Skip to content
Part 27 of 33 in the Series Asabe Reza by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

LINDA

“Ki na haukane? Kin sani ba zan taɓa yarda da wannan ruɗaɗɗan zancen ba. Alhaji Saleh da yake yawo da condom kike cewa ya ma Bitil ciki? Ina ce ko mu lokacin doka ce fita babu Condom ko Shan Pills? Me S.Tumbi Zai ji jikin Bitil, Ina ce ko lokacin takai shekara arba’in muka wayi gari tana da ciki, kuma wani daban kuka ce ai? Ba ma wannan ba? Ko kin manta Saleh Tumbi ya fara karbar budurcina? Kinga ke nan duk daɗewarki gidan Kankana na fiki sanin shi. Ƙarya ne ya yarda ya yi ciki da wata kilakin karuwa, ki nemawa Fakriyya wani uban, amma ba shi ba, dan kinsan ya mutu kike ƙaryar da shi halan? Tsaya ma… Ba wannan zancen banzan muke son ji ba, ki faɗa mana, yaushe Fakriyya ta yi ciki ta haihu? Wai Ni Soupy? Ina ma Mama Ashana tana da bakin magana yau.”

Haka ta jero kalmomin tana ƙara shaƙe wuyan Linda, ganin tana kakari ya sa Rimo zare ta daga hannunta.

“Easy mana Aunty Soupy… A bita a hankali ta faɗi gaskiya, idan muka rasata wa gari ya waya?. Pencil miƙo ruwa.”

Pencil da ke gefe tana ɗaure yankar wuƙarta, ta juya zuwa kitchen ta kawo ruwa.

Rimo ta ɗago kanta ta tuttula mata. Sai da tasha sosai, ta buɗe idanuwanta tana sauke su kan Soupy da ke ta huci ta haɗa uban zufa.

“Shi ma Alhaji Saleh Tumbin ba mutuwa ya yi ba ta kan, kan shi. Ni ce na yi poisoning ɗin shi ta hanyar babban yaronsa, saboda yana so ya karɓe Fakriyya a bayan ya ƙi ta, haka shi ya sa a kashe Bitil. Sannan ki na ta maganar wani condom, halan kin manta yana fashewa? Ba ma haka ba, bai zama dole sunyi amfani da shi ba tunda ba su suka sassaƙa kansu ba, bari ki ji, ko Ni ce zanyi harka da Millionaire mutum kamar Saleh Tumbi, babu wani abu da zan yi dan kare kaina, saboda zan so na haɗa jini da shi. To kamar haka ne Bitil ta yi amfani da shi. Ta kuma samu riba, tunda gashi ta bar muku abin da ya gagare ku…”

Ta dakata tana sauke numfashi, idanuwanta a kansu ganin yadda suka nutsu. Soupy ta zauna saman kujerar bayanta, ta ɗora hannuwanta duka biyu a kumatunta, tana kallon kumburarren bakin Linda.

“Yawwa gwara ku saurareni har na iso da ku inda kuke muradin sanin, sai dai ku sani, a wannan shekarun nawa da ba na hango yiwuwar sake maimaita ko da kwatar su ne, ba na tunanin zan muku ƙarya. Zan faɗi iyakar gaskiyata ko da hakan na nufin haɗiyar zuciya ga ɗaya daga cikinku.”

“Soupy, na san kina tuna daren Lahadin da muka fasa gidan Alhaji Saleh Tumbi, wanda har kika karya masa hannu? Har aka kama mu? Ban san mai Ashana ta ma Officer ba muka yi kwana guda a bayan kanta ya ba da belinmu, da haka zancen ya mutu, mutuwar da bai ƙara tashi ba. To kina tunanin Attajirin mutum kamar S.Tumbi zai yarda? Ki na tunanin ya yafe mana…?”

Ta furta tana sakin wani murmushi mai ciwo.

“To da wannan damar Bitil ta samu dama kansa. Yana cikin ƙudurinsa na watsa Ahalin Kankana Bitil ta je masa da batun Ashana, wanda a lokacin kin sani Kankana ta daɗe da rasuwa, Ashana ita ce ke mulkin gidan. Wannan abin shi ya ƙara wutar kiyayyar Bitil ga Ashana. Idan ba ki sani ba ki sani, Bitil ba ta taɓa son Ashana ba, ta rantse, ta ƙara rantsewa ba za ta barta ta yi aure ba ita bata yi ba. Sai dai ita ma ta mutu cikin karuwanci, ke har Bitil ta rasu, tana fatan ƙasar kabari taƙi karbar gangar jikin Ashana, tsabar girman zunuban da take burin ta aikata…

To, a lokacin da muka samu labarin Ashana za ta yi aure ne, hankalinmu ya tashi, ga shi babu wadataccen kuɗin da za a iya ɓata lamarin. Wannan dalilin ne ya sata zuwa gurin S.Tumbi, inda suka haɗu a Higgah Restaurant. Na san kin gansu ai a ranar.

