Skip to content
Part 10 of 33 in the Series Asabe Reza by Asma'u Abdallah (Fulani Bingel)

Shiru ta yi ganin Bitil tsaye a kansu. Kan Soupy ta farga ta warce jaririyar daga hannunta.

Ta ɗaga ta sama tana kallo, sai kuma ta kwashe da dariya tana sake ɗaga jaririyar sama.

“Ina kuke, ku fito, mun samu REZA a yau. ASABE REZA sunanta, idan na haɗa ta da FAKRIYYA ta, ba ƙananun kuɗi za su kawo mana ba!”
“Kuna ina ne!”

“Ku fito muyi bikin murnan haihuwar REZA.”

Ta furta, da maɗaukakin sauti, tana sauke idanuwanta kan Ashana dake ƙoƙarin miƙewa da dukkan ƙarfinta.

“Ƙaryar duniyanci kike yi Ashana! A gabanki zan ba ta abin da za ta shekara goma tana karuwanci.”

Ta faɗa tana buɗe yar kwalbar da ke hannunta ta dangwalo abin da yatsan.

A daidai lokacin Ashana ta gama miƙewa, jiri ya kwasheta, ya wujijjigata ya watsarta can gefe, ƙashin bayanta ya yi wani irin ƙara, akan idanuwanta da ke ƙoƙarin rufewa zuwa inda bata sani ba, Bitil ta dangwalawa jaririyar baƙin abin a baki.

A haka idanuwanta suka ƙarasa lumshewa.

*****

Idan ta ce ga kalar tunanin da take a cikin ruhinta, to ta yi ƙarya. Gaba ɗaya kanta ya gama ɗaurewa, saƙon take ƙara dubawa tana ƙara mamaki akan mamaki.

Miƙawa ta yi da dukkan ƙarfinta zuwa inda ta aje motarta, a hankali ta shiga, tana mai figarta zuwa gida, zuciyarta cunkushe da tarin tunanin da ba ta san inda za ta saita su  ba.

Tun daga ƙofa take kwalama Soupy kira, fitowa ta yi a hanzarce jin kiran ba na nutsuwa ba ne.

Wayarta ta miƙa mata, bakinta ya gaza furta wata kalma, a haka Soupy ta karɓi wayar tana dubawa.

“Menene, bangane me kike son cewa ba?”

“Oh no! Soupy karki ƙarasa tarwatsa kwakwalwata, ki karanta saƙon, ki faɗa mini yadda ya juye haka.

Ƙara duba saƙon ta yi, sai yanzu idanuwanta suka isa gurin, ta ɗago cike da rashin fahimta tana duban Reza.

“Kin sani, shekaru na sunyi nisan da ba sosai nake gane abubuwa ba, ki faɗa mini mana, babu abin da na fahimta sai saƙon Hamoud da kika nuna min ɗazu da safe, gurin sunan ya goge ya zama HAISAM, Date kuma ya zama 17 July 2014, mu kuma a 17 July 2015 muke yanzu, ya za ai na gane? Wa ya yi editing rubutun…”

“Yessss! You’re smart Soupy! Abin da nake ta son na tuna ke nan, amma kwakwalwata ta yi toshewar da na gaza gane komai, sai da kika ba ni haske.

“Tabbas canja min rubutun aka yi, aka goge, aka ƙara turo wani  da sunan HAISAM, kafin na fita, ko waye kuma yana da alaƙa da Fakriyya, saboda akan idona ta waigo ta na mini gaigayin ɓera, alamun ita ke da nasara…”

“Ki gani fa Soupy, Mari na Hamoud ya yi, saboda na taɓa Ree, Mari fa Soupy…?”

Ta furta tana ɗora hannunta a daidai gun.

“Me ke tsakanina da Fakriyya da take mini wannan cin mutumcin? Ki faɗa mini Soupy! Me na yiwa Fakriyya a rayuwa? Ta aure mini mutumin da nake so da ƙauna a duka duniyata, ta canja masa tunani, ya ma manta da Ni a dukkan tunaninsa, yanzu kuma sai da ta yi silar da ya ɗaga yatsansa a fuskata, ki faɗa mini abin da ke tsakaninmu haka!”

Ta furta da tsawa, tana durƙushewa, tana riƙe ƙafafuwan Soupy, hawayen ke sauka, tana jin duminsu har cikin zuciyarta da ke zugi da wani irin bakin ciki.

