Skip to content
Part 20 of 33 in the Series Asabe Reza by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

Da sauri ya buɗe motar ya fito yana dosar gurin. Tun daga nesa yake jin warin giya na bugansa amma haka yake takawa da ƙarfinsa, yana tuna kalaman wani gaye da ya taɓa gani. ‘Kai ma ka sha, na san damuwa gare ka.’

Idan har da gaske abin yana cire damuwa ya yadda zai siye ta duka gurin domin ya sha damuwarsa ta ya ye. Mahaifansa su tsaya a nasa, Reza ta zauna matsayin matarsa. A haka ya isa yana zama ɗaya daga cikin jajayen kujerun da ke gurin.

Yar takardar saman tebirin dake tsakiyar kujerun ya ɗauka yana duba list. Gaba ɗaya kansa kwance saboda bai san wacce zai zaɓa ba. ɗagowa ya yi yana kallon mutanen gurin da kowa ke harkar gabansa, mata ne gasu nan kusan tsirara haka suka cake suna ta tiƙar rawa. Hannuwa ya ji sun sauka wuyansa ta baya, a haka ta kewayo gabansa tana shafa shi. Baƙa ce siririya, ta sa wasu matsiyatan kaya da suka tona asirin baƙin da ɗuwawunta ke da shi tamkar na baƙin alade.

“Kamar yau ka taɓa zuwa, kawo na zaɓa maka wacce za ta dace da yanayinka.” Wani kallo ya wurga mata yana tunkuɗe hannayenta. Idanuwansa ta kalla, abin da ta hango cikinsu ya sata juyawa cikinta na kaɗawa ta bar masa gurin. Wani ya zo ya tsaya kansa da tambayar me yake so. Ta farkon ya nuna mutumin ya gyaɗa kai yana juyawa.

“Lisco idan ka haɗa ba ni na kai masa, wannan kalar da ni ya fi dacewa.” Baƙar budurwar ta furta tana kashe shi da murmushi. “Me ne lada na?” “Na mallaka maka daren yau.” “Ke Pensil, kan wannan me zubin ustazan kike cewa za ki ba ni abin da kika fi shekara baki ba wani ba.” “Ba za ka gane ba ne, ba ni kai dai.” “To gashi, sai ki taka a hankali karya watsaki cikin gayu.”

Karɓa ta yi ta juya, gefe ta yi sanin idon Lisco bai kanta ya sata tura hannu a bra dinta ta zaro wata yar takarda. Warwarewa ta yi ta juye farin garin cikin Tambulan din da aka cika rabinsa da giyar. Take ya ɓace ciki tamkar ba a zuba komai ba. Ƙarasawa ta yi ta aje masa, ta koma gefe, tana ɗora wayarta a kunne. “Na gama, inji alert…” “No, yanzu dai zai sha…” “Okay Madam, zanyi ƙoƙarin ganin ya sha.” Kalaman da ta furta ke nan ta kashe wayar. Tsura masa ido ta yi ganin ya ɗaga Tambulan ɗin zai kai bakinsa. “Kai kauce, kauce, kauce, gata nan za ta faɗooo.” Gayen ya taho a guje yana tuntuɓe da kujerar da Hamoud ke zaune, har sai da kofin glass din ya faɗi, giyar ta watse a ƙasa.

A zuciye ya ɗago yana kallonsa. “Stupid, ji yadda ka zubar min da abu. Me ne zai faɗon.” “Sama mana, kai baka san meke faruwa a sama ba?” Sai kuma ya yi shiru yana mutsittsika idanuwansa, kafin kuma ya tuntsure da dariya yana nuna shi. “Abokinaaaana Reza, ashe kaima kana ɗa niiiiii.” Ya furta yana zama kujerar dake gabansa. Sai kuma ya sunkuya ya dangwalo giyar data zube a ƙasa ya shainshina. “Kai fa wawane, ai ba kalar wannan ta da ce da kai ba, da kamin waya ai, amma tunda na zo bari na kawo maka kalar tamu.”

Ya furta yana miƙewa da tangaɗi, sai kuma ya juyo yana nuna masa yatsa. “Ka fa tare min wannan gajimaren dake shirin zubowa, bari na kawo.” Banza ya masa, yana kallon giyarsa dake ƙasa. Dawowa ya yi da Cock a hannunsa, ɗayan kuma giya. Aje cock ɗin ya yi gaban Hamoud shi kuma ya aje giyar gabansa. Cup ya ɗauka ya zuba giyar rabi, ya daga ya shanye, ya tura ma Hamoud gabansa. “Ka ga yadda na yi to kaima haka za ka yi da wadda ke gabanka.” “Banza, ba wannan nake so ba, irin naka za ka ba ni.” “Yawa kake, zuba ta gabanka rabi, sai ka ƙara da tawa, ka ji yadda zaka hango kanka a fuka-fukin tattabara kuna ratsa gajimare.”