Ta gaya masa buƙatarta na ya sa a kashe Ashana ko kuma a ɓatar da ita, shi kuma ya ce a’a, yana da matsafinsa dake masa aiki, zai kai sunan Mijin da Ashanar za ta aura, a ɓata koma menene, a nesanta mijin da ita yadda zai ji ya tsani ganinta, a kuma ruguza rayuwarta yadda ba za ta ƙara moruwa ba. A haka suka rabu ya ɗau kuɗi mai yawa ya bata. In da suka ƙulla daga ranar har ya dinga tarawa da ita, ƙarshe kuma ta samu cikin da ya ɓata alaƙarsu, a cewarsa ta yi girman da ya kamata ace ba ta haihuwa, kawai makirci ne za ta masa.

Ni ɗin nan Bitil ta saka na binciko komai game da Haroun, ni ce kuma na tafi can unguwarsu a ranar da ta tare, ni ce na samu Almajiri na ba shi Jug na damammiyar furar da aka dama da ruwan tsafi, ya kai gidan Haroun ya ce daga makwafcin sa ne…”

Mama Ashana dake zaune saman kujerarta ta latsa maddanninta da karfi keken ya motsa yana isowa gefen Linda, Hamoud dake duke ya buɗe mata hanya, haka keken nata ya ci karo da ciniyoyin Linda har sai da ta cije leɓe dan zafi.

A cikin idanuwanta da kwalla ta fara taruwa kake hango girman tashin hankalin da take ciki. Ina ma tana da bakin magana?

“Ki yi haƙuri…”

Linda ta furta, duk da kwayar idanuwanta a soye suke babu alamar russuna.

“To, wannan shi ne mafarin ɓata rayuwar Ashana, Alal haƙiƙa, ni kaina ba son raina wasu abubuwan suka faru gareta ba.

Kin sani Soupy, shekarar Ashana ɗaya da aure Bitil ta haifi Fakriyya. In da kuka dage ku san ubanta, muka ce muku wani ne.

Mun ɓoye ne saboda shi Alhajin ya bukaci haka, asalima gargaɗinmu yake mu kashe yarinyar muka ƙi, anan Bitil ta masa alƙawarin ba ta ƙara kusantar shi da zancen, haka za ta manta Fakriyya jininsa ce, sai dai shi ma dole ya raba dukiyarsa kashi biyar ya bawa Fakriyya ɗaya, tunda ba tada gadonsa.

Ya yi na’am da hakan, amma ba lokacin ba, ya ce sai yarinyar ta cika shekaru goma sha ɗaya (11yrs) ta dawo, zai ba ta.

A haka suka rabu da wannan yarjejeniyar.

Bayan shuɗewar shekarun.
Bitil ta komawa Alhaji da wannan batun, in da ta yi kuskuren tafiya da Fakriyya. Ya ganta, a take ya ce sai ta ba shi yarinyar. Ita kuma taƙi, karshe ya tabbatar mata dodon tsafinsa ke son jinin Fakriyya. Abin da ba mu sani ba, ashe duk wannan shaharar dukiyar ta shi, rabinta ta tsafi ce. S Tumbi ba ƙaramin riƙaƙƙen matsafi ba ne. Ance mahaifiyarsa ma shi ya kaita aka zuƙe jininta.”

Ta furta tana sauke idanuwanta kan Soupy, a kallo ɗaya za ka tabbatar ba ƙaramin tsurewa ta yi ba.

“A cikin shekarar suka dinga tafka rikici tsakaninsa da Bitil, a cewarsa ya riga ya sai da Jinin Fakriyya, kawai ba sa ita za ta yi. Kuna tuna ranar da ƙatti suka shigo gidanmu suna ta bincike? REZA ku kuna yara sannan, amma Soupy ke kin sani ai wanda kika na ce a basu Fakriyyar, alhalin ita kuma tana wani ƙauye cikin gidan wani malami da tsafi bai isa ya gano shi ba. To yaran Alhajin ne.

A daren wata Alhamis Bitil ta umarce Ni da na kaita gidan gonar Alhaji, amma na tsaida motar daga can ba ta son ya san tare muke.