Janye ƙafafunta ta yi, ta zauna  a  saman kujera tana dafe kanta, ranta ta ji na ɓaci, ba ta son abin da zai taɓa Asabe ko misƙala zarratin, tana tuna karamcin uwarta, tana tuna abubuwa da yawa da suka faru wanda ita ce silar komai, tana nadamar satar da ta yiwa Alhaji Saleh Tumbi, har suka je ɗaukar fansar da sanadinta mahaifiyarta ta haɗu da uban, tana jin da ba ta aikata hakan ba, da yanzu ba jinin Ashana ba ce gabanta, da yanzu rayuwa ba ta yi majaujawa da su irin haka ba.

Ɗagowa ta yi a hankali tana dubanta, gaba ɗaya ta burkice ta fita hayyacinta. Ta rasa wata irin soyayya ce wannan da Allah ya jarabci ‘Ya da Uwar, bata taɓa ganin kalarta ba, ko a cikin tatsuniyoyin mutanen farko.

Za ta sahalewa kanta komai, ta faɗa mata silar komai ɗin, ba ta so ASABE ta faɗa irin hatsarin da uwarta har yau take cikinsa, so take ta ƙyale Hamoudi da dukkan soyayyarsa, ta sani indai ta ji labarin uwarta, za ta iya barin Hamoud ɗin, hakan ma shi ne kwanciyar hankalinta, idan ya so ta ɗau dukkan matakin da za ta iya ɗauka kan Fakriyya, amma kam ta cire Hamoudi daga rayuwarta, shi ne fatanta ita, abu ne mai girma a tsakaninsu da ba ta iya hango yiwuwarsa, FAKRIYYA, ta riga ta ɓata komai, tunda har ta aure shi.

Buɗe baki ta yi za ta mata magana ta ji motsinta.

Ido ta zuba mata, tana ganin yadda ta danne abin da zai sa  keken ya motsa, tana ƙarasowa gabanta.

A cikin idanuwanta take gane ba ta so ta aikata abin da take son yi ɗin.

Abubuwan masu nauyi suka ƙara dunƙule mata a kirji, tana hango zafin da mutum zai ji a lokacin da ya shafe shekaru sama da  Ashirin a zaune saman wheelchair ba tare da iya motsa ko da yatsar sa ba, tana jin zafin yadda za ta ƙara ɓatawa uwarɗakin nata QURAISHA a karo na barkatai, girgiza mata kai ta yi, hawayen da bata san yadda za ta hana ambaliyar zubarsu ba na ƙara jiƙe gaban rigarta.

“Ki yi haƙuri, na sani ban cancanci riƙe Amana ba, babu wani abu da kika faɗa mini da na cika shi, sai wani ma da nake ƙoƙarin furtawa. Ki barni in faɗa mata domin Allah Quraisha, ki barni in gaya mata abin da za ta ɗau darasin da ba za ta kara kula namiji ba a rayuwarta da ke gaba. Wannan ne kawai mafitar da za ta fidda Hamoudi daga dukkan rayuwarta.”

“Daga zuciyarta take son fiddo kalmomin ta watsosu ga Soupy amma ta gaza, hannunta take son ɗagawa da yatsarta da ya fara motsawa, amma yaƙi daguwar, Allah take godewa, tana ƙara gode masa da ya jarabce ta da wannnan rayuwa, so take ta faɗa mata karta fadawa Asabe komai, za ta ƙara ɓata komai ne, kuma babu abin da zai gyaru, sai ma sabbin tashin hankula da za su ƙara burtso musu, abu ɗaya ta sani kuma take jin tsoransa, ASABE, tunda ta furta tana son Hamoudi, babu wani abu da zai canja wannan soyayyar, komai girmansa.

A hankali hawayen da bata san yadda za ta iya goge su ba suka sauko mata, a haka ta danne madannin, tana juyawa, tana bar musu wurin, ba za ta iya jure tashin hankalin da ɗiyar ta ta za ta shiga ba.

Kallo ASABE ta yi da har yanzu take durƙushe, tana kallon uwarta da ta juya, ita ma ɗin kallo Soupyn ta yi, fuskarta cike da tarin mamakin kalaman da ta furta.

“Menene ba ta so a gaya mini?”

“Kin sha tambayata musababbin ciwon mahaifiyarki ina ce miki daga Allah ne.

Kin sha tambayata ko na san mahaifinki tunda an faɗa miki da aure aka haife ki, ina ce miki ya mutu…”

“…Tabbas dukkan lamura daga Allah ne, sai dai ciwon mahaifiyarki akwai sabab, Bitil mahaifiyar Fakriyya ita ce silar komai!…”

Tiryan-tiryan ta fara mata labarin, tun daga Auren da aka ma uwarta ta gudu, har zuwa ranar da aka haifeta.

tana duƙe, ta dawo zaune, daga zaunan ta miƙe, daga miƙen ta ƙarasa ga bango tana doka goshinta, zuciyarta ta bushe, tamkar yadda hawayen fuskarta suka daɗe da bushewa, a haka take jin kalaman Soupyn na ƙara tarwatsa dodon kunnenta, suna zarcewa can cikin kwakwalwarta inda ba za su taɓa gogewa ba.

