Ƙarasa sakinta ya yi sanin yana cikin mummunan ɓacin ran da zai iya kai ta lahira.
Hannunta ta kai, ta shafa in da ya shaƙeta, tana jin ciwon abin har cikin dunduniyarta, da ruwan hawayen da ba ta san ya za ta hana zubarsu ba take dubansa.
“Karka min haka Hamoud, ban san ya kake so na hana soyayarka ci gaba da wanzuwa a dukkan hankalina ba. Kai ka min alƙawarin ba za ka taɓa bari na ba, ba za ka taɓa duban wata da zuciyar da ka danƙamin ba. ka tuna, ka tuna kyawawan ranakun da suka shuɗe kana sake tabbatar min da hakan…”
“Ban taɓa saninki ba…”
Ya faɗa yana cike gurbin da ke tsakaninsu.
Tana jin yadda hucin zazzafan numfashinsa ke ratsa duk wani tsiron gashi na fuskarta, akan idonta jijiyoyin goshinsa ke wani irin kumbura da ɓacin ran da ba ta taɓa tunanin yana da shi ba.
“Ban san da wane kalar yare kike so na maimaita miki kalmomin da tun safe ya ci ace kin haddace su a wannan tosasshiyar kwakwalwar taki, shekara biyar na yi ina dakon soyayyar Fakriyya cikin raina, a shekara biyar ɗin nan, ban san wata alaƙa da ta haɗani da Nigeria da za ki ce na yi wata watsattsiyar alaƙa da ke wai SO. Idan ki na yi dan ki rabani da wacce dukkan numfashina na cikin ruhinta ba zan taɓa bari ba! Ba zan taɓa yarda wata jahilar karuwa irin ki ta shiga tsakanin jini da hanta ta ba…”
A hankali yake faɗa, a hankali kuma zantukan ke wucewa can cikin kunnuwanta da wani irin shiru da ke hana gudun jininta.
Idanunta ta lulluɓe ta gagara sanin kalar tunanin da take kan kalmomin da ya watsa mata. Tsoro da firgici take ji na kewaya dukkan wani sassa na jikinta. Ta gama sakankacewa da komai na Hamoud ba cikin hayyacinsa yake yi ba. Akwai wani abu mai girma da ke rayuwarsa wanda ba za ta taɓa nutsuwa ba sai ta gano shi.
“…Da kike cewa kin sanni tun ranar da kika fara shiga gidanmu, to, a barshi ma a ina ƙasar kika je, yanzu ke a toshewar basirarki Ni zan iya buɗe ba ki na furtawa yarinyar da ta ɗora ma mahaifina tsinin bindiga kan abin da yake haƙƙinsa ne so? Ki na tunanin idan da na sani zan iya barinki da numfashin da za ki sake wanzuwa gabana? Ke a cikin mahaukata wane layi kike ne wai? Wacce irin kwaya kike kwankwaɗa da ta mai da ke riƙaƙƙiyar mahaukaciya haka?”
Zuwa yanzu firgicinta ya gama cike dukkan wani gurbi da ke jikinta, maƙogwaronta ya bushe, ruwan hawayen da ke sauka saman laɓɓanta sun ƙafe, kakkarwa take yi tana jin yadda laɓɓanta ke datsewa, magana take sonyi ta kasa, idanunta ta tsaida a kan shi, tana ganin girman kiyayyar da ke barazanar tsinke numfashinta, tana ganin yadda gaskiyar zantukan da ya faɗa ke fitowa ɓaro-ɓaro saman fuskarsa.
A cikin baƙin kwayar idanunsa ta hangi tsayuwarta.
Da gaggawa ta waiga tana dubanta, akan ƙafafunta da ke rawa ta ƙarasa gareta.
“Me kika masa?”
Tana ganin yadda murmushi ya fito saman laɓɓanta.
Kewaye ta ta yi zuwa gare shi, akan idonta ta shige jikin da take matuƙar ƙauna a dukkan rayuwarta.
“Ruhi…Wannan me take anan?”
