REZA
Ƙara rungume filon ta yi a ƙirjinta tana lumshe ido, da wayarta saƙale a kunnenta.
“Ka huce ke nan?”
“A’a, kawai muryarki zan ji, yau ko gani na ba ki yi.”
Ya furta ta can ɓangarensa.
“Uhmm, sai na zo ai.”
“Ki na wasa ne, gidan zan bari ai. Oh, kin tsare ni da hira ma na manta abin da zan faɗa miki. Yau Abba zai dawo fa.”
Haka kawai ta ji gabanta ya faɗi, har sai da ta ture filon gefe tana miƙewa zaune.
“Sai na ji tsoro, kamar ba zai yarda da ni ba, mun yi rashin kunya sosai fa.”
Runtse idanuwansa ya yi yana jin ɗacin abin. Sun ma mahaifinsa fitsara, kuma ita yake burin aura. To wai ya zai yi? Haka nan ya tsinci kansa cikin soyayyarta dumu-dumu.
“Karki damu zai fahimta fa, ya sani ba Ni na ɗora ma kai na ba. Haka kuma ba lefinku ba ne, Kawu ne, shi ne silar komai. Da bai tura ku ba ina duk za a yi hakan?”
“Hakane, Allah ya kyauta, amma mamaki nake, da gaske Alhaji Auwal jinin mahaifinku ne?”
“Sosai ma, uba suka haɗa tare, zamanin ne ya yi lalacewar da ɗa ma sai ya cutar da mahaifinsa.”
“To Allah kar ya jarabce mu da kalar wannan. Bari na je, tun ɗazu Soupy ke kira na.”
“Ok, Ni ma shiryawa zanyi na je gida, na san ya ƙara so yanzu.”
Aje wayar ta yi, ta tsaya shiru tana tunanin rayuwar. Tana tuna ranar da ta ɗago haɓar surukinta a hannunta tana buga masa warning cikin matsiyatan suttura. Rayuwar duka abin tsoro ce, ba ta taɓa zaton zai iya zama mai rana a gareta irin haka ba, lalle ne idan ba ka bi duniyar a sannu ba, to za ka yi zuwan Zomo ne kawai cikinta.
Fitowa ta yi daga ɗakin, ba ta ankara ba kawai ta ji an ruƙunƙume ta.
“Oh, oh, Baby na yi kewarku fa, har yau dai kina nan da halinki, ki shige ɗaki ki hana kowa shiga har Aunty Soupy.”
Zare jikinta ta yi a hankali tana harararta.
“Pencil zan zage ki fa, har yanzu ba za ki bar using da wannan Cream ɗin mai warin garlic ba?”
“Share mana, ba na iya canja shi, to ya rayuwar ne? Ɗazu na rabu da Ree na kai mata sako gidan wannan Attajirin Nawaz Sheerif. Kai Baby, Fakriyya shegiya CE ta ƙarshe.”
Ware idanuwanta ta yi sosai tana dubanta ƙirjinta na bugawa. Soupy ma dake gefe da sauri ta ta so zuwa gare su.
“Yah, na ga kuna ta wani…”
“Pencil me kika kai gidan?”
Reza ta katseta da firgici saman fuskarta.
“Wasu twins wallahi, na sa ne da ta haifa masa.”
“Innalillahi Wa inna illahhir raji’un!”
Soupy ta furta tana watsa hannu.
“Yaushe Fakriyya ta haihu?”
Suka haɗa ba ki da ƙaraji ita da Reza.
Wani kallo Pencil ta musu, ta yi baya tana zama saman kujerar bayanta.
“Ban gane ba, na ga duk kun wani ta da hankalinku kamar yaranku. Ni ma tambayar da na mata ke nan, ta ce za ta faɗa mini.”
“Kuma kika karba kika je gidan bayin Allah kika kai musu Pencil?”
“A’A biyana fa aka yi, ya kike yawa ne? Wait… Duk kin ma ruɗa ni, me suke zame miki?”
Kallonta ta yi, tabbas Pencil ba ta san duk abubuwan da ke faruwa ba.
Dan haka ta matsa ta zauna gefenta. Sama-sama ta hau bata labarin komai.
“God! Ke nan a kwanciyar da ta yi da shi ta samu ciki?”
