Skip to content
Part 24 of 33 in the Series Asabe Reza by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

REZA

Har Hammad da bai fi awa guda da shigowa gidan ba sai da ya gane rashin walwalar da take ciki.

A hankali ya baro gurin Soupy da yake ta roƙo ta yarda ta ba shi Mama Ashana ya ci gaba da kula ta ce a’a. Idan ya yi haka bai kyauta mata ba, tare take da Ashana tun lokacin da ake jin daɗin. Ya bari dai har Reza ta yi aure sai a duba lamarin.

Shi kam a gurinsa unguwar ce sam bata masa ba, uwarsa ba ta da wani abu da ya haɗa ta da watsattsu da za ta ci gaba da rayuwa cikinsu. Ita ma Soupy da za ta haƙura ta yi aure ya fiye mata. Duk da ta rantse masa ta bar karuwanci a tun lokacin da Reza ta fara wayo. Sai dai sanin gaibu ai sai Allah.

Da wannan tunanin ya zauna kusa da Reza inda ta dunƙule tana ta kunci.

“Bai kira ki ba ne Juliet?”

Hawayen da take ta ƙoƙarin riƙe wa suka zubo.

“Assha! Zai zo fa, kin sani mahaifiyarsa na asibiti, ta yiwu bai samu nutsuwar zama ba ne.”

“Tun ɗazu fa nake ta kiransa, har Text na masa amma bai koman da Reply ba. Ina jin kamar wani abu ya same shi?”

“A’a ki daina irin wannan tunanin. Babu komai fa, ba ni Number ni na Kira.”

Number ya saka ya kira har sau biyar ba a ɗaga ba, ana shida wanda yake tunanin shi ne na ƙarshe da zai gwada aka ɗaga.

“Wane irin banza ne da bai san ya kira mutum bai ɗaga ba a haƙura. Dallah kar a dame ni, banjin maganar ne.”

“Easy dai Romeo, Ni ne fa?”

“Ɗif!” Ya ji an kashe wayar a fuskarsa.

Da wani irin mamaki ya sauke wayar daga kunnensa yana kallon Reza.

A daidai nan kuma wayar ta ɗauki ƙara.

Karɓa ta yi tana miƙewa tsaye ganin Number Mamyn Hamoud da ta yi saving tun lokacin da ya haɗa su su gaisa.

“Hello.”

Ta furta a hankali.

Hawaye kawai take yi  tana gyaɗa kai tamkar tana gabanta.

“Eh na ji. In Sha Allah.”

Ta furta da shessheƙa tana sauke wayar daga kunnenta.

Soupy da ƙarasowarta gurin ke nan kawai ji ta yi an faɗa jikinta ana sakin gunjin kuka.

“Lafiya, me ya faru?”

Suka tambaya ita da Hammad. Mama Ashana ma data latso ɗan kekenta ta ƙara so gurin.

“Ki yi magana mana, wani abu ya same shi?”

Hammad ya furta yana janye ta daga jikin Soupy.

Kasa maganar ta yi, sai wayar ta miƙa ma Soupy.

Ta gane nufinta, dan haka ta karɓa ta buɗe
Auto Call Recorder ɗin. Gaba ɗaya suka kasa kunne jin yadda kalaman ke fita a ɗan kausashe.

“Quraisha ko? Idan har kinsan illar da ke cikin saɓawa iyaye, kuma kina son gamawa da naki iyayen lafiya, to ki fita daga rayuwar Hamoud. Ki barshi ya rayu da ni lafiya. Ban da ikon hanaki magana da shi ko na tsine miki kan hakan. Amma shi ina da ikon da zan ɗaga masa nono a duk ranar da ya yi magana da ke ba da yawu na ba. Dan haka ko kiran ki ya yi kina da damar da za ki katse. Idan har soyayyar da kike masa ta Allah ce. Kin ji ko? To ki barshi.”

Da haka ta datse kiran.

Kallon-kallo suke. Mama Ashana kawai juyawa ta yi ta bar musu wurin.

Soupy ta sauke ajiyar zuciya tana kallonta.

“Mamansa ta shiga tsakanin, ƙarshen komai ke nan yanzu?”

