HAROUN
"Ba ki mutu ba? Quraisha!! Kai! Sa'idu!!! Buɗ.. Buɗen motar."
Abin da yake iya ambata ke nan a bayan ya saka dukkan ƙarfinsa ya ɗaga ta zuwa cikin jikin jikinsa.
A kusa da shi ya zaunarta yana gyara mata kwanciyar samansa. A take kuma Direban shi ma ya shiga yaja motar da gudun bala'i.
Ba sai an umarce shi da inda za shi ba a yadda yaga Maigidansa yana hawaye. Ba ma wannan ba, sama da shekaru goma da ya shafe da ubangidan nasa tun suna sokoto bai taba ganinsa da wata ɗiya mace. . .