Skip to content
Part 29 of 33 in the Series Asabe Reza by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

FAKRIYYA

9:30PM

Kitchen ɗin take birkitawa tana buɗe duk wata loka da wani lungu, tana haɗa duk wane plates da cups da suka shiga tsakaninta da abin da take neman a bango, suna ba da wani sauti mai kama da rugugin aradu kasancewarsu na tangaran.

Ba ta haƙura da lalata komai da take yi ba, har sai da ta gano yar ƙaramar kwalbar can saman kantocin bayan ta taka kujera. Saukowa ta yi da kwalbar rike a hannunta tana kallon gayen da ke tsaye yana ta haki tamkar wanda ya kasa tsere da Kura.

Poison da yaga an rubuta a jikin kwalbar me kama da ta fiya-fiya ya sashi matsowa da sauri yana ƙoƙarin warcewa. Sai dai, tsawar da ta daka masa a gigice tana warto wuƙar da ke gefenta tana nuna masa ya sa shi dakatawa yana kallonta cikin rashin abin yi.

“Bio, na rantse da Allah idan ba ka  ce mini ƙarya kake yi ba zan sha wannan abin. Kuma ka tabbatar mutuwata tana wuyanka…”

Wani yawu ya haɗiya da ƙyar yana nadamar abin da ya kawo shi gareta da wannan labarin. Da ya sani yake yi irin wacce ba ta da rana. Tabbas da ya sani da Nawaz Sharif ya sallame shi ba tare da an ɗaure shi ba kai tsaye ya ma bar garin. Amma da yake gulma na cinsa, yana burin kawo rahoto ga Ogarsa sai ya kasa daurewa. Shi kam bai san haka ta damu da lamarin mutanen ba da har za ta iya kashe kanta dominsu. A hankali ya sauke kallonsa kan hannunta da ke ɗigar jini wanda duk sanadin zancen ne ya sata dukan madubi hannun ya fashe. Tabbas tunda aka zo nan gwara ya faɗan, ala basshi ya yi saurin kiran ‘Yan sanda ya musu kwatancen inda za su tarda gawarta. Wani yawun ya sake haɗiya muƙut! Yana kallon kalar kyawunta da yake tunanin gushewarsa nan da wasu mintunan masu zuwa. Tabbas za ayi gagarumar mutuwa a Barikin A Watse daga Kano har Lagos. Fakriyya ‘Yar Bitil Jikar Aunty Kankana ta yi mutuwar Shahada A Dalilin Ɗa Namiji. Yo shahada mana, mutuwa A Kan SO ai shahada ce a hadisan ‘Yan Zaria…

“Kai nake sauraro!!!…”

Ta furta da ƙara ji tana ƙoƙarin buɗe kwalbar.

Baya ya fara yi har sai da ya kusa isa ga faffaɗar ƙofar kitchen ɗin tukunna ya dakata.

“Madam, kin sani a harka irin wannan ba zan taɓa miki ƙarya ba. Abin da na ji shi na gaya miki. Tabbas na suma sakamakon bugun tsiyar da ya mini, wanda ya hana ni Jin abin da suka tattaunar, sai dai ki yarda a kunnena bayan Hajiyar ta watsa mini ruwa na farfado aka kira Alhajin. A kunnena kuma yake ta godiya ga Allah da aka ɗaura auren Hamoud da Rezar cikin kwanciyar hankali. Ki yi hakuri…” Ya furta yana ƙarasa ficewa.

Ɗaga kwalbar ta yi gaba ɗaya ta kai bakinta tana ƙoƙarin tuttulawa idanuwanta a rufe suna fidda wasu zafafan hawaye. Wani ƙaƙƙarfan abu ta ji ya dake ta, ya hana ruwan da ke cikin kwalbar sauka bakinta. Ruwan ya watsu a gefe da gefen laɓɓanta, gwalbar ta suɓuce daga hannunta ta faɗi kasa da ƙarfi tana watsewa a dandanyar tayil ɗin. Buɗe idanuwanta ta yi suka sauka kan jakar da aka jefo mata, kafin kuma ta dago su sauka kanta tana takowa gare ta cikin matsiyatan shigarta.