“Ba ita ta shiga ba, Fakriyya ta ɓata komai, ke nan ta ci nasara a kai na, kamar yadda uwarta ta ci kan mahaifiyata?”

Reza ta furta tana share hawayenta.

“Ba na tunanin Hamoud zai iya barin lamarin ya tafi haka. Zai gyara, komai nisan zamani tunda yana sonki.”

“Har yaushe? Abin da ba ta son ya yiwun, nake so ya faru a cikin ɗan lokacin nan. So nake ta ga aure na da Hamoudin cikin idanuwanta. Amma ya zanyi? Mahaifiya ce  a tsakani fa?”

“Idan Allah ya yi sai ya faru, babu wani abin halitta da ya isa ya hana ko wanene. Me zai dame ki? Ki zubawa sarautar Allah ido. Idan aurenki da shi rabo ne har gida zai zo ya same ki. Ni kam zanso inga wannan Fakriyyar taku?”

Kallo Hammad ɗin ta yi, wani abu ya shiga ranta. Da sauri ta juya ga Soupy.

“Ban da ke da Hamoud, wa ya san Hammad Yaya ne?”

“Babu.”

Soupy ta furta da rashin fahimta.

Ɓarin da Mama Ashana take ta kallo, taga bata nan. Jawo hannunsu ta yi zuwa ɗakinta tana faɗin.

“Ku zo kuji.”
********

Bayan Kwana Goma.

Hamoud.

Kwanakin yake jinjinawa cikin ransa, bai san yadda ya shafe su ba. Sai dai yana jin ya yi sune tamkar saman garwashi.

Abinci, sai ya ji baƙar yunwa yake iya kai ‘yan lomomi bakinsa. Gidansu kuwa a tun ranar bai ƙara zuwa ba. Sai Mamy da ta zo masa tana faɗan ya koma bakin aikinsa, ya sanya mata kuka ta tashi ta yi tafiyarta.

Ransa ke ƙara ɓaci idan ya tuna duk kwanakin nan da suka shafe Reza bata kira shi ba. Ta gama nuna masa ba yada wani muhimmanci a rayuwarta, In ba haka ba ai ta san ko kiranta ya gani zai ji daɗi ko da ba su yi magana.

Sumarsa da ta tura yake shafawa yana kwance tsakiyar gadon nasa. Tamkar wani dake zaune gidan yari haka yake rayuwa. Ya zama duk  wani bususu. A kallo guda za ka gane DAFIN SO ke hajijiya da dukkan ruhinsa, gubarsa na illata duk wani kwanjinsa na Ɗa Namiji.

Wayarsa dake ƙara ta katse masa tunaninsa. Ya ja tsaki me ƙarfi yana tunanin ko yaransa ne na Company.

Wayar ya jawo, ganin Abbansa ne ya sashi runtse ido yana tuna yaushe rabon suyi waya.

Da sauri ya kai wayar kunnensa.

“Hamoudi, kabar kira na ke nan ko. To ka faɗawa Mamynka gobe zan shigo, na kirata ban same ta ba. Yau za mu ta so ne, shi ya sa ba lalle ta same ni ba anjima.”

Da ƙarfi ya fashe masa da kukan da ya daɗe yana cinsa arai ya kasa yi. Kuka yake bilhaqqi dake fita da duk wani baƙin ciki da ya kwasa cikin kwana goman nan.

Alhaji ta can ɓangarensa da yake tsaye cikin Airport, wayarsa ya ɗago ya duba yana tunanin ko ba Hamoud ya kira ba.

Ganin shi ne ya sashi zama yana riƙe goshinsa.

“Kuka kake Hamoud? Me ya faru? Ko wani abu ya samu Mamyn? Idan wancan batun ne ba ance mini komai ya warware ba?”

“Mamy ce Abba, ta raba ni da yarinyar ita da haɗin bakin Kawu.”

“Ikon Allah! Me ya yi zafi to? Yanzu kan yarinyar kake kukan ke nan, ina ƙarfin zuciyar taka da jarumtar?”

“Abba So duk bai san wannan ba, ina jin zan iya mutuwa idan ban ganta yau ba. Kwana goma fa, dan Allah kama Mamy magana ta barni na ganta…

A hankali ya kwashe komai ya faɗa wa Abban, yana jin yadda yake salati. Sai dai ya ɓoye masa sune sukai fashi, ya dai ce masa ya saki Fakriyya saboda ta ci amanarsa.”

