REZA
A hankali take buɗe idanuwanta, har suka gama buɗewa tar! Suna kallon rufin ɗakin.
Zumbur ta miƙe saman gadon tana shafa katifarsa, ganinta da ta yi cikin ɗakinta, a saman gadonta, an rufe ta da bargo, ya sata mamakin sa’adda ta dawo har ta kwanta.
Ji take kamar ba ita ba ce, kanta na nauyi tana son tuna wani abu. Da ƙarfi ta runtse idanuwanta, tuna wayar da ta yi da safe, da yadda sukai da Hamoud, Haisam, tiryan-tiryan abubuwan suka dawo mata.
Jikinta ta shafa, tuna ta faɗa ruwa, a bushe tsaf! Babu wani danshi dake nuna tama shiga ruwa.
‘Mafarki nake?’ Ta tambayi kanta da kanta, ‘a’a’ ba zai taɓa zama mafarki ba, wata zuciyar ta furta mata, hannu tasa tana bubbuga goshinta da ƙarfi, tana hango kalar asbitin da zata je domin a duba kwakwalwarta.
“Tabbas ba Ni da lafiya.”
Ta furta a sarari, tana ƙara shafa jikinta.
“Kalau kike Quraisha.”
Ta ji ƙamshinsa, da sautinsa, da zamansa kusa da ita, duk a lokaci guda, da ba ta san ta inda ya shigo ɗakin ba.
Zabura ta yi ta buɗe baki za ta kwala ihu, ya yi saurin toshe bakin da hannuwansa, ya matsa tamkar zai shige jikinta, a haka ya ɗora idanuwansa cikin nata, ya canja launinsu suka koma kore shar, tun tana mummun,hmmmm,mmmmm, harta saduda, ta yi laƙwas, a hankali ya zare hannuwansa daga bakinta, ga mamakinta ta kasa bude bakin, haka tsoron a hankali ta ji yana raguwa.
Murmushi ya mata, ya jawo ta jikinsa gaba ɗaya, tamkar wacce aka cire ma laka, haka ta biyosa.
“Ba zan taɓa cutar dake ba QURAISHA!”
Ta ji sautinsa cikin kunnuwanta, tana jin yadda ya hura mata wata iska a kunnen. Lumshe idanuwanta ta yi, ji ta yi hankalinta na kwanciya, ji ta yi kamar ma su dawwama a haka, ji ta yi duk wani tsoronsa ya kau a zuciyarta.
Sakinta ya yi, ya dawo gefen gadon ya zauna yana mata murmushi.
ta ma sunkuyar da kanta ta yi tana juya yatsunta, tarin tambayoyi gareta da bata san yadda za ta fara masa ba.
“Ina jin haushin ace ba za ki yi magana da Ni ba sai da ƙarfin iko na, ina so ki bar tsorona ki sa a ranki Ni masoyinki ne da ya zame miki tamkar jini da hanta. Dan Allah ki bar tsorona, ki tuna ranakun da muka kwashe tare, ki tuna kyautatawar da na miki ko yaya ne, ki aje a ranki ba zan taɓa yin wani abu dan na cuceki ba, sai domin maslaharmu.”
“Hmm, me zan ce? Ban san yadda mutum zai iya zama da irinku ba, har kuyi magana ta fahimta, abin ya zo min a sabo.
Karka damu hakan ma ya mini daidai, watarana na san ba zan ji tsoron ba, ka faɗa mini dalilinka na cutata, ka sa na so ka, alhalin kasan ba za mu taɓa wanzuwa tare ba, akwai bambamci sosai tsakaninmu, me ya sa ma ka siffantu da ɗan mutumin da muka je yi sata gidansu? Me ya sa ba ka zo min a ainihin halittar ka ba? Wannan shi ne son? Kana ƙoƙarin haukata Ni ne fa, kai duk wanda ma zai ji labari irin wannan, sai ya yi da gaske, zai hana kwakwalwarsa zarewa.
Me na maka a rayuwa har haka, ka sani fa halittata na da raunin da ba zan iya ɗaukar ɗabi’unku ba. Ka haɗa Ni da Hamoud, kasa ya ci mutunci na, ka sa ya mare Ni, ya shaƙe Ni, duk son ne wannan, wace irin maslaha ce wannan?”