“Ba ki da hankali!! Fakriyya guba za ki sha!!!?”. Ta furta tana ƙarasawa ta jawo ta gaba ɗaya jikinta. Numfashi ta sauke mai ƙarfi tana jin zafin zuciyarta na raguwa, a hankali ta ƙara rungume matashiyar budurwar tana sakin wani rikitaccen kuka da ke fitowa da gaba ɗaya damuwarta.

“Lulu…!! Ki barni na mutu!!!”.

“Shiiiit!” Ta furta tana bubbuga bayanta da ƙarfi. Shirun ta yi tana kukan, ba ta hana ta ba, sai da ta yi mai isarta na fiye da minti talatin. Tukunna ta jawo hannunta zuwa cikin ɗakin. A gefen gadon ta zaunarta, ita kuma ta miƙe tsaye hannunta bisa ƙugunta tana ƙare mata kallo.

“Linda ta kira ni shekaran jiya ta faɗa mini dukkan abin da ke faruwa da kuma abin da take so ni nayin.. Wannan dalilin ya sa yau na baro Jos na taho miki domin kawai cika aikin. Ree, kin sani tun ba yau ba nake miki soyayyar da babu wani ɗa namiji da zai miki irinta, amma ki ka ƙi ni saboda kawai ni irin jinsinki ce. Menene shi namijin  zai motsa miki da Ni ba zan iya ba? Yanzu dai a bar wannan batun, na gama magana da bokana kan batunki, zai miki komai da komai da kike so kan Reza da shi gayen. Ya ce In gaya miki idan ma ridda kike so ya yi ga addininsa shi zai iya sa shin ya yi. Dan haka ki bar damuwa. Yanzu gashin Reza kawai na zo ki ba ni a kai masa, zai yi koma menene dan ganin ya salwantar da ita idan har aka samu gashin. Amma fa ki sani idan har komai ya yiwu za ki ba Ni wannan. Ta furta tana sauke hannunta saman ƙirjinta.

Duke hannun ta yi tana jin damuwarta na raguwa.

“Yar Akuya, na rantse da Allah wutarki daban take.”

“Idan ban tuba ba?” Ta furta tana kashe ta da murmushi.

“Na ji daɗi Lulu, kai banda mai sona a duka duniya sama da Linda, kin san Allah ni nama manta da ke. Na manta kina taɓa harka fa.”

“Ai dole ki manta kin samu maza.”

“Abin naki da wuya, ban san yadda zan iya shiga gidan Reza ba yanzu ba. In dama Linda tana nan ne…”

“Haba ba wuya fa, kawai ki kula da motsin mutanen gidan sai ki fasa. Karki ƙara kuka kinji, bari na tafi kin san ba na iya mintuna talatin babu mace jikina, gobe ki tabbata an samu gashin, a goben zan juya.”

Ta furta da murmushi tana manna mata kiss a goshi ta juya.
*

11:30AM

A kan idonta Soupy ta fice a wata mota da wani Dattijo. A kan idonta Reza ma ta wuce a Motar Hamoud.

Tana da tabbatacin yanzu gidan Mama Ashana ce kawai a ciki. Dan haka ta fito dagaggawa bayan ta ɗauko wani Key.

A saɗaɗe ta isa ga babbar kofar falon. Tana buɗewa idanuwanta suka sauka kanta, tana zaune TV a kunne tana kallon tashar Saudia.

Murmushi ta mata mai kyau bayan ta yaye Tarhar da ta lulluɓe rabin Fuskarta. Kai tsaye ta zagayeta tana ƙoƙarin dosar ɗakin Rezar. Mama Ashana ta danne dan kekenta cikin gigita tana binta, da ƙarfi ta buga mata keken har sai da ta juyo har yanzu da murmushi kwance saman fuskarta.

“Ya kike haka ne? Ke fa kamar Mamana kike, karki damu ba wani abu zanyi ba, gashin Reza kawai zan duba ina so a mayar mini ita ɗanta matsitsi.

A gigice Mama Ashana  ta ƙara danna kekenta tana yin baya, sai ta yo gaba kuma ta buga mata shi a gwiwa. Ganin haka ya sa Ree fusata ta sa hannu ta kwashe ta da mari.

