ya kawo Wannan zancen, ki zo kawai, ban san ya zan iya faɗa miki anan ba.”

“Zan zo.”

Ɗiff! Ya kashe wayar, ta tsaya tana kallon wayar, lissafinta na ƙoƙarin watsewa, tana tuna kalamansa na jiya, tana tuna na yanzu, kamar ma bai san komai ba.”

Taɓe baki ta yi jin kanta na ƙara ciwo, a haka ta miƙe tana ƙara shiryawa, ta fice ta gaban Soupy da ke bin ta da idanuwa.

*****

Da isarta ta hange shi can ɓangaren da suka saba zama, har an aje masa Ice Cream ɗin yana sha, ƙarasawa ta yi a hankali ta zauna a kujerar da ke kallonsa.

“Ya Rabb! Ya furta yana dafe kansa, launin idanuwansa har sun fara canjawa zuwa ja, da ƙarfi ya yi fatali da ice cream din har yana fallatsar mata a ido.”

“Me ya kawo ki nan? Yanzu duk abin da na miki jiya baki manta ba sai da kika sake biyo NI? Wai ke wane kalar zagi kike so na miki ne ki barni, ko dan ke haihuwar titi ce, shi ya sa baki san zafin a zagi iyayenki? Wa ke ma gaya miki duk inda nake?”

“Kai ne.”

Ta furta, zuciyarta na bushewa, gani take rainin hankalin ya fara wuce nutsuwa.

Murmushi ya saki me ciwo, yana takowa zuwa gabanta.

“Ko a mafarkin da babu ranar farkawarsa bana fatar na kira ki, kina haukane da baki san ranar warkewarsa ba da kike tunanin Ni zan iya kiranki, domin ki zo mini, Idan kuɗi kike so ki faɗa mini, zan baki daga ɗaya, har Million 100!…”

Shiru ya yi ganin ta turo masa wayar hannuta alamun ya duba.

Dubawar ya yi, kafin kuma ya ɗaga wayar yana mai nuna mata ita saitin fuskarta.

Hannunta ya fincika da ƙarfi yana dosar jikin garun, hankalin mutanen dake wurin duk ya yo kansu, a haka ya fiddo biron da ke gaban rigarsa yana zana shi a bangon tamkar me koya darasi.

Idan ke baki taɓa ganin harufan ABCD ba, to bari yanzu na nuna miki, idan kika ga an saka H-A-I-S-A-M to Haisam ake nufi NOT HAMOUD. Haisam shi ne ya kira ki daƙiƙiya, ki riƙe harufan! Ki barsu su zauna a cikin tosasshiyar kwakwalwarki!”

Ya furta da maɗaukakin sauti, yana buga yatsansa a mahaɗar kwakwalwarta.

Kallonsa take, tana kallon mutanen da suka taso, lumshe idanuwanta ta yi, zuciyarta ke wani irin ingizata, Hamoud ya kawo ta ƙarshen da bata taɓa zato ba, wannan wane irin cin mutunci ne a gaban jama’a.

Da ƙarfi ta warce hannuwanta tana buga su saman table ɗin dake gabanta.

“Idan Ni daƙiƙiya ce, to kaine shugabana a jahilci da ka iya zama da macen da ta yiwa Ubanka cin mutuncin da komai daƙiƙanci na ba zan yi shi ba…”
Wutar da ta gani a gefen idanuwanta ya sata yin shiru tana dafe kuncinta, tana murmushi me ciwo.
“Karki sake ambatar matata da mahaifina a wannan ƙazamin bakin naki, ke ɓace min daga gabana ko na kira police su kai ki inda ba za ki ƙara ganin hasken rana ba.”

Ya faɗa, jikinsa na tsuma, yana ƙoƙarin zaro wayarsa daga aljihu.

Matsowa ta yi gabansa tamkar za ta shige jikinsa, a haka ta tsaya tana watsa masa kalmomin a hankali ganin mutane na ƙara matsowa.
“Sai me idan ka kira su? Zan gaya musu abin da zan faɗa maka yanzun ko da za ka mutu ka dawo, idan domin na je gidanku sata ka tarwatsa min zuciya, to yau za ka ji abin da zai tarwatsa taka zuciyar.

Da Fakriyya muka je satar, asali ma ita ce silar satar, kawunka kuma shi ne ya samu.

Ina takaicin sanar maka, ba mu baro gidanku ba, sai da Fakriyya ta haiƙewa Ubanka, ta yi zinar da kake goranta min da shi, akan gadon da aka yi na…”

Ta kasa ƙarasawa jin kalaman sun mata nauyi, komai Hamoud zai mata, ba za ta iya cin mutuncinshi har haka ba.

“Idan kana tunanin ƙarya nake, to ga wannan ka fara ganin wacece matarka a jikinsa.”

Ta furta, tana tura hannunta a aljihunta, ta zaro hotan, ta aje gabansa.

Ta juya akan takunta, tana keta tsakiyar mutanen, tana ɓacewa cikin idanuwansa.

Ya kai dubansa, kan mummunan hotan, Fakriyya ce kwance, tsirara, haihuwar uwarta, gefenta wani baƙin mutum ne yana lasar bakinta, a haka akai hotan, alamun SELFIE ne.

