Bayan Kwana Uku
HAMOUD
“Ban baka wannan damar ba, ban aike ka yin abin da gaba za ka zo kana nadamarsa ba, banga dalilin da za ka ce dole sai ka ɗauki fansa ba. Wai Yaushe ka canja Hamoud? Yaushe zuciyarka ta yi ƙeƙashewar da ba ta ƙarbar duk kalar ƙaddarar da ta zo mata. Wannan ba kalar tarbiyyar da na baka ba ce. Wannan wani banzan hali ne ka aro kake ƙoƙarin yaɓa shi a daɓi’arka.
Kwana uku kana matsa min kan wannan maganar Hamoud? Tubabbiyar karuwa fa? Kai ke nan a karuwai za ka ƙare? Duk tsawon watannin da na shafe ina dakon cikinka, na yi naƙudarka, karuwai na haifawa? Inaa! Ba zan yadda ba ne, ka tashi ka tafi!!”
“Mamy dan Allah…”
Ya furta yana riƙo hannuwanta.
“Ba fa daɗewa zan yi da yarinyar ba, ba zan taɓa haɗa miki jini da na karuwa ba. Zan yi ne kawai domin Fakriyya, zan yi ne domin ta ji kwatankwacin zafin da na ji. Mamy ba za ki gane girman tabon da Fakriyya ta bari a rayuwarmu ba ne, ba za ki gane ba. Ki bar Ni inyi auren nan domin Allah.”
“Me kake ɓoye min Hamoud? Menene ya yi girman da zaka ɗaukarwa kanka wannan hukuncin? Menene hikimar da dole sai yarinyar za ka aura?”
“Babu Mamy, babu abin da na ɓoye. Ita yarinyar ‘yar uwar Fakriyya ce, tare suka tashi. Na san kalar kishin Fakriyya, ba za ta iya ganin aure na da yarinyar ba tare da zuciyarta ta buga ba. Shi ne buri na.”
Shiru ta yi tana nazartar zancensa.
“Me zan cewa Abbanka? Shi da baya garin.”
Sosai ya matso yana ƙara riƙe hannuwanta.
“Ai kin ce a rufe masa zancen tunda ya danganci Kawu. Kawai ki ce masa aure zan ƙara. Na san ba zai ce komai ba.”
Ajiyar zuciya ta yi tana zare hannuwanta dake cikin nasa.
“Mamy!”
“Me ye kuma?”
“Kisa albarka dan Allah, kinga wancan baki saka ba kawai cewa ki kai kin yarda.”
“To, zansa.
“Yawwa!”
Ya furta da murmushi yana miƙewa ya fice.
Ta bi shi da kallo zuciyarta cike da taraddadi.
*****
Ya fi ƙarfin minti goma tsaye cikin gate ɗin kafin ta fito cikin yauƙi tana taunar cingam.
“Ya miki kyau!”
Ya furta yana zama.
“Na ɗauka ka tafi ai.”
Ta furta itama tana zaman.
“Sai ki shirya, na faɗawa Mamy ta yarda, ina ga jumma’ar sama za a ɗaura.”
“Da yake ga kaza ka samu ko.”
Ƙanƙance idanuwansa ya yi yana dubanta.
“Ban san lokacin da na furta maka zan aure ka ba balle har ka fara tunanin tsaida rana.”
“Kin san me?”
Bai jira amsarta ba ya ɗora.
“Da za ki taimaka ki fidda cingam ɗin bakinki da kike tauna cakal-cakal tamkar yan tsaki na caccakar hatsi, da na fi fahimtar zancenki.”
Tofarwa ta yi tana ɗame fuskar baƙar maganar da ya watsa mata.
“Na ga sai yau ka dawo?”
“Kamar kina missing ɗi na?”
“Allah ya tsare Ni.”
Murmushi ya yi yana ɗora hannayensa saman tebirin dake tsakiyarsu.
“Ya kamata mu gama maganar nan. Kin amince da batun auren?”
“Ya zan yi? Ai dole na amince tunda ka damu da son aure na. Amma fa da sharaɗi.