“Duk ke kika ja komai da kika haifeta ai, da kinyi barinta ai da kema ba ki rayu a haka ba…”

Mama Ashana da marin ya sa kanta langaɓewa gefe ta kasa motsa shi. So take ta ɗago da shi tunda yana motsawa amma ta gaza, a hakan hawayenta suka fara sauka, a kan idanuwanta da take wulkila su da ƙyar Fakriyya ta karasa ɗakin Rezar.

Matajanta ta kwaso, duk wani gashi da ya maƙale sai da ta zakulo shi ta tattara. Ta fito kai tsaye ta doshi ƙofar fita daga falon. Har ta riƙe handle din ƙofar sai kuma ta juyo tana dubanta. Wani abu ya tsirga mata a zuciya tuna duk dalilin wannan matar ya sa ita ma ta rasa uwarta. Dan haka bari ta ɗan gasata ko da na yini guda ne a rana ko wani abu zai mata sauƙi.

Da wannan tunanin ta juyo zuwa gare ta, ta riƙo bayan Wheelchair din ta fara tura ta da ƙarfi.

“Bari na kaiki ki shakata a waje ko hawayen naki za su bushe.”

A haka ta tura ta waje, tana ficewa da ita daga layin ma gaba daya, sanin ba mutane sai tsilli-tsilli ya sata zagayawa da ita ta can baya. Ta aje ta gefen wani ginin masallaci da ake yi wanda ya fi kallo hasken rana. Ta zare mata dan kwalin kanta, ta saki wani murmushi jin yadda ita kanta ranar ke kona fatar jikinta, a haka tayi juyawarta tana mata bye-bye tana nuna mata gashin Reza da ke hannunta.

Ƙokari take ta motsa keken amma ta kasa, abin da ke sashi tafiyar take ta dannawa amma yaƙi motsa mata kamar wanda aka tokare da dutse, kasancewar nauyinta ya dawo bangare guda sakamakon kanta da ya koma gefe ya sata rikitowa gaba ɗaya zuwa kasa ta gefen. Wani karfe da ke jikin keken ya soketa, tana jin yadda zafin ƙasar wurin ke ratsa jikinta, ba ta da ikon da za ta iya ko da jan cikine, ba ta da ikon da za ta iya ko da neman taimako ne. Ba ta da ikon da za ta ɗaga hannunta domin kare ranar da ke samanta. A hakan ta fawwala komai ga maiduka.

Ta shafe mintuna sama da talatin a wannan halin ba ta tunanin ko Tantabara ta wuce ta layin. Tun zafin ƙasar na kona fuskarta ta kasan har sai da ta zama mai sanyi da zufar jikinta. Maƙoshinta ya bushe, idanuwanta sun fara rufewa. A wannan hali ta juyo motsi na fitowa kamar daga kangon masallacin da aka cimma rufe shi.

A hakan da take ta ji ana ƙarasowa gare ta cikin Salallami, sai dai, ba muryar me ambaton Allahn ba ce kawai ta kiɗimata, hatta ƙamshin nan, wannan ƙamshin dai da ta fara shaƙarsa a daren wata Lahadi, wannan ƙamshin dai da ba zai taɓa goge sanin mai irinsa a cikin kwakwalwarta ba har gaba da abada, shi ne ke kusantota yana ƙarasa rushe duk wani ƙarfinta, a hakan ta ida sa sumewa.

“Quraisha!!!” Ya furta da rarraunar murya a bayan ya yi tozali da sumammiyar Fuskarta!!!.
*******

REZA.

11:40AM

“Ka fa ƙi gaya mini inda za mu je, Allah kai ko kai ta abu kamar da gadara-gadara.”

“Allah ko? To ban isa ba ne?”

Ya furta da murmushi yana kanne mata ido.

“Wai menene, sai wani nishaɗi kake yi? Ka ƙi ma gaya mini yadda kuka yi da su Mama da wannan fargabar na kwana, gashi ka kashe wayarka. Ina Twins din? Ka ga ni ka gaya mini idan nesa za mu nasa a kula da Mama, ka ga Soupy ma ta fita da Alhajin Hammad.”

“Oh ni Soupy? Ya furta yana shafa sumarsa,

“Halan park aka tafi kai ta ko kuma gidan Zoo?”

“Haaa, ka sa mata ido fa, lefe za su siyo ita da shi. Kasan gobe ya ce za a ɗaura auren.”