“…Tsoronta nake ji, ka ce ta tafi, tun ɗazu nake jin maganganun da ke hanani barci…”
Ta faɗi tana cusa kanta tsakiyar kirjinsa, idanuwanta na kafe kan Reza da wani irin kallo mai tarin ma’anoni.
“Kinji abin da ta ce ai?”
“Ki koma inda kika fito ta hanyar da kika shigo kafin zuciya ta kwasheni na fara ɓarin makauniya da ke anan gurin!”
“Ruhi…”
“…Ba na so kana ɗaga murya kan abin da bai kai ya tsaya a fuskar ka ba. Tun rana na faɗa maka tana ɗauke da ciwon haukan da ke motsa mata lokaci zuwa lokaci, so don’t worry about her madness.
“Oh, yeah…”
“I saw her madness through her actions.”
Akan ƙafafunta da suka gagara ɗaukar nauyinta ta yi zaman dirshen, ruhinta da gangar jikinta sunƙi gasgata abin da take ji take gani, wai ita Fakriyya ke gogawa ciwon hauka? Abu ne mai girman da ba za ta taɓa yafewa ba.
“Ba zama na ce ki yi anan ba, ban san adadin sabulu da turaren da zan ƙonar wurin canja najasar da kika cika ɗakin da ita ba, na tsani ganinki, na tsani warinki da ɗakin ke yi yana haddasa min tashin zuciya, ki ɓace min da gani na ce!”
A kan duga-duganta ta miƙe tana dosar tagar da ta shigo, ba za ta iya jure ƙara sakanni biyu tana ganin fuskarsu da ke cikin ta juna ba, hakan zai iya ƙarasa zuciyarta da jinin cikinta ya daɗe a daskare. Da gaggawa take tafiya cikin takunta ganin tagar na ƙara mata nisa.
“Ko da wasa, ka da ki sake gigin shigo min gida, wallahi kinji na rantse da hannuna zan raba kanki da gangar jiki. Banga dalilin ci gaba da rayuwarki a halin yanzu ma.”
Ba ta iya furta komai ba, amma tana jin yadda wani nauyi ke sake danne ƙirjinta, tana jin yadda kalamansa ke tsittsinka mata zuciya, suna zarcewa can cikin kwakwalwarta inda ba za su taɓa gogewa ba. A haka ta ƙarasa dira dandaryar garden ɗin.
Da lalube ta ƙarasa in da Sumoli ke jiranta, tana ta kai-komo cikin tashin hankalin rashin ganin uwargijiyar ta ta a kan lokaci.
Da kallo guda ta hangi rashin nutsuwar da ke tattare da ita, dan haka ta yi saurin tallafota zuwa cikin motar.
“Karki kai ni gida…”
“…Kai ni inda muke zama da Hamoud, ina son jin iskar gurin…”
Kalmomin suka fito a kakkarye zuwa kunnen Sumoli.
“Maa dare ne fa…”
“Ki yi shiru Sumoli, ba na son abin da zai takura zuciyata, dan Allah.”
“Dan Allah?”
Sumoli take kwatantawa a ƙasan zuciyarta dake jinjina girman kalmar, tun tashinta da Reza yau ne rana ta farko da ta ji magiyar ta.
‘Me ya canzata haka?’
Ta tambayi kanta, a hankali kuma ta ɗaga kafaɗarta ta hagu, tana miƙewa da gudun kata’i zuwa inda aka umarceta.
A daidai in da ya saba zama ta ɗosana na ta ɗuwawun, shiru ta yi tana jin yadda sanyin kogin ke ratsa duk wata hudar gashi ta jikinta cikin talatainin daren da sanyin asuba ke ƙara busowa.
‘yan ƙananun duwatsun masu sheƙi ta ɗebo tana jujjuyasu, na sane, shi ya tara su dan kawai idan sun zo jikin kogin ya dinga jefawa suna ba shi sautin da yake so. Hancinta ta kai su, ga mamakinta har yanzu ƙamshin Hamoudi bai bar jikinsu ba.
A cikin kwakwalwarta take ganin ranar, ranar da ta canja duk wani taku na rayuwarta.
Shekara biyu kwarara suka kwashe suna shirya yadda za su shiga gidan Alhaji Nawazuddeen Sheerif. Babban Attajiri mai yawan kyautar da ke firgita ‘yan uwansa Attajiri.