Lefe nake so irin wanda ko ‘yar shugabar ƙasa ba za ta samu kalarsa ba, Akwati arba’in (40) kowanne kuma kar asa abin ƙasa da dubu ɗari(100000). Sai gurin da nake so ayi Dinner, yafi ko’ina tsada a faɗin ƙasar nan, idan ka yarda to.”
Ta furta tana latsa wayar hannunta cikin nuna halin ko’in kula.
“Oh, kina ganin ba zan iya ba ke nan?”
“Ina na sani?”
Numfashi ya furzar mai zafi yana kallon wayar hannunta.
“Ba Ni Number dinki.”
“090…”
Ta dakata tana yatsine fuska.
“Ba zan iya ɓata bakina wurin karanto maka ba, daga 20 ka yo ƙasa, abin da ya haɗa ma number, to ita ce tawa.”
“Amma fa ya kamata ki dinga tauna kalamanki kaina, tunda mijinki nake shirin zama.”
“Idan lokacin ya yi zan gyara in zan iya, kai ma ka dinga kula da abin da ke fita bakinka a kaina.”
“Ban san yadda zan iya tausasa kalamaina kan yarinyar da ta ratsa alfarmar gidanmu domin sata ba.”
“Ko?” Ta furta tana miƙewa da wani ɓacin rai da ya taso mata.
“Za ka iya tafiya, ba na buƙatar hirar.”
Murmushi ya yi mai sauti yana miƙewa.
“Kin kuwa kyauta, dama ji na nake kamar a saman ƙayar salmon fish.”
A fusace ta juya akan takunta tana komawa cikin gidan.
Da wani yanayi da bai san ya zai kwatanta shi ba yabi bayanta da kallo, sai kuma ya kada kai ya wuce.
Har dare da yake kwance saman gadonsa taƙi barin cikin tunaninsa. Shi kaɗai yake murmushi yana tuna kalar tsiwarta.
Wayarsa ya jawo ya fara jera numbobin da yake tunanin su take nufi. Ga mamakinsa ya ji ta shiga.
Cikin barci-barci ta ji rurin wayar, jawota ta yi ta kara a kunnenta.
“Tunaninki nake.”
Ta ji sautin muryar da ya sata wattsakewa tana tashi zaune.
“Haisam!”
A can ɓangarensa ya ji ta ambaci sunan da ya haddasa masa faɗuwar gaban da bai san dalilinta ba.
“Mtsswwwww!”
Ta ji anja tsaki mai ƙarfi da ya ankararta dawa take waya.
“Dan jaraba kina barci kina tunaninsa, to Ni ne.”
Ɗame fuska ta yi kamar tana gabansa.
“Idan masifar za ka yi zan rufe.”
“Rufe, Ni ma bansan dalilin kiran ba.”
“Kai dai?”
“Ni dai me?”
“Ko ɓarauniyar gidan naku ce ta hanaka barci?”
“Kina wasa ne, Allah kar ya gwadan ranar da zan kasa barci dominta.”
“Ni Ko kaga na sha kasa barci dominka, jinka nake araina fiye da tsammaninka.”
Ta furta tana dariya ƙasa-ƙasa.
Shiru ta ji ya yi, ya gaza maganar.
Kafin ta ƙara furta abin da ke ranta ta ganshi cikin hasken da ya sata kashe wayar da sauri tana kallonsa.
Tsaye yake ya rungume hannuwansa yana mata wani irin kallo, kalmomin sun girgiza shi da har bai san sa’adda ya bayyana gabanta ba. Maganganu ne mafi muni da ɗacin da ya taɓa jin an furta a cikin kunnuwansa.
Da sauri ta sauko tana ƙarasawa gare shi, ta gama saddaƙa yaji dukkan kalaman da ta furtawa Hamoud a wasa.
“Was…wasa nake masa, ka yarda da ni.”
Ta furta bakinta na rawa.
“Abin da ke ranki ne Quraisha! Karki damu, ba fa haushi na ji ba, lefina ne dana zauna miki cikin ɗaki. Ki yi haƙuri…”
Ya furta yana riƙo hannuwanta.
“Ki yi haƙuri Quraisha zan tafi, ba zan ƙara zuwa gare ki ba, ba zan iya ba, ba halittar zuciyoyinmu guda ba.”
