Skip to content
Part 13 of 33 in the Series Asabe Reza by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

FAKRIYYA

A hankali take buɗe idanuwanta da suka yi nauyi, ga wani irin sanyi na kada ta. 

Da ƙyar ta lallaɓa ta tashi zaune tana ƙarewa gurin kallo.

Cikin hasken maghribar da bai gama lumewa ba ta hangi saitin akwatunanta, kai harda maclean da brush ɗinta an watsar mata nan gurin.

Ƙara ta kwalla mai ƙarfi, tuna maganganun da Hamoud ya furta mata na ƙarshe.

“Je ki na sake ki, saki uku!”

Haka kalmomin suka ƙara dukan kunnuwanta, ta riƙe kanta da taji ya mata wani irin nauyi, ga hannunta dake mata zugin da take jinsa har a yatsar ƙafarta.

Ba ta damu da cire kwalaben hannunta da suka lume ba, ta miƙe tana tangaɗi, tana haɗa hanya tamkar zararriya, a haka ta ƙarasa ƙofar gidan ta hau bugu.

Tun tana yi da hannu ta hau da dutse, tun tana da dutsen ta koma tana doka kanta, gaba ɗaya ta gigice, sai kwala masa kira cikin muryar kuka tana ta ba shi hakuri take, tana ƙara tabbatar masa da yadda take sonsa.

Tana ganin maƙota na fitowa kowa da irin tambayar da zai mata, amma ko ta dube su, har su gaji su juya suna la’antarta.

Sai da duk wani ƙarfinta ya ƙare a jikin gate ɗin, amma ba su yi ko tari ba, balle tasa ran za su buɗe.

A haka ta durƙushe tana jingina bayanta jikin ƙofar, tana kuka me ciwon da babu nadama, sai tarin burirrikan ƊAUKAR FANSA.

Miƙewa ta yi ganin har an sallaci isha bai fito ba, da haɗa hanya, da dafe bango ta isa ga titin, ɗan taxi ta tare zuwa gida, bata bi ko ta kan akwatunanta dake kangon ba.

A bakin gate ɗin ta tadda mariƙiyar ta ta LINDA, naniƙe da wani baƙin mutum suna lalubar junansu, ga ta dai ta zama dattijuwar da ke ɗaukar shekaru sama da arba’in da biyar, amma fa mutuwar zucin na nan naniƙe da ruhinta.

Yanayinta da ta gani tana  fitowa daga taxi, ya sa ta saurin sallamar mutumin, ta ƙarasa tana tambayar lafiya, da hannu ta gwada mata ta biya mai taxi ɗin kuɗinsa.

Ba ta shiga gidan ba, ta tsaya tana kallon jerin gwanon gidajen nasu, da bariki ta sa suka mai da shi tamkar estate, yadda duk wanda ka gani a unguwar, idan ba tantirin ɗan iska ba, to riƙaƙƙen ɓarawo ne. 

A gida na biyar idonta ya tsaya, wani numfashi ta ja ta furzar, ji take ina ma ta ƙarasa gidan da galon ɗin ta na fetur, ta zazzagawa gidan ta kesta ashana, su ƙone ƙurmus, yadda ko ƙasusuwan Reza ba za a gani ba, balle a samu damar mata suturar da za a kaita makwancinta.

A haka taji hannuwan Linda cikin nata, janta take, tana ganin yadda tashin hankalin ke bayyana saman fuskarta.

A haka ta ƙarasa da ita cikin gidan, ta zaunar da ita a tsakiyar kujerun falon, ta juya za ta ɗebo mata ruwa.

Hannunta ta riƙo tana girgiza kai, hawayen na sauka a zirin kuncinta, tana jin ɗacin kalmomin da take ƙoƙarin furtawa. A haka suka fito, suna daddatsewa a tsakanin haƙoranta.

“Ha… Hamoud ya sake Ni, sakin da ba zan ƙara wanzuwa tare da shi ba.”

A tsaye take, sai gata zaune saitin ƙafafunta.

“Kamar ya, me ya faru, duk ina son da yake miki, kai haba dai, sati guda fa, yaushe akai auren, me kika masa, ina kwallinki, ba na ce karki sake ki wayi gari baki shafa ba?”

Haka ta jero mata tarin tambayoyin cikin hali na kiɗima.

“REZA ce, reza ce silar mutuwar aure na, ta kai masa hotona da na ɗauka tsirara Ni da Disco, ta faɗa masa wannan sirrin, wannan sirrin dai da kika ce gobe za mu je a rufe bakin duk wani da ya san da shi, sirrin nan dai dana kwanta da mahaifinsa, ta ya ya ba zai barni ba..?