“Yanzu ita yarinyar karuwa ce, wacce ka sakar ma haka?”

“Wallahi ta tuba, sahihin tuba.”

“To, zanyi magana da Mamy, idan na dawo sai a yi batun auren.”

“Me ka ce Abba?”

Ya furta yana miƙewa tsaye saman gadon.

“Na ce zanwa Mamyn magana ka je kaga yarinyar yau. Idan na dawo na yi bincike game da ita, sai ayi auren.”

Wani ihu ya saki a kunnen Abban. Da sauri ya kashe wayar yana mamakin abin da ya hau kan tilon ɗan nasa.

Shi ma dire wayar ya yi saman gadon. Ya sauko da sauri yana wucewa Toilet, tun kan Mamyn ta yarda ya fara tunanin kintsa kansa.

A ƙasan ransa yake jin tsoron faɗan da Mamyn za ta masa. Sai dai ya sani koma mene shi dai gwara da ya gaya wa Abban, faɗan nata na ɗan lokaci ne.

Yana fitowa yaga Mamyn ta kira shi har sau uku. Cikinsa ya bada wani sauti ƙululu, kan ya gwada kiranta har wani ya kiran ya ƙara shigowa.

Ya laɗeefu yaja yana kai wayar kunnensa.

“Ka kyauta…”

Ya yi shiru.

“Aka ce mutuwa za kai?”

Nan ma ya yi shiru.

“To ka zo ka ci abinci, sai ka wuce kaga Quraishar.”

“I love You Mamyyyyy”

Ya furta da karfi zai kashe mata dodon kunne.

Kashe wayar ta yi.

Shi ma ya aje ya shirya da gaggawa yana barin gidan.
*

5:30

A ƙofar gate ɗin ya tsaya, yana shirin latsa jeras ya buɗe. Alhajin Hammad ya fito, bayansa kuma Soupy ce riƙe da hularsa.

“Hajiyata ki ba Ni hular nan, zan dawo gobe fa. Satin sama dai a ɗaura auren nan mu huta.”

Zantukan da suka zarce cikin kunnuwansa ke nan. Ya ƙame yana ƙarewa  Soupy kallo da ta sha gayu har da su Eye shadow tana ta gwalli.

Ganin Hamoud ya sa su jin kunya.

Alhaji ya ɗan gyara zaman babbar rigarsa.

“Ah surukina, ƙarasa mana.”

Ya furta yana buɗa masa hanya.

Shigewa ya yi, suka bi bayansa da kallo.

“Alhajina ba na so ka tafi ne, zan maka kuka fa.”

Soupy ta furta tana narke fuskarta da  Foundation ta taimaka gurin rufe tsufanta.

“Ikon Allah…!”

Ya furta yana shafa gemunsa.

“Ni duk kin ruɗa ni fa, kinsa ma na manta da kunyar da naji na ganin yaron nan.”

Murmushi ta yi tana wulkila masa ido.

Ya ƙara hangame baki yawa gonar audugu.

“In ba so kike gayun nan naki ya sa ni kwana ƙofar gidan nan ba ki ba Ni hular nan.”

“Kai Alhajina, ka bar min ita mana in dinga gani ina tunawa da kai, haka ba hular ma ka fi mini kyau.”

Ta furta tana jan gyalenta fuskarta.

“Haka aka yi? To to ai shi ke nan. Bari na wuce.”

Ya furta yana shafa salsalelen kansa, ba dan masoyiyarsa Soupy ta furta yana kyau ba hula ba, da babu abin da zai hana shi yarda ba ba’a aka masa ba. Shi ina kansa yaga fasali ba tare da hula ba, keyarsa zungureriya yawa shantu?

Sai da ta raka shi har jikin motar, ta buɗe masa ya shiga, ta rankwafa saitinsa.

“Goben fa ka zo da wuri.”

“Ai dole na.”

Ya furta yana bawa motar wuta. Kasancewar baya zuwa da Direbansa gudun munafurci.

Dawowa ta yi fuskarta fara’a fal, ta tsaya tana kallon Hamoud da ya zauna saman fararen kujerun da ke gurin.