“Nooo, kai, a’a, wannan sharri ne kawai, ya za ai Fakriyya ta yi ciki ba mu sani ba?”
Kinga Twins din.
Pencil ta furta, tana zaro wayarta da ta ɗauki hotanta da yaran.
Gabanta ya buga ya ƙara bugawa har sai da ta dafe bango tana ganin ainihin kamar da ke tsakanin yaran da fuskar da ba za ta taɓa mantawa ba ta Nawaz.
Tabbas ko a yanayin girman yaran da ba su gaza shekara ba, ta gama yarda na Nawaz ne, sai dai ta ya ya?
“Ba abin damuwa ba ne, Fakriyyar za mu nemo ta faɗi komai.”
“A’a, ba za ta taba faɗi ba, Linda, tsohuwar kilakin ita ce za ta warware komai.”
Reza ta furta.
“Shi ke nan kuwa, bari na kawo muku ita, shi kaɗai ne abin da zan iya na wanke lefi na Baby, wallahi da na san boyfriend ɗinki ne tun farko ban karɓar aiki.”
“Share kawai, je ki yi aikinki, kira Rimo ku ɗauko ta tare, ki ce ta taho da filayarta. Ni kuma bari na kira Hamoud, yanzu zai je gidansu, ba na so ya ji komai ta ɓangaren su, ba zai iya ɗauka ba…”
“A’a wait, bari na ji inda Fakriyyar take.”
Reza ta furta, tana furzar da wani zazzafan huci.
Pencil ta miƙe tana rungume hannuwanta.
Wayarta ta ɗauko ta latso number Hammad.
“Oh, Juliet ki na ɓatan yanayi.”
Ta gane nufinsa, dan haka ta gyaɗa kai.
“Ka yi koma menene ganin ba ta dawo gida ba, akwai aikin da za mu yi.”
Ta furta, tana kashe wayar.
“Shi ke nan kuwa, kira Hamoud ɗin da sauri ya zo nan kafin su kawo Lindar.”
Soupy ta furta.
Pencil kuma ta juya tana ficewa bayan ta ɗauko wata kakkaurar igiya a kitchen.
*
“Ni wallahi duk kin ta da mini hankali, sai na ɗauka wani abu ya same ki ai.”
Ya furta yana ɗaga labulan Falon.
Turus! Ya yi ganin tsohuwar surikarsa zaune saman wata kujera an ɗaure ta gabaɗaya jikin kujerar, hatta bakinta an ɗaure shi da tsumma.
Waigawa ya yi yana kallon Reza da ke bayansa.
“Wannan ta’addancin fa?”
“Mu je kai dai ka ji a bakin Soupy, ba zan iya faɗa ma komai ba.”
Ta furta, muryarta na rawa.
Ƙarasawa ya yi cikin falon, ya tsaya kusa da Soupy Yana kallonta da idon tambaya.
“Da ma Fakriyya ce ta yi…”
Ta yi shiru tana tauna kalaman.
“Ta yi me?…”
Ya furta da tsawa-tsawa jin gabansa na faɗuwa.
“Ta aikawa mahaifinka Twins ɗin da ta haifa masa dalilin wannan ranar.”
Shiru ya yi tamkar bai ji ba. Da gaske kalmomin da shirun suka shiga cikin kunnuwansa suna tsinka wayoyin da ke ba da sauti cikin kwakwalwarsa.
Reza ta kula da yanayinsa dan haka ta yi sauri ta isa tana tare shi cikin jikinta a haka suka zube.
Idanuwansa take kallo da ke ƙame, a gigici tasa kunnenta saitin zuciyarsa, tana jin bugun zuciyar da ke fita da wani irin ƙarfi na mamaki. Ɗagowa ta yi tana girgiza shi, sai dai ko kwayar idonsa ba ta juya ba.
Wani irin tsoron ta ji ta ɗago tana kallon Soupy.
“Ba suma ya yi ba… Menene wannan?”
Ta furta tana fashewa da wani kuka mai sauti.
” Zo ki gani wallahi ba ya motsi, ina tsoro, irin ciwon Mama ko?”.
“Kai, a’a, ke ki nutsu, shiɗewa ya yi, dinga tofa masa addu’a cikin kunnuwansa. Kai hasbunallahu Wa na’imal wakeel, wannan wace irin rayuwace, ke dan ubanki me ke tsakaninku da waɗannan bayin Allah?”