HAMOUD

Gaba ɗaya ya ɗimauce, tsantsar firgici da tashin hankali na shimfiɗe a kyakkyawar fuskar ta shi. Hannunsa da ke karkarwa ya miƙa yana mai janye hoton, ya tura a aljihu, kamar dai mai tunanin wani zai karɓe ya gani.

A haka ya miƙe akan takunsa da bai san inda zai nufa ba, keta mutanen yake yi, yana ganin yadda bakunansu ke motsi, amma baya fahimtar me suke faɗi.

Tafiya kawai yake yi da duk inda zuciyarsa ta kai shi, ya manta da motarsa da ke aje acan, ya manta yana da komai ma a rayuwa, a haka ya yi tafiyar me nisan da bai san yadda ta faru ba, har sai da ya wanzu a ƙofar gidansa yana dukanta da duk wani ƙarfi da ya mallaka.
Buɗe wa sukai a fusace, ganin ogansu ne ya sa suka russuna, suna ba da haƙuri.

Bai bi ta kansu ba ya miƙe zuwa cikin gidan.

Bedroom ɗin ya zarce yana kwala mata kira, da isarsa kuwa ya taddata a tsaye, tana ƙoƙarin shafa kwallinta.

Ita ma ganinsa ya sata fasawa, ta taho cike da rangwaɗa ta shige kirjinsa.

“Ruhi…”

“Ina ice cream ɗin?”

“Kai ma ka kasa haƙuri ko? Yanzu nake shirin kiranka ince ka taho na samu tsarki fa…”

“Uhumm, yau ne First night ɗinmu fa, ni dai Please ka kaimu Hotel ɗin da ka ce, na tsani komai ya wanzu a…”

Wani abu ta ji ya takore mata maƙoshi, ya hanata ƙarasa zancenta.

Idanuwanta take buɗewa jin hannuwansa a tsakanin wuyanta da wata irin shaƙa da ke ƙoƙarin tsinka mata maƙogwaro, a haka ya dinga tura ta baya, har sai da ya haɗa kanta da bangon da wani irin bugu da ya sata sakin wani marayan ƙara.

Ƙoƙari take ta raba hannunsa dake wuyanta amma ta gaza, shaƙa ce ya mata irin wacce har sai da ya ɗaga ta sama, ƙafafuwanta na wutsil-wutsil a ƙasa.

Idanuwansa take kallo da suka rikiɗe zuwa na Wolf, ya zame mata tamkar wani Vimpire da ke neman jininta, a haka ta ji ya sake ta ya wancakalar ta a ƙasa, har sai da goshinta ya haɗu da gadon, ta kwalla ƙara yayin da jini ya fara tsartuwa.

Hotan ya jefa gabanta, ta kalla da idanuwanta dake dishi-dishi, zuciyarta ta buga, ta ƙara bugawa a yayin da taji kusantowar mutuwarta a saitin hancinta, tana zarcewa can cikin ruhinta da take fatan ya fita a gangar jikinta, akan dai ace yau Hamoud ya barta, abin da ta hango ke nan, abin da kuma take jin tsoro ke nan, nadamar barin duk wani abu da zai nuna ita karuwace ke mamaye duk wani tsiron gashi dake jikinta.
Gobe ne fa? Gobe suka yi da Linda za su je duk inda za a rufe wani abu da ta aikata a rayuwarta, gobe suka yi da Linda za a toshe kwakwalwar ASABE yadda ba za ta ƙara shiga harkar rayuwar aurenta ba.

A yau, ga auren yana rawa, yana ƙoƙarin tarwatsewa a satinta na farko da yinsa.

‘Kwallina!’

Zuciyarta ta buga da wannan kalmar, jan jikinta ta fara yi tana son isa inda ta jefar da kwallin, ji take shi kaɗai ne.

Zai iya taimakonta, shi kaɗai ne zai iya hana HAMOUD aikata duk wani abu da yake hari.

Dafe kwalbar kwallin ta yi tana ƙoƙarin ɗauka. Da shi da gabjejen takalmin ƙafarsa ya ɗora a hannun nata, ya murje, ya muttsike, ya ƙara murjewa har sai da sautin rugurgujewar kwalbar da yatsunta ya fita, ta kwalla gigitacciyar ƙara jin kwalaben sun lume a tafin hannunta, a haka ta ji sautinsa yana faɗa mata abin da ya dakatar da fitar numfashinta.

“Idan akwai halittar da ba zan taɓa yafewa a duka duniyata ta ba, to ke ce Fakriyya. Ki yi zina da mahaifina, ki keta alfarmar mahaifiyata, ki zo kuma ki aure Ni? Wane irin kwamcala ce wannan? Ki faɗa mini me na miki a rayuwa da za ki min wannan hukuncin? Ta ya ya ma na aure ki, me ya sa na so ki? Me zan miki? Me zan miki na goge wannan baƙin tarihin daga rayuwata? In kashe ki, In kashe me? In barki da rai, In bar me? Ki tafi kawai, ki tafi inda kika san ba za ki ƙara gani na ba, wallahi, summa tallahi idan kika ƙara fitowa a gabana, sai na fasa ƙoƙon kanki, sai dai in ƙarasa rayuwata a Prison, ki je na sake ki, saki uku, idan ma akwai fin hakan, to shi nake nufi…”

Da kalmominsa na ƙarshe ta ƙarasa sumewa.

<< Asabe Reza 10Asabe Reza 12 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×