Ya yi saurin kauce mata yana zame jikinsa.
Kara damƙosa tayi ta ce, “Please Just Once Prince.”
“Stop it, i said stop it Khalesa, ba na so ki je ki tafi don Allah inna gama aiki zan nemeki da kaina.”
Murya a shagwabe ta ce, “Promise?”
Girgiza mata kai ya yi kawai yana gyara zamansa.
“Alright ga abincin ka nan bye bye.” Ta fada tana kokarin fita.
Har taje bakin kofar ta dawo, rungumesa tayi tana kissing dinsa sannan ta raɗa masa a kunne, “for me, you’re like a lethal deadly drug. Once taken, you’re addictive, I Love You So Much Darling Prince.”
Ta karasa maganar tana kara kai masa kiss ta fita tana sakin wani irin ƙayataccen murmushi.
“Yes, komai ya kusa tafiya daidai, burina zai cika Soon To Be Mrs Adeel Muhammad Rohaan (Gimbiya)”
Ta fada fuska fal farinciki.
Ci gaba da aikinsa ya yi hankalinsa kwance.
Adnan ne ya shigo dakin yana fadin, “An kammala komai fa kan Baban Zainab har ma an fidda shi India komai da ake bukata ina tunanin an samu.”
“Okay.” Kawai Yareema ya amsa da shi.
Adnan ya kara fadin, “Ina take ne? Ta zo nan kuwa? Amaryar tamu.” Ya karasa maganar cikin sigar tsokana.
Da harara Yareema ya bisa da shi yana, “mahaukaciya dai.” Daga nan ya yi shiru ya ci gaba da abun da ke gabansa.
Dariya Adnan ya yi, ya fice yana, “haka dai ka gani kana so bara ma inje mu gana, in gaida Gimbiya Matar Yareema.”
Bangaren Uwar Soro ya nufa yana shiga kuwa ya tarar da Gaaji zaune ta baje Uwar Soro ta aje mata wasu manyan teddies ban da sambatu ba abun da take masu.
Tana ganinsa ta mike tana rike haɓa, “ka kawo mun Baffana ne? Ya ji sauki dai ko? Ina yake? Ka kaini gunsa in gansa ka ji.”
Adnan ya karasa gareta yana, “Baffanki na asibiti an fara yi masa aiki zai ji sauki In Sha Allah.”
“To akai ni gunsa mana, ni kam akai ni inga Baffana.” Cewar Gaaji da idanunta suka cika da hawaye tana kokarin yin kuka.
Adnan ya durkusa gabanta yana rike mata hannu, “Aa fa kar ki mun kuka, kin manta ke babbar yarinya ce yanzu? Kuma Kin manta alkawarin ku da Yareema? Sai nan da wata bakwai kafin Baffanki ya gama jin sauki shikenan zaki koma rugarku ki je ki zauna da Baffanki.”
Gaaji ta taɓe baki, “Tom ni dai ka gaishe mun da Baffana in ka je, kuma in ba ka labari?”
Adnan ya ce, “Eh.”
Daidai da fitowar Uwar Soro daga cikin daki kenan.
Gaaji ta kalleta ta ce, “kawo kunnenka in fada ma kar taji Sirri ne.”
Dariya Adnan ya yi ya kalli Uwar Soro ya ce, “barka da fitowa Baba.”
“Barkanmu Dai Adnan kana tare da mutuniyar ne?”
Adnan ya ce, “eh wallahi na shigo ba kya kusa.”
Gaaji ta katse su da fadin, ” Ni kajo ka ji in fada ma, in ba haka na fasa.”
Murmushi Adnan ya yi ya ce, “Oh Sorry gani Ranki Ya Dade Gimbiya.”
“Ni ba Soro ce ba ehee sai dai kaine Soro ni dai sunana Gaaji kuma ba gimbiya ba.” Ta fada tana murguda baki.
Dariya ya yi ya ce, “To afwan gani nan.”