Kwangila mai girma suka samu daga hannun ƙaninsa Auwal Sheerif.
Fakriyya ita ce ta kawo shi, ita ta fara ɗora su kan su amince da zancensa, ya yi musu alƙawarin idan komai ya tabbata zai mallaka musu Kamfanin da suka shafe shekaru suna kwakwarsa.
A haka sukai yarjejeniyar, a haka kuma suka fara shirya yadda za su shiga tun daga ranar.
A yau ɗin da za ai tafiyar take jin abun na fita ranta, wani irin duka ƙirjinta ke yi lokaci zuwa lokaci.
Har suka gama saka manyan hijabansu Fuskarta ba ta bar nuna zahirin damuwarta ba.
“Idan kin san tafiyar nan ba ta zauna a ranki ba ki haƙura Reza, za mu kula da komai Ni da Lulu ke kin sani.”
Fakriyya ta faɗi tana kafe ta da ido, fuskarta na nuna damuwar ganinta babu walwala.
“Karki damu…”
“Komai zai zama daidai idan muka ɗau hanya…”
“Good two years fa Ree?
“Kin sani, ko ina faɗuwa dan ciwo ba zan iya barinsu su wuce haka ba.”
Wannan karan da murmushi saman fuskarta ta faɗa.
“Ba na son matsalane, fita ce wacce ba ta buƙatar kowane irin tunanin rayuwa. Nasara nake so mu aje aranmu Reza, ba irin gurin da muka saba shiga ba ne wannan…”
“Hmm! Bari ki gani, na yi gaba…”
Ta faɗa tana cusa bindigogi biyu a tsakanin ƙugunta.
“A cikin muryarki nake gane girman tsoron da ke zuciyarki, so, ke ya kamata ki zauna, wanene Nawazuddeen Sheerif da kike ta jinjina shiga gidansa?”
Ta ƙarasa tana ficewa daga ɗakin, sauran mutum biyar ɗin na rufa mata baya.
9:30pm
A hankali take kwankwasa get ɗin har zuwa lokacin da ta ji takunsa yana buɗewa.
“Heeee, Jesus!”
Ƙaƙƙarfan kurtun sojan ya faɗi yana yin baya ganin mutum cikin baƙin abu tsaye gabansa.
A sannu ta yaye duka hijabin tana bayyana gabansa, idan ka ɗauke pant da bra, babu wani abu na jikinta dake suturce. Kallonsa take, da murmushi kwance saman kyakkyawar fuskarta.
“Ohhhh! Kin sorotani Fakree,”
Sai kuma ya waiwaiga kamar me jin tsoron wani ya ji su.
“Da kinse na zo ai, Alaji yana gari fa.”
Ya faɗa yana tanɗe bakinsa tamkar kurar da ta shekara ba nama.
“Ka sani ba zan iya jiranka ba, ina jin idan ban zo na ganka ba, ba za ka sake jin ina numfashi ba, amma tunda ba ka so bari na juya…”
Ta juya da wani irin taku da ya mantarshi inda yake.
Gaba ɗaya ya jawota yana lasar dokin wuyanta da wani irin gurnani, jikinsa kawai rawa yake yana ƙoƙarin zare belt ɗin wandonsa a idon duniyar.
A hakan ta watsa masa kakkaurar hodar dake hannunta, a hakan kuma ya dinga ƙasa har ya watse a dandaryar gurin. Amfaninsa da ya yi na shekara biyu na binsa inda yake.
Fito ta musu suka fito daga inda suke ɓoye.
Da sassarfa suƙa ƙarasa cikin gidan.
***** *****
Idan ta ce ga yadda kwana biyar ɗin suka wanzu gareta, to ta yi ƙarya. Kawai rayuwa take tana nesanta kanta da shi zuwa adadin shekarun da ya ɗiba. Tana jin yadda naman wuyanta ke narkewa suna fidda duk wani ƙashi da ke ɓoye cikinsa, ruwa kawai idan za ta sha tana jin ɗanɗanonsa na canjawa da gaba ɗaya damuwarta.