Haka aka yi, a nesa da gurin na tsaya, a gabana motoci biyu suka wuce, Ta Alhaji S.Tumbi, da kuma ta Mahaifinka Alhaji Nawazuddeen Sheerif. Wanda yake Babban Amini ga S. Tumbi, ai ka sani?”

Ta furta tana sauke idanuwanta kan Hamoud da ya ɗago a razane yana dubanta.

“Eh ina tuna shi…Yana zuwa gidanmu lokacin na kammala secondry, amma wallahi Abba ba matsafi ba ne, ba na tunanin ya sani ma…”

Ya furta bakinsa na rawa.

” Ni ma ai ban ce maka matsafin ba ne, duk da ana cewa abokin ɓarawo, ɓarawo ne, koma dai menene can tsakaninku, za ka iya tambayar mahaifinka game da shi…”

“Haka kawai na ji jikina bai ba ni ba, dan haka na sauko daga motar cikin sanɗa na taka zuwa cikin gidan gonar. A haka har na isa bayan gajerar tagar wani ɗaki. Anan kuma idanuwa suka hango mini Bitil zaune da mahaifinka. Ban san me suka tattauna ba, amma dai na ga lokacin da ya fita ya dawo ɗauke da gorar ruwa. Ya tsiyaya ya miƙawa Bitil da ke ta kukan da ban san dalilinsa.

Da shan ruwan da faɗuwarta bai wuce daƙiƙa biyar ba. Nan ta zube tana riƙe cikinta tana nuna mahaifinka. Anan Ni ma razana ta sa na yi motsin da suka jiyo sauti nan. Nan na ga mahaifinka da ke ƙoƙarin ƙarasawa kusa da Bitil ya waigo saitin tagar da nake. Da na ga ya nufo gurin ne na ɓoye
da sauri bayan wata duhuwa dake gefe.

Na fi ƙarfin mintuna goma sha biyar a laɓe gurin kafin na bar jin motsi. Haka na ƙara takawa zuwa jikin tagar na leƙa, abin da na gani ne ya sa Ni fita hayyacina, ban san inda kaina yake ba, har sai gabannin asuba. Anan na farka na ganni jikin tagar inda na sume…”

Ta furta, hawayen dake gangarowa daga kurmin idonta sun cika bakinta, ta gagara furta ƙarashen, sai jan numfashi da take da ƙarfi tamkar mai cutar athma.

Soupy ma duƙar da kanta ta yi tana tuna yadda suka samu gawar Bitil, mutuwa ce ta wulaƙanci wadda ba ta fatanta da maƙiyinta.

An yanke duk wani sassan ɗiya mace dake jikinta, kama daga mamanta biyu, haka gabanta duk an saka wuƙa an ƙwaƙule. Tabbas sun daɗe suna jimamin yanayin, sai dai LEFIN WA?

“Shin wa ce halitta ce za ta ga mutuwar mahaifiyarta a wannan halin ta kasa ɗaukar fansa? Ta ya ya ma ba zance muku Nawaz shi ya kashe Bitil ba, mutuwa ma fi muni, menene lefin Fakriyya dan ta aikata mustahil wurin ganin bayan wanda ya yi hakan…?”

“Nooooo, a’a wallahi. Abba ba zai taɓa haka ba, ina gaya miki kinyi kuskuren gani, baki gani daidai ba…”

Hamoud ya furta da maɗaukakin sauti, yana riƙe kansa dake ƙoƙarin rabewa biyu. Tashin hankali ne yake hango shi muraran, irin wanda bai taɓa sanin akwai kalarshi ba.

Murmushi ta yi mai ciwo tana dubansa, tasa hannuwanta da Pencil da daɗe da kwancewa, ta share hawayen fuskarta.

“To, wannan dalilin ne bayan wata biyu da mutuwar Bitil, na shiga na fita, na haɗa baki da yaron Alhaji aka sa masa guba a ruwa shi ma ya sha ya mutu. Saboda ya ƙi barin zancen Fakriyya, haka shi ne yasa Nawaz ya kashe Bitil, na san kuma shi ne yasa a yanke mamanta biyu, duk ban sani ba ko shi ne ma ya yanke. Koma dai menene, ya cancanci ya mutu da irin hanyar da ta mutu.”

“Ka san me ya sa ban kashe mahaifinka ba?”

Ba ta jira amsar shi ba ta ɗora, sanin ba ya da bakin magana.

“Saboda Fakriyya nake so ta kashe shi, ita nake so ta rama da duk irin abin da take so.

Ka ga dalilin da yasa ta haɗa baki da Auwal da ke muku soyayyar ƙarya, ta shiga cikin gidanku, domin kawai ta kwanta da Nawaz, ta yi Video ta watsa shi duniya. Sai dai dake tana da Sa’a, sai gashi ta samu ciki da shi a wannan kwanciyar da ta yi. Wannan kaɗai ya isa ya goge damuwarta ko?”