Shiru ya masa ya yi yadda ya ce ɗin. Da ƙyar ya haɗiye wacce ya guntsa. Kafin kuma ya ɗaga cup ɗin ya kwankwaɗe tas! Ya ajiye yana lumshe ido jin kansa na tururi. “Ƙara min.” Ya furta yana ware idanuwansa. Ƙara masa gayen ya yi yana dariya. A haka suka shanye tas. “Reza, kaini na ga reza.” Ya furta yana jawo hannun gayen. Miƙewa suka yi a tare, faduwa suke ƙoƙarin yi a haka gayen ya yi ƙoƙarin tare Hamoud. “Ka taka a hankali yanzu fa ji zakai kamar kana tafiya saman ruwa.”

“Kai Ni na ga Reza.” “Kai mayen soyayya, ce maka akai na san hanyar Reza.” “A WATSE QUARTERS za ka kaimu, za ka ga gidan daga nan, da mota na zo fa.” “Uwata nake son gani ba mutawa ba, da na hau ka tuƙa mu zuwa gidan. Wawa! Taxi zai kaimu.” “Ka kaini na ce.” A haka suka mike titin neman Taxi, wannan ya zube wannan ya tada wannan.

Pensil dake gefe taja tsaki mai ƙarfi tana ɗora wayarta a kunne. REZA. Sassanyan ruwa Soupy ke ta shafa mata har zuwa lokacin da ta ja wani ƙaƙƙarfan numfashi ta buɗe idanuwanta tana sauke su ana Soupy da ke ta hawaye. “Yanzu ke nan Hamoud yaya na ne da kika ce Mama ta bari, ko kuwa ta haife shi ne bayan wancan?” Girgiza kai Soupy ke yi alamun ba ta sani ba. Juyawa ta yi tana kallon Mama Ashana da ta daɗe da ƙarasowa gurin, idanuwanta a bushe, babu alamar ɗigon hawaye, sai suyar zuci.

“Ina ma kina da ikon da za ki gaya mana gaskiyar komai, ina jin nadamar kasancewarki haka har zuwa rana irin ta yau da muka fi buƙatar maganarki a duk ranakun da suka shuɗe. Yaron nake tausayawa, ba mu san halin da zai shiga ba da wannan batun. Ina za mu ga  ƙawarki Zenuba ko ita za ta iya ba mu haske?” Cije bakinta ta yi ta juya kanta da ƙyar zuwa hagu, ta ƙara juya shi zuwa dama. Da hanzari Soupy ta ƙara so gabanta tana riƙo yatsunta. “Ban gane ba, ba ɗan ki ba ne?” Ƙara motsa kan ta yi tana cije leɓe. Sai dai har yanzu ba su gane me take nufi ba. “Tsaya, idan ɗanki ne ki juya kanki dama. Idan ba shi ba ne ki juya hagu.” Soupy ta furta tana ƙara matse yatsunta cikin hannunta.

“Hamoud  shi ne ɗan ki?” “Juya kan ta yi zuwa hagu.” Farin ciki ya faɗa ɗa a fuskarsu. “A’a, ta ya ya kika san ba ɗanki ba ne, alhali kina haihuwarsa kika bar shi?” Reza ta furta tana tsare ta da idanuwa. “Duk me sauƙi ne, ayi gwajin DNA tsakaninshi da uban mana.” Rimo ta furta tana ƙarasowa kusa da Reza. Shiru suka yi suna nazarin kalamanta, kafin kuma Reza ta ɗago tana dubansu. “Amma ba a Naija za a gabatar da hakan ba ko?” Kallo ta sukai alamun basu fahimta ba. “Yeah, saboda idan a Naija ne, idan kuma ya kasance abin sharrin abokan gaba ne. Wanda ya ƙulla wannan nufinku bai san da DNA ba? Ke nan ya shirya zuwansa, zai kuma iya siyan result ɗin a canja shi da na boge.”

Jijjiga kai suka yi gaba ɗaya suna nazarin tunaninta. “Amma ni ban yarda Hamoud ɗan uwanki ba ne. Idan kika kula da yadda abin har ya isa gurin ‘yan jarida. Idan da gaske ne likitan ya yi dan ya taimake shi, me zai sa ba zai sa me shi gida ba, sai a idon duniya…?” “You’re smart Sumoli…” Reza ta furta tana miƙewa zuwa gabanta. “…Tunanin da ya kamata mu yi ke nan tun farko ba mu tsaya muna hawaye ba. Tabbas har saƙo an turo min a wayata, ko da wannan ya ci ace na gane ƙulli ne.”

