Skip to content
Part 32 of 33 in the Series Asabe Reza by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

“Majnun sai ka yi sujjada, ta farfaɗo.”

Isma’il ya furta yana dafa kafadarsa.

Wata irin runguma ya masa yana share hawayensa, kamar ba babba ba.

“Muje na ganta.”

Tare suka koma, gaba ɗaya jikinsa rawa kawai yake yi. Tana kishingide saman gadon. Idanuwanta a bude tana kallon kofar.

Gabaɗaya ya haye saman gadon yana janta cikin jikinsa. Bugun zuciyarta da yaji a saitin ƙirjinsa ya sashi ƙara matse ta. Hawayenta ke sauka a dokin wuyansa. Kissing dinta yake tundaga goshinta ya koma wuyanta, ya koma laɓɓanta. Ya kara rungumeta tamkar za a sake ce masa ta mutu.

“Am so sorry Quraisha, am sorry, ba Ni ba ne, ban sani ba, ance mini kin mutu. Ina ta nemanki, ina babyn, Sihiri aka mana, ba nine na barki ba. Ki ce kin yafe mini kinji, ba Zan yafe ba, zan tarwatsa ko wanene da ya mana wannan abin. Ki yi mini magana.

Kalmomin da ya jero ke nan a bayan ya ɗago da fuskarta cikin tasa. Da kyar ta samu ta juya kanta gefe, ta ƙara juyawa. Hakan da ta yi ya sashi sakinta gaba-daya yana juyowa bangaren da Isma’il yake.

“Kana gani ta ki mini magana ko, kai da ka san komai, ka zo ka ce mata ta mini magana.”

Girgiza kai Isma’il ya yi yana goge tasa kwallar. Yana jin nauyin kalmomin da zai hada gurin gayawa masa matar tasa fa ba ta da lafiya, tana dauke da ciwon shanyewar jiki.

Banko kofar da aka yi a fusace ya sasu waigawa suna dubansa.

Sai haki yake yi tamkar wanda ya yi gudun famfalaki. Bai ko dube su ba. Ya karasa gadonta yana ɗora kansa saman cinyoyinta, ya daga hannunta ya ɗora a kan nasa.

“Wallahi da ban same ki ba Zan taɓa yafewa kaina ba. Meyasa kika fito Mama? Na shafe sama da awa biyu ina nemanki cikin unguwa. Har sai da na ga wani Direba ya ce sun same ki  a rana ne suka kawo ki asibiti. Ki faɗa mini ta yaya kika fito?”

“Fitar ta aka yi fa, ba ta taɓa fita ba. Ai na gaya ma an bude gidan da wani key. Thank God Tunda mun sameta lafiya. Bari na kira wayar Soupy na CE ta taho a hankali.”

Reza ta furta da ta shigo a bayansa.

“Ban gane ba, me ke faruwa ne? Ku su waye?”

Haroun ya furta yana jin kamar ya shaƙe matashin da ya saka kansa a cinyar matarsa.

“Mun gode sosai Alhaji da taimako. Mune danginta, Ni ce ɗiyarta, wancan kuma yayana ne.”

Tun daga Ni ce ɗiyarta ya gama fahimtar komai. Dan haka kawai ji ta yi an jawo ta ana tattaba fuskarsa. Kyakkyawan Dattijon da bai gaza shekaru hamsin ba take kallo yana hawaye. A hankali ya jata jikinsa yana bubbuga bayanta.

“Ko ban tambaya ba ke ce ɗiyata. Ya Salam. Ban san me zance ba. Wannan rayuwa…”

Ita dai kamewa kawai ta yi tana jin wannan zance. A hankali ta juya fuskarta tana kallon uwarta. Hasken da fuskarta ke yi kawai ya tabbatar mata da abin da ke faɗa gaskiya ne. A hakanma ma sai da ta juya kanta gefe ta ƙara juyawa. Ganin haka Hammad ma ya mike gabaɗaya ya isa gabansu. Haroun ya ja su duka cikin jikinsa suna dariya.

Sun shafe mintuna sama da Ashirin suna tattaunawa abubuwa ciki harda ciwon Quraisha.

Kafin Isma’il ya kore su bayan ya mata allurar barci kan abarta ta huta. Ko da suka fitan ma labarin ke nan suke yi. Har zuwa karasowar Soupy ita ma kawai daskarewa ta yi tana kallon Haroun. Har sai da Reza ta mata ihu a kunne…

Ku san maghriba Reza ta ja gefe a bayan ta karbi wayar Soupy.

Ba ta Jin za ta kira wancan Sarkin zuciyar duk da shi ya kamata ya zama na uku ajin wannan daddaɗan zancen. Dan haka ma ta dallawa  number ɗinsa a harara a bayan ta buɗo ta.

Kai tsaye kuma ta tafi kuma neman layin da take so. Bugu biyu ya dauka.

“Disco ya dai?”

“Thank God kin kirani. Na kira wayarki rufe. Har gida na je ba ku nan.”

“Sorry, Mama muka kawo asibiti. To ya?”