Soupy ta furta tana takawa gaban Linda, ta ɗauke ta da wani mari, kafin ta dawo hayyacinta ta ƙara ɗauketa da wani marin. Hannu ta miƙa Rimo ta saka mata Filayar, Pencil ta kalla, ta matso ta buɗe bakin Linda da ƙarfi. Filayar ta saka ciki, ta finciko haƙorinta na gaba da wani irin ƙarfi, jini ya yi tsartsuwa yana fallatsa fuskar Soupy. Linda ta fasa wani gigitaccen ƙara da ya yi sanadin dawo da Hamoud hayyacinsa, tana jin ɗumin fitsari na ratsa cinyoyinta, haka ta duƙar da kai a sume, bakinta na dilalar yawun jini.
A hankali take furta masa innalillahi…Cikin kunnuwansa, tun bai ƙarɓa, har ya fara maimaitawa, ya ɗora kansa saman wuyanta yana ajiyar zuciyaa, tana jin yadda zafafan hawayensa ke sauka tsakiyar bayanta.
“Yanzu Fakriyya ƙanne ta kawo mini, ban kwanta da ita ba, wallahi ban kyauta da ita ba.”
“Na sani, ka yi hakuri, ka fawwala Allah, duk abin da ke faruwa da ku bai kai kwatar ƙaddarar wasu ba, ka gode Allah da abin bai zarce haka ba, da kana da yara da ita, Ni kaina ban san ya zan iya ci gaba da rayuwa ba.”
Ta furta tana bubbuga bayansa
“Muna cikin duhu, ban san ranar da haske zai bayyana rayuwar mu, an gama ɓata duk wani future na mu, wallahi ba na tunanin za mu ƙara wanzuwa cikin farin ciki, har biyu fa Quraisha? Ko a kallon yaran da zanyi zuciyata za ta iya bugawa, haka ta mahaifiyata? Ina zan sa kaina rayuwa ta dawo mini tamkar shekaru uku baya, da nake cikin farin cikin da ban taɓa tunanin zan rasa shi ba.”
“Karka ɓata imaninka, duk abin da kaga ya faru da bawa wallahi mai wuce wa ne? Ina waɗanda iyayensu suka rasu ba ki ɗaya? Shin ka ga farin ciki ya wuce a rayuwarsu? Ina uban da ya haihu da ‘yar cikinsa? Shin ba ka ganinsa yana ci gaba da dariya? Ina Ni da ban taɓa ganin mahaifina ba? Shin ba ka gani na a farin ciki? To haka halittarmu take, haka kuma ƙwaƙwalenmu ke aje abubuwa. A yau wani a gabanka zai kashe mahaifinka, a gobe kuma shi zai saka ka dariya. To, kowane yanayi akwai bigiren da yake, babu wata halitta dake dawwama da yanayi guda. Hatta gurgu da kake gani yana da abin da ke saka shi dariya, haka macen da ke ɗauke da cancer nono, haka Almajiri, haka makaho. Kai hatta macen da ke naƙuda, a bayan ta haife za ka ga dariyarta. A Hakan za ta ƙara komawa wani cikin, har ta manta da waccar damuwar. To, kamar haka ne naka labarin zai gushe, ya zama tamkar ba ai ba. Yaran da kake tunanin su za su zame maka tamkar na cikinka da ka haifa. Ni ku bar mini su, wallahi summa tallahi, ba zan taɓa furta ba Ni na haifa maka su ba. Zan yi koma menene ganin labarin bai isa ga kunnuwan jama’a ba, za a rufe labarin ya zama Ni ce na haifa ma su. Ba wai na mahaifinka ba ne. Idan ban kare girman mahaifinka ba wa zai kare? Shin wane halacci zan muku da zan goge lefin da na aikata gare ku idan ba wannan ba?”
Matse ta ya yi a jikinsa yana jin kashi saba’in na damuwarsa na gushewa. Yarinya ce ƙarama take ankarar shi abin da ko kusa tunaninsa bai hango ba, shi ko da mai zai sakawa Reza ban da ya amince da batunta, ta amince za ta maida ‘ya’yan halittar da ta fi tsana a duka rayuwarta na ta, wannan wane irin halicci ne?
