REZA
Suna tsakiyar falon an zaunarta ana ta murje jikinta da kurkum da aka kwaɓa da farin ruwan kwai.
Rimo kuma na tsaye saman kanta tana yarfa mata wasu ƙananun kitso.
Agogonta na hannu ta kalla, ta saki gashin Reza da sauri tana dosar plasmar dake falon ta kunna.
“Yeeesssss! Yanzu My Kanari zai fara labarai, za ku ganshi, amma kar wacce ta yi gigin latsa min shi nawa ne Ni kaɗai, zan iya kashe mutum kansa i swear!”
Shewa suka saka kowa yana son ganin gayen da Rimo ta matowa, harda saka masa suna Kanari wai tsabar daɗin da muryarsa ke mata.
LABARIII DA ƊUMI-DUMINSAAA.
Babban Attajirin nan Alhaji Nawazuddeen Sheerif da ya daɗe yana tserewa ‘yan uwansa attajirai tasa ta burtso yau.
A gurin ɗaurin auren ɗan sa ne muka samu rahoto ango ya turmushe wani likita dake ikirarin Nawazuddeen ba mahaifinsa ba ne. Ya ba su shi ne, saboda matarsa ba za ta taɓa haihuwa ba.
Ya ƙara da cewar, tantiriyar tubabbiyar karuwan nan Ashana da aka taɓa yi a Legos, wacce ba a san inda take rayuwa a halin yanzu ba ita ce Uwarsa. Haka yarinyar da yake shirin aure, ƙanwarsa ce.
Tooo Allah shi kyauta.
Dama dai ance, daga kin gaskiya sai ɓata.
Soupy ta fara ankara da halin da Reza ke ciki, da gudu ta taho tana ƙoƙarin tare ta ganin za ta faɗo, sai dai ina kanta isa harta tsuntsuro ƙasan, idanuwanta a rufe ruf! Babu wani alamar numfashi tare da ita.
HAMOUDI.
“Kar ka yarda in ƙara kiranka ka ce mini yana meeting, ka shiga ka ce masa Yayansa Ishaq ke son magana da shi.”
“Ka yi haƙuri Sir, na faɗa maka banda hurumin shiga wurin nan, sun kusa fitowa ai nan da awa biyu.”
“A cikin awa biyun da kake magana zai iya rasa abu mai girman da ko da zai ƙarar da duk dukiyar da ya mallaka ba za ta iya siyo masa shi ba. Ka faɗa masa matarsa da ɗansa ke halin rai kwakwai mutu kwakwai.
“Sir zan iya rasa aikina kan katse su da zanyi…”
“Ka ci kwal Ubanka, na ce maka ka ci kwal ubanka kai da aikin. Ba ka ji na ce iyalinsa ke cikin matsala ba, kai kaga kafirin yaro da shegen taurin kai. Shi Nawazun ne ya ce maka ko abu ya danganci iyalinsa a jira shi sai ya fito?”
Kawu ya furta yana ta sintiri tsakiyar Asibitin.
Ɗif! Ya ji an katse wayar.
A fusace ya ɗaga wayar zai ƙara kira, shi fa in ba ji ya yi ya tada wa Nawazuddeen hankali yadda nasa ke a tashe ba, ba zai ji daɗi ba. Kiran daya shigo ne ya sashi kara wayar da sauri a kunne.
“Yaya me…”
“Ba sai ka tambaye Ni ba. Na kira ne in gaya maka bara gurbin kwan da ka ɓoye sama da shekaru talatin da huɗu (34) yau ya fashe, warinsa ya cika ko’ina ciki harda gidan Tvn AFA. Dan haka ka gaggauta aje komai ka taho ka rungumi kayanka, ba zan iya ɗaukar tashin hankali kalar naka a wannan shekarun nawa ba.”
“Ban gane ba yaya, meke faruwa ne, me ya samu su Fareedan.”
Sassanyar muryar Dattijon mai cike da kamala ta furta.
“Yo dama ya za ai ka gane ka riga ka toshe tunaninka da son zama ƙaruna, ƙana cuɗanya da yahudawa wai neman arziki. Ba magana ce da za ta faɗu a waya ba. Ka taho kawai.”