Tsalle tayi ta janyo kunnensa ta fara raɗa masa, “Aradun Allah Yareema ɗan ishka ne, tsirara fa yake zama a dakinsa naje na gansa kuma ranar ma na gansa yana faɗa da wata ita ma tsirara, kai dai ba dan ishka bane ba ko?”
Dariya ce ke kokarin subucewa Adnan ya ce, “Ni ai ba ruwana.”
Sake masa kunne ta yi tana, “Yawww to ni kai ma ina sho kai zan aura in Yareema ya sake ni.”
Uwar Soro ta ce, “Kai dai yau ka gamu da gamonka.”
Dariya kawai Adnan ya yi.
Gaaji ta mika masa hannu , “mu ma kulla ƙawance daga yau kai ne babban abokina.”
Mika mata yayi suka kulla Gaaji tana washe baki.
Ya ce, “To Shi kenan dai yanzu bara in tafi ko, ki kula da kanki.”
Gaaji ta ce, “Tom sai ka dawo, ka dawo fa muyi wasa ka ji.”
Murmushi Adnan ya yi, yawa Uwar Soro sallama sannan ya fice yana murmushi.
Bangaren Adeel ya koma.
Yana zuwa ya tarar da shi yana cin abinci.
Zama ya yi kan 2siter ya ce, “Safina tazo gidan nan ko?”
Adeel ya amsa masa da, “Eheen.”
Nan take fuskar Adnan ta canja cikin fushi ya ce, “Na rasa mene ne yake damunka Prince na rasa mene ne damuwarka da ma abun da zaka so ji ajikin waccer yarinyar yar bariki, mace ta dunga kawo kanta gareka kuma kana amince mata, shin wai kana mantawa da matsayinka ne? Ka manta kai wane ne?”
Ko kallonsa Adeel bai ba ya ci gaba da cin abincinsa cikin kwanciyar hankali tamkar bai san da zaman Adnan ba bare batun da yake.
Adnan ya kara fusata ya ce, “Ni dai ba zan fasa fada ma gaskiya ba, duk abun da zaka yi kana tuna kai wane ne da kuma darajar mahaifinka da Masarautar nan in ba so kake ka zubdawa kowa mutunci ba, in ma macen kake da bukata ba ga waccar yarinyar ba ka aura kayi koma miye da ita ba wasu yan iskan titi ba.”
Cikin fushi Prince Adeel ya dago fuska ya ce, “ya isa! Na ce maka hakan ya isa, ni ban aureta don ina sonta ko kasancewa da ita ba, sannan Safina da sauran ma baka da sanin abun da ke gudana a tsakaninmu.”
Ya yi shiru yana ajiyar zuciya kusan second uku kafin ya ce, “ka bar shiga abun da bai shafe ka ba.”
“Ok ok haka zaka ce? Ba za dai ka fasa ba kenan? Ko a addinance kasan…”
Adnan ya yi shiru bai karasa ba can kuma ya ce, “koma miye kayi duk abun da kake so nawa ido ne da fatan Allah ganar da kai.”
Ko kaɗan Adnan baya son abun da zai iya taɓa rayuwar Prince Adeel domin jin hakan yake aransa tamkar shine.
Hakan yasa duk fada basa taɓa iya fushi da juna.
Yana cikin cin abinci yaji wayarsa na kara alamar shigowar sako.
Dubawan da zaiyi ya saki tsaki domin Number ce wacce aka saba turo masa da saƙo a kullum da kalaman soyayya.
Kamar kullum yau ma haka aka rubuto masa,
Duk da cewa baka maida mun da amsa a duk sanda zan turo sako hakan ba zai taɓa sawa na karaya ko inji cewa ba zan iya samun cikar burina ba, Prince Adeel Muhammad Rohaan INA SONKA, INA KAUNARKA, kuma da kai zan rayu har karshen numfashina, kasa a ranka cewa ni kadai ce taka, kuma na dace da kai, muddin ina numfashi cikin duniya baka da wata matar da ta zarce ni, inko ni ban zam matarka ba to ka tabbatar da cewa ba zaka taba yin aure ba, kamar yadda nima ba zan taba yi ba muddin in ba tare da kai ba, na taso da sonka tun kafin in san mene ne so, haka kuma na girma da sonka cike da tsoro da fargaban rasa ka domin nasan cewa zan ci gaba da rayuwa ne kawai muddin kaima kana numfashi a doron kasa, ni kadai ce taka, kuma ni kadai zan amsa sunan Gimbiya Matar Yareema, Ina Kaunarka.”