‘Ba za ka kasheni ba.’
Take furtawa a ƙasan ranta, tana miƙewa a kan duga-duganta zuwa ma’ajiyar kayanta.
A hankali take birkice kayan tamkar wacce ke dakon kwayaye cikin cikinta.
So take ta samu abin da zai suturta ta, so take ta je masa yadda zai gane girmansa a rayuwarta yaji ƙanta, za ta canja dominsa, za ta bar koma menene da zai hanata samunsa. Ya yarda anyi zuciyarsa ne kawai dominta, domin ta hana ta dukkan wani mummun aiki da ke kewaye da ita.
Da kyar ta lalubo Abayar da ba ta san adadin ranakun wanzuwarta cikin kayan ba, ita kawai burinta ta saka abin da zai yarda da dukkan kalamanta.
A haka ta zirata ta fita, a hakan kuma duk wata halitta da ke tsaye gurin ta girgiza da canjawar Ashana.
Abu ne da babu mahaluƙin da ya taɓa aikatawa tun samuwar gidan, shimi da wando, mini skirt da t-shirt shi ne shigar gidan, doka ce me ƙarfi da karyata daidai yake da ka yi tsalle ka faɗa rijiya gaɓa dubu kana nutso dan ma kar aganka, ko dadduma ba a yadda ka aje ba, idan ka matsu da ibadar me ya kawo ka aikata Zina? Idan ka matsu da ibadar ka yi ta a waje, ba gidan da najasarsa ta yi girman da ko kare ba ya iya zama cikinsa. Wannan ce babbar farillar da ake karantawa duk wani da zai shigo.
Haka suka tsareta da idanuwunsu, zuciyoyinsu na kokawa, laɓɓansu na motsawa sun gagara furta abin da suke so. A hakan ta ɓacewa ganinsu, tana barin zuciyoyinsu ɗauke da tarin tambayoyi.
“I think she’s in love…”
“Takunta bai nuna H.I.V da muke zato ba.”
“Linda!!”
Ta kirata a kausashe tana buɗa manyan idanuwanta saman kewayayyar fuskarta.
“Yaushe kika yi ilimin gane H.I.V a takun ɗan Adam?”
“Maa…”
“Stop this nonsense!…”
“H.I.V nake so ki cemin tana da shi, watsttsiyar mutuwarta nake son gani cikin idanuwana, for god sake kina kira min wani SO? Ciwo ne shi?”
“Maa…”
“I swear i saw her late in the night crying, she was crying out loud, calling a name like Haroun?
Believe me, she is deeply in love.”
Kallonta take, idanunta cike da tsantsar firgici, fuskarta na juyewa daga Bitil zuwa wata halittar daban, tana jin yadda gumi ke saukowa tundaga ƙarshen gashinta yana zarcewa can cikin jikinta, kanta take girgizawa, tana takawa a hankali, tana tunkararta, ta warto hannuwanta da ƙarfi zuwa cikin ɗakinta, ta bugo ƙofar da dukkan kwanjinta akan fuskar Soupy da take bin su da kallo cike da tsarguwa.
“Dube ni nan!”
Ta faɗa a kausashe tana Jijjiga kafaɗar Linda.
“Shekaruna nawa yanzu.”
“Tal…Talatin da ɗaya.”
Kalmomin suka fito a kakkarye zuwa cikin kunnuwanta.
“Dan makahon ubanki gaskiya za ki faɗa min…”
“Fourty two (42) Maa.”
Ta faɗa da bayyanen nan tsoro cikin muryarta.
“A haka yarinyar da ba ta san darajata ba za ta zo ta fini ni Bitil? Yarinyar da take ɗaukar duk wani farin ciki da nasarar rayuwata saman kanta, yarinyar da ta karɓe abin da saboda shi na kasa kallon kowa da sunan soyayya, a yau ita kike cewa tana soyayya, har za ta iya barin gidan nan saboda hakan? Ta tafi ta yi aure cikin aminci, abin da ko a hankali na ban kawowa kai na ba? Anan nake so ta dawwama, anan nake so ta mutu tare damu wulaqantacciyar mutuwa, yadda ban bar zina ba, mahaifiyata ba ta bari ba har ta mutu, haka ba zan taɓa barin Quraisha ko wani jininta ya bar ta ba!”