“A lokacin da na ga ta faɗi, hankalina ya yi mugun tashi, ban bi ta kanki ba, na barki a hannun Bitil, muka ɗauke ta zuwa asibiti.

A tashin farko likitan ya faɗa mini abin da ya katse dukkan tunani na Reza.

Quraisha  ta samu Paralysis, cutar Shanyewar jiki, za ta iya mutuwa, za ta iya warkewa, za kuma ta iya dawwama da ita har ƙarshen rayuwarta.
A haka muka dawo bayan kwanaki.

Na sha wahala kan neman mahaifinki, amma ban ganshi ba, banga wanda ya san ko garinsu ba, tun fitar nan da ya yi a lokacin da ake naƙudarki, har rana irin ta yau, ba mu ƙara jin ɗoriyarsa ba.

Haka na haƙura da nemansa, na ci gaba da kula da ku da dukkan ƙarfina, duk  da Bitil na yawan shiga hurumina, kin sani ba sai na tuna miki ba, Bitil ta nuna miki soyayyar da ko Fakriyya ba ta samu rabinta, ina tuna ranar da aka kawo mana gawarta, saboda kawai na nuna halin ko in kula, kika min rashin kunya, kika barma shiga harkata.

To Bitil ba komai ba ce a rayuwarki  Reza, ta zauna da ke ne danta amfana da ke, ta nuna miki soyayya ne danta tarwatsa zuciyar uwarki, ta so rayuwa da ke ne dan ki dawwama a karuwanci, sai kuma Allah ya fita, ya ɗauki ranta a lokacin da take ganiyarta, ta yi mutuwar wulaqanci irin wacce ba na fatarta ga dukkan halitta.

Ki yi haƙuri, na sani ban riƙe amana ba, sai dai ina roƙarki, da ki manta komai, ki manta Hamoud ya taɓa wanzuwa a rayuwar…”

Ta katse ganin Reza ta zube a gurin, jini na fita ta goshinta, bata kula ba, ba ta kula tana ta ƙuma kanta a garu ba.

Da gaggawa ta ƙarasa, tana ɗora kanta a cinyarta, idanuwanta take kallo, so take ta yi kuka, ta sani shi ne kaɗai sauƙƙinta.

“Ki fidda su, ki barsu su zuba, ki fiddo su tun daga zuciyarki za ki ji nutsuwa, za mu ɗau fansa, ba za mu bari ba, ba za mu taɓa kyalewa ba, ni  da kaina zan tayaki ki ɗau duk irin hukincin da kike so kan Jinin Bitil, ko wane iri ne kuwa! Ki yi kukan, dan Allah.”

Hawayen suka zubo, ta miƙe kanta na wani irin nauyi, jiri na ɗibarta, jinin na tahowa tun daga goshinta har ƙasan wuyanta, hannu tasa ta dafe gun, abubuwan da ta kwashe shekaru tana ma mahaifiyarta ke dawo mata.

Ta sha mata tsawa dan kawai ta ƙura mata ido tana kallonta da hawaye, musamman idan ta shirya za ta fita karuwancinta, ashe wannan shi ne dalili.

Ta sha hanata maganinta, ta kwan biyu bata ma kula ta ba, domin kawai ta mirgino kekenta ta ɓarar mata da abu, ashe uwarta mai girma ce a gare ta, girman da ta sadaukar da dukkan rayuwarta domin ita ta ta rayuwar ta yi kyawu.

Ba za ta yafe ba, ba za ta taɓa bari ba.

Yau da ace Bitil na raye, babu abin da zai hana ta yi gunduwa-gunduwa da sassan jikinta.

Amma da Allah ta yi rantsuwa, Fakriyya sai ta biya kowane ɗigar hawaye na mahaifiyarta da ta zubar dalilin ta ta uwar.

Alƙawari ne wannan.

Idan ma ba ta son Hamoudi, to yanzu za ta fara, bare ma tana so, sai ta bi ta kowacce irin hanya ta haramta aurensa da Fakriyya, haramcin da ba zai ƙara ɗauruwa ba.

A haka ta miƙe akan duga-duganta tana dosar ɗakinta, da ƙarfi ta buga ƙofar, tana barin zuciyar Soupy cike da tunani, ba shiru take so ba, so take ta ce mata tabar ƙaunar Hamoud, ta tsane shi, ba ita, ba kula wani namiji da sunan aure.

<< Asabe Reza 9Asabe Reza 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
1
Free daily stories remaining!
×