Ta furta, tana jin zafin abin cikin zuciyarta, ita ce ta shafe fin shekara tana soyayya da Aljani, tana yawo da shi, wata irin rayuwa ce wannan?
“Ban sani ba, ki yarda da ni, idan da na san zai mare ki, da na daɗe da shanye masa hannuwansa. Wannan siffar tawa ce, ita ce ta ainihin halittata, ba wai siffantuwa na yi da shi ba. Bari ki ga bambamcin da ke tsakanimu, amma karki tsorata.”
Ya furta yana miƙa mata hannuwansa. A take taga farcensa sun ƙara tsayi, haka gashi ya fito bakikirin, ya rufe duka saman hannuwan nasa har zuwa gwiwar hannun, ya canja launin idanuwansa suka koma kore, ya buɗe haƙoransa taga fiƙoƙinsa sun ɗan ƙara tsayi.
Ba ya ta ɗanyi da tsoro, duk da ya mata kyau, amma kam ba kamar Hamoud da yake Mutum ba.
“To wannan shi ne bambamcinmu da Hamoud.”
“Shi ne kuma dalilin da yasa naƙi yarda mu yi hoto da ke ko da a wayane, saboda ba zai fita daidai ba, zai fito ne da dukkan siffata da na ɓoye, na san kin tuna ranakun da suka wuce kina min nacin muyi hoto.”
Ya furta da murmushi yana komawa daidai.
Ita ma murmushin ta yi, tuna faɗan da suka sha yi kan hoton
A haka ta ji sautinsa yana ɗorawa.
“Kamar yadda na faɗa miki jiya, YERIMA HAISAM sunana, mu musalmai ne, mahaifina ke da sarautar wani yanki dake can daular Isbaniya(Spain).
Ban taɓa shigowa yankin Afrika ba sai a dalilin Hajjatee.
Matata ta ce, da ban taɓa son wata halitta a duka rayuwata ba sai ita, ke tun ina yaro ƙarami muke soyayya, har muka girma, iyayenmu suka haɗa auren mu.
Mun shafe shekaru ɗari da sittin tare, bata taɓa yin ko da ɓari ba, mahaifina ya damu, saboda ni kaɗai ne ɗansa, gashi ya yi tsufan da dole yana burin ganin jikansa, da zai gaje ni, a bayan na hau mulkin.
Da haka watarana ya samu labarin wani babban malami da ke bada maganin haihuwa, anan lardin Afrika, sai dai ɗan Adam ne shi. Ni ya turo na zo nan a siffa mai kyau, na sadu da malamin, ya ba Ni maganin.
In takaice miki, da shanta, da samun cikinta ba a rufe wata guda ba. Muna ta mamakin girman siddabaru irin naku na ‘yan Adam.
Haka muka ci gaba da renon cikin har zuwa lokacin da ya isa haihuwa. Tana kan ƙoƙarinta, har yanzu ina hango lokacin cikin idanuwa, tana kan ƙarfinta, ta mutu, daga ita har jaririn, babu wanda ya rage min, sun tafi sun barni, a lokacin da ba Ni da wani sama da su. Ki hango yadda rayuwata za ta kasance…”
Ya furta yana hawaye, itama hawayen take yi, a hankali ta kai hannunta fuskarsa, tana jin sanyin hawayen, haka ta goge masa su.
Tana girgiza masa kai cike da tausayi.
“Daga ranar da aka share arba’in ɗinta, na shiga duniya, na bar yankinmu, saboda bansan inda zan aje girman bakin cikin da zanji a yayin da zan shiga gidana banga HAJJATEE ba.
To, a yawan da nake yi ne, na zo har nan garinku Kano, a wancan gurin da muke yawan haɗuwa dake (Cindrella Park) na fara ganin HAMOUDI, mamaki nake ina girmama girman halittar Ubangiji.
Na gansa da irin siffata, hatta muryarmu, iri ɗaya ce, babbancin kawai shi MUTUM ne Kuma ALJANI.
Abin ya burgeni, na bisa na ga gidansu, ke ƙarshe ma sai in shafe watanni ina rayuwa cikin gidansu, ina ganin yadda rayuwar mutanen ke sanya Ni nishaɗi.
Na kuma ajewa raina, tunda naga me kama da Ni, to kuwa zan iya ganin me siffar matata kila a cikin yan uwanmu ma Aljanu, to daga ranar na fara bincike ina nema ko zan samu wata irin HAJJATEE.