Shiru ta yi tana danne ƙirjinta da ke wata irin suya. Tana jin yadda ɓacin ran ke Jijjiga rayuwarta.
Bata taɓa tsanar wata halitta a duka duniya irin Ashana ba, ita ta ƙarɓi muƙamin da nata ne, haƙƙinta ne a matsayinta na ‘ya ɗaya tilo ga Kankana, ita ya da ce ta ƙarbi dukkan ragamar gidan, amma Ashana ta mata karan tsaye, ta rabata da duka burinta, yarinya ƙarama da aka kawo a kan idonta, abu ne mai girman da ba za ta taɓa bari ba.
Da girman wanda ya halicceta daga gudan jini, zuwa tsoka, zuwa abin da take yanzu ta yi rantsuwa. Ashana ba za ta taɓa jindaɗi ba har cikin kabarinta.
Da girman wanda ya halicceta domin bautarsa ta sake rantsuwa, sai ta mata abin da za ta ji zafi da raɗaɗin da take ji a duk ɗora ido da za ta yi kanta, sai ta fahimtar ta yadda ba ta ƙaunar kwanciyar hankalinta ko da na motsawar tsinken agogo kan babban ɗigonsa ne. Sai ta ɗaiɗaita rayuwarta ta ɓatar da tarihinta tamkar ɓacewar Allura tsakiyar teku.
“Yanzu aka fara!”
Ta faɗa tana watsar da kayan da ke jere saman madubinta, tana ganin yadda suke watsewa a dandaryar ƙasan.
Awowin da ta shafe tsaye gurin take jinjinawa ƙasan ranta, har yanzu idanuwanta na kafe ga kofar, kunnuwanta a buɗe tana son jin sautin fitowarsa. Gajiyar da ke tare da ita take jin na ɓacewa da wani irin tsoro da ke mamaye dukkan ruhinta.
Tun gabanin maghriba take tsaye gun har zuwa yanzu da agogonta ya buga ƙarfe 11:00pm na dare ba ta ga alamun akwai muhaluƙi cikin shagon ba.
‘To ina ya shiga?’
Ta faɗa, tana jin tsoron amsar tambayarta, tana hango girman abin da zai faru gareta idan ya zamana hasashenta gaskiya ne.
“Har an shekara biyar ɗin?”
Kalmomin suka ruga cikin kunnuwanta, suna zarcewa can cikin zuciyarta da take taushi da wani irin sanyi. Muryarsa kaɗai ta dakatar da duk wata laka ta jikinta, jikinta ya yi sanyi a haka take juyowa gare shi, cikin duhun daren take ganin kyallin da idanuwansa ke yi da wani irin kyawu.
“Me ya sa baki tafi ba ganin ba na nan?”
Ya faɗa yana nesanta tsakaninsu.
Shiru ta yi jin nauyin da bakinta ya yi.
“Akan idona kika zo, saboda ke na yi zamana cikin masallaci tun bayan la’asar, ban taɓa zaton zaki zauna zaman jiran wanda ba ki da muhimmanci a dukkan rayuwarsa irin haka ba. Me ya sa ba za ki gane kora da hali na miki ba? Ba na ƙaunar duk wani abu da zai sani tsayuwa da ke har mutunci na ya zube a idon duniya Quraisha.”
‘Ya san sunana.’
Ta faɗa a ƙasan ranta murmushi na bayyana saman laɓɓanta, da sauri da sauri ta shiga share hawayen da zafafan kalaman da ya faɗa mata ya sa su sauka.
“Ina kasan sunana? Ko a gida mutum uku ne suka san ainihin sunana.”
“Ke kika faɗa min, ba kuma wannan ne damuwata ba.”
Girgiza kai take tana ƙin gasgata zancensa, ba ta tuna sanda ya tambayeta sunanta a haɗuwar farko da suka yi ba.
“Koma dai ba ki yarda ba, ina rokonki dan Allah ki barni da rayuwata, wannan rayuwar da nake yi, wallahi tafi tsayuwarki anan muhimmanci gareni. Ki yi haƙuri, na barki lafiya.”
