Bari na saka miki ZOBEN ALƘAWARI
Ya furta, yana riƙo hannayenta.Lumshe idanuwanta ta yi tana jin yadda gefen zuciyarta ke wani irin zafi-zafi daga tsakiya na mata wani irin daɗi-dadi, daga ƙarshe na mata wani irin zuma-zuma. Tunda take, bata taɓa jin irin wannan abin ba. Hannunsa na da wani irin maganaɗisun da ke fuzgar zuciyarta ya cilla ta wani yanayi da har ba ta so jikinsu na gogayya da na juna.
Tana wannan halin take jin yanayinta na canjawa, tana jin damuwarta na dawowa, a haka kafin ta. . .