“An gama komai fa tun dazun. An samu ta wata tsohon pastor, yanzu haka tana inda kika umarta.”

“Da kyau! Ban san me zan maka ka gane farin cikin da nake ciki ba. Amma dai kawai ka fara haɗa lefe, aurenka da Sumoli kamar anyi ne an gama.”

Ihun da ya kurma mata a kunne ya sata kashe wayar tana murmushi.

A hankali ta sauke kallonta kan Hammad da ya zuba mata ido yana duba. Yafito shi ta yi ya taso suka yi can gefe.

“An gama komai fa, saura naka aikin. Mu kammala a daren nan. Wallahi ba zan iya barci idan ban ji Fakriyya a hannu ba. Ina da tabbacin ita ce ta kai Mama rana. Na ga alamun har daki na aka shiga. Ban dai san menene ta yi ba. Amma koma menene a yau nake so komai ya kare, na gaji da azabtarmu da yarinyar nan ke yi. Tunda Mama na tare da su Soupy ka je kawai, Pls Hammad.”

Idanuwansa ya ɗago da sukai jajir yana dubanta, jijiyoyin kansa har tashi suka yi dan ɓacin rai. Lalle har abin da baya cikin plan dinsu dole ya yiwa Yarinyar nan yau.

Dan haka ya juya kawai ya fice, ko sallama bai musu ba.
******

FAKRIYYA.

Sau biyar tana kiransa, sai ana shida ya daga kiran. Haka kawai da yammacin nan take jinta cikin wani irin feeling, Namiji kawai take bukata kusa da ita, namijin ma ba kowa ba sai Hammad.

“Idan ba so kake na mutu ma dan Allah ka zo yanzu ina gefen titin Nassarawa. Wuri za ka rakani..”

“Dole na zo. Ni ma ji nake idan ban ganki yau din ba mutuwar zanyi.”

Da haka ya hau kan taxi ya karasa inda take.

Tundaga buɗe motar warin taba ya buge shi. Zama ya yi gefenta yana rufe motar. Haka kawai yau yaji so yake ya yi maganin iskancinta. Idanuwansa suka sauka kan wayarta da ke gefe. Dan haka ya yi wani shegen murmushi. A hankali, a kuma karo na farko da yaja ta cikin jikinsa yana kissing din wuyanta. Sai da ya tabbata ta lula ya ja wayar a hankali ya shiga videos. Tas! Ya yi deleting komai da komai. Sauran shi Flash. Ya tabbata kuma yana cikin jakarta. Ganin yadda take abu kamar zata cinye shi ya sashi kwace jikinsa yana gyara zaman rigarta. Yar karamar kwalbar giyar ya jawo ya tura mata. “

Mu sha wannan, ya furta yana kashe ta da ido. “Ni dai aa”

Ta furta tana komawa cikin jikinsa. Share ta ya yi ya bude kwalbar ya daga kamar ya sha, a hankali ya jefa yar ƙaramar ƙwayar ciki. Ɗagowa ya yi daga rungumar da ta masa ya mika mata kwalbar ita ma. Cikin halin shauki ta daga kwalbar sosai ta kwankwaɗe tana dariya. A haka ya biye mata yana ci gaba da haukata ta, har zuwa lokacin da nannauyan barcin ya kwashe ta.

Tsaidata ya ce jikin kujerar sosai ya daura mata belt. Da sauri ya jawo jakarta ya hau zazzagewa. A take dan karamin Flash ɗin ya fado ya dauke shi. Mai da tarkacen jakar da rabinsa Condom ne ciki ya yi. Hannu yasa a Aljihun cikin Suit ɗinsa da wando ya fiddo da wasu ƙananun ledoji na cocain(Hodar Iblis) Da sauri ya tura mata cikin jikar.

Ya dade tsaye yana mata kallo me ciki da tausayi. Yarinya ce ƙarama sa’ar ƙanwarsa, amma an bata rayuwarta da bakar zuciya.

Sanin karma ya canja ra’ayinsa ya sashi ficewa. A bayan ya mata wani rubutu da a yar takarda. Ya aje saman cinyarta.

Go to hell Fakriyya. Kinyi losing. Hammad yayan Reza ya kawo karshen komai kuma. Karki damu. A shekara zan dinga zuwa ganinki sau biyu a PRISON.

Da wannan ya fice daga motar, ya yi tafiya mai ɗan nisa kafin ya dakata, ya fiddo wayarsa, ya saka sabon sim ɗinsa da ya siya saboda ranar nan.

A hankali ya latsa lambobin. Bugu uku aka daga.

“Kamala ne daga nan Nassarawa.”

“Muna jinki kamala.”

“Na san tun safe kuke neman gawar Pastor Joseph da ta yi layar zana ko?”

To tana nan cikin motar wata karuwa, ita ce ta sace shi domin ta yi kudi da romon kansa. A yanzu haka tana kan titin Nassarawa. Cikin mota kirar Mercedes me dauke da bakin fanti. Za ku iya zuwa ku dauki dan uwanku ta kwatancen da zan turo muku yanzu. Ku kuma taho da yan sanda.