Har Allah ya kawo ranar da kuka je gidan fashi, shigowata ke nan toilet ɗin da waya a hannuna, kika buɗe, Ni kaina ban za ci kina gani na ba sai da naga kin ƙame kina kallona.
Na sha mamakin abin da ya raba hijabin da ke tsakaninmu har kike iya gani na, na kaɗu matuƙar kaɗuwa a lokacin da na ganki da Siffar matata HAJJATEE, hatta ‘yan kunnewan da kika tara a fuskarki, ita ma shi ne a tata fuskar.
Abin bai ƙara ruɗani ba, sai da na binciko cewar, hatta sunanku iri guda ne.
Ita ma QURAISHA sunanta ba…”
Ya furta yana sauke numfashi.
Hangame baki ta yi gaba ɗaya tana jinjina girman duniyar nan. Ashe shi ya sa ya hanata cire barimomin fuskarta.
“Yanzu nufinka hatta muryar mu iri ɗaya ce?”
“Hatta tafiyarku iri ɗaya ce, idan na ce kama, ina nufin komai da komai fa.”
“Taɓdijam! Amma abin akwai ɗumbin mamaki, yanzu ke nan za a iya samun wasu masu kama damu?”
“Me zai hana, ta yiwu ma fin dubu, ko za ki bi Ni mu kewaye duniyar mu zaƙulo su?”
Ya furta da alamun zolaya, yana hango zallar yarintarta.
“Niiiiii?” Ta furta tana yin baya.
Murmushi ya yi.
A daidai nan kuma suka ji motsin buɗe ƙofar za a shigo ɗaki, kallonsa ta yi a tsorace tana masa alamar ya ɓoye, murmushi kawai ya yi ya juya yana kallon ƙofar.
“Ikon Allah, yaushe kika dawo gidan nan ban sani ba? Duk kin tada min hankali fa Reza.”
Soupy ta furta tana ƙarasowa bakin gadon.
Kallo Soupy ta yi, ta juya ta kalle shi, yatsansa ya ɗora a bakinsa, ya mata alamun bata ganinsa.
“Magana fa nake miki?”
“Da na shigo fa kina Toilet nake zato.”
“Amma shi ne ba za ki iya zuwa ko mahaifiyarki ki gani ba, duk kinsata a damuwa fa.”
“Kuyi haƙuri, ba na jin daɗi ne, gobe zan fito ai, ki tafi dan Allah, so nake na samu barci.”
Ta furta tana kwanciya, ta ja blanket ɗin ta ƙudundune.
Ganin haka Soupy ta kashe mata fitilar, ta fice tana mita.
Miƙewa ta yi tana yaye blanket din.
“Hmm ka CeCe Ni, da Soupy ta ganka anan, bansan kalar rawar borin da za ta yi ba.”
Dariya ya yii
“Ai ba za ta ganni ba, dole sai idan Ni ne na so.”
“Ina jinka, ci gaba, mamaki nake yi ina ƙara mamaki” ta furta, zuciyarta take ji na mata dadi, kamar ma ba tada wani ku ƙunci a rayuwarta.
“To, daga ranar na rasa duk wani kwanciyar hankalina idan ba na haɗu da ke ba, sonki nake fiye da duk yadda zan kwatanta miki. Na yi duba cikin rayuwarki, na ga akwai tarin kurakurai, to kinji dalilin da yasa na zo miki da soyayyar, kika amsa, na hanaki karuwanci, na kuma koya miki kula da addininki da duk abin da zan iya.
A lokacin da muka yanke batun aure ne, na jewa mahaifina da zancen. Anan fa ya ce mini, kuskure ne zanyi da mahalliccina ba zai barni ba, babu yarda za ai mutum ya auri Aljan, idan na aureki to na cuceki, ba zaki taɓa haihuwa ba, haka na kassara dukkan rayuwarki.
Na ji bakin ciki sosai da wannan zancen, na ga ba zan iya cutar dake har haka ba, dole na haƙura, to shi ne kafin na dawo kika tafi walimar Fakriyya, anan kuma kika ga Hamoud, kika ɗauka Ni ne.
A bayan na dawo na ga halin da kike ciki, shi ne na miki wannan wasikar, ina mai baki haƙuri, tabbas na je gurin ina jiranki ki zo, In faɗa miki komai, sai kuma wani barana ya zo ya kira Ni, mahaifina kwance rai a hannun Allah Quraisha.