“A’a Haisam…”
Ta furta, tana jin yadda wani maƙoƙo ya taso ya datse sauran kalaman a maƙogwaronta.
Mamaki take yadda ‘yan kalmomin da basu fi Shida ba ke shirin yin girman da ba ta san yadda za ta hadiye shi ba.
“Na tafi…”
Ya furta yana sakin hannayenta.
“Kar ka tafi…Domin Allah mana.”
Ta furta, tana shan gabansa.
Juyowa ya yi yana kallon wayarta dake ringing.
Ƙarasawa ya yi ya ɗauki wayar idanuwansa suka canja launi da wani irin ɓacin rai, hannu ya ɗora kamar zai ɗaga kiran sai kuma ya fasa, ya kai wayar saitin bakinsa ya hura mata iska, a take kiran ya tsinke, wayar kuma ta kashe kanta.
Ratsawa ya yi ta gefenta ba tare daya dube ta ba ya ƙarasa jikin toilet. Sai da ya riƙe handle ɗin ƙofar tukunna ya juyo yana dubanta.
Zuciyarsa ta karye ganin yadda take kuka tana toshe bakinta. Ji ya yi kamar ya rushe duk wata katanga dake tsakaninsu ya ɗauke ta zuwa ƙasarsu suyi rayuwa tare. Sai dai kalaman mahaifinsa da yake jin kuwwarsu cikin kunnuwansa tamkar yanzu ake zuba su sun kashe duk wani kwarin gwiwarsa. Ba zai iya ba, ba zai iya zaluntarta a cikin ƙananun shekarun nan nata ba.
Menene amfanin rayuwarsu taren idan ba za su dawwama tare ba adadin nasa shekarun?
Idan ya ɗauke tan shekara nawa zasu yi ta tafi ta barshi da wani sabon ƙuncin? Zai rayu da ita ne yana taraddadin kusantowar mutuwarta duk da babu wanda ya san gawar fari. Sai dai shi zai iya ƙara shekaru dubu nan gaba yana nan a matashin shi, amma ita fa?
Shekaru Saba’in (70Years) idan aka ƙara kan shekarunta ba za ta ganu ba. Ke nan idan hakane za ta barshi da tabon da shi ma sai dai ya yi sanadin mutuwarsa. Lumshe idanuwansa ya yi yana jin dama ya kasance kalar jinsinta, da babu abin da zai hana shi samunta ko da kuwa ya kai girman kogin nilu.
Bai san ya tako zuwa gabanta ba sai da ya jita a jikinsa ta ɗora kanta saman ƙirjinsa.
Hannuwansa ya kewaya a nata ƙugun yana ƙara janta cikin jikin shi.
“Ban san kana nan ba da ba zan furta ba duk da wasa ne. Ai ance kuna shiga jikin mutane, ka shiga ka duba cikin zuciyata ka gani idan gaske nake.”
ThTa furta da hawayen da yake jin ɗuminsu a sassanyan jikin nasa.
Murmushin da ba shi da alaƙa da yanayin da suke ciki ya yi, yana shafa bayanta a hankali. Kalaman da yake son furta mata yaji sun masa nauyin da ko harshensa ba ya iya ɗagawa, kawai sai ya ɓige da hura mata iskar bakinsa a saitin kunnenta. Yana jin yadda take sauke ajiyar zuciya tana ƙara ƙanƙame shi a haka barcin ya sure ta.
Shimfiɗe ta ya yi saman gadon ya rufa mata bargonta ya tsaya kawai yana kallonta. Yana jin yadda ɗumin hawayen ke sauka har a saman alkyabbarsa amma bai damu da ya goge su ba.
A hankali ya sunkuya ya sumbaci goshinta, ya ɗago yana riƙo hannunta. Zoben dake ƙaramin yatsansa ya zare ya saka mata a nata yatsan.
Ya ɗade tsaye yana kallon hannun kafin kuma ya juya yana barinta. Ba garin Kano kawai yake tunanin bari ba, ita kanta Afrikar gaba ɗaya ta fice masa a rai, baya tunanin akwai abin da zai sa ya ƙara biyowa ko da ta samanta ne.