Ƙarasawa ta yi suka gaisa. Ta ɗauke ƙaton gwangwanin chocolate ɗin da Alhaji ya kawo mata. Ta ƙarasa cikin gidan domin kiran Reza.

Da shigar Soupy da fitowarta duk bai fi minti biyu ba.

Ta tsaya kawai daga nesa idanuwanta na kawo ruwa.

Tashi ya yi ya ƙarasa ya gare ta.

A hankali ya riƙo ya hannuwanta ya jawo ta zuwa gurin kujerun.

“Wannan kallon…Ni ne fa.”

“Hmm!…”

Ta sauke numfashi.

“Mamaki nake, Mamy fa…”

“Da yardar ta.”

“Ta yaya?”

Kwashe komai ya yi ya gaya mata.

Shiru suka yi gaba ɗaya tana ƙara jinjina lamarin.

“Duk ka rame.”

“Ba dole ba an raba ni da zuciyata, ke kuwa wani kyalli ma kike yi. Uhmm ki koyi salo gurin Soupy.”

Ya furta yana ƙunshe dariya.

“Kai dan Allah, na fa fika damuwa. Hammad ne kawai ke ɗeben kewa.”

“Please shekararta nawa ne?”

Murmushi ta yi.

“Ka fa sa mata ido, ba ta fi 43 zuwa 45.”

Ya kwashe da dariya harda dukan table.

“Shi ne ake kawo mata chocolate?”

“Wai me ruwanka ne?”

Ta furta tana ƙunshe dariyarta.

“Ke kwalliyar ne? Kinga jambakin ne? Kamar Angelina Jolie ta shafa mata.”

Ta tsintsire da dariya.

“Hamoud anya kai ne? Dama haka kake?”

“Kawai sun sani nishaɗi ne, ga farin cikin ganinki, ga yadda na tadda su…”

“Ke kinga har mota ta buɗe masa fa, in ba idona ya mini ƙarya ba kamar fa har kiss ta busa masa irin SRK da Kajol ɗin nan.”

“Na shiga uku, dan Allah ka barni. Laɓewa ka yi kana kallonsu?”

Ta furta, dariya harda kwalla.

“Hmmmm share… Ina Hammad ne?”

“Ya fita da Fa…”

Ta yi shiru tana ɗan shafa laɓɓanta.

“Da wa?”

Ya furta yana tsare ta da idanuwa.

“Share kawai. To komai dai ya ƙare ke nan?”

“A’a…”

Ya furta yana sauke idanuwansa saman zoben hannunta.

“Ina zai ƙare ina ganinki da wannan abin a hannu.”

“Kamar ya?”

“Ina nufin ki cire zan baki nawa ki saka.”

“Ka sani abu ne da ba zai taɓa yiwuwa ba.”

Ta furta yanayin fuskarta na canjawa zuwa ɓacin rai.

“Amma kinsan ba za ki shiga gidana da kayan wani gardi hannunki ba.”

“Yaushe zoben nan ya shiga cikin sharuɗan aurenka? Wai me ya sa zai tsaya ma a rai? Me ruwanka da shi ne? Ka kawo na kan mana zan ƙi karɓa ne?”

“Ba na san ganinshi ne a hannun matar da zan aura, alhali wani banza ne ya ba ta.”

“Ba fa banza ba ne, meke damunka  ne? Dama zuwa kayi ka gaya mini maganganu?”

“Kamar kina son goge duk wata siqa da na bawa zancenki, kamar kina nunan mai zoben nan mutum ne ɗan uwanki kike raina mini hankali, idan Aljani ne ki cire mana, me zai rage miki?”

“Hamoud… Zargina ka ke?”

Ta furta muryarta na rawa.

“To ya kike so na yi? Na ce miki idan na ganshi ji nake kamar ana yanka zuciyata. Na tsani ganinsa, idan kin na ce sai kin rayu da shi za kuwa ki dawwama hannunki da safa.”

“Tashi ka tafi.”

“Da kyau…”

Ya furta yana miƙewa, ficewar ya yi har yana doka gate ɗin tamkar shi ya masa.

Dafe kanta ta yi tana mamakin kalar rikici na Hamoud.

<< Asabe Reza 23Asabe Reza 25 >>

1 thought on “Asabe Reza 24”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×