Skip to content
Part 25 of 33 in the Series Asabe Reza by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

Fakriyya

5:30 SM TM

“Ban san yadda zan maka ka gane bana ƙaunar sake wata alaƙa da  ɗa Namiji ba.”

“Ban san yadda zan miki ki gane soyayyar ki ta zama tsuntsun Kanari, zuciyata ta zama hatsin da tsuntsun ke caccaka a kodayaushe.”

A karo na farko da ta masa murmushi tun kwanaki taran da ya shafe yana bibiyarta.

“Washhhh!” Ya furta yana dafe saitin zuciyarsa.

“Da ki kai murmushin nan sai na ji kamar ana yayyafin diamond a zuciyata.”

“Hammad ka ke ko?”

“Kwarai My Princess.”

Ya furta yana tsare ta idanuwansa dake kaɗa yan hanjinta a duk lokacin da ta ganshi. Tabbas guy ɗin ya yi, ba dan soyayyar wani da ta birkita rayuwarta ba, da tuni ta ba da kai.

“Ka bar Ni dan Allah, ka barni na ji da damuwata.”

“Kai!!!!”

Ya furta yana dafe ƙirjinsa tamkar mace.

“Kinga waccar?”

Ya nuna mata wata Trailer da ta yanko titin da suke tsaye.

“To ki tura Ni gabanta ta bi ta kaina, shi ne kawai abin da zai raba ni da ke.”

“Ya Rabb!”

Ta furta tana dafe kanta.

“Me zan maka ne?”

“Marry me.”

Ya furta yana buɗa hannuwansa, ya sunkuya gabanta akan gwiwowinsa.

Baya ta yi da sauri tana masa kallo na mamaki. Wai wannan haɗaɗɗen guy ɗin ne ke durƙushe gabanta. A sannu ta sauke idanuwanta saman laɓɓansa masu tudu. Ta haɗiye yawu da ƙyar wani tunani na ɗar suwa a ranta.

“Na ji tashi Ni dai Please.”

“Sai kin yarda za ki aure Ni zan bar wurin nan, ki tausaya mini mana.”

Ya furta yana langaɓe kansa

“Na ji zan aure ka, amma da sharaɗi.”

Da sauri ya miƙe, a karo na farko ya riƙo hannuwanta.

Runtse ido ta yi jin wani yanayi ya ratsa ta.

“Za ka sake ni bayan  sati guda na komawa tsohon mijina?”

“Kin kashe ni”

Ya furta yana zare hannuwansa.

“Please!!”

Ta furta tana ɗora hannunta saitin zuciyarsa.

Da ido yabi hannun da kallo, kafin kuma ya sauke su cikin idanuwanta da suka fara cika da kwalla.

Murmushi ya mata.

“Zan yi tunani.”

A haka suka tako ya kawo ta har cikin unguwarsu.

Idanuwanta suka sauka kan motar Hamoud da ke girke ƙofar su Reza.

Gabanta ya faɗi, farin cikin da ta samu na tsawon kwanaki goman nan ya fara gushewa.

A fusace ta warce hannunta daga na Hammad, ta miƙe da gudu zuwa gidansu.

So take ta kira Bio, ta ji yadda akai yau Hamoud ya zo gidansu Reza, alhalin ya tabbatar mata mahaifiyarsa ta raba su.
********

ALH NAWAZUDDEEN!!!

Wani farin ciki yake ji sa’ilin da ya shaƙi daddadar iskar ƙasar tasa ta haihuwa, da rabonsa da ita, wata biyu ke nan.

Godiya yake ƙarayi ga ubangiji da ya daidaita masa dukkan lamuransa ta inda bai taɓa zata ba.

A haka ya taka zuwa cikin gidansa, yana jin yadda ƙamshin Humrar ta ta ke ƙara kusanto Hancinsa.

“Mamynmu.”

Ya furta yana tura ƙofar falon.

Idanuwansa suka sauka kanta, tana zaune tsakiyar falon, ta tasa wasu kwawawan yara gaba tana kallo.

“Tooo, ina muka samu yara haka.”

Ya furta yana ƙarasa shigowa ciki, ya aje jakarsa  rataye saman kujerar, ya ƙarasa gabanta ganin ba ta so ta tare shi ba yadda ta saba.”

“Na ka ne.”

Ta furta da wani sauti da ya saka shi tsayawa nan inda yake.

Kafin kuma ya ɗan yi murmushi tuna kalar zolayarta.

“Haba kika kawo min irin waɗannan yanzu ai ajiye tsufa na zanyi inta miki rawa da li…”

Kalmomin suka datse cikin bakinsa sakamakon ɗagowa da ta yi ta sauke idanuwanta cikin nasa. Tunda yake da ita, sunga tashin hankali kala-kala, bai taɓa ganin tsanar sa cikin idanuwanta irin wacce yake gani yanzu.

“Sai ka yi rawar…ko ban kawo ba… Karuwarka ta kawo maka…”

Ta furta, tana jin ɗacin kalaman na caccakar zuciyarta, sai yanzu ta ji saukar hawayen da ta daɗe tana fatar zubarsu ko za ta ji sauƙin raɗaɗin zuciyarta.

Bai fahimci komai cikin kalamanta ba, sai ‘karuwarka.’

Dan haka ya yi baya ya zauna kujerar gefensa, a hankali ya zare hular kansa jin ta masa wani nauyi. Mamakin abin da ya sauka kan Fareeda yake, har take binsa da wannan mummunan kalmar. A rana mai girma irin ta yau da yake farin cikin ganinsu.

Idanuwansa suka zarce kan yaran da basu gaza shekara ba. Da ƙarfi da kuma wata irin gigita ya miƙa tsaye yana ƙarasawa gabansu.