“Amma Yaya ga ka ga Husein ga Auwal mai zan zo na yi kan abin da na san bai fi ƙarfinku ba. Koma mai ya faru na sani ƙaddarar mu ce da ba za mu taɓa kauce mata ba. Har gwara ma ka ce mini babu su da ka dinga faɗa mini maganganun a dunƙule ina jin ba daɗi. Karka matsa mini sai na zo ba zan iya ba, ina cikin matsalar da ban san yadda zan maka bayaninta ba. Ƙoƙari suke su rufe Kamfanina na nan, su kuma ɗaure ni tsawon shekaru goma kan lefin da ni ban aikata ba. Idan ka tuna fashin da aka min na wasu takadduna to sune silar komai dake faruwa anan. Ban san wake son ganin bayana ta hanyar tozarci irin wannan ba. Ta ya ya zan iya barin wannan abin na taho domin iyalina da na san da babu raina dole kune za ku kula da komai. Ban san me zuwa na zai rage ko zai ƙara kan abin da aka riga aka tsara faruwarsa tun kafin wanzuwar mu ba. Koma menene idan har zai taɓa mutuncina tunda na ji kana ambatar gidan Television ayi ƙoƙarin dakatar da yaɗuwarsa, sai dai da za ka faɗa min yanzun ina ga zai fi min adalci.”
Numfashi Kawu ya sauke yana jin sassauci a zuciyarsa. Gashi dai a baki ya iya kiran ƙaddara amma idan ta zo masa bai iya tarbar ta ba. Da ya iya da yanzu abin da ke faruwa bai faru ba.
A hankali ya fara warware masa komai.
Salati kawai yake yi yana kiran sunayen Allah. Mamaki yake yi ga dukiyar har dukiyar amma kwanciyar hankalin da zai samu ya ci ta na neman gagararsa.
“Wannan Sharri ne, ka sanni sanin da ko mahaifanmu ba su yi mini ba. Ba zan taɓa aikata wannan abin ba. Ta ya ya ma Hamoud zai zama ba jini na ba, wane kalar ƙulli ne wannan?”
“Mu dai mun gasgata da shaidar sa hannunka da muka gani jikin takaddar, me za ka ce kan haka? Ka ji tsoron Allah ka tuna tarbiyyar iyayenmu ka faɗa mini gaskiya. Shin Hamoud ɗanka ne ko kuwa sayan shi kuka yi yadda likitan ya faɗi? Idan har kamin ƙarya na gano zan cire ka daga Family, sai dai ka sake wasu, wannan ne kawai hukuncin da zan iya maka, tunda ban haifeka ba, ba lalle ina da darajar da za ka iya faɗa mini sirrinka ba. Sai dai ka sani, duk yadda kake da mace ba ta kai ɗan uwanka ba. Za ka iya canja ta sau ɗari! Amma ni ba za ka iya zuƙe jinina dake cikin naka ba. “
“Hasbunallahu wa na’imal wakeel! Yaya Allah kar ya gwada mini abin da zan iya ɓoye maka. Makirci ne da idan ka tuna fashin da aka min na sirrika na da babu wanda ya sani sai Hamoud za ka ga ba abin mamaki ba ne dan an samu irin waccar shaidar cikin files ɗinmu. Sa hannu kuma akwai mutanen da aikinsu ke nan a duniya su kwafi sa hannun mutum. Ƙulli ne kawai aka yi dan a raba kan iyalina. Ko kuma tunda ka ce wai yarinyar da Hamoud ke shirin ƙara aura aka ce ƙanwarsa ce, ta yiwu abin ta ɓangarensa ne aka haɗa domin ganin bai aureta ba. Dr Igwe ya ba ni mamaki, bantaɓa zaton zai iya cin dunduniyata irin haka ba, ku nemo shi Yaya, shi kaɗai ma zai iya warware batun idan ya ji zai amshi hukunci.”
“Ina zan ganshi? Ya tafi ai. Amma wanene a rayuwarku haka da yake ƙoƙarin tozartaku irin wannan, anya baka taɓa cin zarafin wani ba Nawazu? Abin ya yi girman da ba zai yiwu abokan kasuwancinka su maka ba. Kamar kiriss fa ake jira nan da labarin ya fara watsuwa.”
“Ku dakatar da yaɗuwarsa, su kansu gidan Tvn sai na yi shari’a da su tunda suka yaɗa labarin da ba su ji gaskiyarsa daga gare ni ba. Wallahil azim kowane ya mini wannan abin ba zan taɓa kyale shi. Dole inyi ƙoƙarin kammala komai cikin satin sama in taho. DNA kawai za mu yi mu watsa result ɗin duniya su tabbatar kaidi ne aka ƙulla.”
“Shi ke nan kuwa. Ga abu mai sauƙi ban yi tunaninsa ba tun ɗazu. To ka yi ƙoƙari ka taho ko domin yaron, ka sani baƙar zuciya gare shi marar jin rarrashi. Ya kuma gama yadda da batun likitan tunda ya ga sa hannunka.”
“Ya suke yanzu?”
“Karka damu, ban kira ka ba sai da aka gama komai, dama shock din zancen ne ya zubarsu. Fareeda ce dai jininta ya hau sosai dole tana buƙatar hutu. To sai ka zo ɗin ke nan, bari na leƙa su.”
Ya furta yana kashe wayar.
