Skip to content
Part 12 of 33 in the Series Asabe Reza by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

A gurin ya zube yana rike kansa dake ƙoƙarin tarwatsewa, sai yanzu hawayen suka zuba, sai yanzu yaji ɗuminsu a kasan fatar idanuwansa. 

Mutanen da yake so a gabaɗaya rayuwarsa suka ci amanarsa. 

Mutum na farko KAWUNSA, kawunsa fa da yake jin babu wani mutum da yake ƙaunarsa sama da shi, wai shi ne ya tura karuwai gidansa, su ɗauko masa abin da ba zai ƙare shi da komai a lahirarsa ba, shi ne sila, tabbas shi ne silar komai.

FAKRIYYA, yarinyar da ya san so akanta, yarinyar da bai taɓa jin wata halitta a ransa irin yadda yake jinta ba, yarinyar da ya kwashe shekaru biyar yana dakon soyayyarta a ƙasar da babu dangin iya bare na baba, yarinyar da mahaifiyarsa ta dinga kwaɓarsa kar ya aureta amma ya lallameta, saboda kawai ta ce masa bata taɓa karuwanci ba, saboda kawai ta nuna masa a gidan karuwan kawai ta tashi, saboda kawai ta gwada masa ita ma so take ta bar gidan, so take ta tafi inda za tai rayuwa me kyawu.

Da wannan tausayin nata, da wannan soyayyar ta dake kwankwatsa zuciyarsa, ya aureta, ba tare da ya yi bincike ba, to, me zai bincika ma tunda ta ce iyayenta sun mutu, me zai bincika ma tunda yana sonta a yadda take ɗin, so mai sunan sp.

Bai san akwai tashin hankalin da ba a sanin yadda za a hukunta shi ba, sai yau.

Bai san akwai tashin hankali da ya fi ƙarfin ɗaukar mataki sai dai a bar shi ga lillahi azza wa jallah ba sai yau.

‘Why me?’

Ya furta a ƙasan zuciyarsa, yana doka kansa a jikin gadon, Me ya sa za a hukunta ta shi da auren yarinyar da ta yi zina da ubansa, shi da yake kiyaye duk wani doka ta mahallicinsa, ga mutanen da ke ta aikata tarin zunuban da ko ƙasa ba ta iya ɗaukar su, me ya sa su ba a jarabce su da wannan ba.

“Astagfirullah! Allah karka ba Ni ikon da zan kaucewa imanina, Allah ka ɗauki raina idan har zan kasance mai saɓa dokokinka.”

Ya furta da maɗaukakin sauti, jin zai tagayyara imaninsa, yana tuhumar mahallicinsa kan abin da yake ƙaddararsa ne, ya sani, haka tasa rayuwar ta juye masa, zai godewa Allah, ya ƙara godewa, bai san hasken da hakan zai ba shi a gaba ba.

Miƙewa ya yi, ya cire waya ya kira masu gadinsa.

Umarni ya ba su, su janye masa Fakriyya daga gidan da duka tarkacenta, su watsar da ita can nesa da gidansa, idan ta farfaɗo ta nemi gidan nata uban. 

Ya gargaɗesu da idan duka duniya za ta taru, kar su sake su buɗe mata gidansa ta shigo, zai iya ɗaukan kowane irin hukunci ga wanda ya karya dokarsa.

Da haka ya juya yana faɗawa Toilet.

Janta sukai kamar kayan wanki, suka fitar ta, ita da tarin akwatunanta, suka watsarta a wani kango da ke nesa da su kaɗan, suka jera mata akwatunanta a gefenta, suka dawo bakin aikinsu, ba tare da wani ya yi ƙoƙarin tashinta ba.

*****

REZA.

Gudu take cikin motar da wani irin speed, hawayen ke sauka har saman cinyoyinta, haka take share su akai-akai tana ƙara take motar.

So take ta isa bakin kogin, ta zauna, ta yi tunanin abin da ke rikita lissafin kwakwalwarta.

Ga fa sautinsa a muryar da ta yi waya, me ya sa sai ta je gabansa komai zai canja, ya CE ba shi ba ne? Me yasa sunansa da ta yi saving da Hamoud yake canjawa, me ke damun kwanwalwarta ne, ko dai ita ce take kallon Number a matsayin ta Hamoud tsabar zarewa.

Akai-akai take kiran Number amma taƙi shiga. A haka ta ƙarasa kogin da bata san yadda akai ta iso lafiya ba. 

Fitowa ta yi, ta ƙarasa inda suka saba zama, ta yi zaman daɓaro a gurin, hannunta saman gashinta tana watsa shi, ta zama tamkar mahaukaciyar da ke murnar samun tikitin zama cikin ‘yan uwanta mahaukata.

Tunani take, idan har wancan saƙon Fakriyya ta yi shi, ta sa kuma agoge shi kafin ta bar gidan, aka kuma ƙara turo wani irinsa, to ya akai Date ɗin ya zama 17July 2014. Ya akai sakon ya zo da haka? Ya akai shekarar da suke ciki ya koma 2014.

Ba ma wannan, wayar da ta yi awa ɗaya da rabi ta fi komai tarwatsa dukkan nutsuwarta, yadda akai sunan ya juye zuwa HAISAM, alhalin ba ta aje wayar ba, balle ta ce an canja.

Tunanin da take ke ƙoƙarin dakatar da tafiyar jinin dake kewaye ƙwakwalwarta, ta idasa zarewa. 