Kinga abin da yasa na tafi. Ban san yadda akai abubuwan suka juye ba, da ace na san Hamoud zai je da Fakriyya gurin, ba zan ma fara cewa ki zo ba. Babu Aljanin da ya san gaibu Quraisha, sai abinda ya gani shi ma.
Da jikin ya lafa ne na dawo, na kira ki ki zo mu haɗu gun Ice Cream, Ina jiranki, aka ƙara kirana, mahaifina ya rasu Quraisha.
Shi ke nan ba Ni da kowa ba Ni da komai sai Sarautar garinmu, sai kuma ke da kike sanyani farin ciki, a yanzu haka rufe shi kawai aka yi na dawo dominki, domin ban san duk abin da zai tada miki hankali.
Ki yi haƙuri ki yafe mini domin Allah, Hamoud Kam alƙawari na miki sai kin aure shi, da ikon Allah.”
“Amma kasan kai nake so ko? Ka san yadda ya tsani gani na ko? Ta ya ya zan auri mutumin da ba ya so na?”
Ta furta, hawayen har sun fara zuba.
Matsowa ya yi ya ɗora yatsansa yana share mata, a hankali ta shige jikinsa tana ƙanƙame shi. Komai nasa ya mata, ita dan dai haihuwa ta haƙura, yana da sanyin hali, tausayi, girmama dan Adam, ba kamar Hamoud ba, da yake ɗan Adam, me tarin butulci, ita ko me take nema gurin namiji banda wannan?
Shi ɗinma ƙanƙame tan ya yi yana juya yanayin rayuwar tasu, abu ne da ba zai taɓa yiwuwa ba ko da a mafarkinsu. Halittarsu ta yi bambamcin da zamansu ba zai taɓa haɗuwa ba ko da a cikin hankali ne. Yarinta ce ke damunta, shi ya sa take hango yiwuwar lamarin. Ina ɗan Adam ina Aljan? Kai ko a cikin ƙissoshin mutanen farko, wannan ba ya yiwuwa.
Hamoud ɗin dai yake so ta aura, zai yi haƙuri da zafin kishinsa, zai danne duk wani abu dake ta so masa, ya barta ta yi rayuwa da mutum ɗan uwanta.
Shi kam zai koma garinsu, ya ci gaba da rayuwarsa, a duk yadda ta zo masa.
“Kamar kina manta Ni Aljani ne, kamar kina manta bambancin halittar mu, karfa ki ganni me kyau, a garinmu wasu kansu na kwaɗo ne, wasu jela garesu irin ta kada, wasu ga kyan har kyau amma ƙafafunsu na doki ne, wasu ga kyan har kyau amma haƙoransu na zomo ne. A hakan kike tunanin za ki iya rayuwa da su?”
Gyaɗa kanta take yi cikin hawayen.
“Ina sonka ne kawai, ina son komai naka.”
“To ki maida soyayyar kan Hamoudi, na san kuma kina sonsa, kin kasa gane zuciyarki ne.”
“Zanyi tunani, amma dole za ka faɗa masa dalilin da yasa nake cewa na sanshi.”
“Uhm! Me zai hana kuwa, ban dai yi alƙawari ba.”
“Yawwa na tuna, wannan gidan nasa da ka kaini ka ce naka ne, ya akai ya zama irin wanda nake so, alhali kuma Hamoud ne ya gina?”
“Ni na dinga ɓata lissafinsa a lokacin da yake ginin, ana sa komai irin wanda kike so, ai na gayamiki gidansu nake zaune. To a gidan da yake ginawar nake so mu zauna tare.”
“Hmm! Lamarinku akwai ban mamaki, tun ina ganewa har na daina.”
“Shekararka nawa, naga kana min kallon yarinya?”
Murmushi ya yi
“Yanzu a cikin ta dubu da dari biyar (1500) nake, Bari na koma, kwanta ki yi barci ki yi ta mafarkin Hamoud.”
Baki ta hangame da murmushi, sai kuma takwanta, shi kuma juya, a kan idonta ya ratsa bangon yana mata murmushi.
Juyi ta yi, sunan Fakriyya ya faɗo mata arai.
Ko dan ita sai ta auri Hamoud, balle ma tana jinsa aranta ma.
‘Hmm yanzu aka fara’
Ta furta a ƙasan zuciyarta.