“Innalillahi Wa inna illahhir raji’un.”

Ya furta yana ɗora hannuwansa dake rawa saman fuskarsa.

Kama ce suke yi da wani hotansa da yake yaro, Tunda yake a duniya, bai taɓa ganin kalar kamar ba, hatta ɗan wani ɗigon baƙi dake haɓarsa, suma yaran suna da su. Ɗaya mace ɗaya Namiji. Tabbas ya gama yadda jininsa ne, sai dai ta ina ya same su?

‘Baƙin ganin’

Ya furta a ƙasan ransa.

“Ka ga abin da ya sa na karɓe su ke nan. Ko za ka nemi mata, ban taɓa zaton za ka nemi kalar wannan karuwan ba…Wata mummunan karuwa fa wai Pencil ta kawo su, take ikirarin naka ne, ta kuma yi tafiyar ta ta barni da su. Me za ka ji a jikin irin waɗannan yaran? Yaran da ka haife su?”

Ta furta, tana dafe saitin zuciyarta da take jin kamar za ta faso, idanuwanta na saman fuskarka da ke riƙiɗewa da tsantsar rashin gaskiya.

“Ba nawa ba ne wal…”

“Karka rantse, nike da ikon rantsewa, wallahi na ka ne!”

Ta furta tana jefa masa wata ‘yar farar takarda.

“Gashi nan da yaran aka haɗo, ba zan iya dubawa ba dan kamanninsu da kai sun gama faɗa min komai.”

Da sauri ya ɗauka yana warwareta.

Hey Nawaz!

Na san lokacin da saƙon zai riskeka za ka shiga ruɗu.

Babu wani mamaki idan za ka iya tuna ranar da wannan ɗiyar cikin naka ta haiƙe maka. Lol.

Karka damu fa, ba haka na so ba, na yi ne da wata niyyar daban ba wai wannan ba, to kuma sai na samu sauƙin lamarin ta hanyar dakon abin da ke jininka a cikina.

Gasu nan har yara biyu na kawo maka. Haamin da Haajir, na san ko su kaɗai sun isa ka mallaka min rabin dukiyarka idan ina buƙata.

Sai dai ba wannan nake so ba.

Hamoud! Idan ba ka san shi na aura ba to ka sani yau. Ya kuma sake Ni a sanadinka, domin kawai na yi mu’amala da kai.

Barin Hamoud daga rayuwata daidai yake da barin farin ciki daga taka rayuwar.

Wallahi zan iya komai dominsa, idan na ce komai ina nufin komai ɗin.

Ka hana shi auren da yake shirin yi, ka umarce shi ya jira ni na yi aure na fito mu maida auren mu.

Hakan shi ne zai sa na yafe maka dukkan abin da ka mini, shi ne zai sa ka karasa rayuwarka cikin salama.

Barin haka daidai yake da watsa komai media, idan na ce komai ina nufin abin da baka taɓa tsammani ba.

ka kula da yaronmu, shi ma fitar gashi guda daga jikinsu, wani tashin hankalin ne gare ka.

FAKRIYYA S. TUMBI

In maka gwari-gwari.

Fakriyya BITIL…

“Bitil!!!”

Ya furta a sarari yana jin yadda iskar falon ta tsaya masa cak! A.C dake girke falon yana aiki ya fara buso masa wani irin zafi. Ƙafafuwan suka gagara ɗaukar nauyinsa.

Duhu-duhu yake gani haka ya lalubi jikin kujera ya zauna, yana fidda wani wahalallen numfashi.

Kallonsa take duk ya zame mata wani abin tsoro.

“An tabbatar maka naka ne ke nan.”

“Ban sani ba Fareeda…Ina yaran nan da suka zo gidan nan fashi? Ban taɓa gaya miki ba ne, a daren sai da  ɗaya daga cikinsu ta haiƙe mini, shi ne dalilin samun yaran nan. Wallahi ba a san raina ba ne.”

“Ko?”

Ta furta tana murmushin da bai da alaƙa da yanayin da suke.

Haɓar zaninta ta jawo tana goge hawayen fuskarta, tana jin ta gama ganin tashin hankalin da zai ƙara kwantar da ita a tun ranar da aka sheganta Hamoud.

“Na gani ba a san ranka ba ne, shi ya sa har abin ya yiwu aka samu ribar yara da ita yarinyar da dattijo kamarka me ƙarfin da za ka hana faruwar lamarin? Ashe ana ma maza dole ko da basa so. Ashe abin zai yiwu ko da baku muradi?”

Sarai ya gane kalaman da ta jefa masa a ƙudundune. Sai dai ya zai yi ya fahimtarta? Ya zai yi ya ce mata har wata hoda yarinyar ta busa masa, ta yiwu ita ta gusar da hankalinsa har komai ya faru yadda take so.

“A tsawon shekarun da muka kwashe tare kin san halina, kin san abin da zan iya da wanda ba zan iya ba. Ki yarda da ni, wallahi ba san raina ba ne, haka karki manta Ni fa….”

“Namiji ne kai, hakane…”

Ta furta tana haɗiye da wani yawu me ɗaci da ya tarar mata a baki.

Da ya san yadda kalmar ‘Ba San Raina Ba Ne’ ke mata suya a ƙirji, da ya daɗe da barinta. Ita ta isa ta yi yaƙi da abin da Allah ya ƙadarta, abin da ya riga ya faru?

“Sai yanzu na gane, dukkan abubuwan da ke faruwa Ni ne sila.

Karanta kiji za ki gasgata.

<< Asabe Reza 24Asabe Reza 26 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×