Ya faɗa yana juyawa.
A takunsa na uku ta zube gabansa kan gwiwowinta, kan ƙasar dake cike da duk wasu kalar duwatsu.
“Subhanallahi!” Ya ambata yana komawa baya. A cikin ransa yake jin ciwon abin da take yi, mace ce ita, duk lalacewarta tana da darajar da ba zai iya sa ƙafa ya shure ba.”
“Menene haka kike yi, ki tashi dan Allah, akwai ciwo fa…”
“Ba zan tashi ba, har sai ka faɗa min yadda zan daina sonka, ban san dalilinka na guje min bayan na yi alƙawarin barin komai dominka.”
Zazzafan numfashi ya fesar yana dubanta.
Zuwa yanzu ta fara zame masa ciwon kai, bai ma san a muhallin da zai aje taurin kanta ba.
“Ban san yadda hankalinki ke baki ni zan iya auran karuwa, ina da zafin kishin da matata ma bansan ya za mu yi da fitar ta kasuwa ba, bare ke da kowane jaki da kare sun gama saninki, ta ya ya kike so in nutsu da aurenki ban san adadin mazan da kukai tarayya ba? Bari ki ji, a wannan zamanin mazinaci sai mazinaciya, shiryayye sai shiryayya, kowacce kwarya akwai abokin burminta…”
“Ba ma wannan ba, yanzu ke a tsarin hallitta ta ma kinga ina da abin da zan iya riƙe gabjejiyar mace irinki? Ko kuwa so kike na aureki na ci gaba da cin dukiyarki da aka tara ta hanyar saɓon Allah, kina so ne in ƙarasa guntuwar rayuwar da ta rage min da haram? Akwai kariyar da za ki iya ba ni ranar da dukkan rai yake hannun mai shi? Akwai kariyar da za ki iya ba ni ranar da ‘ya’yana za su tatsiyeni in faɗa musu asalin uwarsu? Ko kuwa ki na da abin kare su lokacin da mutanen duniya za su na zunɗensu, suna aibatasu kan zinar da kika yi? Ba ki san duk abin da ka aikata yana komawa kan ‘ya’yanka ba? A hakan kike so in aure ki Quraisha? Wannan shi ne son…?”
Girgiza kai take yi tana jin ɗacin wanzuwarta mazinaciya a ƙasan zuciyarta, ba za ta iya tuna wani alkhairi da ta taɓa yi a dukkan rayuwarta ba. A cikin idanuwanta take hango lokacin, lokacin da ta caka masa abin da take zaton ba zai barshi da rai ba, a hakan ta tsallake ɗanta cikin tsummansa, a sa’adda ya fi buƙatarta a duniya fiya da kowa da komai, ta taho cikin duniya, domin kawai ta yi rayuwa irin wacce take so.
Girman zunubanta take hange, tsoro take ji, tsoro irin wanda ba ta taɓa sanin akwai irinshi a dukkan rayuwarta. A wannan halin ya ɗora zancensa.
“Yanzu a barshi a gamu mun yi aure.
Ta yaya za ki goge tarihin karuwancinki a zamantakewarmu?”
“Ki amsa min Quraisha!”
Ya faɗa a kausashe, yana duban tsakiyar idanuwanta da ruwan hawaye ya gama dulmiyarsu a wani nisantaccen yanayi.
“Zan bar komai, zan rabu da duk wani abu da na samu ta hanyar haram ko da tufafin jikina ne, zan canja sunana na ƙaura daga wannan duniyar zuwa inda ba a taɓajin wanzuwata ba, ko da cikin jeji ni zan zauna dominka…”
“Really?”
Ya furta da wani murmushi a gefen kuncinsa.
“To ki ɓace daga gabana, duk sa’adda ki kayi tunanin barin dukkan munanan ayyukanki domin Allah ki dawo mu yi aure.”
Da haka ya juya akan takunsa, yana ɓacewa idanuwanta, yana barin zuciyarta cikin tashin hankalin da ba ta san inda za ta aje shi ba.
Fatastic