“Ban san me ya sa ba, ban san me ya hanani kashe Reza ba a tun ranar da ta furta ta san Hamoud, da shi ne take soyayya…”

“Ni ma na rasa gane lamarin, na rasa gane wurin da ta san shi, shi dama baya ƙasar, da dawowarsa da aurenku wata biyu fa, har a raina, na ɗauka kawai sharrinta ne, tana son raba ku ne ta ɗau fansar uwarta akanki.”

Linda ta furta, tana kallon cikin idanuwanta.

“To ai bata san abin da ya faru ba, kin sani Soupy ba ta gaya mata ba, Ni kaina na ɗauka wasa ne, musamman da na tambaye shi, ya ce shi bai taɓa ma saninta ba, In ba Ni da na nuna masa ita ba a matsayin ƙawata, na rasa gane kan lamarin, a ranar da na tare ma fa sai da taje gidana, tsakar dare, ya mata rashin mutunci…”

“Na daɗe ina mamakin yadda akai ta san gidan, alhalin ba wanda ya kaini, balle ma aga gidan nawa, sosai mukai faɗa da shi a daren, ya rantse min da mahalliccinsa bai santa ba, na san halin Hamoud, wallahi da ya taɓa saninta zai faɗa mini…”

“To Ina ta sanshi? A ranar da aka ɗaura auren kika kirata walimar ko, ki tuna reaction ɗinta a lokacin da ta yi arba da shi, ki tuna yadda ta dinga fashe-fashen kaya, tana furta ya ci amanarta. A yanayinta da maganganunta, za ki gane soyayya ce tsantsa a ruhinta, sai dai ikirarin da ya yi bai santa ba shi ya kauda tunanin kowa, aka fara tunanin ko ta zare ne.

Sannan ga zuwa gidanki da ta yi, ta ina ta san gidan, idan ba shi ne ya kaita ba? Ke, bama wannan ba, na daɗe ina tunanin abin araina, na dai kasa furta miki ne kawai, shi kansa ginin gidan, da komai da aka saka na gidan zaɓin Reza ne, shi ne irin gidan da take so, hatta da launin labulayen, irin nata ne, wanda take buri! 

Akwai wani abu a ƙasa, wannan ba zai taɓa zama arashi ba, tabbas Hamoud ya san Reza, sai dai ta ya ya?”

“Bai san ta ba, ki yarda da ni, Ni na san waye Hamoud, wallahi da ya santa zai faɗa mini, ya tsani ƙarya, ya tsani kuma a masa ita.

Na sani tabbas Reza tana soyayya, sama da shekara ɗaya da rabi ma, a tun ranar da muka je gidan Nawazuddeen, gaba ɗaya takun rayuwarta ya canja, ke kin sani, bata ƙara harka da wani namijin ba, sai dai taƙi nuna mana saurayin, ko da a hoto ne, ina jin Soupy kawai ta san shi, bata taɓa kawo shi gidan ba, balle mu ganshi. Na fi tunanin tana ɓoye mana shi kar mu kwace mata.

To Ni mamaki na, ina nata saurayin da zata matsawa nawa mijin, ba zan barta ba, ba zan taɓa yafewa Reza ba, idan har ta yi ne danta rabamu ita ta aure shi, zanga yadda auren zai yiwu. Wallahi, na rantse da girman Allah, idan sama da ƙasa za ta haɗu, ba a isa anyi auren nan ina numfashi ba, Hamoud nawa ne Ni kaɗai, ko babu Ni, ba zan taɓa barinsa ya yi rayuwa da wata macen ba.”

Ta furta, zuciyarta na bushewa, hawayen na ƙafewa, sai tsananin zafi da zugi dake danƙare a ƙirjinta.

“Ree, Ke yarinya ce har yanzu, baki san namiji ba, namiji fa Ree, namiji shi ya yi sanadin mutuwar uwarki, namiji, kuma mahaifinki, shi ya sa a kashe uwarki fa, duk kin manta da wannan? Kike ikirarin Hamoud baya ƙarya. Saboda soyayya ta rufe miki ido.

Lefin ki ne, duk ke ce silar komai, sai da na hanaki  auren shi, tunda har kin fara sonsa da gaske, amma kika ƙi, ke kin sani, tunda har kinyi kuskuren kwanciya da mahaifinsa, ta ya ya zamanku zai ɗore? Me ya sa kika ƙi gane abin da nake hango miki, me ya sa dole RAMUWARKI sai ta kasance har a kan ɗansa, abin da kika yiwa mahaifinsa, ya isa ya goge miki koma menene da ke ranki, cin mutunci ne, irin wanda da wahala ya goge a rayuwar wanda aka yiwa, yaushe zuciyarki ta ƙeƙashe har haka? Yanzu wa gari ya waya? Yanzu menene ribarki? Yanzu ina kike so na kai girman alƙawarin da na ɗaukar wa mahaifiyarki?”