Ta furta tana share hawayenta da gaggawa. “Amma wanene maƙiyin Hamoudi da zai ƙulla masa wannan sharri me girma haka? kuma me ya sa aka danganta shi da ni?” “Fakriyya…” Suka ji sautin daga baƙin kofa. Juyawa suka yi gaba ɗaya suna kallonta. Tana duƙe kamar me ruku’u tana haki alamun ta sha gudu. Miƙewa ta yi ta ida ƙarasowa cikin falon.

“Ban gane ba Gisma, lafiya kike ta haki?” Reza ta furta, tana ƙara takunta zuwa gabanta. “Daga gidanta nake, na sa hannu zan kwankwasa mata ƙofar cikin na ji sautin muryarta da ƙarfi tana waya. Umarni take bayarwa a bi bayan Hamoud duk inda yabi a kawo mata shi. In ta kama ma a ba shi abin da zai gusar da hankalinsa ayi hakan. Ita kawai a kawo mata shi. Ta yi komai ne dominsa. Kamar kuma da Pencil da Bio take wayar na ji ta ambaci sunansu.”

“Pencil kuma? Ba tana Kenya ba?” “Ta dawo, na ganta shekaranjiya a Cheesy Bar.” Ta furta, tana karɓar ruwan da Rimo ta miƙo mata. “Kai amma Fakriyya anyi dabba, ba ance saki uku Hamoud ɗin ya mata ba. Me kuma take nema gurinsa, ya ma akai duk suka samu waɗannan abubuwan game da shi?” Sumoli ta furta da takaici. “Na ganta rannan, gaba ɗaya ta fita hayyacinta. Son sa take irin son da za ta iya mutuwa dominsa. Shi ya sa ta zare gaba ɗaya. Rimo ta furta.

“Wannan ba so ba ne…” Soupy ta  furta tana tashi daga gaban Mama Ashana. “…Wane irin so ne  za ka sheganta abin da kake so? Ka raba shi da kowa na sa. Ta san tana son shi tun farko me ya kaita haiƙewa ubansa?” “Jaraba mana, irin wacce ta ɗauka a jinin kakarta Kankana.” Rimo ta furta tana ɗaga kafaɗarta. “Ni ce bata son ganin na aure shi, ba ta san kuma ko uwarta Bitil ce ta yi fatalwa dan ta hana auren nan ba ta yi kaɗan wallahi.” Reza ta furta a fusace tana dosar ɗakinta. Katifarta ta ɗaga ta jawo wata yar pistol ta fito.

Abin da suka gani hannunta ya sa su dosarta gaba ɗaya suna riƙeta. “A’a Reza, idan tunani ya ɓata, hankali ke nemo  shi. Me za ki je yi gurinta da Bindiga? Kina so ta ci nasara ke nan? Kin kashe ta kin tafi Prison, kinga ke nan duk kun rasa.” “Soupy ki barni na fasa ƙoƙon kan Shegiya. Ita daƙiƙiyar ina ce da ba za tai abu da hankali ba? Ta san halin da Hamoud zai shiga kuwa? Wata irin zuciya gare shi da idan ransa ya ɓaci baya gane kalar tunanin da zai yi. Wallahi zai iya cin mutuncin iyayensa kan wannan batun.” “Yo ai abin da take so ke nan, ya rabu da kowa ya zama nata. Tana ganin idan ta haramta tsakaninku dole zai waiwaiyeta. Yanzu ki yi haƙuri, mu jira har zuwa lokacin da za a kawo mata Hamoud ɗin. Sai kawai mu fasa gidan. Muna tare dake ako wane irin hali Reza. Ba za mu taɓa bari kiyi yaƙin nan ke ɗaya ba.”

Rimo ta furta tana bubbuga bayanta. “Pencil! Gashi duk amintar dake tsakani na da Pencil aka haɗa baki da ita a cuci mijin da zan aura? Ban ga yadda zan ƙara yadda da amintakar bariki ba.” “Ba ta sani ba, ba na tunanin Fakriyyar za ta mata bayani. Da kuma bariki babu aminci, da ba ki tashi kinga Soupy da Mahaifiyarki ba. Ni kuma ina miki biyayya tun tashin mu.” Sumoli ta furta tana komawa baya. “I’m sorry guys, really sorry. Ban san me ya hau kaina ba.” Ta furta, tana zama gefe ganin kamar kalamanta ya taɓa su. Murmushi suka yi gaba ɗaya, suna ɗan shafa kanta, alamun ta share.

<< Asabe Reza 19Asabe Reza 21 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×