Ta can ɓangarensa dafe kai ya yi yana son tuna wanene ya ma abu da zai dinga bibiyar rayuwar iyalinsa haka. Amma ya gaza tunawar, so yake ya san wacece yarinyar da Hamoud ɗin zai aura abin ya fito ta ɓangarenta. Dole ne ya yi ƙoƙarin barin komai ya taho idan har yana son gano
bakin zaren.
*
Da sauri ya ƙara sa ɗakin jin sautin kuka na tashi. “Ni ce mahaifiyarka, ka dawo hankalinka Hamoudi, babu yadda za ai na siyo ka wallahi sharri ne. Ba sai ina rantse maka ba, a jikinka ya kamata ka ji hakan.”
Ya ji furucinta tana tsaye tana ta jijjiga Hamoud dake ƙame yana hawaye.
Matarsa ya kalla Fainusa, ita ɗin ma hawayen take tana girgiza kai.
“Ya za ki barta ta zo gurinsa kin sani hutu take so?”
“Ita ta fito, na riƙeta ta kwace, tunda ta farfaɗo take kuka a kaita ta ga Hamoudin.”
Waigawa ya yi yana duban Hamoud ɗin.
“Kai ka yi haƙuri kabar batun nan haka, na yi magana da mahaifinka yana nan zuwa za ai gwajin DNA ka gani da idon…”
“Ba mahaifina ba ne!!!
Ya furta da ƙaraji da tunda aka fara batun sai yanzu bakinsa ya buɗe.
Hannuwansa ya sa ya ture hannayenta da ke jikinsa yana komawa baya.
“Karki ƙara cewa Ni ɗanki ne, ki maida ni ga mahaifiyata da baki ji tausayinta ba kika raba ni da ita a lokacin da tafi buƙata ta ko da ba ni da uban. Ban san yadda zan iya yafe muku wannan abin ba. Ƙanwata? Jinina kuka sa nake shirin aura? Me ya sa duk jariran da ke duniya ba su muku ba sai Ni? Karki ƙara taɓa ni ke ba muharramata ba ce, ko shayar da ni da kika yi ban yaf…”
Tau! Ta sa hannu ta ɗauke shi da marin da sai da ya yi taga-taga zai faɗi ya yi saurin dafe bango yana kallonta tamkar baƙin kumurci.
Hannunta ta kalla kafin kuma ta tura su duka cikin bakinta tana sakin gunjin kuka. Ta riga ta yi kuskuren da idan zai fahimta ma, yanzu kam an riga an wuce wurin.
“Ehen gashi kin ƙarasa nuna min baki haife ni ba. Mahaifiyata ba za ta mare ni ba saboda tana sona za ta fahimce ni ta kula da damuwata.
Ya furta da murmushi mai ciwo, yana yin baya kafin kuma ya juya a guje yana ficewa daga gurin.
Kawu nata kwala masa kira amma ina ya nausa. Da ido ya bi shi yana mamakin irin zuciyarsa da babu abin da ya bambanta da tashi, ko da kuwa basa kama a halittar jiki.
Durƙushewa ta yi a gurin tana dafe saitin zuciyarta, Kawu take nunawa da hannu ya riƙe shi kar wani abu ya same shi, a haka ta ida sanƙamewa wurin.
Direban dake zaune cikin motar Kawu yasa hannu ya fisgo tamkar shi ya kar zoman haka ya watsar shi waje. Ya shiga motar ya bata wuta yana figar ta da wani irin gudu da ya haddasa wata ƙaramar guguwa a gurin.
Cikin rashin hayyaci yake tuƙin, shi kansa ba zai ce ga yadda ake yake ta kaucewa titin ba. A haka ya fara fita wajen gari ya take motar da ƙarfi yana mata mazauni ƙasan wata bishiya cikin duhun maghribar da ya fara kunno kai.
Ɗora kansa ya yi saman sitiyarin a karo na farko da yake nadamar zuwansa duniya. Matar da ya gani a zaune saman Wheelchair wai ita ce mahaifiyarsa. Yarinyar da yake mafarkin mallakarta a matsayin mata wai ƙanwar sa ce cikin ummansa. Ke nan da ace abin nan bai bayyana ba da yanzu yana zaune da ƙanwarsa a matsayin haka. Shi kuwa ya za ai ya yafe musu?
Dunƙule hannuwansa ya yi ya kaima gilas ɗin gaban motar wani wawan naushi har sai da ya tsage. So yake ya yi duk wani abu da zai sa ya manta damuwarsa amma bai ji komai ba, sai hannunsa da yake jin wani irin zugi na mamaye su.
Lumshe idanuwansa ya yi yana jin wani sauti na dukan kunnuwansa. Sautin yaji na ƙara yawa, a sannu a hankali ya ji yana son leƙawa dan ganin me ke faruwa.
“CHEESY BAR”
Ya ga an rubuta da wasu kalar kwayaye da suka ƙara ƙawata rubutun.