Sai dai zuwa yau yana jin ba haka kawai ba ne, yana jin akwai dalili mai ƙarfi tsakaninsa da Fakriyya. Ba wai dan tana son shi ba ne take haka, ba ya tunanin an halicci soyayyar da ke watsa rayuwar mai yin ta. Idan ma akwai son, to akwai wani abu mai girman dake daƙushe ƙarfinta.
Dan haka ya miƙe da duk wani ƙarfi da ya sauran masa na Ɗa Namiji, yana ƙarasawa gaban Linda.
Durƙushewa ya yi yana haɗe hannuwansa guri guda alamar roƙo, ruwan hawayen da ke sauka saman kuncinsa sun cika bakinsa da wani kakkauran yawu, a haka yake girgiza hannuwansa ya gaza maganar.
Linda da ke ɗigar ruwan sanyin da Rimo ta watsa masa, ta ɗago a hankali tana kallonsa da idanuwanta da suka koma jajir dan azaba.
Soupy ta share kwallar idonta ta ƙara so gabanta.
“Ki faɗa masa gaskiyar abin da ke tsakaninku, ba mu yarda domin soyayyar Fakriyya gare shi ba kuke haka.”
Kuka take a hankali tana nadamar zuwan wannan ranar, bakinta dake kumbure ta buɗe da ƙyar tana sauke idanuwanta kan Mama Ashana da ke can gefe.
“Ina nadamar da ya kasance sanadin duk wani abu da muka miki ne ya kawo mu wannan halin, ki yafe mana…”
Ta furta a wahale tana sauke idanuwanta kan Hamoud da ke durƙushe gabanta.
“Mahaifinka shi ne ya kashe Bitil mahaifiyar Ree ta sanad…”
“Ƙum! Ji kake bakinta ya haɗu da wata ƙaramar taɓaryar ƙarfe da Reza ta saito ta sauke mata a baki.”
Kafin kuma ta yi wata sufa tana cika hannuwanta da gashin Linda. Ta fincika da ƙarfi tamkar wacce ifritai ke jikinta haka take zare ido.
“Ki ka sake kika ce Fakriyya ƙanwar Hamoud ce wallahi summa tallahi sai na yanka ki da wannan wuƙar. Ba kunce mahaifin Fakriyya ya kashe Bitil ba?”
Ta furta tana finciko wata ƙaramar wuƙa da ke ƙugun Pencil, har sai da ta yanketa ta yi baya tana furta ‘Auchh’.
Ƙarar da Linda ke yi ne yasa Soupy matsawa da sauri tana zare hannun Reza dake gashinta.
“A’a barta karki ƙara bugunta, wallahi Linda kinji na rantse ko wacce ƙarya kika mana daidai yake da fitar haƙorinki guda. Menene alaƙar Nawaz da Bitil da ita Ree?”
Ta furta tana ɗaga mata filayar hannunta.
Linda ta ɗago da murmushin wahala tana duban Soupy.
“Idan na so ina iya shan guba na mutu a tun lokacin da Pencil ta zo ɗaukata, yadda ma ba za ku taɓa sanin komai ba, Fakriyya kuma kun sani ko za ku yankata gunduwa-gunduwa ta fiku taurin kai saboda jinin Bitil ce, na shirya faɗa muku rufaffen sirrin, sai dai ina roƙon ku da ku yafe ma Ree, Mai lefi Ni ce da na faɗa mata silar mutuwar uwarta, kowane ɗa kuma da ya haifu zai so ya ɗau fansar mutuwar nasa.”
Ta furta tana sauke idanuwanta kan Hamoud da lissafinsa ya dade da kwacewa.
“Kai kana tare da mahaifinka, ba ka san ainihin kalarsa ba, tabbas Nawaz shi ya kashe Bitil, a kan ido na ya ba ta gubar da ta yi sanadiyyar mutuwarta, shekaru goma sha ɗaya da suka wuce…”
Alhaji Saleh Tumbi shi ne mahaifin Fakriyya, na sani kina tuna ranar da kika fara ganinsa da Bitil, ina laɓe a lokacin da kike faɗa wa ASHANA…
“What!!!! Saleh Tumbi dai da na yiwa satar Agogon da sanadinsa Ashana ta haɗu da Haroun?”
Soupy furta da ƙarfi tana sauke hannuwanta wuyan Linda.