Ba ta san sa’adda FAKRIYYA ta fara tsafi ba, tabbas wannan tsafi ne irin wanda take jin ana yi. Idan ba tsafi ba ne to menene?

Sanin babu mai bata amsar tambayarta, ya sa ta ƙara fashewa da kuka, tana danƙar yashin dake gurin da hannuwanta.

“Dan Allah ki bar kukan, kukanki na hana duk wani gudun jinin da ke kewaye sassan jikina, ina jin ba zan taɓa yafewa kai na ba.”

Ta ji saukar muryarsa a saitin kunnenta, da ƙamshinsa da ya daɗe da zama cikin zuciyarta, tana jin yarda sassanyan hannun nasa ya sauka a kafaɗunta.

A haka ta ɗago ta dube shi, idanuwansu suka sarƙe da juna, zuciyarta ta buga tamkar za ta faso daga ƙirjinta ta faɗo a gabanta, a haka ta yi wata irin alkafira ta koma can nesa da shi da wani irin firgici, bakinta na karkarwa haka take nuna sa da yatsa.

Alkyabba ce sanye a jikinsa da aka saƙata da zaren gwal tana ta walwali cikin hasken ranar, a cikin kwayar idonsa da take launin kore me haske ta gane bambancin wannan Hamoud ɗin da yake gabanta, da kuma wancan HAMOUD din da Fakriyya ke aure. Ban da wannan, babu wani abu da ya canja kamarsu, kai hatta da tsiron farcensu, iri guda ne.

“Wa…wa ne.. ne kai?”

Ta furta, tana ƙara yin baya, ganin yana kusanto ta.

“Dan Allah karki tsorata, karki guje Ni QURAISHA, abin da nake tsoron faruwarsa ke nan, abin da ya hanani faɗa miki gaskiyar lamari na ke nan, na sani, idan kika gane Ni, ba za ki taɓa yadda da Ni ba, ba za ki taɓa so na ba, shi ya sa na je miki da sunan takwarana a halittar duniyarku ta BIL’ ADAMA, wallahi ina sonki, soyayyar da da ta hanani in aureki Ke nan, domin kawai kar na cuceki, na aje a raina, zan yi duk yadda zanyi na haɗa soyayyarki da Hamoud, da yake mutum irinki…”

“YERIMA HAISAM sunana, ina roƙarki, da girman mahallicinmu, karki guje Ni, ki barni ko da abokin ki ne, ki barni na rayu da ke kina ɗebe min kewar MATATA HAJJATEE, da take kama da ke, hatta a sunanku, iri guda ne, QURAISHA sunanta.

Ya furta yana kusantarta, hawaye na zubo masa, hawaye irin namu na mutane, take gani suna fita a halittar da ya kira kansa da HAISAM, a halittar da ta shafe shekara tana wujijiga cikin soyayyarsa, a halittar da ta fara haɗuwa da ita a banɗaki, a gidan Alhaji Nawazuddeen Sheerif.

Tirƙashi!

Tabbas sai yau ta samu amsar tambayarta, ya za ai ta je sata gidansu, ya kuma ga fuskarta lokacin da ta tsaya tana kallonsa, amma ace bai kaita Prison ya rufe ba, Yana kuma jinin gidan, ashe ba Hamoud ba ne, wannan wani ne me kama da shi, hatta a sautin muryarsu.

Sai yanzu ta tuna ranar da suka je gidan wani babban malami zai ba su fatawa kan yadda za tai Istibra’i, sun doshi gidan za su shiga, yana sa ƙafarsa a dokin ƙofar taga ya dawo baya da sauri, ya ce ita ta shiga, tana tuna yadda kalar idanuwansa suka koma kore, amma ko a kanta.

Tana tuna yadda duk inda ta je za ta ganshi, tana tuna sanyin dake jikinsa, sai yanzu ta tuna ranar da HAMOUD ya shaƙeta babu wannan sanyin, tabbas babu, amma bata taɓa kula ba. 

Sai yanzu ta tuna ta taɓa tambayar Fantasia, lokacin da taje tana jawo hannunta su bar gidan Alhaji Nawazuddeen, ko ta kula da wani kyakkyawan mutum a toilet, ta CE mata ita bata ga kowa ba, amma bata taɓa nazari ba.

“Ki yafe min, Ni kaina bansan yadda akai hijabin da ke tsakanimu ya yaye a ranar ba har kika gani, ban san yadda zan hukunta zuciyata ta daina sonki ba, wallahi ina sonki, fiye da duk wata halitta da ta taɓa nuna miki so.”

Bakin shi kawai take gani yana motsi, kunnuwanta sun daina jin sauran zancen, tashin hankalin da take ji cikin maganganunsa sun sa komai ya tsaya mata cak! Tsoro da firgici ya sa ta ci gaba da yin baya, a haka ta yi tuntube da wani dutse, ya kwasheta zuwa cikin kogin, tana jin lokacin da ruwa ya toshe duk wani jinta da ganinta, a haka ta nutse can ƙasan kogin.

“QURASHAAAA!”

Ya furta da wani maɗaukakin sauti da ya tada wata yar ƙaramar guguwa a gurin.

Da tashin hankalin da bai san inda zai aje girmansa, ya yi tsalle ya faɗa shi ma, yana mai lalubarta.

<< Asabe Reza 11Asabe Reza 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×