“Ah gaskiya kira wanda zai tsaya da Maman, abu za ki mini fa.”.

Shiru ta yi tana latsa wayarta.

Ta ɗora wayar a kunne tana faɗin

“Hello!”

“Ke Juliet tun jiya nake cike da ke, ki yi ƙoƙarin raba ni da matar nan, jiya ba dan Hamoud ya kira ni na tafi ba ƙoƙari take ta mini fyaɗe.”

“Ah, jiya Kun haɗu da shi ne?”

“Aww! Wai ba ki da labari? Ya akai to?”

“Ya zo mun fita ne yanzu, ban san za mu yi nisa ba, kuma Mama ita kaɗaice a gida, Soupy ma ta fita da Alhajinka, shi ne na ce ka je ka kula da Mamar…”

“Ba na son shashanci fa, ya za ki baro ta ita ɗaya ina su Sumoli din da ke zama gidan, wa zai bata  ruwa idan tana buƙata?”

“Ka yi haƙuri, ba za a ƙara ba.”

“To na yi.”

Da haka suka katse wayar. Ta sauke numfashi a hankali tana hararar Hamoud da ke ta tukinsa.

“Ke yanzu fa idan kika mini kyakyawan kallo lada ne, idan kika mini mummuna zunubi ne, ki bi ni kawai, kin sani ko kaushi ne a ƙafata sai na ɗaga ta za ki shiga Aljannah.”

“Ban gane ba?”

“Za ki gane.”

Ya furta yana ƙara kashe ta da wani murmushin.

Da haka har suka ƙarasa gidansa.

Ta fito tana ƙarewa gidan kallo.

“Ban san me zanyi a gidanka ba ni kam”

“Ke dai muje, ba na cikin masu cin mutane.”

Murmushi ta yi tana mamakin yadda kullum halayyarsa ke canjawa.

A haka suka ƙarasa cikin gidan. Sai dai tun a falon ta yi turus ganin yadda aka ƙawata shi da wasu jajayen flowers. Sai kawai ta juyo tana kallonsa ya wani rungume hannu a kirji yana kallonta.

“Karki ce komai, kin san me za ki yi?”

“A’a.”

Ta furta, mamaki na ƙara kashe ta.

“Kawai ki yi hugging ɗi na na Ten minute sai ki juya ki yi tafiyarki.”

‘Haaaaaaaa’ ta buɗe ba ki kawai tana kallon kalar shegantakarsa.

“Yanzu saboda wannan ne ka taso ni tun daga gida?”

“Do it mana…”

Ya furta yana langaɓe kai.

“A’a fa, a wane dalili?”

“Ba Alhajin Hammad ya baki wasu kuɗi dazu ba?”

“Eh ya ba Ni yana mini wasu addu’o’i da ban gane kansu ba. Ya akai ka sani?”

“To sadakinki ne, yanzu matata ce ke Quraisha!”

Shiru ta yi tana jin yadda zancen ya shege ta da shirun.

“Ka zama mijina na dole…”

“Ƙara faɗa, kalmar daɗi.”

Ya furta yana shafa sumarsa.

“Nufina kun mini auren dole fa.”

“Ita ma maimaita ta da gaske daɗi.”

“Hamoud,  ƙalau kake ko?”

“Ke Maigida za ki ce.”

“Hmmmm!”

Ta furta tana zama daɓas saman ɗaya daga  cikin kujerun.

Shi ma ƙarasowa ya yi ya zauna gabanta saman gwiwowinsa, a hankali ya dora hannayensa yana dafe hannunta da ke saman cinyoyinta.

“Ina sonki sosai Quraisha, sosai da sosai sosai, har bansan ya zan miki misali ba, sai dai ina jin tamkar numfashinki na wucewa da nawa numfashin. Karki barni duk rintsi domin Allah.”

A hankali ta sauke idanuwanta kan nasa, tana ganin yadda fuskarsa ta  nuna zallar gaskiyar  maganganu  da ya furtan sun fito ne tun daga ƙarshen zuciyarsa.

Bari na saka miki ZOBEN ALƘAWARI.

Ya furta, yana riƙo hannayenta.

<< Asabe Reza 28Asabe Reza 30 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×