HAMOUD
12:00PM
Ta masa kofar gidan. A hankali yake takawa yana jin nauyin abinda ya ma Amaryarsa na kara danne shi.
Surutu ya ke ji sama-sama dan haka ya karasa da sauri ya kwankwasa ƙofar.
Hammad ya bude. Aiko kawai ya cafke hannunsa ya na jansa. Bai dire shi ko'ina ba sai gaban Haroun. A kunnensa ya rada masa.
"Kai ka yi ladab, surukinka ne, Baban Juliet.
Fuskarsa ta fadada da murmushi yana kallonsa. A sannu ya fara kai gaisuwa. Haroun na amsawa cike da farin ciki, sosai ya yaba da zabin yar tasa.
Ya. . .