“Heeehyh Chineke! Jesus! Joseph?”
Ihun da aka fasa ke nan cikin wayar. Ya yi sauri ya kashe wayar yana murmushi a karo na farko ya zama criminal saboda uwarsa.

Tura musu kwatancen ya yi da gaggawa, ya zare layin wayarsa, ya karairaya, ya watsar shi gurin.

Daga inda yake tsaye, yana iya hango duhun motar Linda da Fakriyyar ke ciki. A haka ya juya yana barin wurin. Yana ji zuciyarsa a karo na uku ya yi wani abin kirkin tun haihuwarsa!!!

FAKRIYYA.

Cikin halin barci take jin hayaniya tamkar a cikin kwakwalwar kanta. A hankali ta fara ɗagowa, kanta na mata nauyi da wani irin zababben ciwon.

Da wata irin razana ta kwada ihu. Ganin wani bakin basamuden mutum me zubin doya ya zuro kansa yana dubanta. Da karfi ya sauke mata wata mahangurba a gefen baki, kafin ta dawo daga hayyacinta ya bude motar ya cika hannunsa da ita, ya fiddo ta waje tamkar yar tsana.

Sosai ta ji wani dumi-dumi na bin cinyoyinta, wanda ya tabbatar mata ba cikin kabari take ba, walakiri na ɗibgarta. A dan karatun ta ba ta taba jin mamaci na fitsari ba. Tabbas! Rayuwa ce ta zahiri take yi gaban wadannan bakaken mutanen.

“Karka kara dukanta!”

Muryar da ta ratsa kunnenta kenan a bayan ta farfado daga nauyin shin da ta sha.

Yan sandan take kallo har su uku sun kewaye ta, akwai tarin bayyanannen rashin mutunci a kodaddiyar fuskarsu.

“Madam, muna son ganin bayan motarki.”

“Sa…sir.sss…menenn?”

Ta furta, harshenta na sarƙewa.

Wani kallo da babban ya mata, ya sa ta juya a hankali tana ratsawa ta tsakiyar matan masu zubin tukwanen biki, ta isa ga bayan motar, a hankali ta fara kokarin budewa, dan ita dai a saninta, banda katon na ruwa, babu komai cikinsa.

Da budewarta da yin bayanta, da fasa kururuwarta ita da ilahirin mutanen gurin duk bai fi dakikai ba. Haka ta buga wani tsalle ta koma bayan dan sandan jikinta na wata irin karkarwa. Tunda Bitil ta kawo ta duniya. Yau ne ta taba ganin gawa, mummuna, irin wannan.

Hannuwanta da ta ji an riko ana shirin daure ta ya sata dawowa cikin rabin tunaninta tana kallon dan sandan.

“Sirr me na yi?”

“Ubanki kika yi, wannan gawar a ina kika sato ta?”

Dan sandan ya bata amsa da sigar renin hankali.

Kanta farka wata tutturnan mata ta ƙaraso gare ta da wani irin ƙarfi ta cika hannunta da wuyan Fakriyya, da alama ita ce matar pastor.

“Ban sata, wallahi ban san shi ba!_

Ta furta cikin rudani tana ƙoƙarin raba wuyanta da hannun matar.

Da kyar yan sanda suka zare matar daga jikinta, a bayan wani ya buga mata kulki.

“Za mu yarda da hakan, idan kika kawo shaidu, ko kuma ba mu ga wani abin lefin ba, cikin motar taki.”

Dan sandan ya kara furtawa da sigar reni hankali.

Da sauri ta juya sanin a hannu daya aka ɗaura mata ankwan ta karasa cikin motar ta ta, jakarta ta jawo, yar ƙaramar takardar ta faɗi. Dukawa ta yi ta dauka tunaninta na kara kwancewa, tana tuna kamar da Hammad suke zaune a mota.

Da karanta wasikar da gushewar tunaninta bai fi ce sakanni ba. Ta yi wani irin shiru. Kamar mai sauraren tafiyar jinin da ke  kewaye kwakwalwarta.

Suna ta magana tabar ganewa, suna ta magana tana ganin bakinsu na motsi. A haka ta fito da jekar ta mika musu.

A cikin idanuwanta da suka bar tuna komai suka juye kayan cikin jakar a kasar. A cikin idanuwanta da suka bar tuna ina take? ledojin Hodar Ibliss din suka zubo. Ta bisu da kallo. Kwakwalwarta na gaza fahimtar me ke faruwa ne.

A haka dan sanda ya mike, ya hada hannayenta duka biyun, ya saka ankwan.

Dukan keyarta da ya yi yana fadin mu tafi, ya sata juyowa tana kallonsa, a hankali, kuma da karfi, ta fashe da dariya.

“Hahaha! Na yi losing. Allah kuwa!
“Hahaha! Na yi losing. Allah kuwa!
“Hahaha! Na yi losing. Allah kuwa!

Da haka aka tura ta cikin motar, da wadannan kalaman, har suka isa kotu. 

<< Asabe Reza 31Asabe Reza 33 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×