A kasa sakon aka rubuta
Gimbiya S.
Ajiye wayar ya yi gefe yana cewa, “Adnan ina so mu dan fita kaina juyawa yake.”
“Okay.” Adnan ya fada yana tashi.
Jakadiya na ganin Khalesa ta koma bangaren su tabi bayanta.
Sai da ta basu labarin yadda suka yi da Yareema ita da Hajiya Rabi kafin Jakadiya ta numfasa ta ce, “Yo ke hajiya ai sakarki ta yanke saƙa domin ina tunanin hakar mu na dab da cin ma ruwa, yanzu wannan aikin naki ne, kai tsaye ki nufi bangaren Fulani ki sanar da ita wannan labari cikin siga mai jan hankali za ki dawo ki ba ni labari.”
Hajiya Rabi ta bude baki tana fadin, “Kuma fa har na dau hasken dadina dake kanki na matukar kawo wuta, ba zan bari abun nan yayi sanyi ba, yanzu yanzu ina zuwa.”
Hajiya Rabi ce zaune a parlourn Fulani Babba kanta na kasa take fadin, “Allah ya ja da ran Fulani daman wata magana ce na zo da ita ban sani ba ko nayi laifi ko kuma zaki ga dacewar hakan.”
Fulani ta ce, “Ah Bismillah mana ina sauraren ki In Sha Allah.”
“Umm Daman nace batun Yareema da Khalesa ne, ban sani ba ko kina da masaniyar cewa sun daidaita juna, umm kuma daman kin ga a tsari ma sune manya ita ke bi masa in aka hadasu aure zumunci zaifi kara danko.”
Cike da mamaki Fulani ta ce, “Khalesa da Yareema kuma? Amman ko in hakan zai kasance zan ji dadi gaskiya, kuma shine na tambayesa ko da wacce yake so ya ce mun babu?”
Hajiya Rabi cikin in ina ta ce, “Ranki Ya Dade ai da ke kinsan Yareema da miskilanci ba zai taba furta hakan da bakinsa ba.”
Fulani ta girgiza kai, “kuma hakane kam tabbas akwai bukatar in sanar da Mai Martaba cikin gaggawa na tabbatar da cewa sai yafi kowa jin dadin hakan ba jan lokaci za a yi duk abun da ya dace, wannan albishir ne mai kyau ai.” Ta fada cikin bayyanar da farinciki fal fuskarta.
Daga nan suka ci gaba da taba hirar yadda ya kamata abubuwa su kasance.
Jakadiya na jin motsin alamar fitowar Hajiya Rabi cikin Sauri ta nufi bangaren Fulani Kilishi.
Ta kwashe dukkanin abun da ta jiyo daga dakin Fulani Babba kan ana shirin bawa Yareema Khalesa.
Fulani Kilishi ta ce, “Ah lallai Hajiya Rabi na son shiga gonata, tabbas tana so takai kanta da ɗanta kogin mutuwa na tabbatar da cewa bata san ni wace ce ba har yanzu ganin cewa ina raga masu amman yanzu kam anzo gabar da zan yi fito na fito da kowa ba tare da shakka ba.”
Jakadiya ta ce, “abun takaicin ma Yarinyar nan bata ji fa, bin maza take kamar karya a kalla an zubda mata ciki yafi sau uku.”
Zaro ido Fulani Kilishi tayi ta ce, “kee? Ina masarautar ban sani ba? Garin yaya? Ba ni bayani domin hakan ma wani babban taimako zai mun.”
Magana take ciki ciki kamar zata shake ta ce, “Sirri ne zan fada miki amman mu…
Ta fara leke leke kafin ta karasa, “mu shige can ciki.”