Ta furta, tana hawaye, ji take kamar ta ci amanar Bitil, da ta kasa hana Fakriyya zubar hawaye a DALILIN ƊA NAMIJI.

“Ina sonsa ne, a tun  ranar da ya dawo ya furta mini kalmar so, da burin ramuwa na so auren shi, da burin wargaza duk wani jinin NAWAZUDDEEN na so auren shi. Sai dai soyayyarsa ta hana komai, ina jinsa a wuraren da ban san ya zan kwatanta miki  girmansu ba, ba za ki gane ba, saboda ba ki taɓa soyayya ba, ba ki taɓa jin ɗacin rabuwa da masoyi ba, baki taɓa jin daɗin da zuciya ke samu a yayin da masoyinta ke zaune kusa da ita. Ba zan iya barinsa ba Aunty Linda, Ina hango mutuwata a ranar da na ga Hamoud da wata, ina hango mutuwata a ranar dana tabbatar ba zai sake zama nawa ba.”

Ta furta, har yanzu idanuwan a bushe, hawayen yaƙi ɗiga, zafi saman zafi, ga na zuciyarta, ga na hannunta da take jin kamar ta yanke shi ta jefar.

Jawota ta yi gaba ɗaya jikinta, ta rungume ta tana bubbuga bayanta. Ita kanta hawayen ke sauka, nadama take, irin wacce bata taɓa sanin akwai ranar da za ta yi ta ba.

Da ta sani, basu saka Hamoud a cikin tsarin ramuwar su ba, da ta sani, ba ta amso kwallin kwarjini ta bawa Fakriyya ta shafa ta je ta haɗa idanuwa da Hamoud ba.

Ta sani, ba kwalli ne na saka soyayyar bogi ba, kwalli ne na sanya kwarjini a duk idanuwan da ka haɗu da shi, za su daɗe ba su manta ka ba.

Ta sani, soyayyar Hamoud ga Fakriyya, soyayya ce me girman da ta daɗe tana jinjina ƙarfinta, duk da ta san kwallin ne ya fara karkato da hankalinsa kanta, sai dai da gasken, sonta yake.

Soyayyar Fakriyya ga Hamoud ke taɓa ranta, ba ta so ba, kai ko a wasa, bata kawo yiwuwar Fakriyya za ta iya auren wanda ya haɗa jini da babban maƙiyinsu, a gaba ɗaya rayuwarsu.

Lalle SO, abu ne me girma, da yake fidda ɗan tsironsa a zuciya, da idan ba ka taka a hankali ba, yanzun nan tsiron zai fara yabanya, ya zama bishiya me ƙarfin da ba ka san yadda za ka sare jijiyoyinta a zuciyarka ba. Kamar dai halin da Fakriyya ke ciki yanzun, ta je da burin ramuwa, ta bige da dakon bishiyar so a zuciyarta.

To wa gari ya waya?

“Ki yi hakuri, kin sani ba zan taɓa bari ki tagayyara ba, alƙawari ne wannan, ba dai Hamoudi kike so ba, to za ki koma ɗakinki, ke za ki rayu da Hamoudi, ko da ta hanyar dadiro ne, sai ya zama dadironki, idan har ina numfashi. Kin riga fa kin gama da zuciyarsa, Hamoudi yana miki son da yake iya ketare zancen mahaifiyarsa a kanki. To ta ina wata za ta samu wurin zama a zuciyarsa?

Ki kin sani, abu biyu gare mu, masu girman da za su samar mana duk abin da muke so.

To ga na uku ma na samo yanzu cikin raina, wannan ukun, sun ishe mu tarwatsa duk abin da mukai niyya. Karki damu, zan gaya miki na ukun idan lokaci ya yi. 

Ki je yanzu ki gyara jikinki, zan kira Dr ya duba jikin naki, ki kwantar da hankalinki, ki aje ma ranki kamar kin samu Hamoud kin gama ne, kamar kin tsarwatsa rayuwar Reza kin gama ne.

Tashi ki je ki ga su  Haamin da Haajir, sunyi ɓul-bul abin su gwanin sha’awa, na sani ai kina kewarsu ko?”

Ta furta cike da rarrashi tana ɗan bubbuga bayanta.

Gyaɗa kai ta yi, ta miƙe da ƙyar tana dosar ɗakin.

Linda ta bita da kallo, zuciyarta na ƙara tsinkewa, tausayinta take ji, har bata san me za ta yi ta dawo da ita yadda take so ba.

Sauke numfashi ta yi, ta ɗauko wayarta, ta fara latso number likitan.

<< Asabe Reza 12Asabe Reza 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×