Tsalle ta kama yi saman katifar tana watsa hannu, sai kuma ta sauko da gudu zuwa falon, ta yi kan matar da ke saman wheelchair ta manna mata kiss, ta ƙarasa ga Soupy da ke ƙoƙarin kunna TV, ta mata kyakkyawar runguma ta baya sai da suka kai ƙasa.
"Kin gani ko Soupy? Na faɗa miki ai Hamoudi ba zai taɓa bari na ba, alƙawari ne ya mini, kalli fa ki ga abin da ya rubuto mini."
Ta faɗa tana nuna mata saƙon.
"Ni ce komai na shi, ya gaza barci domina..."
"Idan ma. . .