“Soupy, kina tuna ranar da na ce muku Fakriyya ta samu wata kwangila za ta Ghana? Ba ta dawo ba sai bayan watanni goma? To laulayin da ta fara ne ya sa muka shirya tafiyar. Domin kawai karku gane sirrin da muke ta binnewa.”

Ta furta, tana sauke idanuwanta kan Soupy, kafin ta juyo tana duban Hamoud.

“Ko ka san kafin aje ga mahaifinka kai muka fara zuwar ma? Ni ce na karɓo ma Fakriyya kwallin kwarjini, domin kawai ka so ta, ka kuma aureta yadda za ta ji daɗin ruguza familynku. Allah da ikon sa kuma a bayan dawowarka ta fara sonka da gaske, wannan shi ne kuskuren Fakriyya, shi ne kuma abin da ya ɓata duka shirinta ya mayarta mai rauni. Wallahi da na san za ta so ka, da na daɗe da kashe ka a tun ranar da ta fara haɗa ido da kai…”

Ta furta tana sauke kallonta kan hannun Soupy ganin tana juya filayarta, alamun ta iya bakinta.

Shiru suka yi na kusan mintuna goma, kowa yana juya lamarin cikin ransa.

Reza ce ta fara kauda shirun, ta hanyar miƙewa tana ƙarasawa gaban Linda.

“Me Zan miki ne?”

Ta furta tana ɗago haɓarta.

“Ke a cikin mugayen ban taɓa jin kalarki ba, kin ɓata rayuwar yarinyar da ya kamata ki riƙe amana, kin kuma yi kisan kai. Ƙara jaddada mana kike kin kashe wani?”

“Ki kashe ni kawai, amma ki sani, duk wani abu da kike ganin na yi, Fakriyya za ta yi finsa, asalima duk plan ɗin nata ne, sai dai ina roƙarku, da idan ma hukuncin za ku yi, to banda ita, Ni za a hukunta tunda Ni ce silar gaya mata komai, Ni kuma na dasa mata ƙiyayyar Killer Nawazuddeen…”

“Tau!!!” Ta ɗauke ta da mari, tasa hannu tana matse bakinta.

“Kar ki sake kiran sunan surukina da wannan ƙazamin bakin naki. Kin sani zan iya kashe ki, dama kin ragen nauyi tunda ke haddi ya hau kanki.”

“Suruki?” Ta furta tana fashewa da dariyar dake tahowa da hawaye.

“Kamar ba ki san saboda kar ya zama surukinki ta aika masa da yaran sa ba? Saboda Hamoud ya barki ya aure ta ita, bayan ta fito daga gidan yaron da suke soyayya. Ko kin san barin zancenta daidai yake da watsa Video dinta da Nawaz duniya?”

“A ina Bidiyon yake?”

Reza ta furta tana cafko gashinta taja da ƙarfi.

Cije bakinta ta yi tana jin azaba, amma dan bala’i a haka ta yi magana.

“Yana inda wannan ɗan tsugunnan naku bai isa ya sani faɗi ba, ko da kuwa za ku yi gunduwa-gunduwa da sassan jikina.

Hamoud, ka bawa mahaifinka shawara ya cika umarnin Fakriyya kawai.”

Reza cika kan ta yi ta komo can gefe tana dafe kanta, ta sani tunda ta furta ba za ta faɗa ba, to kuwa magana ta ƙare.

A hankali ta sauke numfashi tana kallon su Pencil.

“Rimo, ina wayar tsohuwar kilakin nan take?”

“Gata nan wurin Pencil.”

“Yawwa, ku yi ta kilarta har sai ta yarda ta turawa Fakriyya saƙon gaggawa. Cewar ta tashi zuwa Abuja da Dadironta, ba za ta dawo ba sai nan da 2weeks.”

“Nan za mu ci gaba da ajiyeta cikin wancan store ɗin, abinci kuma sau ɗaya a yini, har muga yadda rayuwa za ta yi damu.”

“Soupy, idan za ta ɓata lokaci ki kwashe haƙoranta talatin, ki bar mata abin da za ta mulmula gora.”

Ta furta, tana miƙewa ta ƙarasa kusa da Hamoud, ɗago shi ta yi ganin baya iya wani kwakkwaran motsi. Ta ja shi zuwa wajen gidansu.

Rimo, Pencil, Madam Soupy, suka yi kan Linda dan cika aikinsu.

<< Asabe Reza 26Asabe Reza 28 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×